Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 27


Farhatal Qalb 27
Viral

PG:27_

=====

Tunda ya dawo daga office yake a gajiye. Kansa har wani sara sara masa yake yi. Abun ka da farar fata tuni har tayi ja. Jijiya katuwa ta futo radau ta wajen goshin sa.

First aid box ya dakko dake kan beside drawer. Ya bude ya zaro panadol pain and fever . Ya ballo biyu ya kurba da ruwa ya sha.

Ya dan jima a bakin gado yana jiran kan ya dan lafa masa. Dan so yake yaje ya dubo mahaifiyar su ganin motar ta a fake ta dawo.

Kan ya na dan lafa masa ya miqe ya shige bandaki ya watso ruwa. Ya sauya kayan zuwa farar riga ta jallabiya. Da dogon wando aciki da singlet. Ya dakko turaruka ya feshe jikin sa da su.

Ya kullo dakin sa bayan ya kammala ya tunkari sashen Haj Hameedah. Bakinsa nata motsawa sakamakon zikirin da yake yi

Da sallama ya shige cikin gidan. Mahaifiyar tasu na zaune akan kujera hannunta da remote control tana kallon tashar labarai ta aljazeera.

Juyawa tayi tana amsa sallamar sa. Yayinda kunnuwan sa suka dauki sautin karatun Waheedah daketa rerawa a daki.

“Maaa!”

“Na’am Zayn ..”

“Ashe kin dawo …? Ya aiki?”

“Alhamdulillah. Munyi mun kammala lapia sai fatan Allah ya bata lapia Amin ”

“Amin Yaa rabbi.”

“Tunda na dawo ai ko sama ban hau ba ”

“Labarai kike kalla… Amma ai ba murya.”

“Eh wallahi. Na rage ne. Saboda karatun Waheedah. Qira’ar dadin sauraro. Kai Alhamdulillahi ala ni’imatul Islam and all it entails.”

“Aamin Amin…. Karatun dadi kam.”

“Wallahi.   Karka so kaji yadda nake ji a raina. Beauty with brains. Yarinyar nan tayi kokari wallahi ”

Shi dai bai sake cewa komai ba. Illa dai ya maida kansa ga tv da suke kallon kurame.

“Baka da lapia ne.”

“Kai na ne yake ciwo.”

“Allah ya kara sauki. Ga abincin ka can akan dinning. Na dawo late so spaghetti ce kawai da soyayyen kifi.”

“Nagode sosai Maa. Allah ya saka miki da alkhairi.”

“Amin…”

Tashi yayi ya tafi dinning din. Kamshin abincin nata dukan hancin sa. Ya ja kujera ya zauna yana mai matso da kayan abincin gaban sa.

Can sai ga Waheedah ta sakko kasan. Caraf suka hada idanuwa da Maa .

Ta zube a kàsa fuskarta dauke da murmushi

“Ashe kin dawo? Sannu da zuwa. Ina wuni. Ya aiki?”

“Alhamdulillah Waheedah. Ai na dan jima da dawowa. Ina zaune anan ina sauraron karatun ki da kira’ar ki mai dadin sauraro.”

Waheedah tayi murmushi kawai . Kafin tace,

“Umman mu na gayshe ki. Tace a miki godia, Allah ya saka miki da alkhairi Amin.”

“Allahumma Aamin……. Kinci abincin rana kuwa?”

“Ai a koshe nake Maa.”

“Ah haba dai . Abincin safe ai baya rike ciki Waheedah. Kije kitchen naki yana nan dana Umman ta ku. Sai ki tafi dashi ”

“Mungode Allah ya biya ki da aljanna.”

“Amin Waheedah. Tare da ku baki daya…. Ina yayyunki maza.?”

“Suna gidah na baro su. Amman daya ne ya girme ni. Muna kiran sa da Yaya Kamal. Dayan kuma kanina ne Najib.”

“Allah sarki.. … Suma suna wani abunne na aiki haka?”

“A’a saboda basuda lapia ”

“Toh pha. Wacce irin rashin lapia ce haka?”

“Sickle cell. Amosanin jini.”

“Wayyo. SubhanAllah! Allah yabasu lapia mai dorewa Amin . Allah sarki hadiza. Waye me sickler agidan na ku.”

“Gaskia ba kowa. Dan de likitoci sunce da Umman mu da baban mu dik AS ne ko me ne shysa suka haifo sikila.”

“SubhanAllah. .. Allah yasa kaffarane Amin. Ke de me lapia ce amman ko?”

“Eh ni AS ce ..”

“Yauwa gwara da kukayo gwaji. Saboda fadaawa halakar haifo yara marasa cikakkiyar lapiar da za’ayi ta magani har karshen rayuwa.”

“Wallahi…” Waheedah ta fada a sanyaye

“Je ki ci abincin Waheedah. Allah ubangiji yana tare da ku. Ya kuma san komai. Da yardar Allah . Zai kawo muku saukin rayuwa kinji?”

“Amin.. Insha Allah .”

“Allah ya basu lapia Amin.”

“Amin”

“Idanun ki short sitedness ne ko long?”

“Short …..”

“Allah yabaki lapia kema kinji ko?”

“Amin Maa.”

“Yauwa yalla. Je kici abincin. Allahumma bareek.”

“Amin Maa.”

Mikewa tayi ta shige cikin kitchen din. Babban plate ne da yaji tuwo da miyar egusi da tasha nama.

Basmala tayi. Ta zauna tana ci. Dadin sa baa magana. Ci take tana kada kai. Tana kuma godia agare su.

Tana karasa ci. Ta dauki plate din ta wanko tas. Ta koma parlor wajen su Maa.

“Akwai abunda za’ayi. ?”

“Kwanukan can zaki wanko kawai Waheedah…. Wanda Yayan ku yaci.”

“Tohm Maa.”

Ta wuce dinning ta dakko kwanukan. Ta kai sink ta wanko su tas ta jera su a plates keeper .

Ta dakko food flask din da akace abincin Umman su ne. Parlorn ta koma ta durkusa tana wa Maa sallama da ke tare da Zayn. Yana zaune a kujerar da ke gefen ta Maa

Kamshin turaren ta yaci ka hancin sa. Sai lumshe idanu yake, Moment dinsu na kwanaki na kara dawo masa .

“Science ki keyi ne ko art?”

“Science..”

“Masha Allah,.. menene future ambition din ki?”

“Inason zama nurse ….”

“Masha Allahu. Allah yabaki iko. Ya bada sa’a Waheedah ..”

“Amin Maa.”

“Masha Allah……!!! To shikenan Waheedah, ki gayshe da Hadizan kinji? Ki kuma yiwa yan uwan na ki sannu ”

“Insha Allah Maa. Zasu ji baki daya ”

“Tohm sai da safe. Allah ya kai mu ”

“Amin…..” Cewar Waheedah. Ta nufi kofa ta bude kofa ta fice.

Tana tafiya akan hanya tana mamakin kirki da mutunci irin na Haj Hameedah. Har zatabi ta layin majalisar su Ibrahim ta fasa.

Ta layin baya ta ketara ta bi. Ta shige gidah bakinta dauke da sallama.

“Ina wuni Marka?”

“Yana gidan uban ki…🤣 Saboda yanzu kuna cin cima mai dadi ta gidan masu hannu da shuni shine kuke hura hanci kuna wami fankama da dagawa. ”

Waheedah tayi shiru. Don sam bataga abun da su kayin ba da har Marka ta dameta taketa fadan maganganun marasa dadi

Ji kake kwas ta sakar mata rankwashi a tsakiyar kanta. Waheedah ta dafe wajen da sauri. Idanunta suka cicciko saboda tsananin zafin rankwashin da Markan ta sakar mata.

Da sauri tace da ita cikin ladabi,

“Kiyi hakuri Marka .”

Marka taja dogon tsaki. Ta fi ce waje ranta na dada sosuwa ganin katuwar kular abincin da ke hannun Waheedah. Babban takaicin ta yadda nasu ne abincin sede su sanmata. Abunnan yana ci mata tuwo a kwarya dole ta nemo mafita….

Waheedah ta girgiza kai kawai ta karasa shiga ciki tana sallama. Ta wuce dakin su da sauri tana yiwa mahaifiyar ta sannu .

Taci tuwon sosai Umma Hadiza. Har dare ya kai musu. Suka karasa cinyewa a abincin dare. Marka ma an zuba mata an kai mata ..

××××

Rayuwa nata garawa cikin aminci da yardar mai sammai da kassai. Lalle Allah qadirun ne ala manyasha’u.

Sannu ahankali Umma Hadiza sai da tayi kwanaki 10 tana jinya chas. Waheedah ce kullum ke zuwa gidan na The Adams family. Sashen Umma Hadiza.

Sunyi matukar sabo da shakuwa ga dukkanin yan gidan baki daya. Idan ku ka tsame Zayn ku ka ajiye a gefe. Shi kadai ne kaf a The Adams Family basa shiri kwata kwata . Har ta dau rashin shirin su a matsayin tsantsar kiyayya da kyama aganin tah .

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰_*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply