Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 30


Farhatal Qalb 30
Viral

PG:30_

====

*Waheedah* da ta zura waina a baka dakyar ta iya hadiyewa tana kallon Umma Hadiza.

“Kaman muryan Ya Nadra ko…?”

Umma Hadiza ta leka ta taga nan ta hango Nadra a tsaye

“Wallahi itace ”

Tana karasa fada ta fice tsakar gidan. Alokacin Marka tafuto daga daki itama tana karewa Nadra kallo. Hakama inna Sa’adatu dake leqe ta wundo. Marka da saadatu sai bin ta suke da kallo kaman jinjirayen mayu.

“Ina wuninku?…” Ta gayshe su a ladabce.

“Nadra…” Cewar Umma Hadiza da ta fita tsakar gidan tana murmushi

“Naam Waheedah . Ina Waheedah ? Lapia take? Naga shiru shiru Abbas bai dakko ta ba. Sai da na kira shi a waya yace shi dai gashinan a zaune yana jira waheedah bata fito ba. Shine nasa jibril ya kawo ni. Abbas din ya kwatanta mana. Da mukazo layin kuma se na fadi sunan abban su Waheedah sai aka nunamun gidan ”

“Allah sarki Nadra.. An wahalar da ke. Tana daki Waheedan….” Tayi shiru ta kasa karasawa don rashin sanin abunda zata fada. Tunda dai Marka ta hana zuwan.

“Waheedah… Dear sis” Nadra ta fada. Yayinda Umma Hadiza tayi mata nuni da dakin.

“Naam Ya Nadra…Ina wuni?”

“Lapia Lou. Na jiki shiru. Meya faru?”

Waheedah tayi shiru tana lankwasa hannaye. Can ta sauke zuciya kafin tace.

“Kai na ne yake dan saramun…”

“Ayya bakya jin dadi?sannu Allah ya kara sauki.”

“Amin Yaa rabbi…”

“Karasa cin abincin. … Sai muje pharmacy.”

Cikin rawar murya Waheedah tayi hanzarin girgiza kai kafin tace,

“Ai .. Kan ya de na.”

“Toh Allah sa kaffarane.”

“Aamin…”

Ta zaro wayarta da ke ringing. Dauka tayi ta kara a kunnenta.

“Naam Maaa. Eh naje, Ashe batajin dadi ne. Tohm Insha Allahu, Aamin. Amin. Alright.” Ta katse kiran ta mayar Jakarta. Gumi sai sharara yake a fuskarta. Abun ka da aje butter tazo gidan aje kuka. Bata saba da zafi ba.

Waheedah ta janyo muhuci da sauri ta miqa mata.

“Kiyi fiffita..”

Dan murmushi tayi ta karba tana yi.

“Zaki je bikin amma de ko?”

Waheedah ta dan yi yake kafin ta miqe ta fita zuwa tsakar gidah. Umma Hadiza na tsaye . Marka na daga gefen kofar dakinta a tsugunne.

“Umma….”

“Na’am Waheedah…”

“Ya Nadra na tambayar zanje amma taron yau ko?”

Umma Hadiza tayi shiru bata ce komai ba. Marka ta yamitsa fuska tana kallon gefe,

“Ba inda za ki ”

Can sai ga futowar Nadra da wayarta kare a kunnenta

“Nazo daukan Waheedah ne… Gamu nan insha Allah…”

Tana rufe baki Marka tace,

“Kin tsaya sandandan yarinya tun dazu take jiran ki. Ko sai kin nuna mata daya daga cikin baqar halayyar taki? “.

Waheedah ta cika da mamakin da yasa ta kasa ko motsi.

“Ina miki magana kin tsaya chak kina bina da kallo? Wannan yarinya, Wannan yarinya na rasa yadda zanyi da halin ki.”

Nadra ta dan matsa kusa da Marka tana bata hakuri .

“Kiyi hakuri …..”

“Kiyi hakuri Marka .. Amman da kikace ba zani dinba shysa na hakura. ”

Nan da nan Marka ta fashe da kuka wiwi tana dukan kirjinta.

“Ni wahidin zata wulakanta? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Wayyo! Wohoho, Duniya ina zaki damu?? Ke ni kikewa karya? A’ina mukayi haka da ke? Da girman Allah yarinyar nan karya take mun. Wato kin zauna da uwar ki a daka tana kitsa miki munafurci ko?”

Waheedah ta fashe da kuka. Hannun ta daya akan bakinta. Jikinta sai rawa yake… Hakama Umma Hadiza da baki dayan abun da Marka tayi na kunyata su duk ya dubibiyeta tamkar kasa ta tsage ta fada haka take ji.

“Wadannan biyun basuda mutunci…Jikatah.” Marka ta fada tana wa Nadra murmushi. Hakoranta sun gauraye sun zama kalar ja saboda goro.

Nadra ta rasa abun cewa. Tayi gaba kawai bayan tace,

“Toh Umma sai kun fito… Bari na jiraku a mota. Baba sai anjima.” Ta dan rausayar da kai datace wa Marka sai anjima. Ta fice .

Umma Hadiza baki daya tarasa abun cewa. Yau Marka ta tabbatar bata kaunar ta itada yaranta. Da har zata kirkiro sharri ta fada.

Wasu hawaye sirara suka zubo mata. Saboda ba kadan ba ta kunyata su . Agaban Nadra . Yarinyar da take aiki a karkashin inuwar mahaifiyar ta . Yanzu me zata ce musu?

Waheedah ta ja jikinta ta shiga dakin . Leda ta janyo ta zura material da mayafin ta da takalmi.

“Umma wanne zan dakko miki a kayan ki?”

“Dakko kowanne ma Waheedah….”

“Tohmm”

Ruwa ta diba a babbar buta da soso da subulunta a kwando . Ta shiga bandaki ta wanko jikinta ta tsane. Ta shiga daki wajen waheedahn. Da sauri ta zura doguwar rigar da Waheedah ta dakko mata. Wadda sukayi a wata sallah ita da Najan Isubu.

Waheedan ta shafa mata hoda da kwalli a girar ta. Da dan man lebe kadan.

“Bari kawai na saka nawa nima ”

Ta nufi karshen kuryar dakin ta ta zura material din. Ba karamun kyau ya mata ba. Ta yafa mayafi da takalman da Nadra ta bata.

Ta janyo yar kwalbar turaren ta ta shafe lunqu da sako na jikinta dashi .

“Muje Umma.”

“Yauwa …”

A tare suka fito daga dakin. Alokacin Najib ya dawo daga futar da yayi. Umman tayi masa nuni da abincin su shi da Kamal. Sannan suka baro shi aciki suka fita. Bayan Umma ta dan daga murya tana,

“Tohm Marka mun fita. …”

“Allah ya raka taki gona…”

Fita sukayi suka shiga cikin motar. Nadra na owners corner. Yayin da Umma Hadiza ta zauna a kujerar kusa da Nadra. Ita kuma Waheedah ta zauna a gaba.

“Laa har kun shiryo?”

“Eh Nadra mun shirya.” Umma ta fada tana mai gyara zaman mayafinta

“Masha Allahu. Waheedah ke saura kwalliya. Na baro me mana makeup a gidah…”

“Makeup??? ” Waheedah ta maimaita.

“Eh ko bakyaso?”

“Ah haba .. Bantaba yi bane.”

“Ai kuwa zakiyi kyau sosai masha Allah. Tunda ba yi kike ba.”

“Sannun ku da kokarin da ba gajiyawa Nadra. Allah ya saka muku da mafificin alkhairin sa. Amin! Ki kuma yi hakuri ga duk abubuwan da Marka ta fada. Kakar su Waheedah ce. Tsuf…”

“Laa bakomi wallahi Umma ai ku zaa bawa hakuri. Nasan kuma duk da ban jima da sanin Waheedah ba, ba halinta bane. Tunda mai hali baya fasa halin sa. …”

“Wallahi kuwa Nadra. …. ”

“Allah ya tsare gaba ..”

“Aamin…”

A haka suka karasa unguwar su Nadra ta : NEW GRA SHURAH!!

Manyan motoci ne kosassu tunda ga farkon titin layin zuwa karashen sa. Yayinda yan sanda da sauran masu tsaro ke zagaye da cikin unguwar da wajenta. Ko wanne da makari a hannun sa.

Haka cikin gidan ma tun daga gate bouncers aka zuba kowanne da bindigar sa a hannu. Lamarin sai wanda ya gani kawai. Anata hada hada. Duk kuwa da ahakan ma sai yamma lis zaa fara shagalin taron bikin.

Kai tsaye suka shiga sashen Haj Hameedah bayan driver ya kai su dai dai kofar da zai sadaka da gidan . Sashen ya fara taro da mutane yan uwan Haj Hameedah da kawaye kai har ma da wa’ensu na abokan arziki da makota.

“Masha Allah. Sannun ku da zuwa Hadiza. ”

“Yauwa Hajia. . sannun ku Ina wunin ku?”

“Ina wuni Maa. Ina wunin ku?”

Waheedah da Umma Hadiza suka hada baki wajen gaysar da Maa da kuma sauran matan da ke parlorn. Dukkanin su suka amsa a sake. Yayinda Nadra ta ja hannun Waheedah sukayi parlorn sama inda me makeup ke nan.

“Ina wuni…. ?” Waheedah ta gayshe da mai makeup din da ke zaune tana danna wayar hannunta

“Sunanta Beelanah beauty (08034697302) A nan kano take. Ta mugun iya makeup zaki ga yadda zatayi transforming dinmu into beauties.”

“Masha Allah ..” cewar Waheedah tana murmushi.

“Thanks for the hype Nadra. Yar kanwata ya naki sunan?”

“Sunana Waheedah …”

“Masha Allah … Sunan larabawa yan gayu. ..Ni sunana Nabeelah…”

“Masha Allah ..” Waheedah ta amsata tana murmushi

“Bata taba makeup ba fa ”

“Haba dai ..?”

“Wallahi ..” cewar Waheedah tana mai lankwashe hannuwanta

“Masha Allah .. ai Kwa makeup zai miki kyau masha Allah ”

Daria kawai Waheedah tayi. Yayinda Beelanah beauty ta shiga unboxing akwatin kayan kwalliyarta. Ta fara jera duk sauran abubuwan makeup irin su ring light, reflector , Da sauran su…

========

Yana daga kwance akan gadon dakin sa. Kansa na kallon pop. Tunani ne maqil cikin zuciar sa. Kansa har wani sarawa yake saboda tsananin yadda ya zurfafa.

Ya sauke zuciya yana jan kasan labban sa. Baki daya duniyar ta masa duhu. Yayinda sauran yan uwa suke ganin ta da haske.

Ya rasa wacce irin jarabawar rayuwa ce ta samu dangin su. Da dole baka da wani say akan rayuwar auren ka sai dai kaga anayi. Ko kanaso ko baka so. Ba kowa bane ya janyo wannan kaddara irin Ummimi mahaifiyar mahaifin sa, da ke da ikon hanawa ta saka akan komai daya hada da aurarrakin su.

Tashi yayi ya nufi kofa ya saka mata mukulli . Ya koma kan kujera ya zauna. Ipad dinsa ya dakko yana duba wani article ..

====

Nadra ce a tsaye agaban wani dogon mudubi da jikinsa an rubuta Nads mirror selfie…

Sai kallon kanta take. Tana gyara zaman mayafinta data yafa a kafadarta. Yayinda Waheedah ke a zaune ana mata makeup.

Tana gama daukar hotunan wayarta ta fara kara. Dauka tayi ta saka a kunne.

“Hello our wife…. Eh an gama. .. Okay zaraah.Ng tazo? Alright gani nan. ”

Tana gama wayar ta mayar da ita cikin side clutch bag dinta ta dolce and gabbana.

“Soo sorry. Ni zanyi gaba. Amarya na kira na. Sannan kuma me hotan ta ta iso tana kasa zan rakata ta fara mata hotunan daban kafun sauran photographers su zo . Wata zaraah.Ng ce me hoto ta bala’in iyawa. (08093194306)…”

“Okay tohm….” Nabeelah me makeup ta amsa ta.

“Na saka miki kudin. Ai zaki shigo event din ko?”

“Zanzo dai wannan na larabawa da kukeyi”

“Okay derira? Allah ya kai mu ”

“Amin”

“Shikenan, Waheedah zan sa azo a dauke ki .”

“Na dauka acikin gidan nan wajen taron yake ba sai kin wahal da kan ki ba ”

“Eh aciki ne. Amma da tafiya sosai. Saboda ko gate dinsa ma ta bayane. Da ke da ba acikin nan gidan yake ba. Shima waje ne daban . Sai baba ya saka aka shigo da shi. So wallahi da tafiya. Duk taron da muke a motoci ake zuwa ”

“Okay Ya Nadra ”

“Alright ni na tafi ”

Ta fice tayi kasa. Bayan sun gaysa da me hoton, Kai tsaye ta shiga motar ta kirar element maroon color. Zaraah. Ng din na biye da ita a tata motar suka dau hanyar sashen baki inda Ahlam take itada kawayenta.

Bayan sun sauka. Suka shiga ciki da temakon maaikata dake riqe da kayan hotunan me hoto. Nan da nan kuwa suka shiga shiryawa ta fara yi musu

Nadra ta futo ta sake tafiya wajen event din . Kamfanin masu abincin nan na gidah da waje. Wato la comida corner(the food corner: 08091209352) Suma har sun zo suna jera kayayyakin su.

Yayin mutane ma sun fara halarta. Kowanne da wajen zaman sa. A access card din da aka bayar na matsayin invitation card per person.

Ko da me makeup ta gama yin makeup. Sakkowa tayi ta fice abunta. Yayinda su Haj Hameedah ma sukayi gaba. Dama su Umma Hadiza su suka fara gaba.

Waheedah na zaune a dakin Nadra. Can ta gaji da zama ta koma kasa ta zauna.

Ta saka ta ware. Aka turo kofar parlorn . Zayn ne sanye cikin manyan kaya. Wagambari baka data sha aiki fari. Yayinda hula da takalman sa duk farare ne. Agogon dake wutsiyar hannun sa kuma ash ne samfurin yvsl. Da facemask a fuskar sa.

Idanun sa suka sauka akan Waheedah dake tsakure a kasan kujera

“Ke zaa dauka…..?” Ya tambaya da karfi don sam bai gane ta ba. Saboda ta kara kyau akan kyawun da take da shi.

Da sauri ta juya. Ta miqe tana kada kai. Ya fuce tabiye masa a baya. Ta rufo kofar.

Mota ya shiga . Ta bude gaba ta zauna tana jan kasan mayafin ta. Ya dan kifa kansa akan sitiyari na yan wasu mintina kafin ya kunna motar da addua suka bar farfajiyar zuwa wajen taron. Gari har ya fara duhun sai sautin kida ne ke tashi.

Yaja numfashi yana shakar niimataccen kamshin da hancin sa ba zai taba manta kamshin sa ba. Ballanta ran sa da zuciyar sa kai dama gangar jikin sa. Da suka illata da kaunar sinadarin kamshin …. Ashe waheedan sa ce?

Suna zuwa yayi parking. Zata fita kenan ya dan janyo kasan mayafin ta,

“You smell so incredible, I think you should give me your perfume..,…” Ya furta a hankali da alama bai masan ya fada ba.

Ta juya tana tunanin ko waya yake yi ne? Saboda ganin Bluetooth a kunnen sa.

“Zan fita. ..” Ta fada cikin muryar ta mai dadin sauraro .

Da sauri ya daga kan sa ya danna button. Ta murda handle din ta fice. Tana fita ya sauke zuciya. Hannun sa dafe a kirjin sa…

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply