Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 21


Bibiyata Akeyi 21
Viral

Page 21

*

Har sun “zo dasu tsallaka” titi, wanda ke wajan makarantar su” Wata motace tatsaya, a dai-dai gabansu. Sunyi matukar “tsorata ganin gilashin motar bakine wulik, zuge gilashin motar akayi” yaya jalal suka gani, hakanne yasasu sauke ajiyan zuciya, da mamaki fall aransu, na tambayar yaushe yazo, saurin bude bayan motar *hanna* tayi tashige, sannan amira tabi bayanta, juyowa yayi ya galla musu “harara , shine zaku barmin wannan uwar rawan Kan a gaba??? Kayi hakuri yaya, Allah nagaji ne baxan iya zagayawa ba” juyawa kawai yayi, a dai-dai lokacin” hameeda ta iso” bude motar tayi tashiga.

Amira yafaara kaiwa yasauke”. Sannan suka wuce gida.
Agajiye kowa ya shiga gida, wanka suka fara yi, sannan sukaci abinci, Sai Bayan sunyi sallar isha” suna zaune, *hanna* ce” ta tabo hameeda ke ga yaya nan yazo, na tabbata zai amsa mana tambayoyin mu. Tashi sukayi suka nufi d’akin da yaya yake.

Isowa kafar d’akin sukayi, *hanna* ce ta kwankwasa kofar dakin” shigo kawai yabasu amsa shiga sukayi da sallama suka sameshi, azaune yana chartting, zama sukayi akusa dashi, ta gefen katifar da yake zaune, yaya yaushe ka isoh, dazu” yabasu amsa atakaice.
Yaya dan Allah kabar chartting dinnan magana mai mahinmanci zamu, kallonsu yayi sannan ya gyara zamansa, ehem Ina sauraronku!!!!

Yaya Dan Allah akwai wani cin amana da mama da umman kano suka taba yi neh???? Kallonsu yayi cikin mamaki me yasa kukace haka???? Tambaya kuma akan tambaya kabamu amsa mana, hade rai yayi Idan baku futo kun min bayani ba ya ya za’ayi na fahimta???
Ammah na yawan kiranmu da dangin maciya aamana” wani lokacin har ma cewa su adda hafsa da rabi’ah takeyi wai mu maciya amana neh” wai suyi hankali damu, cikin bacin rai yadago ya kallesu, itah ammanneh tafada muku Haka???? Ehh!! *Hanna* tayi saurin daga Kai, furzar da Wata iska yayi.

Sannan yafara cewa “mu asalinmu yan garin bauchi ne, kakaninmu asalin su yan dambam ne, sunan kakanmu Mal Ahmadu da matarsa rabi’atuh, Allah ya azurtasu da yara guda takwas, inda yawancin su tun suna yara suke rasuwa, guda biyu kawai Allah ya zaunar musu Wanda sune baba na bauchi da kuma abba na kano”, wato muhammadu shine baban bauchi, da kuma yusuf shine karami wanda ake kiransa da abbah.

 

Mal. Ahmadu ne ya yanke shwarar tura babban bauchi, makarantar allo, sunyi yawo garuruwa kala-kala, inda akarshe suka yada dogon zango a bauchi, ganin zaman da yakeyi ne yasa ya nemi sana’a yafarayi, bayan sana’ar tafara karfi ne yasa ya yanke shawar shiga makaranta, alokacin yanada shekara sha daya yasa aka bashi aji hudu, sanda yayi shekara biyu sannan yagama makarantar primary.

Sai alokacin yasamu damar zuwa wahaifinsa, “ya yi iya kokarin sa wajen yin sana’a, yasamu kudin da zaisaya wa iyayensa abubuwa da yawa”
Alokacin yasamu kaninsa Dan kimanin shekaru takwas a duniya,
Bai dade ba yasake koma wa” dan yin karatun secoundry nasa.

Ahaka “yanayi yana zuwa kallon mahaifansa, Ana Haka Allah yayiwa mahaifiyarsu rasuwa, gaskiya sunji zafin wannan rashi Amma Haka sukayi tawakkali.

Bata dad’e da rasuwa ba Allah yakarbi ran Mal. Ahmadu, sunyi kuka na rashin mahaifi, damuwarsu daya” yadda yusuf zai kasance” dama bawani dangi ne garesu ba, Koda sunada su ma babu Wanda zai iya rike yusuf, dan kowa fama yakeyi da kansa.
Haka yatattari kaninsa, sukayi cikin garin bauchi ya rungumi sana’a sosai Dan ganin ya ciyar da kaninsa.

Ahaka yasamu aiki, awani shago nan yaci gaba da karatunsa, ba’a dad’e ba yasa kaninsa shima.
Ahaka Har yagama karatunsa, bedade da gamawa ba” yasamu aikin koyarwa, dan kunsan zamanin da basai kanada wani ba” kake samun aiki, bezaya ba yaci gaba da karatunsa na NCE a lokacin da yagama ne albashinsa yayi kwalri, tara kudin yafarayi Har yasaya fili, Ahaka suka hadu da Ammah, Ya aureta, dafarko sunfara zaman lafiya, inda daga baya suka fara samun matsala,
Sai da yayi da gaske tafuto ta nuna masa ita kaninsa ne bataso, aikuwa anan Wata babbar matsala takara tasaowa, Dan ya nuna mata duk duniya bbu Wanda yakeso kamar sa,
Bakin hali kala-kala tafara nuna masa”
Ganin Haka yasa yayansa turashi garin kano karatu, kodan hakan da yayi ma bawai ya Mata bane, Sai kuma ta tada rikici Kan, duk wani dukiyarsa takare akan karatun kaninsa, dan Haka adole tasa shima yakoma karatu, Amma hakan baisa yafasa turawa kaninsa kudin karatu ba.

Koda yusuf ya ga Haka sayya daina dawowa hutu, “Har Allah yasa yagama karatu, inda dama ya dade yana soyayya da umma (khadija), ba’ad’au lokaci ba baba yaje ya tambaya masa auranta, anyi biki masha Allah alokacin yaran Amma daya, Ahmad Wanda yaci sunan babansu tanada wani tsohon ciki takusa haihuwa.

Abba yasamu lecturing a buk inda yaci gaba da karatunsa na masters” ba’a dade ba umma tahaifi danta santalele ” Wanda yaci suna aminu sunan baban umman kanwarta akaturo dan tayata zama, daganan kuma taci gaba da zama awajanta.

Irin halin Ammah ne yasa baba tafiya kasar waje karo karatu, kozai rabu da masifarta.
Amma Haka yaje yadawo, saima abinda yakaru, hakanne yasa abba yanke shawarar, yimasa maganr karin aure” baiyi musu ba Amma yashaida masa baida wacce zai aura, shaida masa yayi ya dad’e yana masa sha’war kanwar matarsa tanada hnkali, da farko ” baba yaki ganin cewa abin kunya ne ya auri kanwar matar kaninsa , Amma daga baya ya amince, ba’a samu matsala ba aka fara gudanar da biki, Koda Ammah taji labari ba’ayita da dadi ba” dan cewa tayi tun yana talaka take tare dashi, Sai yanzu da yayi kudi, ganin ba Wanda yadamu da ita yasa ta lafawa, mama da baba suna matukar zaman lpy amma tana fuskantar kalu bale, daga wajan Ammah.

To be continued

_Ur’s_
_Z33yyb3rw3r_

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply