Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 31


Farhatal Qalb 31
Viral

_PG:31_

=======

 

Kwantar da kansa yayi akan sitiyari. Yana hango ta harta bacewa ganin sa. Ta shiga cikin event center din. Bayan ta bawa bouncers access card dinta na shiga ciki.

Ya lumshe idanun sa ya bude yana istigfari. Ba dan dole ba ba zai shiga cikin taron nan ba. Ya sake kallon screen din wayar sa dake haske. Kira ne aketa doka masa saboda amaren zasu tarbesu a waje su, Su yi musu shigar couples and friends special entry.

Ya kifa wayar yana mai sakin siririn tsaki. Nadra ta futo daga cikin marque din tana dube dube. Motar sa ta hango. Ta sauke numfashi tana sauri harta cinma motar. Ta kwankwasa

Kafin ya bude mata sai da ya fara lekawa ya gano ita ce din. Tukun sannan ya cire lock. Ta shiga ta zauna .

“Akieey… Aka Ya Zayn ..”

“Na’am Nadra…”

“Kayi looking down…. Comman take a deep breath .. Deep breath ”

A tare suka daga numfashin na su suka sauke. Sai a sannan yaji dan dama dama. Ta kalle shi sosai tana mai sake nazartar sa.

“Ko bakada lapia ne?”

“Lapia ta kalau ……”

“Kayi hakuri…. Ya zamuyi haka kaddarar mu take ”

“Auren dolen??? ”

Ta gyada kai cikin karshen gaskiyar ta . Zayn yayi murmushi kawai.

“Ke kinason auren ki da Osman??”

“Idan ma banaso ya zanyi? I have no other choice ..”

“Look Nadra…. Auren zumunci idan be dadi ba yana lalata zumunci. Zai wargaza mutuncin da ke tsakan….”

“Bama fatan haka …” Cewar Nadra. Ta kuma cigaba da cewa,

“Kai ake jira. … Ga su can a tsaye zamu shiga da ku.” Tana mai masa nuni da couples train din dake waje sun jeru a layi.

“Na kuma gode da kawo Waheedah da kayi. Na manta ba waya a hannunta wallahi duk mutane sun taho sai ita daya…. ”

“Anytime…”

“Shall we …?” Ta karasa fada tana nuna waje.

“Yep.. It shall be well…”

Futar sukayi. Suka jera har wajen sauran angon da amaren. Ahlam na ganinsa ta nufe shi. Ta rarumo hannun sa ta riqe tana murmushi

“Hubby …..” Ta karasa tana zagaye ruwan cikin sa da hannuwan ta . Kawaye da abokanan su suka fashe da dariya suna ihu. Wasun su har da tafa hannuwan su.

Waheedah na daga gefe a tsaye . Badan Nadra ta matsa mata sai ta fito sun shiga da couples din ba da ba zata fito ba sai an tashi. Ita sam bata saba da irin wannan abubuwan yan gayun ba. Ba kuma ta kaunar ta saba din. Gwara ta tsaya a matsayin ta. Dai dai ruwa , Dai dai tsaki.

Zayn yana juyar da kallon sa. Idanuwan sa suka sauka akan Waheedah da ke rakube a gefe. Tanata lullube jikinta da mayafi.

Wani daga cikin abokanan ya isa gareta. Cikin muryar sa ya mata sallama irinta addinin musulunci. Ta amsa hade da gayshe da shi cikin ladabi .

“Yaya sunan kanwar tawa?….”

“Waheedah ..”

“Wow .. Very sweet name. Waheedah!! Well, Ni sunana Dawud. ”

“Masha Allah ….”

“Yar kanwata ta temaka ta bawa yayanta number wayarta dan Allah kar taje a’ah. Don baki daya ta sace zuciyar Dawud ta tafi da ita…”

Wannan maganar da yayi ce ta sa Waheedah dariya. Kyawawan fararen hakoranta suka bayyana.

Zayn ya kasa hakuri. Shi kansa ya rasa dalilin daya sa gaba daya yaji haushin Dawud da ya je ya nayiwa Waheedah magana . Gashi har ta saki baki tana masa dariya.

Ya zare hannuwan Ahlam a hankali zai tafi ta sake kankame shi

“Ina zaka je? Yanzu zamu shiga fa.”

“Ina zuwa. Sorry.”

Da sauri ya tafi har yana tuntube ya karasa wajen su yana mai sosa keyar sa.

“Ah Maza yane…?” Dawud ya bashi hannu suka tafa.

“Naam. Dawud . Steady ne kawai. ”

“Masha Allahu ango .. Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lapia Amin ”

“Aamin…”

Suka yi shiru dukkanin su. Can Dawud din yayi breaking silence yace,

“Waheedah .. Wannan dan uwa na ne kuma aboki na ne .. Nasan dai kinsan shi ma yau ango ne ko?”

Waheedah ta daga kai ta dubi Zayn kafin ta sauke da sauri

“Eh na san shi ….. Umman mu na aiki a wajen su.” Ta fada kai tsaye batare da wani karya ko sauya zancen ba.

Zayn yaja kasan labban sa. Duk sai yaji kunya ta dubibiye shi. Ya dan daki kafadar Dawud

“Ta sanni na santa… Infact ni na kawo ta wajen bikin yau. Tare mu ka zo ”

Waheedah tayi shiru kanta a kàsa. Tana mamakin ashe yana magana haka?

Dawud ya sake dashare hakora yana gyada kai,

“Komai yazo cikin sauki….. Saboda kai zaka zamo mun tsanin da zan hau katanga na shiga zuciar Waheedah. Ke na ke so ba usulin ki ba. Ba duk wani abu daya shafe ki ba. Da aure nake k….”

Bai karasa ba Zayn ya kware. Dawud ya hau masa sannu. Idanun sa har sun sauya saboda wuya yace.

“Yarinya ce fa Dawud… Me zakayi da wannan? Idan ba reno ba ”

“Reno …?” Waheedah ta maimaita acikin zuciyar ta. Wannan wane irin cin mutunci ne?

“Kai kake ganin ta a yar reno… Ni idanuwana da zuciya ta ganin cikakkiyar mace suke mata wallahi….”

“Lalle fa….” Zayn ya fada yana kauda kansa. Ji yake tamkar ya rufe Dawud da duka haka kawai

Dawud ya sake yin kasa da muryar sa. Ya langwabar da kai hadi da karyar da shi. Cikin muryar tarairaya da lallami yace,

“Dan Allah ki ban number din wayar ki…please! Kinji pretty Waheedah ..?”

Zayn yaja dogon tsakin da shi kansa bai san na meye ba ,

“Waheedah … Kiyi magana mana . Ko nayi lefi ne uhmmm? Please …”

Yadda yake karya harshe da lankwasa shi ne yasa Waheedah yin murmushi. Dawud din shima murmushin yayi. Ya sake cewa,

“To me zanyi aban number wayar nanne eh?”

“Allah banda waya….”

“Kina emmata baki da waya. Wait a wane school kike?”

“Ina ss2…”

“Ah dai dai kenan. .. Ashe mun kusa kammala school dinma ko?”

Ta gyada masa kai da sauri tana murmushi . Zai sake magana kenan. Nadra ta kwalawa Waheedah kira

“Zo nan sis zamu shiga ciki.”

Waheedah ta amsa da sauri. Don dama tsaiwar dole take agaban su. Ta ketare ta gefen Zayn zata wuce. Awawwaton hannunta ya riko zaren aikin hannun rigar sa .

Ta juya da sauri. Yayinda shima juyowar yayi. Karen hancin su saura kadan ya hadu. Yayin da numfashin junan su ya shiga haduwa a tare.

Kamshin turaren jikin ta dana Zayn suka hadu suka bada wani ni’imattaccen kamshi mai wuyar fassarawa .

“Sorry…… ” Ya fada kasan maqoshi. Yayinda ya daga hannun sa ahankali yana zare zaren daga jikin awawwaron nata .

Waheedah tayi tsit. Tana sauraron bugun zuciyar sa da ke bugawa da sauri sauri. Irin bugun nan da zuciya keyi idan tana cikin farin ciki ..

#FARHATAL QALB
(FARIN CIKIN ZUCIYA)

 

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰_*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply