Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 1


Sakon So 1
Viral

EPISODE 1️⃣

 

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

~Masjid Ibn Taymiyah~
Aka rubuta ajikin babban masallacin dake cike makil da jama’a kowa yaci manyan kaya manyan shaddoji da kanagani kasan daurin aure ake shirinyi, wani matashin saurayine ke sanye da manyan kaya dakuma babban Riga na shadda datasha aiki yana tsaye daga ta wajen masallacin yana kallon agogon hannunshi da alamu lokaci yake dubawa chan kuma yadago kanshi yana leken kan titin da masallacin ke kai, tabashi akayi daga baya dayasa dasauri ya waigo wani matashin saurayine yatabashi shima yana sanye da manyan kaya yasha hula kube, cikeda damuwa yace “he’s 20minutes late Arif kazo mutafi koda na’ibin limamum masallacin nanne ya karba maka Auren, duk an taru mutum daya ake jira haba mana is not cool” girgizamai kai wanda aka kirada Arif yayi yace “I know he will come let’s just give him some time, Uncle Hamma is just…..” dasauri abokin yace “sociopath” wani mugun kallo Arif yamai zaiyi magana daidai wata Babban jeep na parking abangaren masallacin dayadan sami space na parking, wani kalan walwala ne ya bayyana akan fuskan Arif baisan lokacin dayabar abokin nashi yafice daga cikin premises na masallacin dasauri ba dudda jama’a na kwalamai kira ta ko’ina suna ango ango baibi takansu ba yay wajen motan dayake nan bamaka ganin kowa na ciki sabida tinted glass ne duka kuma arufe, ahankali yasa hannunshi batare daya jiraba yabude gaban motan bangaren mazaunin direba tareda tsugunnawa har kasa cikeda girmamawa batare dayama kalli fuskan mutumin dake cikin motanba yace “barka da zuwa Uncle Imran” wani magidancin mutum ne zaune cikin motan da akalla zaiyi 48/49yrs yana sanye dawani soft milk yadi daya haska bakar fatanshi dake bala’in sheki tsabagen hutu.

Yanada cikan gashin gemu sosai gasunan baki sidik masu tsayi kadan dawasu sirarren saje dakenan a kwance suma lublub, ga cikan gashin gira dakuma suman kai dudda lafiyayyan hulan minister na kanshi hakan bazaisa kagane cewa yanada cikan sumaba, yanada wasu kalan kananun yet manyan idanu idan ya zubamaka su idanba ka natsu ka kalleshi ba zaka dauka idanun nashi a lumshe suke amman abude suke ras kwayan idanun farare fat, hancinshi dogone sosai kuma siriri sai lips dinshi dakenan jazur, kallo daya yama Arif dake tsugunne kanshi akasa babu wani murmushi ko fara’a akan fuskanshi sannan kuma babu wani bacinrai ko wani yanayi akan fuskanshi saima fuskanshi dake nan adake dake lullube dawani kalan warm rahama akai, kaman baiso yay magana yace “Arif” wani kalan murmushi Arif din yasaki cike da mugun girmamawa yace “na’am Uncle Imran” tareda dago kanshi yadan kalleshi saikuma yasake sauke kan nashi kasa dasauri baitaba ganin mutumin dake tattare dawani kalan mugun kwarjini dakuma haiba irin na Uncle Imran ba, duk yanda kakai ga bushewar idanunka baka iya kallon tsabaragen idanun Uncle Imran kamai, Ahankali kaman baiso yay magana cikeda wannan natsuwan yace “get up kayanka will get dirty” tashi Arif yayi babu gardama still kanshi na kasa hakan yasa anatse ya sauko daga cikin motan yafito ya tsaya kusada Arif duk tsayin Arif akafadar Uncle Imran yake dan Uncle Imran giant ne sosai, dudda babba ne shi ya manyanta amman jikinshi da gabobinshi gabaki daya atsaye suke tsaf kana ganinshi kaga wanda yake gyara jikinshi ta hanyar cin lafiyayen abinci dakuma excercise, yana sanye da babban riga dake kyalli da wandonshi daya tsayamai a daidai idanun sahu, kafanshi na sanye da ankle sock dake cikin wani givency covershoe dake sheki sosai, juyawa yayi yadauko wani bakin glasses dan idanunshi basason haske sosai yasaka sannan yakalli Arif dakanshi ke kasa yace “muje ko”? Gyadamaikai Arif yayi yace “to bismillan mu Uncle” yay maganan suna jerawa tunda yake baitabajin mutum dake kamshin turare kwatankwacin irin turaren Uncle Imran ba, turaren Uncle Imran nada bala’in dadi gasu da sanyaya rai, tun kafin su karasa cikin masallacin mawaka da maroka kemai wake wanda ko kadan bayaso hakan yasa baice musu komiba koyabasu kudi ba yawuce suka shiga masallacin nan da nan abokin Arif yace “waliyin Arif ya iso” karasawa sukayi cikin aka zazzauna nan da nan aka daura aure tsakanin Arif da Salma akan sadaki 500k wanda Uncle Imran yabiya mishi akai addu’a ana gamawa ko sec daya tal bai karaba yamike yajuya Arif yatashi dasauri yabishi abaya, abokin Arif yataba wani abokinsu da duk sukabi Arif da Uncle Imran din dasuka fice daga masallacin da kallo yace “dan Allah jibi Arif saikace yaga God” dayan abokin mai suna Muhammad yace “to ai kusan hakane wannan Uncle din nashi shiyamai komi aduniya tundaga primary school konine abinda yafi hakama zanmai wlh Aliyu tunda mahaifinshi ya gudu yabarsu bai kuladasu ba” tabe baki wanda aka kirada Aliyun yayi yace “bakasan waye mutumin nan ba idan kasan irin kalan bakin girmankan dayake dashi saikai mamaki bakaga yanda babu wanda yagaida a masallacin nan ba sai uban dingile wando shi adole ustazu da ijiye gemu” wani kallo Muhammad kema Aliyu yace “waikai Ali me mutumin nan yamaka ne danni wlh banga aibunshi ko daya ba”? Mugun kallo Arif yama Muhammad yace “bazaka gane bane waini mutumin nan zai hana aiki sabida wai inashan taba yay rejecting application dina a company shi, shi wayasan kalan abubuwan dayayi lokacin dayake matashi yana soja kafin yay retire”? Kalan kallon da Muhammad kemai yasa yace “me to ai gaskiya nafadi ni to even tell you the truth gwara dabai daukeni ba dan ance mahaukaci ne tuburan tuburan saidai in alluran sojojinshi basu tashi ba wlh bakaga saisa har yanzu babu wacce ta yarda ta aureshi ba sai tsufa yake agidan tsohuwarshi” wani mugun harara Muhammad yamai yace “kainedai kaga tsufan dan ni bangani ba wlh ko mahaifin Arif daya girma yafishi tsufa, haushin shi kawai kakeji sabida yahanaka aiki dayayi, kuma aure dabaiyiba shine baiyi niyya ba tunda akazo har gida aka kashemai mata da yara biyu” dasauri kaman jira Aliyu yake yace “kasan shekara nawa yanzu da mutuwansu? This is the 13th year amman har yanzu bai kara aure ba, wlh basabida mutuwan matanshi bane ba, matsalan haukanshi yasa babu wacce ta yarda ta aureshi” zai cigaba da magana ganin Arif na tahowa wajensu yasa yay shiru yamike tsaye yana kakkabe rigan jikinshi.

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply