Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 96


Bibiyata Akeyi 96
Viral

Page 96
*
Wani soldier ne yazo wajanda suke, fuskarsa ko annuri bbu, yace kufice awannan block d’in dan yallabai zaifuto yanzu, yana fad’i yana hucii, kukan *hanna* yatsananta, mitumin da tafii kowa kusancii dashi, shine wanda ake mata iyaka dashi.”
Juyawa tayi kawai tana tafiya bawai dan tasan yanda take zuwa ba.”
Suma Juyawa sukayi suka bita abaya.”
Sanda tafice a hotel d’in tazube agate a k’asa tana rusa kuka, kamar wanda mahaifiyarta tarasu.”
Duk rarrashinda yakamata sumata sunyii amma takiyin Shiru.”
Inne tariqeta tana cewa habba bodd’i dan har yanzu *hanna* bawai ta fad’a musu sunanta bane, kitashi azaune ak’asa, kwananki biyu da haihuwa, hakan zai iya zama miki illah.”
Kuka takara kecewa dashi tace, barni kawai nayi kuka, rayuwata gabaki d’aya bbu haske cikinta, da irin wannan rayuwar gwara na mutu ma.”
Hussentu ne tamatso kusada ita tace, haba bodd’i wannan wace irin maganace?”
Kisan cewa kowani d’an adam da nasa jarabawar, kidubeni ki gani, aranarda aka d’aura aurena aranar mijina yarasu, sannan matar yaya i’shaq wajan haihuwa tarasu, mahaifinmu yau shekara, ishirin da biyu da b’acewarsa amma haryanzu bamu ta6a jin labarinsa ba.” ki godewa Allah daya kasance kindawo cikin hankalinki, zaki iya fad’a mana k’asarku, kokuma garinku mu kaiki, idan kuma bazaki je ba, Wallhy zamu riqeki har iya k’arshen rayuwarmu.”
Girgiza kai *hanna* tayi tace, mahaifana suna raye bansan wani hali suke ciki ba.” shikansa wannan da nazo wajansa mij,,,,,,, ai bata k’arasawa ba motocin marshall suka fara futowa, kallo tabi motocin idanuwanta nazubda kwallah, kallon motarda marshall yake kawai takeyi.”
Bak’in glass ne kawai, yarufe ko’ina, sanda motar ta6a cewa ganinta kafin ta kawarda ido, tak’ara fashewa da kuka, ba tafiyarsa bace tasakata, kuka A’a sai tunowa datayi dole yanzu su biyu ne awajansa.”
Koda takoma ikonta yadawo kad’an awajansa, share hawaayenta tayi, tatashi tamiqe, tana tafiya wanda ita kanta batasan ina zataje ba.”

 

Marshall wanda gabansa yayi wata mummunar fad’uwa a lokacin da akazo dabb gate d’in hotel d’in kuma haryanzu bawai gabansa yabar bugawa dasauri bane.”
Wani tunanine yasa yace kai tsayarda motannan, afili kuma yace, nasan a mutum d’aya kacal nakeda wannan feellings d’in, buga goshinsa yayi yace kuma idanna ji, aiyakamata natsaya naduba. Shikad’ai yaci gabada magana kamar zaccauce,” kallon d’an driver d’in yayi yace, kajuya zuwaga hotel d’in da muka baro.” waya yayi yasanarda sauran motocin.”
Juyawa sukayi, itakuwa *hanna* tana ta tafiya akan titin, hussentu nabinta abaya itada i’shaq, yayinda jaririn yake cikin mota shida diddi, dakuma inne, sadik najan motan ahankali yana binsu abaya.”
Sunzo dabb da ita, *hanna* kuwa hankakinta baya jikinta balle taga dawowarsu, fad’uwar gabanda yajine yasashi cewa tsaida motan, hange yafaryi ta cikin glass ya hango wata yarinya tana tafiya tad’an wuce motocin da d’ayan tsallaken titin, jikinta tafiyarta sakk na *hanna* tsayawa tayi tariqe cikinta dake ciwo, dasauri hussentu da i’shaq suka k’araso wajanta, su inne dake mota ma suka fito suka nufeta, inne ce tafara magana, bodd’i kiyiwa giraman Allah kizo mutafii amota, jikinki bbu k’arfii.”
Tsallaka titin marshall yayi yanufii wajan dan tabbatarwa idanuwansa cewa itace.” tsayawa yayi akanta kawai hawaye yanabin idanuwansa, jikin *hanna* yabata ana tsaye akanta ana kallonta, gashi kamshin datafii so duk duniya ya mamaye wajan.”
Hawaye tajii a idanuwanta wanda ita kanta batasan na mainene ba.”
Bata d’agoba cikin muryar kuka tace, maiyasa kadawo?” kallonta sukayi duka suna tunanin kwakwalwarta, tak’ara samun matsala,” Marshall bai iya Bata amsaba sai cewa kawai yayi, ya Allah idan mafarki nakeyi ka dawwamar mun da wannan mafarki har iya k’arshen rayuwata, sai alokacin suka d’aga ido suka dubeshi, kallon tsoro suka masa, wanda su atunaninsu balarabe ne, amma kuma ga hausa rad’al abakin sa.”
*Hanna* na kuka tace nikam zanfii buk’atar mafarkinne amma kuma nafarka yanzu.”
Honey please kafad’amun abunda kunnena yajii k’aryane, please kafad’amun bakayi aureba.” Marshall yarasa mai zaice, ganin yayi Shiru yatabbatar mata da gaskene, wani kuka mai cin raii *hanna* keyi, tace mai yasa bazaka iya jiranaba?” alokacin su inne sun fahimci cewa mijinta ne, juyawa marshall yayi yadubii, soldier dinda wayarsa ke riqe ahannun sa yace, ban phone d’ina jiki yana 6ari yaciro yabashi.”
Number d’in intisar yayi dialing tana d’auka yasaka a handsfree, itakuwa intisar farincikine yasaka tadauka dawuri, tattaro kawayenta tana cewa, bebs habibiy yakirani, ku matso kusa, itama tasaka a handsfree, duka k’awayenta suka matso danjin mai zaice, itakuma tayi hakanne, dan d’aga ajii, k’arya tayiwa k’awayenta akan aikine yahanshi halartan bikin, koda suka nuna cewa aibaya kiranta saita nuna musu, yana jejii ne Wajen aikii.”
Shiyasa yanzu ta gayyataosu.”
Da wata irin murya tayi sallama wanda yasa marshall murmushi, tace sannu da aikii, mijina, yawwa ya amsa, yagajiyar biki, sanda tayi wani farr tace, ai gajiya tanan, saika dawo zamu sauketa tare, maganar Sanda tayiwa marshall banbarakwai, yana godiya ga Allah dayabashi *hanna* mace mai kunya.”

Jikin *hanna* duk yagama yin sanyii wato namiji ba d’an goyo bane, agabanta ma yake gwada mata yanda suke soyewa.”
Kawarda kanta tayi hawaye yana zuba, a idanuwanta shikuma duk maganarda yakeyi idanuwansa yanakan *hanna*
yaushe aka d’aura auren?” yatambayi intisar, hmm d’azu ko 2hour’s ba’ayiba, dan Allah kadawo yau wallhy ina bukatarka, murmushi yayi yace, dole ndawo yau, tunda burinki ycika, wata dariya tayi tace tabbas burina yacika, ok tom dama sak’o ne nakeson fad’a miki kanna iso, dan nasan idan na iso ba lallai nasamu damaba, hayaniya da kuma abubuwa, cikin kissina tace hakane kam my love inajii.”
Intisar nasakeki saki d’aya, dasauri *hanna* tad’ago tana kallonsa, 😳intisar nasakeki saki biyu, intisar nasakeki saki ukuu, Wallhy banta6a sonki ba, bakuma na tunanin zansoki, koda nan gaba, Wallhy bazan ta6a son wata mace ba, bayan *hanna* murmushi ne yahad’e da hawaye fuskar *hanna* idanuwanta nacikin nasa kamar yanda shima nasa idanuwan ke cikin nata tunda yafara magana.”
Idan kinsamu miji ayanzu and’aura miki aure, baki da idda, Wallhy sau dubu za’a d’auramun aure, aranar saina saki matar.”
*Hannan* nandai ita kad’ai nakeso, kuma bazan daina sontaba har k’arshen rayuwata.”
Yafad’a had’eda kashe wayar itakuwa intisar tun kafin yagama magana tasume, sai kqwayenta dasuka gamajin komai.”
Suka ruga kiran umma (kilishi).”

 

Sukam su i’shaq anbarsu da kallon abun al’ajabi.”
Ware mata *hannu* yayi dasauri tana tatashi tana guduu ta fad’a jikinsa tana, kuka kamar ranta zaifita, shima rufeta yayi ruff, yanajin, wani irin farincki.”
Sunfii 20minute ahaka bbu wanda yagajii, dan kanta yana dai-dai zuciyar sa, tanajin bugawar zuciyarsa, ta lumshe idanuwanta.”
D’ago kanta tayi tafara dukan k’rjinsa hannu bibbiyu, dariya kawai yakeyi dan bazai iya hanata ba.”
Ta turo baki tace, da tafiya zakayi kabarni ko?” girgiza kai yayi yace duk yanda kike jikina yana bani.”
Bazan iya barinki ba.” yanzu harna kama hanyar airport najuyo jikina yabani kina nan.”
Murmushi tayi tace, tun jiya nake zuwa wajanka, tanuna wani soldier wancan mummunan ya hanani ganinka, nida mijina.”
Kama kunne yayi yace, amai afuwa cutie baisonki bane, nasake sabon soldier ‘s.”
Sai a lokacin ta tunoda da su inne kunya takamata, tafara kokarin kwacewa yak’i sakinta, ahankali tace ana kallonmu fa honey, d’aga gira d’aya yayi yace ina ruwana.”
Dakyar takwace tajuya garesu tace, diddi ga mijina nan, da fara’a diddi tace ainagani, yanzu muje gida amiki wanka sai kutafii naga yana hanya.”
Tajuya ta kalleshi tace sune way’anda suka rik’eni tsawanon 8month, dinnan.”
Marshall yabawa i’shaq da sadik hannu suka gaisa, yagaidasu diddi yace, yanzu please muje gida, sai muyi magana acan, sunfara, mota suka nufa.”
Amota yake ce mata, cutie cikin yazube ko?” girgiza kai tayi tace, A’a jiya nahaihu, matarda kabawa jini a hospital niceh, murmushi yayi yace jikina yabani kina asibitin.” yanzu ina gudan jinina.”
Harara ta wulla masa tace ni kad’ai fa nayi nak’udar, marairaicewa yayi yace cutie kinsan da ina nan, da tare zamuyi, yanzu ina yake ya fad’a cikin zumud’i.”
Yana wajan diddi bari mu isa.”
Suna isa marshall bbu kunya yazage yatambayi d’ansa kawo masashi akayi.” kallon yaron yakeyi kamar ya had’iyeshi dan soyayya, kamninsu d’aya, sai peck yake bawa yaron, inne tatsaya tana kallon yaran zamani.”
Aka shigada *hanna* wanka.” Sanda diddi tamata wanka tace, takawo mata abincii, tazauna takii, dan tunda sha tea takicin komai tun jiya.”
Ai kuwa cin abincinta tayi sosai.”
Tana gamawa marshall yaroqi akan dan Allah su tafii nigeria tare, yanzu yasan ana jiransa agida.”

 

Dake bawani abuu sukeyi ba, yasa suke amince aka dugunzuma duka akayi nigeria.”
Nan jirginsu yad’aga.”

 

 

To be continued
[9/1, 6:28 PM] Maryambawa: *BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’S_

_Here is your third Page my *HAJJA CE* ILYSM_

 

*NOTE*_ _naga sakonninku dayawa nacewa wai baikamata marshall yasaki intisar ba, kusani cewa Allah yace ka aurii mace d’aya idan zakayi mata adalci, sannan yace idan kaza iya adalci zaka iya auren mata biyu, idan zaka iya yiwa uku adalci, ka auresu har izuwa hudu, amma kowanne sai ankira adalcii atsakani, d’ayanma idan baza ka mata adalci ba and’auke maka baizama wajibi ba, kusani cewa bawai sonkai bane yasa marshall yasaki intisar ba A’a saidan yana nemawa kansa adalci, baiso yatashi gobe kiyama b’arinsa d’aya ashanye, yasan bazai iya adalci bane yasa Bai cutar da itaba.”_

.
================

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply