Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 28


Farhatal Qalb 28
Viral

_PG:28_

========

Shirye-shirya ake gadan gadan na bikin dangin Ambassador Nasser Family.

Gaba daya dukkanin yan dangin ciki da wajen sa sun fara hallara a garin na kano. Wadan da suke Kaduna dana Abuja da Lagos duk sun zo .

Yayin da sauran dangi na Sudan dana Egypt duk sun fara sauka a kasar ta Nigeria.

=========.

Yana zaune a bakin gadon sa. Hannuwan sa dafe da kansa.

Ya sauke ajiyar zuciya a karo na ba adadi. Kasancewar asabar ce ba aiki miqewa yayi ya fita kansa tsaye zuwa sashen mahaifin su.

Da sallama a bakin sa ya shiga babban parlorn dake sashen mahaifin su.

Professor Adams Nasser yana daga zaune akan wata hadaddiyar kujera kirar royal chairs samfurin turkey.

Har kasa ya durkusa ya rissina ya fara gayshe da mahaifin na su cikin biyayyah da ladabi,

“Abiey barka da safiya….!”

Ipad din hannun sa ya ajiye a gefe. Ya daga kansa yana kallon Zayn dake durkushe. A hankali yace da shi,

“Kana lapia ..?”

“Lapia kalau Abiey ….. Ya murar? Allah ya kara afuwa, Aamin.”

“Na warware Zayn. Ya aiki?”

“Alhamdulillah Abiey. Muna ta hutun weekends .”

“Masha Allah .. Allah ya temaka ”

“Aamin Yaa Rabbi.”

“Akwai wani abunne Zayn ..?”

Kasa cewa komai yayi duk kuwa da abunda ke damun sa a kasan zuciyar sa.

“Babu komai … Abiey ”

“Ka tabbata?” Professor Adams ya sake tambayar sa cikin kulawa da lurar yanayin ‘dan na sa.

“Eh .. Bakomi Abiey ”

“Tou shikenan Zayn. … Allah ya temaka, Amin”

“Amin Abiey. A huta lapia ” Ya sake durkusawa yayi masa sallama ya tafi.

Daga can ya hangota a tsaye suna guje guje da auta Moha . Kayan jikinta sari ne irin na indiya dinnan . Kirar riga da wando. Mayafin kayan ta daura shi akanta .

Mayafin ya zume ya fadi. Yalwataccen gashin kanta baqi na larabawan usuli ya bayyana.

Zayn ya samu kansa da tafiya ahankali. Hannuwan sa acikin aljihun sa biyu na wandon dake jikin sa.

Tafiya yake. Yayinda iska na kadawa ahankali. Yadda suke guje gujen da Moha kwarai matuka ya kawatar da shi. Ya saki tattausan murmushin daya kasa gane na menene.

A haka ya karasa sashen na Haj Hameedah. Moha ya tafi da gudu ya rungume shi . Waheedah tayi saurin jan mayafinta tana gyarawa.

“Akieee. ”

“Na’am baby brother. ”
Ya dauke shi yana jujjuyawa dashi

“Me kake ci ne ..? Ka kara kiba tubarkaAllah…”

“Anything flour Akieeey .. Su waffles , Pancakes. Pies and the rest ”

“Um dan gayu. Maa na ciki?”

“Yep”

“To muje ka rakani.”

Suna shiga ciki Waheedah tabi bayan su. Itama bakin ta dauke da sallama

Haj Hameedah na zaune akan kujera tana rubuta sunaye. Hannunta riqe sa biro da notepad.

“Maa ”

“Naam Zayn.”

“Barka da safiya. ”

“Yauwa … Ka tashi lapia?”

“Alhamdulillah Maa. Ya aiki?”

“Alhamdulillah yau ina off… Sai yamma.”

“Masha Allah! Allah ya temaka Amin.”

“Aamin Zayn .”

“Waheedah zo muyi hide and seek …” Moha ya fada yana tsalle.

“Ka kyelata ta huta baby.”

“Ah Maa.. inaso muyi shiyasa.”

“Waheedah taga ta kanta.”

Waheedan ta nufi wajen sa. Ta kama hannun Moha suka fita waje. Zayn ya bisu da kallo. Maa tayi murmushi kafin tace,

“Ai sun saba sosai. Waheedah ta zama babbar kawar sa. Kwana biyun nan na huta da fitinar sa.” Ta karasa fada hade da daga kai sama tana tunani. Can ta mayar da kanta kan notepad ta cigaba da rubutu.

“Maa list din menene kike yi…?*

“Na bikin nan da zaai. Saboda kar na manta ban inviting wasu ba. ”

Kada kai yayi can ya nisa yace,

“Maaa . Dama inason magana da ke…”

“To ni kuma?”

Ya ‘daga kansa kafin yace,

“Eh ..”

“To Allah yasa muji alkhairi…..”

“Aamin ..”

“Ina sauraron ka ..” Ta ajiye biron da notepad din a gefe.

Ta bashi nutsuwar ta baki daya. Zuciyar ta nata waswasi akan zancen da zai fada… Ta kasa gano koma menene..Don tabbas ta lura baya hayyacin sa.

A hankali kuma a nutse yace da ita,

“Maaaa… Dan Allah a fasa auren nan.”

Shiru tayi tana nazarin sa. Can ta nisa kafin ta bashi amsar maganar sa,

“Kai ma kasan abune mai wahalar yiwuwa. Wanda ba zaa fasa a kan ka ba. You know that, don’t you?”

“Yeah I know right Maa. But ku duba zancena pls . Infact ba wanda na samu akan zancen nan sai ke ”

“Eh saboda ni ce marainiyar wayon ka ko? ”

Dariya ya kyalkyale da ita kafin yace,

“Maa gaba daya kin koma cikakkiyar bahaushiya wallahi ”

Itama murmushin tayi kawai ta gyara zaman gilashin fuskar ta.

“Eh inada gaskia. Meyasa ba ka samu Wanda suke a samana ba? ”

“Allah, Maa naje har sashen Abiey na kasa gaya masa. Dama kune options dina shi da kuma ke. Nasan idan na gaya miki zaki sanar masa. Shi kuma ya gayawa Ummimi. Please ”

“Toh ai Zayn. Zancen da kazo da shi kasan ko ni bazan amince da shi ba. Ballantana naje har wajen Abiey dinku na same shi da maganar. Ka zauna kayi tunani. Dangi na kusa dana nesa sun fara hallara saboda taron bikin ku ba? Kai kadai zaa yiwa auren ko kuwa sauran duk suna raayi ne? Tambayar ka na ke?”

Ya girgiza kansa kawai yana sauke zuciya.

“Maa ban gama fuskantar Ahlam ba.”

“Yo kai ai ko gaba daya lokacin zaa baka ba zaka amince ku fuskanci juna ba. Yarinyar da gaba daya bata gaban ka. Kullum ranka a hade kana muzurai tamkar wani shugabanmu. Kama dauke maganar nan. Maganin kar ayi kada a so ma kaji na gaya maka.”

Ya saka hannu ya shafo keyar sa da saman goshin sa.

“Maa. Yarinyar nan is too lazy wallahi. Gashi ta baci da kashe kudi. Beside idanunta sun bude Maa. I can’t stand her. Ita smooching a wajenta ba wani abu bane….”

Haj Hameedah ta karasa sauraron sa. Can tace,

“Toh idan ka aureta sai ka tankwarata. Kayi kokarin nuna mata dai dai da akasin haka. Ka mata wa’azi da jan kunne akan haramcin taba wanda ba muharrami ba. Ka wayar mata kai. Sannu ahankali zata dena….”

Ya sake sauke zuciya a karo na takwas kafin yace,

“Dole ne auren dangin nan ne Maa? ”

“Dole ne. Kana gani ai ba akan ka farau ba. Junan ku kuke aure, Mutum yanaso ko bayaso haka ze hakura dole yayi. Haka kuma ba kai kadai za’a aurar a wannan karon ba kai da wasu daga cikin yan uwa zaa aurar. Na menene zaka janyowa kan ka ka janyo mun? Salon ace ni na hana ka saboda ban taba aurarwa ba sai akan ka. …”

“Maa ni fa bansan yadda ake kaunar mace ko so ba. Bantaba ba wallahi ”

“To ka fara akan Ahlam… Sai Allah yasa albarka a abun ”

“Maa please….”

“Tashi ka fita Zayn. Zan saba maka idan har ka sake tarata da makamancin zance irin wannan wallahi, Kaji na gaya maka ”

Dai dai sanda Waheedah suka shiga itada Moha. Nadra na biye da su.

“Tashi ka fita Zayn ” ta fada a tsawance

Da sauri ya mike ya fice. Waheedah tabi bayan sa da kallo. Mamakin ganin dazu sunata hira yanzu kuma ga akasin haka .

Ta cigaba da rubuce rubucen da take a notepad. Su kuma suka haye sama.

Dakin Nadra suka shiga. Dakinta mai dauke da kayan gado da furnitures komai purple and white.

Suka zauna akan wasu sofas. Moha yanata tsalle tsalle. Nadra can ta nisa tace,

“Auren su zaai kinsan.!”

“Oh haba?”

“Allah… Shi da Ahlam.”

“Allah sarki Allah yabasu zaman lapia.”

“Amin… Kinsan mu bama auren bare sai iya cikin dangin mu kawai. Ko kanaso ko baka so .”

“Masha Allah… Allah ya kara muku zumunci ”

“Amin. Nima an mun miji . First cousin dina ne .. Dan yayar Abiey dinmu yana Istanbul ”

“Masha Allah. ALLAH sa albarka. Amin”

“Amin .. Ahlam ita yar yayan Abiey dinmu ce.”

“Kuna kama ma ….”

“Tohm shi yayan namu bayaso. Kuma shine auren farko da zaa fara na dan dakin mu. Kuma ba yadda zeyi sede ya hakura. ”

“Tab… Allah sarki .”

“Hmm! Kede bari wallahi. Allah yabamu saa duka kawai ”

“Amin..”

“Yauwa na manta…” Ta bude drawer dinta ta dakko wani material ja daya sha dinkin gown da dankwali harda mayafin sa baki sabo ta ajiye wa Waheedah akan cinyar ta. Ta sake ciro laffaya sabuwa pink me torches black ta ajiye mata ”

“Na menene wannan?”

“Kayan fitar biki ne .. Na Zayn and Ahlam.”

Waheedah ta girgiza kai kawai. Ta kasa ma magana.

“Meye size din takalman ki?”

Waheedah ta sauka daga kan kujerar ta zube akan gwiwoyin ta. Hawaye daya na bin daya na farin ciki.

“Na rasa bakin godia…”

“Kar ma ki soma sis.”

“Nagode Ya Nadra.. Allah ya saka miki da mafificin alkhairn sa. Ya biya miki dukkanin bukatin ki na duniya da lahira ”

“Bar kuka please. ”

“Ahhh Waheedah .” Moha ya rungume ta shima zeyi kukan

“Ga yaron ki nan zeyi kukan shima.dan Allah ki dena wannan kokekoken meye haka? Ai an zama daya ”

Waheedah kuwa sai da ta tabbatar ta karasa godia. Ta sauka kasa wajen Maa nanma ta shiga nuna mata tana godia. Ita dai Maa murmushi kawai take. Ta dakko wani material da ba a dinke yake ba wanda tayiwa dukkanin ma’aikatan da ke karkashinta su. Ta hada da debo kudi yan dari biyar biyar guda 5 ta mika mata wai na dinki.

Nanma Waheedah ta cigaba da godia. Again Nadra ta sake bata takalmi sabo dal. Ranar haka Waheedah ta wuni agidan nan tana farin ciki .

Mai kunshi datazo yi har ita akayiwa. Nadra kuma ta wanke mata kanta ta mata stretching ya sake tsayi.

Sai yamma lis ta koma gidah da tarin kayan. Umma Hadiza ta Yaba sosai ita dasu Kamal.

Har kwanciyar bacci Waheedah bata dena godia ba. Tayi sallar nafila rakaa biyu tanata shararawa su Nadra godia. Da fatan dacewa a rayuwa.

××××

Kamar ko da yaushe a al’adun bukukuwan bikin su. Daurin aure ne yake zuwa farko. Bayan sunje sunyi gwaje gwaje komai nasu kalau zasu iya auren junan su

Ranar alhamis akayi bridal tea party a wani eatery dake kan nassarawa GRA. Iya kawaye mata kawai

Ranar jumu’ah bayan an sakko daga masallaci. Dubban mutane. All the who is who. Suka hallara wajen daurin auren amare da angwaye

Ango Zayn Adams Nasseer da amaryar sa Ahlam Nouh Nasser. Sai amarya da ango na biyu wato: Jannat Adams Nasser da angonta Zaid Nouruh Nasser.

‘Yayan Yaya da kanne. Biyu daga yaran professor Adams. Saia daya a yayan su wato Nouh Nasser. Sai daya ta kani gare su wato Nouruh.

Aka daura auren a babban masallaci. Akan sadaki mafi daraja. Daga nan akayi reception a farfajiyar dakin taro da ke gidan na farfesa Adams. Anci an sha anyi hani’an. An kuma yi addoin zaman lapia ga amare da kuma angwayen su….

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰_*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply