Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 50


Gurbin Ido 50
Viral

50

 

Itako maimunatu ko daya ta manta da sha’anin unaisa,tunda ta wuceta ta isa sashenta,sai ta kulle falonta abinta,da farko ta rasa me zatayi,don babu wani aiki da zai debe mata kewa,daga bisani ta tashi ta debo litattafanta na makaranta ta soma dubawa,don tunda ta dawo rashin lafiyar da tayin bata barta wannan karon tayi karatun kirki ba.

 

Bata bar kan litattafan ba sai da aka kira sallar magrib,bayan tayi sallar ta kuma ci abinci sai ta jawo wayarta tahau watsapp,shaf tama manta dashi,kasancewar bata wani saba ba,ya kuwa debe mata kewa sosai,don bata sauka ba sai da aka kira isha’i,tayi isha’in,ta kashe dukka wutar dake falo ta wuce dakinta,kayan bacci ta canza,ta haye gado,sannan ta duba last episode data tsaya a drama dinta ta kunna abarta ta dora daga inda ta tsaya.

 

Karfe tara harda mintuna ya shigo gidan,ya jima sosai yau a office fiye da yadda ya saba,duk da cewa dama lokaci irin wannan da suke soma shirye shiryen lissafin shekara da kuma tafiya hutun qarshen shekarar yana dan samu jimawa a office din fiye da ko yaushe.

 

Daga yanda yake takowa kadai zakasan ya gaji tubus,ya tura qofar falon ya shige kansa tsaye,don yasan babu wanda zai samu a falon,sannan ya soma haura samansa kai tsaye,yadan dubi sashen da qofar falon sassanta yake,yadan sasssuta saurinsa kadan kamar xai tsaya,sai kuma yaci gaba da tafiyarsa zuwa saman da dan sasssarfa.

 

Fridge ya fara isa ya ciro ruwa mai madaidaicin sanyi,sannan ya dawo saman daya daga cikin qawatttun turkish chairs din da suka qawata falon ya zauna,ya bude murfin gorar ruwan ya kafa bakinsa,yanajin yadda sanyinsa da baiyi yawa ba yana ratsa hanjinsa,rabi kawai yasha ya dire robar,ya sunkuya yana sabule takalmi da socks na qafarshi hadi da janyesu gefe,sannan ya miqe yana dauke briefcase dinsa,daya hannun nasa kuma yana sassauta tie din wuyansa,don burinsa shine kawai yayi wanka a yanzun,ko qafafunsa da hannayensa da suka sage zasu samu sassuci

 

“Oh shit” ya furta a hankali sanda wayarsa ta dauki daddadan sautin ringtone,ya murda handle na bedroom din nasa ya tura ya shiga gefe guda kuma yana qoqarin ciro wayar ya duba me kiran.

 

“Anni kuma?” Ya fada da dan mamaki a ransa,don yasan ko dazun sai daya biya ta gida,jakar ya wulla saman gado ya soma rage suit din jikinsa,sannan ya danna alamar kore na amsa kira,ya kuma dora wayar saman qawataccen dressing dinsa ya sanyata a hands free.

 

A kasalance yayi mata sallama,saidai yanayin yadda ta amsa sallamar yaja hankalinsa,har ya maida dubansa ga madubi yana kallon kansa da kansa,tare da jiran jin abinda zata fada

 

“Kana jina jafaru?” Ta fadi a kausashe kuma kanta tsaye,idanunsa ya lumshe ya kuma bude duk a kusan lokaci daya sannan yace

 

“Ummm”

 

“Idan kaga ma ba zaka amsa ba duk bazanyi mamaki ba,tunda dai xuwa yanxu wuyanka ya isa yanka,sannan kayi sama da haka ma……inason a gobe kafin ka wuce wajen neman kudin daka maidashi ibada sama da komai,ka tattaromin kan matanka ka kawomin su dakai kanka,dukkanku inason ganinku” qit ta kashe wayarta,sai ya aza idanunsa akan wayar tasa ba tare da yace komai ba,kwanyarsa na masa bita yanayin sautin muryar anni da kuma abinda tace masa goben yayi

 

“Matansa?, what’s happening?” Ya yiwa kansa tambayar da bashi da amsarta,sai kawai ya zabi jefa damuwar samun amsar tambayar a bayan damuwoyinsa,ya dage kafafa in i don’t care manner,yaci gaba da zare kayan jikinsa ya kuma wuce toilet ya hada ruwa me zafi yayi wanka,wannan kusan dabi’arsa ce,ba kowa ne zai iya wanka da ruwan da yake wanka dashi ba saboda yayi zafi da yawa.

 

Daya fito yana sharce sassalkar sumarsa dake jiqe da ruwa,qugunsa daure da towel wanda ya bayyana dukka wata kyakkyawar qira ta jikinsa,gefe guda maganar anni na dawo masa,sai ya janyo wayarsa a hankali sanda ya tuna voice note din da amna tace tayi masa ta wayar khadim,ya lalubo number dinsa ya shiga,ya kunna na farko yana samun waje ya zauna yana ci gaba da goge jikinsa.

 

A hankali tsadadden murmushin nan nasa ke fita a fuskarsa,abune me mugun wahala ka ganshi ga fuskarsa,duk da yadda yake qara masa mugun kyau,sai daya gama ji tsaf sannan ya jawo wayar yana kasheta,can qasan ransa yace

 

“You deserve my time amne na,i promise you,i will make you happy ending month in sha Allah”.

 

Sai daya gama shiryawa sannan ya tuna bashi da abinda zaici,ya sani yau baba tabawa ta koma gida,it means zaici gaba da bulayin neman abinci?,anya ba cook zai dauko ba kuwa ya aje cikin gidan?,sam ba girmansa bane a dinga ganinsa a eatery da sunan siyan abinci,bayan yana da komai,Allah ya mishi komai,yana da arziqin da idan abincin wata qasar yakeso yaci kullum to fa zai sameshi,sai ya miqe yana fita zuwa ga fridge din falonsa ko zai zamu wani abu da zai iya ci,gefe daya yana tunanin yadda zai gaya musu su shirya goben zasu wajen annin.

 

**********Karfe goma na safiyar washegari,wata safiya da aka tashi da haduwar gajimare wanda me dan duhu,cikin abubuwan dake alamta fara saukar damuna kowanne lokaci daga yanzu.

 

Tsaye a gaban daya daga cikin motocin dake fake a harabar gidan yake,sanye da wata shadda sky blue me matuqar kyau da daukan hankali,anyi mata dinkin zamani wanda ya dace da yanayin qirar jikinsa,ya kuma tafi da structure na jikinsa a matsayin cikakken namiji da ya amsa sunansa,mai haiba cikar kamala da kuma zati.

 

Qarasowarsa wajen kenan,cikin hanxari drivernsa ya fito yana karbar jakar hannunsa,gami da qoqarin bude masa seat din baya kamar yadda suka saba duk sanda xasu fita.

 

Hannu ya daga masa ya qarasa cikin coolness dinsa ya sanya hannu zaya bude gidan gaba,a dai dai lokacin ta qaraso cikin shigar wata irin gown da aka mata wani dinki,kanta yane da qaramin mayafi,yayin da fuskarta ke dauke da wani makeken sun glasses da yayi shigen kala da kayan jikinta,wani babban bangul ne a hannunta ke zobe guda daya,sai hig hill shoes data sanya a qafarta,mahadin figigiyar hand bag dinta,ta fito a unaisarta sak,unaisar shekarun baya,diyar gidan minister,shigarta gaba daya batayi kama da shigar wadda zata gidan surukanta ba,ga mutumin da ya fara ganinta yanzu,zaiyi zaton wani taro daya shafi siyasa ko kuma jiga jigan ‘yan boko zata je.

 

“Good morning” ta fada cikin salo,idanuwanta na kan ja’afar,wanda tuni ya bude gaban motar yana yunqurin shigewa

 

“Morning” ya amsa mata a taqaice,sannan ya zura jikinsa a hankali kafin ya dauke qafafunsa dake saye cikin wani lafiyayyen half cover shoe na kamfanin louise vuitton,hannunsa dake daure da wani lafiyayyen gogon kamfanin Blancpain ya zura da niyyar rufe murfin motar,unaisa tabi hannun da kallo bayan ta gama qarewa takalminsa kallo,take ta sake sallamawa,da gasken gaske dan gayu ne shi din na qarshe,wanda yasan sirrin kwalliya tare da ta’ammali da designers kayayyaki,bata sake cewa komai ba itama,saiya bude back seat amma ta saitinsa ta shige,tana dora idanuwanta kan fuskarta da take iya hange ta madubin gaba,wanda tuni ya bude news paper ta safiyar ranar da drivern sa ya miqo masa,yawanci dukka safiya yakan dudduba jaridan data fito a safiyar,musamman page din da suke wallafa al’amuran da suka shafi kasuwanci.

 

Tana so ta tambayi wanda suke jira amma wani irin kwarjininsa daya cika motar ya hanata cewa komai,sai ta fidda wayarta ta bude watsapp dinta,ta hau turawa anty talatu saqo,abinda ya dan janye hankalinta kenan,saboda maganar da suke da anty talatun nada matuqar muhimmanci.

 

Karo na uku kenan ya daga kansa yana duban hanya da niyyar idan bata fito ba zasu wuce kawai,ta biyosu daga baya,har yadan fafa hasala,saidai bai nuna ba kamar yadda ko sau daya baiyi qorafi ba,kasancewarsa mutum ba mai yawan magana ba,saidai a cikin sa’a ya hangeta tana tahowa.

 

Glass din fuskarsa da yakanyi amfani dashi lokaci lokaci ya zare a hankali tare da qoqarin kau da idanunsa daga sashen da take tahowan,bawai don yana tunanin tana ganinsa ba,a’ah……daya daga cikin dressing na shaheeda tayi,dressing din da kusan zai iya cewa ita daya ce macen da yasan tana yinsa,kuma har yau shi dai bai sake ganin wata da irin shigar ba sai ita….bai sani ba,ko don idanun gaske dana zucin ma gaba daya tare da hankalinsa kacokam basa tare da kowacce mace?.

 

Shigar lafaya tayi blue black me adon gold a jiki,ko ba’a fadi ba kalar tana daya daga cikin kalolin dake haska farar fata ainun,rashin sabo da yanayin shigar ya sanyata take jin kamar zata harde,wannan ya sabbaba mata taku cikin nutsuwa da takatsantsan,abinda ya zame mata kamar ado,kamar wadda ke yin tafiyar da gayya da kuma wata manufa ta daban.

 

Dukka cikin sakannin da basu haura goma ba ya gama kallonta kafin ya zare idanunsa ya maida kan news paper din nasa,dai dai lokacin da ita kuma unaisa ta daga kanta da xummar gyara zamanta,idanuwanta sukayi kyakkyawan ganin da ya sanya tunaninta qwacewa na wasu daqiqu

 

“Damn it” ta fada can qasa,tana jin wani abu me qarfi yana fusgarta,kishinta ya soma huda zuciyarta yana ratsata da gasken gaske,bata iya dauke idanuwanta ba,har zuwa sanda ta iso dab da motar.

 

Batasan waye da waye a ciki ba,don haka tadanyi knocking kadan,drivern ya motsa da niyyar fita ya bude mata kamar yadda ya yiwa unaisa,sai ya cira kansa a hankali daga cikin news paper din

 

“Ummm ummm”, ya fadi a taqaice,sai ya waiwayo ya kalleshi,yayi masa alama da ya zauna,a ladance ya amsa masa,ya ajjiye news paper din,sannan ya kama handle na motar ya bude,ya zuro qafarsa waje guda daya.

 

Kusan a tare suka hada idanu ita dashi,dukkansu cikin gaggawa kowa ya killace ganinsa,cikin dakakkiyar muryarsa ya magantu

 

“Bana iya zaman jiran kowa….wannan ya zama shine lokaci na qarshe da zaki aikata hakan” ya qarashe fada da muryar warning gamida da kausasa maganar tasa.

 

Sauka idanuwanta sukayi kan unaisa,wadda tadan rage glass din xuwa qasa kadan saboda ta samu damar jin a inda zasu fada,ita unaisar ke kallo,sai da suka hada idanu kuma sai ta tabe baki ta kuma janye idanun nata daga kansu ta mayar ga wayarta,a hankali maimunayu ta dauke idanunta daga wajen itama,tana jin yadda idanun nata suka cika da qwalla,cikin muryar nan tata dake cike da rauni….wadda ga wanda bai snata ba zai kira hakan da zallar shagwaba tace

 

“Kayi haquri” lafazin suka fita da sanyi da kuma zaqun muryarta,bashi ba,hatta da unaisa sai da salon da tayi maganar yaja hankalinta,ta sake maida idanunta kanta ba tare data shirya ba,tana jin kamar ta samu abu ta boye maimunatun,idanu su daina kaiwa zuwa gareta.

 

Sai daya lumshe idanunsa kana ya bude duka kusan lokaci guda,ya sake zube dubansa akan fuskarta,yana kallon yadda idaninta keta qyalli saboda ruwan hawauen da sukayi guzuri,yana mamakin saurin kukanta….me yasa ita din bata da tsayayyar zuciya,saurin bada haquri saurin kuka da kuma shagwaba kamar wata yayayya.

 

Qaramin tsakin da ita daya ta iya jinsa yaja yana maida jikinsa cikin motar

 

“Shiga mu tafi” ya fadi s gajarce,sai tasa hannu ta buda murfin motar ta kuma shiga bakinta dauke da sallama,driver ya amsa,yayin da da bakin J din yadan motss kadan alamun amsawa,ta fannin unaisa kowa ko uffan bata ce,can qasan ranta a mugun quntace.

 

Kaf maganganunta na jiya bata ga inda ta sanyo maimunatun a ciki ba,don me xa’a tafi da ita,ta maslahar aurenta ita daya kawai takeyi,bata qaunar ganin kowacce mace ta giftawa wannan buri da muradin nata.

 

Sosai qamshinta ya cika motar,har yaso yayi gogayya da nashi turaren,ya rufe news paper din a hankali ya ninketa gida biyu yana jan numfashi sosai wanda ya cika da qamshin nata,yana fesarwa kiran anni na shigowa wayarsa,ya dubi fuskan wayan bayan yayi kamar bazai dauka ba

 

“Am on my way” ya fada a taqaice,ya zame wayar daga kunnensa ya maidata inda ya dauko ya ajjiye,gefe daya na zuciyarsa yana cike da mamakin kiran meye haka anni ke masa da har ta qagu su iso,tabe bakinsa yayi,baisan da wacce rigimar zata zo masa yau ba,don bata rabo da rikici,amma koma dai meye…… he’s ready akan duk wata rigima da takeji da ita,don yayi mata iya abinda zai iya,duk da ransa da zuciyarsa basa so.

[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply