Hausa Novels Sakayyah Book 2 Complete

Sakayyah Book 2 Page 6


Sakayyah Book 2 Page 6
Viral

 

Ikon Allah sai kallo wai fa Modibbo takeso. 

 

*Littafin SAKAYYAH dai na kuɗi ki biya ki karanta cikin
Aminci yafi ki karanta na sata kuma na Allah ya isa, 1k ne kacal 0661110170 GTBank
AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276.
Sai in tura miki littafin*

 

 


By

      *GARKUWAR
MARUBUTA**SAKAYYAH book 2 page 6*

           Na

*Aysha Aliyu Garkuwa*

 

*Alamomin infection sune kamar haka*. Rashin sha’awa.
Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko
ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko
ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni’ima. Buɗewar
gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani
yayi al’ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko
kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da
kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban
lissafa. Sune manyan alamomin infection.

Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman
kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari
kiji illolin infection wato cutar sanyi.

Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin
kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi
bare wata ni’ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta
lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin yana kwaranya.
Zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk
tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki
nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.

KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA
BAYYANA KANSA sai ya gama yi miki illah. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar
kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni’imomin ki, da
sha’awarki, duk kyan kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan
arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA’AURATA, amman ke in
kinsha jiya I yau,  duk nacin oga da yi
miki wasannin bazaki ji sha’awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata
bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure.
Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor’s suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma
fibrod duk a cikin sherrin chronic infection ne yar uwa.

INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara,
Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar
komai na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin
infection koda na cikin mahaifane bi’izinillahi ta’ala zaki rabu dashi, cutar
infection cutace mai masifar naci, so yar uwa dole kema ki nace masa da maganin
mu,  set ɗin10k ne kuma maganin kala
biyarne nasha kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin
saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya
saya mata, domin ko kin rabu da shin indai ita tana dashi tofa kin kashe
macijine baki cire kaiba, ma’ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a
saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya’ya mata ya buɗa miki
ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da
baku iya bada tarbiyaba dan kun kai mishi amarya a rarake bayan kun san kuɗin
sadaki ya ƙara sama. Saboda yanayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa
miki komai rabi-rabi a 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga
account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki
kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER’N na 09097853276 sai ki turo min shaidar
biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai
taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3
ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah
in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce
dai GARKUWAR MA’AURATA.

 

 

Cikin yanayin ɓacin rai Mommy ta ture kanta dake kan cinyar
ta babu walwala atare da ita tace.

“To ai shikenan Khausar hankalinki ya kwanta, zagine da abin
kunya kunja min, kukan me kuma zaki zo kina min, in banda rashin hankali dama
rashin kunya Khausar yaushe Moddibo yace yana sonki yaushe Moddibo ya taɓa zuwa
wajenki?”.

Kasa cewa komai Khausar tayi sai hawaye dake cigaba da
kwaranya a Idanunta Shar-shar.

Cike da takaici Mommy ta cigaba da cewa.

“Mutumin da ko Amakaranta tsakaninki dashi sai dai faɗa
kyara da hantara. Duk abinda ke faruwa ina sane ai ana bani labari amma saboda
tsabar shashanci ki rasa wanda zaki ce kina so sai mutumin da bakwa zama inuwa ɗaya!”.

Kuka sosai Khausar ta fashe dashi cikin sheshsheƙan Kukan
tace.

“Wallahi Mommy ba haka bane dan Allah ki tsaya ki
saurareni”.

Kai Mommy ta Girgiza tare da tsira mata Ido tace.

“Hmmm Khausar kenan me zan saurara kuma, ai babu abinda
zanji daga gareki tunda ke kika haifi kanki ke zaki yankewa kanki hukunci
sannan ke zaki zaɓawa kanki miji wai ki kalli tsabar Idanunmu saboda tsaurin Ido
kice Modibbo  kike so to yaushe yace yana
sonki?”.

Girgiza kai kawai tayi cikin matsanancin kuka da tashin
hankali tace.

“Dan Allah Mommy kiyi haƙuri wallahi ba rashin kunya bane
dolene yasa haka Mommy ki sanya mana al’barka acikin rayuwar auren da zamu yi”.

Cike da takaici Mommy ta kalleta kana tace.

“Toh Khausar tambayar da zan miki Moddibo yace yana sonki ko
kuma ke kike haukanki?”.

Girgiza kai Khausar tayi cikin rawan murya tace.

“Mommy I don’t know either he love me or not”.

Miƙewa Mommy tayi tare da jan dogon tsaki ta fice daga ɗakin
ta nufi Falon Lamiɗo.

 

Khausar kuwa kanta ta kife ajikin katifa ta fashe da
sassayan kuka tana sheshsheƙa Ajiyar zuciya Haiydar ya sauƙe tare da kallon
Khausar cikin sanyin murya da rashin fahimta yace.

“Addah Khausi ban fahimci abinda Mommy take faɗa ba wai
Malam Moddibo kike so ko kuma wa?”.

Kai ta gyaɗa masa Muryanta na rawa tace.

“Eh shi nake so”.

Zare ido Haiydar yayi tare da sanya salati kana yace.

“Toh shi Malam Moddibo yana sonki ne?,”.

Kai Khausar ta girgiza tare da ɗago Idanunta dake jiƙe da
hawaye cikin raunin murya tace.

“Ban saniba Haiydar I really don’t know”.

Cike da matsanancin mamaki da damuwa Haiydar yace.

“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Khausar baki sani ba
kuma?”.

Jinjina kai Khausar tayi cikin raunin murya tace.

“Bansani ba Haiydar Bansani ba Haiydar”.

Miƙewa Haiydar yayi cike da takaici yaja dogon tsaki tare da
faɗin.

“Wallahi dama nasan hakane babu abinda zaisa in rakoki wajen
Mommy”.

Ya ida maganar tare da ficewa cike da takaici da ban haushi.

Cikin rauni Khausar ta miƙe tare da nufar Bedroom ɗinta tana
shiga ta faɗa bisa gado tare da sakin kuka mai masifar ɗaci da ƙuna.

 

Mommy kuwa kai tsaye falon Lamiɗo ta nufa bakinta ɗauke da
Sallama tashiga falon zaune ta samu Abba akan 2sitter.

Anutse Lamiɗo ya ɗago kansa tare da sakar mata da lallausan
murmushi kana yace.

“Shatu Ikon Allah mai kuma ya ɓatawa Gimbiya Aysha rai”.

Fuska Mommy ta ɓata tare da narkar da murya kana tace.

“Na lura ma al’amarin Khausar dariya yake baka, baki ɗaya
tun jiya Yarinyar nan ta ɓata min rai ta hargitsa min lissafi, sam kakarta bata
da kirki tsohuwa ce mai zafi ta saba da iko da gadara akan ƙannenta ta saba da
maganar ta kamar yankan wuƙace”.

Kallonta kawai Lamiɗo yake yana murmushi.

Cikin yanayin damuwa ta cigaba da cewa.

“Duk abinda ta faɗa haka ne babu wanda ya isa ya musan ta
mata gashi Khausar tazo tayi mata abinda bashi neba ta tafi tana zagina yanzu
tana zuwa Rugar nan zata baza sunan Khausar hakan zanji daɗi ne?”.

 

Murmushi Lamiɗo yayi tare da gyara zaman sa kana ya miƙa
mata hannunsa tare da cewa taho nan zo nan Shatuna”.

Maƙe kafaɗa tayi tare da tura baki kana ta narkar da fuska.

Murmushi Lamiɗo yayi tare da cewa.

“Ki zauna mana”.

Kallonsa kawai take amma ba tace Uffan ba.

Ahankali ya sanya hannunsa ya janyo tsintsiyar hannunta tare
da zaunar da ita agefen sa cikin sanyin murya yace.

“To amma ai akwai abinda baki sani ba”.

Asanyaye ta kallesa tare da cewa.

“Toh menene ban sani ba?”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da tsira mata ido kana yace.

“Jiya Hajja Nana bata bani dama inyi mata Magana ba saboda
yanda ta ɗauki abin da zafi take ta ihu da kururuwa da Masifa sannan dole mu
bita ayanda taso”.

Jinjina Kai Mommy tayi tare da sauƙe numfashi.

Cikin sanyin Murya ya cigaba da cewa.

“Tun da kinga tsohuwa ce sannan tana da ƙarfin iko akan
Khausar babu yanda muka iya, amma Baffanta ya fahimta domin yau kafin ya koma
Ɓadamaya yabiyo nan munyi magana dashi”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana ya
kalli Mommy da itama shi take kallo yace.

“Sannan yace ba zai mata dole ba kamar yanda idan Mahaifinta
yana raye ba zai mata dole ba kamar yanda zai yiwa ƴaƴan sa haka zai mata
saboda yana da ƴaƴa mata da yawa kamar yanda bai musu dole ba haka itama ba zai
mata dole ba dan mahaifinta baya raye”.

 

Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da fesar da numfashi kana
tace.

“Na sani shi yana da fahimta, amma ita tsohuwar ce gaba ɗaya
ba zata fahimta ba”.

Lakace mata hanci Lamiɗo yayi kana da murmushi afuskarsa
yace.

“Kada ki damu ɗan zai fahimtar da ita, dan yace ya bata
haƙuri sannan idan ta huce zai sake dawowa ya bata haƙuri kuma Insha Allah zata
fahimta”.

Jinjina kai Mommy tayi tare da gyara zamanta kana tace.

“Toh naji ta wannan gefen an samu fahimta amma fa Moddibo
baya Son Khausar din ita da bakinta fa tace min bata san yana sonta ko baya
sonta ba, ka taɓa ganin Moddibo yazo wajen Khausar ne?”.

Kai Abba ya gyaɗa tare da cewa.

“Eh na taɓa gani mana kwanaki sunzo da Asma’u”.

 

Girgiza kai Mommy tayi tare da fesar da numfashi kana tace.

“Zuwan da kaga yayi ta’aziyyan Ramadan yazo min domin yace
alokacin da suka zo yimin ta’aziyya sun haɗu da Ori da ya muku bayani gawar
Jameel toh sun fita bai shigo ya min ta’aziyya ba, shine suka zo da Asma’u
yamin amma fa baice yana son Khausar ba hasalima Khausar da Moddibo basa zama
inuwa ɗaya”.

 

Ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauƙe tare da gyara zamansa ya
fuskanceta tare da cewa.

“Ki nutsu mana Ni nafi so ki nutsu Ayshatu idan kin nutsu
sai in miki bayani”.

Marairaice fuska tayi tare da langwaɓar da kai kana tace.

“Toh ai yanzu ma Anutse nake ranka shi daɗe kai nake
sauraro”.

Murmushi yayi tare da riƙe tafin hannunta acikin nasa kana
ya lumshe idanunsa tare da cewa.

“Jiya ma hargowar Hajja Nana ce ya hana in miki bayani
shekaran jiya baki ji cewa nayi baƙi ba?”.

Kai ta gyaɗa tare da cewa.

“Eh naji”.

Ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauke kana ahankali yace.

“Toh Malam, Arɗo ne da Alh Bashir mai Dala Mahaifin marigayi
Malam Jameel da kuma Malam Ahmad Baban Asma’u suka zo”.

Jinjina kai Mommy tayi kana cikin sanyin murya tace.

“Ooh sune suka zo!?”..

Kai ya gyaɗa mata still hannunsa na cikin nata yace.

“Eh”.

 fesar da numfashi
yayi kama yace.

“Toh kinsan me yaka wo su?”.

Kai ta Girgiza kana tace.

“A’a sai ka faɗa”.

 

Atake yanayin fuskarsa ya sauya daga murmushi zuwa rauni
cikin sanyin murya da rauni yace.

“Magana suka zo akan wasiyyar da Marigayi Jameelu ya bari”.

Saurin Kallonsa Mommy tayi cikin sanyin murya da damuwa
tace.

“Wasiyya kuma!?”.

Jinjina mata kai Lamiɗo yayi tare da fesar da numfashi kana
yace.

“Eh”.

Ahankali tace.

“Wasiyya kuma Jameel ya bari akan me!?”.

 

Zamansa ya gyara tare da janye hannunsa ɗaya daga cikin na
Mommy ya dafe goshinsa cikin raunin murya yace.

“Jameel yabar wasiyya ne akan Moddibo da Khausar”.

Lokaci ɗaya idanun Mommy suka ciko da Hawaye cikin raunin
murya tace.

“Wasiyya akan Moddibo da Khausar kuma to akan me?”.

 

Jinjina mata kai yayi still muryarsa Araunane yace.

“Tabbas Mahaifinsa ya faɗa min cewa akwai ranan da suka je
shi da Moddibo gidansa alokacin saura kwana uku asace sa har yake faɗa masa
yafa zaɓawa Moddibo matar da zai Aura Amma shi kansa Moddibo bai sani ba domin
koda Jameel ya faɗa murmushi Moddibo yayi alokacin har yake cewa Alhaji
Bashiru. Abba kaji fa wai ni J zai za ɓawa mata kamar wani yaro ko makaho”.

Lumshe ido Lamiɗo yayi cikin rauni ya cigaba da cewa.

“Alokacin Abban sa yace ya faɗa masa wace mata ce sai
Jameelu yayi dariya  yace sai ya dawo
asirri zai faɗa masa to bayan da ya dawo sai yace wa mahaifinsa dan Allah Abba
ina neman alfarma acikin kwanakin nan domin wata ƙila akwai abinda zai iya
faruwa acikin kwanakin nan wataƙil agaban ido na wataƙil kuma abayan Idona”.

 

Cikin sauri Mommy ta rintse Idanunta Hawaye masu zafi suka
zubo mata ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauƙe kana yace.

“A lokacin sai mahaifinsa yace.

“In sha Allah a gaban idon ka nema Jameeluna ina zakaje”.

Sai yayi murumshi tare da sunkuyar da kansa murya a sanyaye
yace.

“Wata ƙil kafin nan na tafi Marocco ko wata duniyar. Dan
haka ga mata na zaɓawa Moddibo koda bayan bana nan Abba ayi ƙoƙari ahaɗa auren
Moddibo da Khausar sai Abban sa yace to Meyesa kace haka sai yace wa Mahaifinsa
shi dai yana fata kuma yana buri ahaɗa auren Moddibo da Khausar domin Moddibo
yana ɓuƙatar Aure fiye dashi shiyasa ya fara yi masa zaɓin mata”.

A hankali Lamiɗo ya fesar da numfashi mai zafi kana ya
cigaba da cewa.

“Sannan Marigayi Jameelu ya sanar da mahaifiyarsa maganar
kana ya sanar da Kakar Moddibo maganar har ta kira Malam Arɗo ta sanar dashi
maganar domin wasiyya ce alokacin yake cewa ayi ƙoƙari ayi auren cikin gaggawa
domin Moddibo yana bukatar aure shiyasa yake so ayi kokari ayi auren cikin
gaggawa koda baya nan babu wanda baisan da maganar  ba sai Moddibo shiyasa shekaran jiya suka zo
akan neman alfarma  ga Uzurin da suka zo
dashi”.

Sai kuma ya numfasa kana yaci gaba da cewa.

“Akan wasiyyar da yabari toh na faɗa musu lallai Nine mariƙin
Khausar Kuma Khausar tamkar ƴa take awajena, saidai bani da iko da kuma ƴan cin
da zan bada Auren Khausar garesu batare da izinin Yayan mahaifinta ba da kuma
sahalewar kakarta”.

Gyara zama tayi tare da kallon Mommy da tayi sanyi hawaye na
zuba daga idanunta numfashi ya fesar kana yace.

“Toh nace suje bayan kwanaki zasu jini, toh dana niyyata
zamu je Jauro yaya muyi wa Hajja Nana bayani sannan mu faɗa mata wasiyya ne duk
abinda ake ciki dama nace idan muka dawo zan faɗa musu”.

Kallonsa kawai Mommy take bako kyaftawa tana sake jin tsoron
Allah Mabuwayi gagara Misali aranta cikin sanyin murya Abba ya cigaba da cewa.

“Kuma tunda kika ji Khausar ta furta haka wataƙil itama
akwai abinda ta sani acikin wannan al’amarin”.

 

Dogon numfashi Mommy taja tare da fesarwa kana ta lumshe
Idanunta hawaye masu zafi suka zubo ahankali ta sunkuyar da kanta cikin raunin
murya tace.

“Allah sarki toh Ubangiji Allah ya jikansa da rahma  idan al’khairi ne Allah ya tabbatar idan kuma
ba al’khairi bane Allah ya sauya musu da mafi al’khairi”.

Jinjina kai Lamiɗo yayi tare da sauƙe numfashi kana yace.

“Yawwa Aysha yanzu kika gane addu’ar da zaki yi kenan,
sannan kada kiyi fushi da Khausar fadan nan dakike yi bashi da amfani zama
zakiyi da ita ki fahimci Meye dalilinta na fadar haka”.

Kai ta gyaɗa kana cikin sanyin murya tace.

“Toh shikenan Insha Allah zan kiyaye”.

 

Sai da aka kira sallar azahar Lamiɗo ya fita ya tafi
masallaci kana Mommy ta miƙe ta nufi sashenta tana shiga falon ta fara jiyo
sheshsheƙan Kukan Khausar abakin ƙofar Bedroom ɗinta ta tsaya tare da ɗaga
labulen ta kalli Khausar ba yabo ba fallasa tace.

“Idan kin gama kukan ki tashi kije kiyi al’wala kiyi
sallah”.

Cikin sanyi ta gyaɗa mata kai kana ta miƙe tashiga toilet ta
ɗaura al’wala ta fito Anutse ta gabatar da sallah.

 

 Mommy ma na shiga
Bedroom ɗinta ta ɗaura al’wala sannan ta gabatar da sallah.

Bayan Khausar ta idar da Sallah kai tsaye ɗakin Mommy ta
nufa.

 

Acan ɓangaren Hajiya Lami kuwa zaune take akan kujera taji
ƙa garin magani da tsamiya da kuma ruwan zafi ta kalli Samira dake zaune
gefenta ta zabga ta gumi cikin sanyi tace.

“Gashi ki karɓi maganin kisha dama wannan yace sai da
rana-rana zaki riƙa sha wanda kika sha jiya da daddare kuma dare-dare zaki
sha”.

Karɓan kofin Samira tayi tare da tsira masa Ido ganin yanda
ta tsirawa kofin Ido yasa Hajiya Lami cewa.

“Kisha mana”.

Cikin raunin murya Samira tace.

“Mommy nifa na jiya da daddare nan ma dana sha babu abinda
ya ragu saima zubar ruwan daya ƙaru”.

Ahankali Hajiya Lami tace.

“Toh Sokuwa wataƙil ruwan ai zai zube ne ya gama ƙarewa idan
ya gama zuba shikenan magana ya ƙare”.

Cikin raunin da tashin hankali Samira ta kalli mahaifiyar ta
da Idanunta dake cike da ruwan hawaye kana tace.

“Toh Mommy ruwan fa da ƙarni da wari yake zuba yanzu ma
bakiji yanda nake ƙarni ba?”.

Cikin tsinkewar zuciya ta kalli Samira sai kuma ta basar
domin bata son bawa ƴartata tsoro amma baki ɗaya hankalinta ya tashi kar dai
ƴarta ta samu wata matsala numfashi ta fesar tare da kallonta kana tace.

“Ni dai banji wani wari ba hancin kine dai da shegen
jiye-jiye kina nan da hanci kamar na kule ke dai kisha magani tunda yace kisha
na tsawon sati biyu kafin mu koma”.

Zare ido tayi cike da tashin hankali tace.

“Mommy har sati biyu kuma?”.

Kai Hajiya Lami ta gyaɗa kana tace.

“Eh saboda zaiyi tafiya so koda munje baza mu same shiba”.

Ajiyar zuciya Samira ta sauƙe tare da cewa.

“Toh bari in sha”.

 

Aɓangaren Naseer kuwa zaune suke afalon Mahaifiyar sa da
Addarsa Hindu da kuma Mahaifiyar su Hajiya Kubra yayin da akwatuna ke jere
agabansu cikin su sanye da Atamfofi, Leshuna, Shadda, English wear, Turaruka,
Mayuka,Takalma.

Gyara zama Naseer yayi tare da kallon Addah Hindu murmushi
ya sakar mata tare da ɗage mata gira ɗaya kana yace.

“Insha Allah Addah Hindu burina ya kusa cika”.

Murmushi tayi tare da jinjina masa hannu kana tace.

“Ƙwarai kuwa nan da ƙanƙanin lokaci ma kuwa”.

Gyara zama Hajiya Kubra tayi tare da kallon Naseer tace.

“Toh yanzu me yarage acikin kayan Auren nan ba asaba!?”.

Ajiyar zuciya Naseer ya sauƙe tare da cewa.

“Kayan Aure kam yanzu ai kusan an gama komai kawai yanzu
gishiri da goro za asiya sai kuma sadaki i think suka ɗaine suka rage”.

Kai Addah Hindu ta gyaɗa
tare da faɗin.

“Eh saura kayan rufi ba ahaɗa ba”.

Kai ya jinjina kana yace.

“Toh badamuwa yaushe za akai?”.

Kallon akwatunan tayi kana ta kallesa numfashi ta fesar ta
da sakin murmushi tace.

“Idan Allah ya yarda nan da sati za akai saura gyalullulka
dana aika akawo min daga Kano basu iso ba tukunna”.

Kai ya gyaɗa kana yace.

“Toh ba matsala sai sun iso”.

 

Bayan Moddibo da Abba sun idar da sallar Azahar Amasallacin
Kofar gidan Abba kai tsaye gidan Ummi suka nufa bayan sun isa Moddibo yayi
Parking suka fito daga motar kana suka tsaya daga coumpund ɗin Moddibo yayi
sallama daga ciki Malam Ahmad ya amsa kana ya fito ganin Abba yasa ya faɗaɗa
Murmushin fuskarsa tare da cewa.

“A’a Alh Bashir yau har da kaine agidanmu sannu da zuwa
sannu da zuwa maraba lale ku iso mana”.

Kai Abba ya girgiza kana yace.

“A’a nan ma yayi”.

Ahankali malam Ahmad yace.

“A’a bakomai Abban Jameel mu shiga mana ai an zama ɗaya haba
dai mushiga dan Allah”.

Murmushi Abba yayi cikin sanyin murya yace.

“Toh shikenan Nagode”.

Sannan suka nufi falon Ummi Asma’u dake zaune ta miƙe tare
da yi musu Barka da zuwa kana ta koma kichen ta dauki Plate ta kawo musu ruwa
da drinks da kuma Fruit ta ajiye masu kana ta Gaishe su cike da ladabi.

Ahankali Moddibo ya jingina bayansa da jikin kujera ya
lumshe idanunsa baki ɗaya ya tsani garin Gembulan da jahar Taraba ji yake
tamkar ana yayyafa nasa garwashin wuta ajiki baiƙi ace ko yaushe yana ɗaki baya
fita ko ƙofar takashi ba.

 

Ummi dake Bedroom zaune kan Sallaya ta miƙe ta fito jin
muryan Asma’u na gaishe da Moddibo kana tace.

“A’a Moddibo ne”.

Ganin Abba zaune yasa ta tsaya cike da Mamaki tace.

“A’a Alhaji Bashir”.

Cikin sanyin murya Abba yace.

“Na’am Fatima”.

Kallonta Malam Ahmad yayi sanye take da hijabi har ƙasa
hannunta riƙe da Carbi cike da kulawa yace.

“Ki ƙara so mana ku gaisa”.

Kai ta gyaɗa tare da ƙarasawa ta zauna daga gefe.

 

Anutse Moddibo ya daga kai ya kalleta kana yace.

“Ummi ina yini”.

Kallonsa Ummi tayi ba tare data amsa gaisuwar ba tace.

“Babana jiya duk  baka
leƙoni ba”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.

“Eh Ummi”.

Cikin sanyin murya tace.

“Kuma na kira wayarka baka ɗaga ba sai nayi tunanin ko kana
bacci ne?”.

Kai ya girgiza tare da sunkuyar da kansa ƙasa yace.

“Kuma Ummi ban kulaba ban miss call ɗin ba”.

Jinjina kai tayi tare da fadin.

“Ayyah”, Kana suka gaisa.

 

Anutse Abba ya kalleta tare da cewa.

“Fatima ina yini”.

Ahankali ta gyara zamanta tare da faɗin.

“Lafiya”.

Cikin sanyin murya yace.

“Ya muka ƙara ji da haƙuri”.

Lumshe Idanunta tayi kana tace.

“Haƙuri ya zama dole”.

Jinjina kai yayi tare da cewa.

“Toh Allah yajiƙan Jameelu Ubangiji ya masa rahama”.

Baki ɗayan su suka amsa da Ameen ya Allah.

Gyara zamansa yayi kana yace.

“Fatima kada ki yiwa Jameelu kuka ki tayi masa addu’a shine
abinda ya dace kinji ko?”.

Kai ta gyaɗa tare da sunkuyar da kanta ƙasa tace.

“Insha Allahu bazan yiwa Jameelu na kuka bai Insha Allah zan
ta binsa da addu’a”.

Kai ya gyaɗa tare da faɗin.

“Hakan yafi”.

 

Anutse ya gyara zamansa tare da kallon Moddibo da kansa ke
ƙasa kana ya kalli Ummi da itama still Kanta ke ƙasa ajiyar zuciya ya sauƙe
kana yace.

“Dama nazo da Moddibo ne inne ma masa uzini awajenki”.

Cikin sauri ta ɗago kanta tare da Kallonsa tace.

“Izinin me kuma?”.

Numfashi ya fesar tare da cewa.

“Dama Abune da yashafi kasuwanci na acan Company mu na
Marocco wanda Jameelu ne yake komai na Company nin toh kuma yanzu kin gani
Allah ya dauke mana Jameelu”.

Cikin sauri Ummi ta lumshe Idanunta tare da gyara wuyan
hijabinta.

 

Abba ya cigaba da cewa.

“To Kuma Manager company shima ba shida lafiya toh sun nemi
da Inje kuma nima bana jin daɗin jikina bazan iya zuwa ba”.

Ahankali Ummi ta ɗago kanta tare da kallon sa gani tayi baki
ɗaya ya rame ya zama wani so silent dashi.

Cikin sanyin murya da tausayawa tace.

“Toh Abban Jameel Idan bamu sa haƙuri aranmu ba ya zamuyi ka
kwantar da hankalin ka Ubangiji Allah yajiƙan Jameelu shine kawai fatan mu da
addu’ar mu”.

Kai ya gyara tare da sauƙe numfashi yace.

“Insha Allah zan kiyaye.

Yanzu mshawan jinin ne baki ɗaya yasani agaba duk kan
magungunan da nake sha sai yazama kamar basa min aiki”.

Jinjina kai tayi cikin sanyin murya tace.

“Allah ya sawwaƙa amma ka rage tunani koda kana shan magani
idan baka rage tunani ba ba zaiyi aiki ba”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana yace.

“Toh Fatima ya zanyi idan banyi tunani ba!?”.

 

Ahankali ta sunkuyar da kanta hawaye na zuba daga idanunta.

Gyara zama Abba yayi cikin sanyin murya yace.

“Toh dama shine nake so Moddibo ya wakilceni yaje shine yake
cemin bawai zuwan bane baya so amma baya so yayi nesa da Umminsa”.

Ahankali ta ɗago Idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye ta kalli
Moddibo murmushi tayi kana tace.

“Ba komai Babana kaje wannan ma ai abin farin ciki da
al’fahari ne zaka cika burin da Jameeluna yake son cikawa. Ubangiji Allah yakai
ka lafiya ya dawo da kai lafiya Allah ya maka albarka”.

Cikin sanyin murya da tausayawa Moddibo ya amsa da Ameen
asaman laɓɓansa.

Ahankali Ummi ta cigaba da cewa.

“Insha Allah zanyi ta binka da addu’a ba komai Babana ai
muna tare ina nan ina Marocco amma idan ya gama zai dawo ko?”.

Ta ƙarasa maganar ta sigar tambaya tana kallon Abba.

 

Kai Abba ya gyaɗa mata kana yace.

“Eh zai dawo Insha Allah bazai wuce sati biyu”.

Jinjina kai tayi tare da kallon Moddibo kana tace.

“Badamuwa Babana ai zamu nayin waya”.

Kai ya gyaɗa tare da cewa.

“Shikenan Ummi ba matsala tunda kin amince.

Murmushi tayi still Idanunta cike da ruwan hawaye tace.

“Na amince Babana Allah Ubangiji ya kaika lafiya Allah ya
dawo da kai lafiya Allah yasanya alkhairi da albarka acikin tafiyar.

Ahankali yace.

“Ameen Ummi”.

 

Ajiyar zuciya Abba ya sauke tare da kallonta kana yace.

“Yanzu  kuma sai batun
kuɗin ku da aka har haɗa”.

Sunkuyar da kai Ummi tayi Atake hawaye suka cigaba da zubowa
daga Idanunta cikin raunin murya tace.

“Toni me zanyi da kuɗin nan ne Abban Jameel?”.

Kai Abba ya Girgiza cikin rawan murya da rauni yace.

“Toh nima ɗin idan kun barsu awajena me zanyi dasu ga kuɗin
Aliyu ga naki kowa ya karɓi kuɗin sa kowa yana da bukatarsa motar ki da
Sarƙoƙinki kika siyar ki sayi wata mota amfani dashi”.

Kallonsa ya mayar kan Moddibo kana yace.

“Kaima Moddibo ka karɓi kuɗin ka ka sayi mota sannan sauran
kuɗin kayi abinda ya dace dasu”.

Kai Moddibo ya girdiza ciki rauni yace.

“Abba me zanyi da kuɗin?.

Ai kuɗi na gama abinda ya dace inyi dasu Babu abinda zanyi
dasu tun da har basu tseratar min da J ɗina ba wani amfani zasu yimin?”.

Cikin rauni Abba yace.

“Bakomai Moddibo ka karɓi kuɗin nan idan ka barsu awajena
kun barmin tashin hankali da damuwa”.

Jinjina kai Malam Ahmad yayi tare da faɗin.

“Kuyi hakuri duk kan tsanani yana tare da sauƙi addu’a kaɗai
zamuyi wa Jameelu amma kamar yanda yace ne Moddibo ka karɓi kuɗin nan sannan
kema Fatima ki karɓi kuɗin na shine abu mafi a’ala”.

 

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe kana yace.

“Yawwa shine dai ki bani account number inyi Miki transfer”.

Kai Ummi ta shiga Girgizawa hawaye na kwaranya daga
Idanunta.

Ganin haka yasa Malam Ahmad ya karbi wayarta tare da fito da
account number ya faɗawa Abba Atake Abba ya mata transfer kuɗinta Naira million
goma da dubu ɗari takwas kasancewar yana da account number Moddibo Shima Atake
ya Masa transfer kuɗinsa.

Anutse ya gyara zamansa tare da Kallonsu cikin sanyin murya
yace.

“Nagode da halarcinku agareni musamman ma kai Moddibo Allah
Ubangijin ya biya da mafificin alkhairi”.

Atake Moddibo yaji wani irin rauni ya mamaye sa kallon Abba
yayi muryarsa na rawa yace.

“Abba akan J ne kake min godiya?”.

Numfashi Abba ya fesar tare da sauƙe ajiyar zuciya yace.

“Toh Aliyu ya zanyi kayi min halarci duk kan inda Aboki na
gari ya cika ka cika Ubangiji Allah yasaka da alkhairi Nagode da halarcin ka”.

Cikin raunin murya Moddibo yace.

“Ameen Abba”.

Kallon Ummi Abba yayi kana yace.

“Toh insha Allah sammako zaiyi ya tafi kinsan akwai tazara
tsakaninmu da Adamawa kuma can zai shiga jirgin zuwa Abuja”.

 

“Toh Allah ya kaimu Allah yakai ka lafiya Babana Allah ya
kareka”.

 

Cikin sanyin murya yace.

“Ameen Ummi”.

Miƙewa Abba yayi tare da cewa.

“Toh bari mu tafi”.

Godiya suka masa har sun fita Ummi ta miƙe tare da bin
bayansu abakin barandar ta tsaya tare da cewa.

“Babana amma ai zaka dawo daddare muyi sallama ko?”.

Jinjina kai yayi kana yace.

“Insha Allah Ummi zan zo”.

Bayan sun fita kai tsaye gidan Malam Arɗo Abba ya ajiye
Moddibo zaiyi masa sallama kana Abba ya wuce gida.

 

Cikin sanyin jiki Khausar ta isa Bedroom din Mommy,  a hankali ta zauna agabanta cikin Muryan kuka
tace.

“Mommy kiyi haƙuri kada kiyi fushi dani”.

Tsira mata Ido Mommy tayi ba tare da tace Uffan ba.

Cikin raunin murya Khausar ta haɗa hannunta waje ɗaya kana
ta fashe da matsanancin kuka da sheshsheƙan tace.

“Mommy dan girman Allah kiyi haƙuri ki daina fushi dani”.

Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da fesar da nunfashi kana
tace.

“Khausar to ni me zan ce miki?.

Bani da abinda zan ce miki tunda ai hukunci ne kin riga da
kin gama yanke shi baki nemi shawarata ko izinina ba”.

Girgiza kai Khausar tayi hawaye na cigaba da kwaranya daga
Idanunta.

Ita kuwa Mommy kauda kayi tayi gefe kaba ta cigaba da cewa.

“Kawai kin fadi maganarki gaba gaɗi, sannan koda akeɓance
baki taɓa faɗa min tsakanina ni dake ba, sai da kika zaɓi cikin mutane sannan
kika faɗa saboda ki kunya tani kin bani mamaki ban taɓa zaton haka daga gareki
ba”.

 

Khausar kuwa kai take Girgiza cikin muryan kuka mai gunji
kana Muryanta na rawa tace.

“Mommy nima ina tsoron Modibbo bafa, dan nasan baya sona”.

Kallonta Mommy tayi cikin da mmki ta tsareta da ido tare da
cewa.

“Toh kina tsoron Auren Moddibo kuma, akan wani dalili zaki
ce zaki Aureshi? Kuma bayan kina sane baya sonki”.

Sunkuyar da kai ƙasa tayi cikin gunjin kuka ta lumshe
Idanunta tare da taune Lip ɗinta cikin raunin murya tace.

“Mommy wasiyyar Yah Jameel ne Yah Jameel ne ya roƙi al’farma
awajena sannan tun lokacin daya faɗa min yace min wasiyya ya barmin yace koda
ya mutu kada in manta ya nemi wannan al’farma awajena”.

Sai kuma ta kasa ci gaba da mgnar  sakamakon kuka da yaci ƙarfinta hannu ta
sanya ta goge hawayen fuskarta wani na sake zubowa Muryanta na rawa ta cigaba
da cewa.

“Aranan da za’a ɗauke Yah Jameel bayan mun taho amota yace
min yana neman alfarma awajena in na ɗauka Alfarman da yake nema awajena tamkar
wasiyya ce”.

Sai kuma ta kife kanta kan cinyar Mommy tana mai sakin wani
irin raunataccen kuka murya na karkarwa taci gaba da cewa.

“Mommy a ranar a gabana Yah Jameel yayi ta kuka kamar yaro
ƙaramin ya rinƙa haɗani da Allah da Manzonsa cikin sanyin murya da neman
alfarma yace dan Allah kada ince bazan yi masa ba yana so koda bayan Ransa in
Auri Moddibo”.

Kallon ta kawai Mommy keyi bako ƙyaftawa yayinda itama hawaye
ke zubo mata.

 

Cikin sheshsheƙan Kuka Khausar ta lumshe Idanunta tana tuna
lokacin da suka kasance da M Jameel amota yana faɗa mata magana da sauri ta
sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta kana muryanta na rawa tace.

“Mommy alokacin Cike da damuwa na kalli Yah Jameel nace ya
Jameel Meyesa kake Fadar haka Meyesa kake magana me karyar da zuciya dan Allah
kada kace wasiyya nidai ka faɗi ko wace irin alfarma kake so zanyi maka domin
kafi ƙarfin alfarma awajena”.

Taja hanci tare da kallon Mommy da yanayin ta ya sauya
Muryanta na rawa kana numfashinta na fusga tace.

“Sai yace min Khausar koda ace kin riski labarin mutuwa ta
ki tuna da Alfarman da kuma Wasiyyar da na bar miki ki Auri Moddibo idan kuma
Allah yasa ina raye zanfi kowa farin cikin ganin An ɗaura Aurenki da Moddibo”.

 

Ahankali Mommy ta sun kuyar da kanta ƙasa cikin wani irin
yanayi na tsananin tausayawa da kuma tsoron Allah Mabuwayi gagara Misali
tol-tol haka hawayenta ke zuba jin Khausar taci gaba da cewa.

“Mommy Yah Jameel ya faɗa min cewa ya fadawa. Kakar Moddibo
cewa dan Allah ayi Aurena da Moddibo Mommy dan girman Allah ki tayani cikawa
Yah Jameel Wasiyyar daya barmin bani da abinda zanyi masa a wannan duniyar
wanda zaisa Yah Jameel farin ciki amakwancinsa sama da in cika masa burinsa
naji na gani zan rayu da Moddibo duk da nasan ya tsaneni zan rayu dashi sabida
darajar Yah Jameel da wasiyarsa zan juri dukkan uƙubar da Moddibo zaimin koda
kuwa zai kasheni zan zan cikawa Yah Jameel burinsa”.

Cikin sheshsheƙan Kuka da fisgar numfashi tace.

“Mommy wannan buri da fatan Yah Jameel ne dan Allah da
Manzonsa ku barni in cika masa burinsa, tun da muke rayuwa da Moddibo
Amakaranta yace ko yaushe kallon mu yake amatsayin mata da miji yace bashi da
buri sama da wannan Mommy yace min da ɗan Adam yana da zabi idan ajalinsa yazo
to da zai roƙa ajinkirta masa ajalinsa yaga kasancewa ta da Moddibo a Inuwa ɗaya
a gidan aure”.

Sai kuma tayi saurin dafe ƙirjinta jin yanda numfashinta ke
fusga.

Ta sauƙe wani irin numfashi tare da dafe kanta kana ta
cigaba da cewa.

“Yace min Khausy zanso naga wani irin zama zakuyi keda
Moddibon.

Yace min  zaiso ace
Allah ya bashi Aron Rai ya rayu ya ganni gida ɗaya a Inuwa ɗaya da Moddibo yaga
wani irin Rayuwar aure zamuyi koda na wuni ɗaya ne.

Allah sarki ya Jameel ashe bazai ganiba.

Dan Allah Mommy ki barni in cikawa Yah Jameel burinsa Mommy
Dan Allah kiyi haƙuri ki barni in cikawa Yah Jameel Wasiyyar sa”.

Taƙarashe mgnar tare da fashewa da matsanancin kuka mai
masifar ƙuna da ɗaci sai kuma tace.

“Mommy wallahi ina tsorin son Moddibo har Raina, kawai na faɗa
ne domin kada Hajja Nana tace dole sai na Auri Yah Aliyu shiyasa na faɗa
alokacin, amma bawai dan in kunya taki bane Mommy kinfi kowa sanin halina banyi
hakan da wata manufa ba face cika wasiyyar Yah Jameel”.

 Numfashi mai tsawo
taja cikin Muryanta da baya fita tace.

“Mommy ina matuƙar girmama Yah Jameel Mommy Ina so in cika
Masa burinsa wannan shine wasiyyar Yah Jameel na karshe kuma shine karshen
maganarmu dan Allah ki tayani cika masa wasiyyar sa na roƙeki”.

Wasu irin hawaye masu zafi ne suka fara bin kuncin Mommy
cikin sanyi da raunin murya tace.

“Insha Allahu Khausar da izinin Ubangiji za acikawa Jameel
burinsa…!

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply