Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 23


Sakon So 23
Viral

EPISODE 2️⃣3️⃣

 

Wanka yashiga yafito ya shirya cikin wasu milk pajamas masu bala’in kyau yazauna kan gado, drawer jikin gadon yajawo yadauko wani babban english novel na UK mai suna the soulless love, wani akwati yabude na glasses yabude yaciro wani white glass yasaka sannan ya jingina da gadon tareda kashe wutan dakin yakunna wutan side lamp kadai ya jingina da gado tareda jan bargo ya lullube kafanshi yabude book din yafara karantawa yanajin kukanta sama sama dan daga nan dakinshi yakanji abinda ke faruwa acikin dakinta, almost 2hrs yayi yana karanta book din sannan ya maida yarufe ya ijiye saman drawer ya kwanta ahankali yanaso yay bacci amman baya iyawa kuma bayaso yanashan magungunan shi, dan lumshe idanu yayi yabudesu jin ko’ina tsit that means tayi bacci kenan, wayanshi yadauka ahankali yabude wani locked folder hotunane aciki na wata black beauty mata maidan jiki kaman yanayin girman Anty Binta, kaganta kamanninta da Kausar daya sak kaman tayi kakin Kausar ta tofar, lumshe idanunshi yayi ahankali yabudesu yasake daurawa akanta yatsanshi yakai kan fuskanta yana shafawa murya chan ciki yace “I’ve missed you Muna, why did you have to go and leave me alone at this stage of life” shiru yayi tareda lumshe idanunshi again yaja wayan yakaishi kirjinshi ya rungume tsamtsam.

Karfe uku daidai kaman wata mayya tabude idanunta sabida azababben yunwan datakeji kaman wacce ta kwanta bataci abinci ba tsabagen yanda tasaba cin abinci tsakar dare, ga kanta dake wani kalan sarawa hancinta taji yatoshe da majina hakan yasa dabaki take numfashi ma, ahankali tabi dakin da kallo dan wutan dakin a kunne yake, saukowa tayi daga gadon dasauri zuwa wajen kulolin dake dakin tashiga budewa amman babu komi cikinsu dan tas tacinye komi jiya da daddare, mikewa tayi tsaye tana kallon kofan dakin gabanta na faduwa saikuma ahankali tai wajen kofan gabanta nawani kalan mugun faduwa bude kofan dakin tayi kadan ta leka wutan corridor a kunne hakan yasa tafito da sauri tana gyara daurin towel din kirjinta kanta ba dan kwali, waigawa tayi takalli falon saman gabaki daya babu kowa ko’ina tsit, tafiya tafara ahankali tana taba cikinta da har wani ciwo ciwo yake mata yanadan kugi sabida yunwa stairs tayi tafara sauka tana kallon falon da wutanshi akashe yake gabanta nawani kalan fadi har hadiye yawu take tana sauke ijiyan zuciya takarasa sauka tana tafiya sadaf sadaf kaman wacce zatai sata tayi dining area dayake akwai dan haske dake haskowa daga wutan falon sama, ahankali kaman mai sata tashiga bubbude warmers na abinci dake kan dinning table din tana dubawa ganin akwai naman kaza soyayye dayawa dakuma rice a warmers din yasa tajuyo ahankali zata dauki plate daka cikin dankin wankakkun plate din dake kan dinning table din, mutum tagani tsaye abayanta yay folding hannunshi akirji kaman gunki, wani kalan zaro idanu tayi tawani kalan bude baki zata kwala ihu danta bala’in tsorata cikin zafin nama Abee yawani kalan fizgota tawani fado jikinshi taredakai hannunshi kan bakinta yarufe gam dan yasan tana ihu Hajiya zata farka dan batada nauyin bacci ko kadan tafito tagansu anan and that’s the last thing he needs now, cikin wani kalan low voice kaman mai whispering yace “don’t you dare scream” wani kalan zaro manyan cat eyes dinta take tana kallon fuskanshi dadan haske kadan din dake wajen wanda yazo daga falon sama jikinta ko’ina rawa yake jin gabaki dayan jikinta na manne danashi banda fuskanta dake facing nashi takasa kwace kanta gashi yataushe mata baki kamshin dayake narawa ni ratsa mata hanci, wani kalan kallon kwayan idanunta data zaro yake dudda the place is dark amman harwani kyalli suke, yanda yake kallonta batare daya zare hannunshi daga bakinta ba yasa taji wani kalan natsuwa nashiganta ahankali jikinta yadaina rawa hakan yasa tasaukar da idanunta kasa ahankali danta kasa jure idanunshi akanta, kaman wanda yatuna wani abu zare hannunshi yayi dagakan bakinta dasauri tareda tureta daga jikinshi tangal tangal tayi zata fadi tabuge da table kaman wacce batada stamina dasauri yakama hannunta yarike hakan yasa bata bugeba adan kufule yace “what are you doing here”? Dan kallonshi tayi adan tsorace akuma hankali cikeda sigan shagwaba tace “I am hungryyyy” tai maganan tana kokarin kwace hannunta daya kama dayasa taji hannun yamata wani iri, sakin hannun yayi shima dasauri strictly yace “go back to ur room” kwabe kwabe tayi da fuska kaman zatai kuka saikuma tawuce dasauri batare datace komiba takoma sama kanta na bugawa sosai, shiga dakin tayi batare data kulle kofanba dan tsoro takeji takoma gado tazauna tana dafe kanta dakemata ciwo sosai tana numfashi da baki, kugin da cikinta yayi na yunwa yasa ta kwanta ahankali kan gadon tareda kife cikinta tajuyayar da fuskanta tana kallon mirror ta hakan yasa tajuyama kofan baya ahankali tana lumshe idanu wasu zafafan hawaye na sauko mata daga idanu sabida shegen yunwan datakeji gashi yakorota ciki, almost 5min tana kwance ahaka kaman daga sama taji kamshin turaren mai dadi nashiga hancinta dudda muran datake hakan bai hanata jin dadin turaren ba, ahankali tajuyo da kanta batare data tashi zaune ba dantaga waye yashigo dan ko kadan bataji alamun tafiya ba, Abee tagani tsaye bakin kofanta dauke da tray a hannunshi yana kallonta ba yawo ba fallasa, dawani kalan sauri takai hannunta tashare hawayen dasuke kwance kan fuskanta sannan ta yunkuro ta tashi zaune dan dafe kanta tayi tareda yatsine fuska sabida ciwonkan dataji kaman kanta zai tsinke yafadi, daukekai yayi daga kallonta batare daya shigo dakin ba yace “tashi kisa kaya” babu musu ta tashi gaban wardrobe taje tabude wani dogon rigan bacci tadauka sannan tajuya tadan saci kallonshi ganin yana tsaye inda yake har lokacin yasa ahankali tazo tawuce bathroom tamaida kofan tarufe, towel din jikinta ta cire tayi hanging sannan tasaka rigan baccin peach ne very decent ya tsaya mata iya knees dinta rigan yamata kyau sosai gadan katon tebanta daya fito daga rigan, gashin kanta dukya kara hargitsewa sabida yanda tasaka rigan dagaka, bude kofan tayi ahankali taleko cikin dakin, baya dakin amman ya ijiye mata tray abincin akan carpet, jellof rice ne da naman kaza kusan 5 akai sai tururi suke alamun yamata microwaving sai goran ruwa akan tray mara sanyi da spoon, da wani kalan sauri tafito har murmushi take ganin abincin zama tayi tadauki spoon dasaurinta zata fara ci daidainan aka sake bude kofan dakin dasauri tadaga kanta daidai tanakai rice bakinta hada ido sukayi da Abee dake rikeda kwalin magani guda biyu a hannunshi, ahankali tasauke kanta kasa tana ijiye spoon na abincin dazata kai baki tarasa mesa dazaran taganshi she use to become restless yatsunta tashiga wasa dashi batare dako motsin kirki takarayiba, karasowa cikin dakin Abee yayi har zuwa gabanta ya tsaya tareda ballo paracetamol biyu da actifed guda daya murya chan kasa kaman wanda bayason yay magana yace “take” dan kallonshi tayi ganin kallonta yake ba wasa kan fuskanshi yasa kaman wata yar yarinya tabashi hannunta, palm dinta yafara kallo sannan yasamata pills din aciki raurau tayida idanu tana kallon magungunan babu abinda ta tsana arayuwanta kaman magani, bottle water daya kawomata mara sanyi yadauka yabude yabata hannu tasa takarba shima sannan tadan kalli fuskanshi kaman mara gaskiya awani irin hankali akuma tsorace tace “in sha?” Wani mugun kallo yamata yace “no kishafa” raurau tasakeyi da idanu, sannan ahankali ta daura pills din kan cinyanta tadauki guda daya rak acikin guda ukun tana kallo sannan takalli fuskan Abee adan tsorace ganin ita yake kallo yasa dasauri ta dauke kanta takai maganin ta wurga baki taredakai ruwa ta kurba wani kalan kakarin amai tahau yi Abee dake kallonta yace “kikamin amai anan saikin lasheshi tass” yay maganan yana fizge ruwan daga hannunta ganin tana shirin zubarwa, sauran pills din yadauka daga kan cinyanta yarike a hannunshi sannan yakai ruwan bakinta ahankali yace “open your mouth” babu musu tabude bakin zuba mata ruwan yayi aciki sannan yace “raise your head” daga kanta sama tayi sannan yadan matso kusada ita faduwa gabanta yashigayi sosai amman tadaure, watsa mata pills din acikin bakin yayi dasauri tahadiye tana wani kalan tabe fuska da baki kaman taci kashi tadauki spoon tadebi rice dasauri takai bakinta tanaci hawaye yayi fall acikin idanunta, AC dakin yakalla ganin akashe yasa yakalleta har lokacin tabe fuska take irin na wanda yasha magani yace “da ruwan sanyi kike wanka”? Kaman daga sama taji tambayan, dan kallon fuskanshi tayi saikuma ta gyadamai kai ahankali kafin tadauke kanta tace “ban iya kunna ruwan zafi ba” dan shiru yayi yana kallon yanda take magana, jin baice komiba yasa tadago kanta hada ido sukayi dasauri tadauke kai, mikewa tsaye yayi yawuce bathroom nata yabude ya tsaya daganan bakin bayin yana kallon ciki bayin is very clean towels ne kusan guda 5 ta shaya ajikin hanger juyawa yayi yakalleta ganin tana zaune inda take bata tashiba yace “sainace kizo zakizo” dago kanta tayi tadan kalleshi saikuma ta taso ahankali dauke kai yayi yashiga bayin tabiyoshi ta tsaya daga nan bakin kofa nuna mata yanda zata kunna hot water yayi sannan yajuyo yace “kingane”? Gyadamai kai tayi ahankali kanta akasa ganin yana tahowa yasa tafice daga bayin dasauri takoma wajen abincinta tazauna tafaraci shikuma yafito daga bathroom din yawuce yafita daga dakin.

Tass tacinye abincin da naman tasha ruwa sannan tahau gado sai bacci.
4:30 Abee yafito cikin jallabiya yatada mutanen gidan batare daya shiga dakin Lujain ba, yawuce masallaci.
Wuraren 7 nasafe Hajiya tafito falo taxauna kan kujera daidai Kausar dake cikin kitchen tafito da kula zata ijiye kan dinning Hajiya tace “Kausar jeki cema Auntyn ki Lujain tashirya tsaf ta sauko Babanku zai kaita yasata a makaranta yau” Gyadamata kai Kausar tayi tawuce sama.

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply