Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 65


Gurbin Ido 65
Viral

65

“I hate it,i already told you,duk sanda kika sakemin kuka irin hukuncin da zan miki kenan” sai ya matsa a hankali ya bude mata qofan yana dubanta

“Open your eyes” kasa budewar tayi,shi wai bazai fuskanci halin da take ciki ba

“I said open your eyes ko na sake punishing dinki” jin haka yasa ta bude idanuwan nata a hankali,tana ganin qofar a bude ta taka da hanzarinta kamar zai sake kamata ta fice.

Gaba sink ya tsaya ya dafe hannayensa yana jin yadda mararsa ta riqe sosai,wani abu da yayi fama dashi shekarun baya kafin aurensa da shaheeda,wanda kusan shine silar aurensa na farko,sai yayi qas da kansa yana tattare hankalinsa waje daya,yana jiran komai nasa ya dai daita,wanda a qalla ya kusa kashe minti goma sha biyar a haka kafin ya sakarwa kansa ruwa mai bala’in dumi sosai,yana jin yadda mararsa keta murdawa tana saki.

Sanda ya fito bata dakin,koda duba falo bata nan,sai ya sanyama qofar key ya shirya a hankali,sallah yaso fita yayi cikin jam’i amma sai ya kasa,cikin daki yayita,yana idarwa amna na shigowa nan ta zauna tana masa zubar tata.

Bayanan duka duba aikin yakeso ya shigar su tattara za’a miqawa gwamnatin lagos tare da wasu muhimman takardu da kuma roqan a qara musu wasu gurare dake daura da wajen,ya debo duka kayan aikin ya jona system a charge amma sai ya kasa komai,jikinsa ya mutu murus,mararsa kuma ciwo take da gaske,bai dauki ciwon a bakin komai ba,ya zaci surutun amna ne zai hanashi aikin,don haka ya zaunar da ita,ya jawo mata suratul mulk yace tayita biyawa,cikin qarfin hali ya jawo system din ya kunnata.

Tun aikin baiyi nisa ba yaji ciwon ya matsa masa,sai ya dauka wayarsa ya turawa jabir tex don ba kasafai ja’afar din ya fiya son kiran waya ba,yace ya fiddo key din mota zai rakashi wani waje,ya maida wayar ya ajjiye yana jingina jikinsa da bayan kujera,dai dai lokacin da maimunatu ta shigo dauke da coffee.

Duk lokacin daya dawo takan dafa masa,saidai amna take bawa ta kai masa,yau din da bata ga amnan ba batason sake shigowa su hada idanu,amma dole ta dauko ta shigo dashi.

Idanuwansa a kanta,har ta qaraso ta ajjiye masa,sannan ta danja baya tana fita a dakin ya bita da kallo,kunnuwansa nakan karatun amna da yake saurare yana mata gyara inda ta kuskure kadan kadan kuma marar tasa naci gaba da murda masa.

Maimunatun ce ta sake turo qofar

“Yaa jabir yana magana” ta fada masa idanunta a qasa,baice komai ba sai ya miqe kawai ya dauki wayoyinsa yana duban amna

“Ina zuwa,yanzu zamu dawo” ya fada yana fita daga dakin,ya wuce ta falo ya fice.

Cikin mota ya sameshi zaune yana jiransa

“Ina zamu?,na gama tsara bazan fita ba sai gobe,gaba daya hutun da naso samu aikin nan bai barni na sake ba” ya fahimta sarai me yake nufi,baice masa komai ba sai ya karba key din motar,sukayi exchanging seat ya tada motar suka fice bayan ya saita map ta wayarsa,ya dinga directing nasa zuwa nearest private hospital.

Da mamaki jabir ya kalleshi bayan ya sanya hancin motar cikin asibitin

“Waye ba lafiya?”

“Nine” ya amsa masa kai tsaye, cikin damuwa jabir din yace

“Subhanallah,me ya sameka?,daga dawowarmu?”

“I don’t know” ya amsa masa a taqaice,sai ya qyaleshi kawai,da alama ‘yan miskilancin ne suka motsa.

Sanda suka shiga akwai likita,amma kuma da layi,saidai akwai special service,amma kudinsa ya ninka normal consultancy fee din da ake biya.

Jabir ne ya biya komai kamar yadda suka saba,duk sanda wani zaiyi wani lalurar rayuwa indai daya yana wajen shike biyan komai,kai tsaye suka isa qofan consultancy room

“Ka shiga kawai,zan jiraka a nan” jabir ya fada,bai matsanta masa ba ya shiga ya barshin.

Musabaha ya bawa inyamurin likitan hannu sukayi,ya tarbeshi da fara’a da girmamawa da alama yasan aikinsa,duk wani bayani daya kamata yayi masa yayi masan,ya kuma dubashi harda scanning,ya daga takardar yana kalla,sannan ya dawo da dubansa kansa cikin harshen turanci

“Yallabai,ka taba samun matsala irin haka?” Idaonsa ya lumshe yana gyada masa kai

“Amma ba’a taba gaya maka kayi aure ba?”

“An taba” ya amsa masa kai tsaye

“Seriously dole kayi aure,kana buqatar hakan,binciken da nayi ya nuna ba zaka iya zama a haka ba,kayi qoqari kayi,zan rubuta maka magungunan da xaka samu relief,pain din ya ragu” shuru yayi kawai yana saurarensa,kamar yanzunne ake gaya masa wannan maganar a shekarun baya,akwai case kenan ya fada a ransa.

Har suka fito jabir baice masa komai ba,shi dinne ya cewa jabir zasu tsaya a pharmacy zai karba magani ya ajjiye takardar a tsakiyarsu,kallon takardar jabir yayi,har zai tada motar yace

“Am sorry,ina zuwa” ya bude murfin motar ya koma ciki,bai wuce mintuna goma ba ya dawo,still bai sake ce masa komai ba ya tashi motar suka wuce.

Jin shurun yayi yawa sai ja’afar din yayi gyaran murya

“Jibi ne zamu koma….ka siya mana ticket?”

“Zan siya” ya amsa shi a taqaice. Kusan zaman kurame sukayi har suka siya maganin suka koma masauki,fuskar jabir din kamar akwai abinda yake nazari.

°°°°°°°°A nutse ja’afar ya daga kai ya kalli jabir bayan ya miqa masa ticket din guda biyu ya kuma gama karanta abinda ke jiki,hankalinsa kwance yake cin abincinsa

“Ticket din lagos to gombe ya kamata ka siya mana,amma ina ganin na lagos to johannesburg”

“Eh,daga nan can zamu wuce,ya kamata mu dinga samun lokaci muna dan hutawa koda ba yawa,just one week kawai zamu dawo” shuru yayi na dan sakanni yana duban jabir din,jabir din wani mutum ne na musamman cikin rayuwarsa,yana da matuqar muhimmanci a rayuwarsa,hakanan ya isa ya yanke hukunci cikin rayuwarsa kamar yadda yasan shima hakan take a wajen jabir,bayason ya maida niyyar alkhairin da yayi masa,uwa uba kuma shi kansa yasan yana buqatar wani hutun, tunda ko da sukazo nan din wani irin ayyuka ne suka hadar musu,ba wani hutu ko qanqani,amma kuma bai shiryama wannan tafiyar ba kwata kwata

“But…..kasan amma tayi maganan amna,akwai biki a dangin mommynta,jibi kuma zasu wuce har da ita”

“Nayi waya da hisham,yacemin ya shigo lagos jiya,yaje wani aiki a teaching hospital,gobe zai koma,so na yankan musu ticket shi da amnan zasu wuce gombe gobe da yamma,mu kuma zamu bi south african airways flight sha biyu na rana” boyayyar ajiyar zuciya ya sauke yana ajiiye ticket din a gefansa,duk wani hanzari nasa jabir ya kasheshi,bashi da wani sauran uzuri kuma da zai bayar.

Shuru kawai maimunatu tayi tana binsa da kallo sand ayake ficewa daga dakin,bayan ya gama gaya mata inda zasun,idanuwanta suka tara ruwan hawaye sosai,saura kwanaki hudu kacal a koma makaranta,tana murna gobe zasu koma sai kuma wata tafiyar bagatatan ta taso?,hakanan ta shiryama amna kayanta da sauran tsarabarta ta nan,ta hade jakankunan dana qananun kayan da fatima ta lodo mata,don babu inda zata je dasu.

Tun tara na safe hisham yazo ya dauki amna,bata damu sosai ba don ta saba da uncle hisham din,ta kuma san cewa gwani ne wajen iya kula da yara da biyewa shirmensu,haka kawai ja’afar ya hanata fita su ko gaisa da hisham din bare suyi sallama da amna,ya rufe qofan dakin ya fita da card key din suna sallama dasu a farfajiyar hotel din,sai ta window ta leqasu,tana nan a tsaye har suka fice,shi kuma yana tsaye suna magana da jabir din.

Maimakon ta saki labulen ta koma kamar yadda take so saita kasa,ta aza idanuwanta akansa tana kallonsa,sanye yake da long sleeve zip up hoodie wine color da wandonta,gashinsa a kwance kamar ko da yaushe baqi sidik,kana kallonsa kaga baqin bafullatani,qafafunsa slipper ne,ya dan kere jabir tsaho da kadan,amma kana duban fuskarsa zakasan ba ma’abocin fara’a bane,saboda yanayinsa ya nuna,sabanin jabir da ko yaushe fuskarsa ke a sake,kadaran kadaham.

Kamar wanda aka yiwa cunenta ya daga kansa zuwa saman yana saukesu a bakin window din,cikin jikinsa yaji kamar ana kallonsa,cikin hanzari ta saki labulen taja da baya ta fada saman gadon gabanta yana faduwa,idanu ta fitar

“Allah yasa bai ganni ba” ta fadi tana dafe goshinta,idan ya ganta aita tafka abun kunya.

Sauke idanunsa yayi daga kallon wajen,yaga labule ya motsa alamun an koma da baya,gaba daya lissafin tafiyar ne cikin ransa,baisan me jabir ya qulla ba,amma yafi kowa sanin halinsa,bai taba wata magana data dangancin iyalinsa dashi ba,amma ya tabbatar da biyu ya shirya wannan tafiyar,koma meye zaiyi qoqarin kame kansa da mutuncinsa,ba zaiyi abinda mutuncinsa zai zuba a idanun qaramar yarinya ba(niko nace sannu gembo sarkin son girma,muje dai zuwa 😒).

Tun kafin sukai ga shiga jirgi ta fahimci tafiyar gaba daya kamar ta musamman ce,kamar kusan koma fiye da rabin matafiyan couples ne(wato miji da mata),kowa ka ganshi tallafe da matarsa,harda jabir wannan karon murje idanunsa ya ja fatimansa jikinsa sunata hirarrakinsu qasa qasa.

Karon farko da taji abun ya burgeta,sai ta dauke idanunta zuwa sashen da ja’afar din ke tsaye tun dazu yana amsa waya,cikin sa’a ta samu ita yake kallo,kallo kuma na kai tsaye,abinda bata sani ba ya dan jima a tsaye yana karantar expression nata directly,ya karanci akwai wani abu da ya motsa zuciyarta.

Cikin kunya ta kauda idanunta daga kansa,sai ta zaro wayarta daga qaramar jakar da tayi amfani da ita ta kunna data ta shiga watsapp dinta,rasa me zatayi tayi,bata da interest nayin chart yanzu da kowa,sai ta koma viewing status na mutane,kafin ta gaji da wannan,ta shirin sauka notification na wani app ya shigo mata,sai ta danna ta shiga,tana duba sabbin pictures da quotes na soyayya da suka dora,wannan yadan dauke mata hankali.

Sanda suke wucewa zuwa jirgi fatima da jabir suna bayansu su kuma suna gaba,ya daidata kafadarsa da tata,abinda yasa ta sake gane tazarar tsahon dake tsakaninsu,batasan me ya faru ba,a hankali ta tsinci tattausan hannunsa cikin nata,ya hada dukka tafukan hannayensu ya matse guri daya,daga ido tayi ta kalleshi jikinta yana amsawa sai taga idanuwansa na kallon wani waje,a hankali ta maida dubanta wajen,sai a sannan ta fuskanci me yakewa,daya daga cikin ma’aikatan airport din ne,sanye da kayan aiki,ya zuba dukka idanuwansa a kansu,kafin daga bisani ya janye ganin ja’afar din ya kama hannunta,qaramin tsaki yaja bayan sun giftashi da kadan,ta zaci zaici zai sakar mata hannun amma sai taga yaci gaba da riqeta,har suka isa cikin jirgin.

Batasan seat number dinsu daya bane sai da tazo zama,kallonta yayi sanda yake sanya luggage dinsa daga saman kansu,hannunsa daya dauke da da wata sweater mara nauyi me kyau

“Anzo wajen,Allah yasa ba sanyi garesu ba” ta fada cikin ranta,don babu abinda yake takura ta a rayuwarta irin sanyi,batason zafi,amma kuma idan sanyi yayi yawa yana damunta.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply