Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 25


Farhatal Qalb 25
Viral

PG:25_

_INA MASOYA MATA YAN GAYU DA KE NEMAN GANGARIYAR KAYAYYAKIN GYARAN FATA TAYI LAUSHI, KYAU DA CIRE TABO HADI DA MAYAR DA FUSKA DA JIKI KALA DAYA TA CIRE KNUCKLES? TO KU MATSO KUSA. DOMIN ZAFAFA BIYAR WANNAN KARON MUN LEKA MUN ZAKULO MUKU MAI KAYAN GYARA FATA DA TURAREN WUTA MASU KAMA GIDA DA KAMSHI. WATO: J-SKINCARE PRODUCTS_

_J-SKINCARE PRODUCTS_

_0813 801 1240_

_TANADA KAYAYYAKI KAMAR HAKA: Black soap, Kiddies Black soap, Sugar body scrub, Body butter, Kojic acid soap
Turmeric soap,Goat milk soap,Honey soap,Carrot soap,Face and body cream, Hair growth oil
Muna yin contract na sabulun cold process ga masu yin biki ko suna. Akwai spices na girki dana shayi. Kai dama sauran kayayyakin masu inganci, kyau da kuma karko acikin farashi mai rahusa.

_Instgram page:J-skincare products_

_Tiktok:jannatskincare_
_whatsapp/Phone number 0813 801 1240_

_KYAU!! INGANCI, DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN: J-SKINCARE PRODUCTS_

_100% tested and trusted_

========

*WASHE-GARI*

*DA* wurwuri ta karasa dukkanin abubuwan da zatayi ta yo wanka . Daki ta shiga ta zura wata doguwar riga da yayar Umma Hadiza ta dinko mata a sallar bara.

Batayi kwalliya ba. Illa dai ta zizara kwalli ta kuma shafa Vaseline (basilin) a labbanta masu taushi.

Ta dakko yar kwalbar turaren ta ta goga a jikinta da kasan hammatar ta bayan ta shafa alumun mai dauke da lemon tsami.

“Sannu Umma! Ya karfin jikin na ki?”

“Da sauki Waheedah…. Ga biredin can. Akwai ruwan zafi a jug dincan da sukari a gefe.”

“Tohm Umma.”

Nan da nan ta hada shayin. Ta gutsiri biredin tana ci tana hadawa da shayin. Cikin haka yayan su Kamal ya shiga dakin.

“Umma barka da safiya! Ya jikin naki? Allah ya kara miki lapia mai dorewa yasa kaffarane. Amin..”

“Aamin Aamin ….Ya naka jikin?”

“Da sauki Alhamdulillah…”

“Masha Allahu. Allah ya baku lapia yasa kankarar zunubai ce. Amin”

“Aamin. Yaya ina kwana? Ya jikin?”

“Alhamdulillah Waheedah.. Kin tashi lapia?”

“Lapia kalau. ”

“Masha Allah…”

Can sai ga Najib ya shigo shima. Hannunsa kan bakin sa yana hamma.

“Ina kwana Umma ya jiki?”

“Da sauki Najib… Ya naka jikin?”

“Da sauki sosai …”

“Masha Allahu… Allah ya kara lapia Amin.”

“Amin…Yaya Kamal ina kwana ya jiki? Ya Waheedah ina kwana?”

“Lapia kalau Najib ..Ya jiki?”

“Alhamdulillah Yaya ..”

“Alhamdulillah Najib. Allah kara afuwa ”

“Amin Amin Yaya Waheedah.”

“Ga kayan karin kumallon naku nan… Waheedah dakko musu.”

“Tohm Umma.”

Waheedah ta janyo kayan karin ta ajiye agaban su. Kowanne ya hada shayin sa da biredi. Suna ci. A haka har suka kammala.

Kamal yace.

“Umma bari na tashi na tafi … Kanin malam shuaibu ne ya rasu. Jana’iza karfe 10. ”

“Allahu Akbar… Rai yayi halin sa. Allah ka jikan musulmai ka kyautata namu zuwan.”

“Amin Amin…”

Haka dai sukaita yan addoin su. Kafin Kamal da Najib su tashi su fita don halartar jana’izar.

Sai da Waheedah ta tabbatar ta kammala duk wasu aiyuka tukun sannan ta dauki kwandon kulolin abincin .

“Umma zan tafi.”

“Tohm Waheedah Allah ya kai ki lapia ya dawo da ke lapia. Tsautsayi da asara Allah ya kiyaye. Sharrin mutum dana aljan baki daya Allah ya tsare. Ki kula dai sosai. Yi nayi bari na bari. Duk kuwa da ba halin ki bane. Amman dai ki tsaya amatsayin ki idan kinje. Ki kauda kai akan komai kina ji ko?”

“Eh Umma…”

“Yauwa, To Allah yayi albarka. Dan Allah ki sake yiwa Hajiar godia sosai. Ki kuma ce ina gaysheta. Dan Allah ”

“Tohm Insha Allah Umma.”

Waheedah ta fice daga gidan. A bakin zaure ta hango mahaifin su malam na lado. Yana jera rake akan wheelbarrow.

“Baba ina kwana…..?”

“Lapia kalau … Ya jikin Hadizan?” Ya tambaye ta muryar rada rada yana magana yana kalle kallen kofar gidan da kwanar layin. Waheedah tayi murmushi kawai. Kasan zuciyar ta mamakin ashe Umman su zaman su take. Babu auren mahaifin su akanta.

“Ina tambayar ki kinyi shiru ”

“Da sauki .. Da sauki jikin.”

“Toh Allah yakara lapia. Ki mata sannu idan kin koma.”

“Tohm..” kawai Waheedah ta amsa masa. Da ta dan tsaya ko zai ce wani abun dangane da Umman ta su

Wani rake ya dakko ya miqa mata acikin leda fara.

“Ungo kya sha…”

Hannu biyu ta saka ta karbi raken.

“Nagode … Allah ya karo kasuwa mai albarka.”

“Amin….” Ya amsata , Ya cigaba da gugar bayan raken da wuka.

Cigaba da tafiya tayi tana mai jujjuya ledar raken da ke hannun ta. A haka har ta karasa unguwar ta new gra shurah.

Kanta tsaye ta shige gidan bayan ta gaysar da masu gadin dake bakin gate din a zazzaune.

Ta murda kofar sashen na Haj Hameedah. Kofar gam take a rufe ba a bude ba kamar jia. Wani madanni mai zanen (bell) kararrawa ta gani a jikin kofar

Nan da nan ta danna shi sau uku. Ba jimawa kuwa a ka bude mata kofar. Ta shiga ciki bakinta dauke da sallama.

Nadra ce a zaune da Yayan su da suke kira da Zayn. Sai Ahlam daga gege tana danna waya, Tunda ta yi sallama ta shiga ya zuba mata idanu. Dakyar ya janye ya kauda kansa gefe bayan yaci magani.

“Ina kwanan ku?” Ta durkusa har kasa ta gayshe su

Suka amsa da fara’a lullube a fuskokin su. Banda Zayn daya sake tamke tasa fuskar .

“Ina Maa?” Ta tambaya ahankali cikin zazzakar muryar ta.

“Maa tana asibiti. Ba daddwa aka kirata surgery’ na gaggawa ta tafi.” Nadra ta fada tana murmushi.

“Allah sarki.. Allah ya temaka, Amin.”

“Amin . Tace idan kinzo ga abincin ki nan kusa da wata food flask . Na food flask din tace na Umman ku ne ”

“Alah sarki. Mungode Àllah ya saka da alkhairi.”

“Aamin Amin Waheedah. Je kici abincin ko?”

“Ai a koshe na ke….Sai dai ko na kai na Umman mu.”

“Hakan ma yayi ..”

Ahlam ta dan daga kai kafin tace,

“Waheedah kin iya dama kunu please?”

“Eh Yaya na iya.”

“Okay akwai wai garin a kitchen. Pls ki hadamun yanzu. ”

“Tohm Yaya….”

Zayn ya bi Ahlam da kallo. A hankali yace,

“Yanzu ke ba zaki dama kunun ba?”

“Ban iya ba ne shysa…” Ta amsa shi kanta tsaye.

Bai sake cewa komai ba. Ya maida kansa kan tv. Hade da kallon agogon da ke daure a wutsiyar hannun sa.

Waheedah na shiga kitchen ta shiga dudduba inda garin yake. Cikin ikon Allah kuwa ta hango shi.

Kasa kunna gas din tayi. Ta sake komawa parlorn.

“Ya Ahlam… Ko zaa kunnamun.”

“Okay Gas cooker din?”

“Eh…”

“Nadra kunna mata please.”

“Tohm…”

“Kinga uhmm Waheedah please ki soyamun hadda wainar flour pls ”

“Tohm….”

Zayn dake jiyo komai ya tabe bakin sa kawai yana girgiza kai.

“Ya akai babes???”

“Bakomai, Ahlam..”

“Ahlam gatsal? Oh please . ”

“Ai sunan ki ne…. Shine sunan ki”

“Koma sunana ne ai be kamata kana fadansa zalla ba. Badan pet names…. Taya zamuyi marital life dinmu ba soyayya ne pls….”

“Sanda ZUKATAN mu suka samu FARIN CIKIN kasancewar mu…”

“Bangane ba… Kana nufin yanzu ba acikin farin ciki muke da junan mu ba?…. Zayn Adams.. Bangane ba…

___
J-SKINCARE PRODUCTS..
0813 801 1240
NATION WIDE DELIVERIES.

Black soap
Kiddies Black soap
Sugar body scrub
Body butter
Kojic acid soap
Turmeric soap
Goat milk soap
Honey soap
Carrot soap
Face and body cream
Hair growth oil
Muna yin contact na sabulun cold process ga masu yin biki ko suna
Instgram page:J-skincare products
Tiktok:jannatskincare
Phone number 0813 801 1240

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰_*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply