Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 23


Farhatal Qalb 23
Viral

PG:23_

===

Yana shiga idanun sa suka sauka akan na Waheedah dake tsaye tana goge hannun freezer.

“Maaaa ” Ya fada a ahankali yana takawa wajenta

“Naam Zayn. Ka dawo?”

“Eh.. Yau baki je asibiti ba?”

“Sai da daddare insha Allah inada appointments da Nol da Maxicare.”

“Okay Allah ya temaka Maa.”

“Amin Zayn. Abincin ka na kan dinning ”

Har ya juya zai tafi sanyayyar muryar Waheedah ta doki kofofin kunnen sa,

“Ina kwana?”

“Lapia.” Ya amsa ta kasan makoshin sa ya fice.

Sam Waheedah bata jiyo amsa gaisuwar da yayi mata ba. Ta tabe baki tana mamakin da alama shi daya ne me halin shariya agidan.

“Ungo kai wa Zayn cup dinnan na manta.”

“Tohm.” Waheedah ta saka hannu ta karbi cup din da ke kan wani karamun tray ta tafi .

Kalle kallen inda zata hango sa take. Can ta ganshi akan dinning yana bude food flasks.

Ta je ta ajiye masa tray din agaban sa . Ta juya zata tafi ya dakatar da ita.

“Goge shi da handkerchief .”

“A’ina yake?”

Yai banza bai amsa ta ba. Sai ma sake zuba liver sauce da yake akan soyayyiyar doyar gaban sa.

Dudduba wa ta shiga yi tana mai kaude kauden kayayyakin gabanta. Dogon tsaki yaja ya janyo handkerchief din dake kan despenser.

“Afuwan ban gani ba ne.”

Bai kulata ba ya cigaba da yankar doyar yana hadawa da sauce. Gashi zuciyar sa tamkar ta faso kirjin sa ta fado kasa.

Ta dan dakata can ta matsa daga wajen ta koma kitchen.

“Je ki huta Waheedah.”

“Da zan dauraye kwanukan ne.”

“No kakki damu, Ai akwai masu wankewa ”

“Tam. ”

“Ki zauna a parlor idan kuma zaki kwanta to akwai daki idan kin haura stairs din bene daga daman ki ”

“Tohm Maa ”

Tana fita daga kitchen ta zauna akan wani center carpet dake kan wata corner an yi ado da console awajen da wasu vases na decoration .

Tsayawa tayi tana karewa wajen kallo don ba kadan ba ya kawatu.

Ta dora hannunta akan lallausan carpet din tana shafa shi.

Sai ga Ahlam ta shigo cikin sashen bakinta dauke da sallama .

“Wa’alaykm Salam…” Waheedah ta amsata tana murmushi.

“Ahh me sunan yan gayu. Kina hutawa ne?”

“Eh …”

“Allah sarki, Ina Nadra?”

“Wallahi bansani ba. Ko tana sama? Bari na kirawo ta .”

“No basshi zan hau. ..”
Har ta kai matattakalar bene na biyu ta hango Zayn ta cikin wani mudubi da akayi kwalliya da shi .

Fasa hawan tayi ta koma wajen sa da sauri tana dariya.

“Zayn Adams….”

“Na’am Ahlam… Ya kike?”

“Lapia kalau … Shine baka mun magana ba? Ba dan na hangoka ba da shikenan ba zaka mun magana ba… Uhm?” Ta dora hannunta akan nasa tana murzawa.

Ya janye da sauri yana goge hannun nasa da tissue paper.  Murmushi tayi me hade da fari.

“Baka ce komai ba … Zayn.”

“Ahlaam. Nagaji ne. I’m exhausted beyond your expectation… Please.”

“Nayi lefi ne? Nace nayi lefi saboda nazo wajen ka?”

Ya girgiza kai ahankali . Hade da sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Waheedah na jiyo dik abubuwan da suke cewa. Da sauri ta mike zata haye dakin da akace yana hanyar bene.

“Zo nan Waheedah….”

“Wa…Heee.. Dah.…! ” Ya furta kasan maqoshi yadda shi kadai ya jiyo abunda ya fada. Ya na mai satar kallonta ta gefen idanu.

“Ga ni Aunty…..”

“Ahh … Kicemun Yaya dai. Sis Ahlam ko Yaya Ahlam, Kinji yar kanwata ? ”

Waheedah ta daga mata kai alamun toh. Kafin tace,

“Tohm Insha Allah..”

“Yauwa! Good girl… Kalle mu muna kama da shi ko bama yi?”

Waheedah ta daga idanunta a hankali. Hade da gyara zaman gilashin idanunta. Ta sauke kallonta akan Ahlam kafin ta sake juyawa ta kallo Zayn. Da sauri tace,

“Kuna yi…”

“Jayyid.. Kaji ko itama tace muna kama. ?”

Bai ce komai ba. Sai ma janyo tissue da yayi ya goge bakin sa.

“Hubba bubba. Tace muna kama… Say something pls ”

“Muna yi…” Ya fada badan ya so ba.

Waheedah dai na tsaye a akansu. Tana lankwasa yatsun hannuwan ta.

“Shikenan dear sis .. . Mungode, Hubby na ne.” Ahlam ta fada wa Waheedah tana murmushi.

Waheedan ta gyada kai kawai itama tana dan murmushin. Ashe ma miji da matane amman yake shareta? Lalle bashida mutunci. Kuma da alama yana cikin maza marasa darajta matayen su.

“Kije sis ..”

“Tohm.” Daman ta gajin da tsaiwar da tayi akan su. Ta haye ta shige dakin da Maa tace ta shiga. Bandaki ta shige ta watsa ruwa. Sai da tayi da gasken gaske kafin ta gano yadda ake bude famfon.

Ta dauro alwala jin ana kiraye kirayen sallar azahar na daya saura. Sallaya da hijabi gasunan an shimfida da carbi akai. Don haka tayi sallah da adduoi. Ta dan zauna tana zikiri kafin ta miqe ta koma kasa wajen Maa.

Already Maa din ta kammala gashin da take. Har ta zuzzuba komai a food flask . Maaikatan na dauka suna kai wa Ummimi a sashen Haj. Barr Aisha.

“Sannu da aiki Maa.”

“Yauwa sannun mu Waheedah. Ga naki abincin can a cikin plate. Na food flask din kuma na Hadiza ne. Idan zaki tafi seki tafar mata dashi ”

“Tohm Maa. Angode Allah ya saka da alkhairi.”

“Allahumma Aamin Waheedah, Bara nayo wanka na sakko ”

“Tohm sai kin dawo ”

Da sauri ta karasa wajen plate din. Fried rice ce lafiyayyiya da taji hanta sai sauce din nama da gasasshiyar kaza a gefe. Sai wani kwano karami daga kasan da aka dora plate akan sa. Soup din catfish ne daya gaji da haduwa.

Ta wanko hannunta da sauri a sink ta shiga cin abincin bayan tayi basmala. Kunnuwanta har wani motsawa suke saboda tsananin dadin da abincin yayi mata .

Kasa boye farin cikin data samu kanta akai tayi. Hawaye suka shiga reto a cikin kyawawan idanunta. Tunda mahaifiyar ta ta haifo ta duniya bata taba haduwa da cima kawacacciya mai madaukakin dadi da gardin dandano irin wannan ba.

Maa ce ta bude kofar kitchen din ta shiga tana sallama.

“Wa’alaykm Salam…” Waheedah ta amsa tana goge hawayenta

“SubhanAllah! Waheedah…kuka? Kukan me kike yi? Fadamun wani abun akai miki? Eh Waheedah? Menene.?”

Waheedah ta kasa cewa komai saboda farin cikin dake dankare a harshenta ya mata nauyin furtawa.

“Menene . Eh?” Maa ta sake tambaya hankalin ta baki daya ya tashi .

“Ba… Bakomi wallahi.”

“To kukan me kike yi? Ko ni ce? Kinga wayata na manta nasan kuma zaa neme ni kinganta akan microwave na barta. Sai Kuma zan ce miki soup din kifin ma nakine na manta nace iya abincin plate. Dan Allah menene Waheedah?”

Waheedah kulawar Haj Hameedah tasa ta kara kaunarta a ranta. Da sauri ta goge hawayen dake tsiyaya tace

“Allah maa ba komai. Kawai abincin ne yamun dadi. Gashi kala kala. Bantaba ci haka ba. Shine nake hawayen farin ciki. Allah ya saka muku da madaukakin alkhairi ya kara muku arziki mai albarka Amin. ..”

Haj Hameedah ta janyo ta jikinta da sauri ta rungumota . Hawayen itama suka shiga kwarara a nata idanun.

“Ssssh! Kukan ya isa haka nan Waheedah. Nan ai gidan ku ne. Ya zama na ku. Kema din yar gidah ce Waheedah. Allah ya miki albarka ya baki miji nagari inda zaki je ki huta. Yan uwan ki su huta, Na kusa da ke ma su huta. Gidan jin dadi da kwanciyar hankali. Amin, kinji ko?”

“Eh Maaa ”

“Yauwa yi sauri ki cinye abincin. Kinji ko?”

“Tam…”

Daukar wayarta tayi. Ta janyo tissue ta goge nata hawayen sannan ta fice. Waheedah ta sake daurayo hannunta ta zauna ta shiga cin abincin tana korawa da ruwa mai sanyi….

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply