Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 24


Sakon So 24
Viral

EPISODE 2️⃣4️⃣

 

Knocking kofarta Kausar tayi jin shiru yasa tabude kofan dakin akan dadduma taganta dan yanzun nan ta tashi ganin tana salla yasa tace “Hajiya tace ki shirya kizo kasa” tana maganan tajuya tafita daga dakin.
Saida ta idar da salla tai azkar sannan ta tashi bathroom takara shiga tai wanka da ruwan zafi sosai ciwon kan datakeyi yatafi batajinshi kuma saidan hancinta dayay blocking shima kuma yaragu sosai dan tana iya numfashi da hancin yanzu bakaman jiyaba, fitowa tayi daure da towel tazo gaban wardrobe tabude tana kallon kayan wajen, wani abaya tajawo black ne gabaki dayanshi mai kyau kana ganinshi kaga saudi abaya, yauma bata saka bra ba singlet tasa da pant sannan tadaura abayan akai bayan tashafa mai, tadau gyalen abayan tadaura akan yamutsassen gashinta tabude kofa tafito ahankali tafara tafiya chak ta tsaya ganin Abee na hayowa sama idanunshi akanta hakanan jitayi gabanta na faduwa sosai, saida yazo daidai dap da ita bakinta yadan fara rawa takasa ma magana, wani kalan kallo yamata daga sama zuwa kasa sannan yace “go back inside kidauki hijab kisa” yana maganan yawuce yabarta awajen, saida taji karan ya maida kofan dakinshi yarufe sannan tajuya ahankali takoma dakinta, wardobe taje tabude tana kallon hijaban wajen wani maroon hijab tadauka tasaka yamata wani kalan kyau kaman balarabiya ne tasaka hijabin sannan tadauki takalmin da Baba yasaya mata tasaka dan babu wani takalmi adakin shima hala dan ba’asan size nata bane tafito ahankali take tafiya tazo stairs sauke kanta kasa tayi sabida yanda suka cika falon duk ana shirin yin breakfsat tunda tafara saukowa idanun Hajiya kyam akanta maroon hijabin datasaka ba karamin kyau yamata ba deep down tana addu’a Allah yasa suzo juna itada Imrana dan tanamai mugun kwadayin Yar yarinyar nan, murmushi tayi tace “Lujain an sakko” dago kanta Lujain tayi tadan kalli Hajiya wani kalan kunyan matan taji hakan yasa tamaida kanta kasa takarasa wajenta saida tazauna akasa kusada ita murya chan kasa tace “ina kwana Hajiya” murmushi tamata tace “har yanzu muran bai sakeki ba? Duk muryanki ta chanza kinsha magani kuwa”? Gyadama Hajiya kai tayi ahankali, Hajiya tace “waya baki maganin”? Dan shiru tayi dan batasan yaya zata kira sunan Abee ba hakan da Hajiya ta lura yasa tace “Imrana yabaki”? Gyadamata kai tayi ahankali, Abdallah dake saukowa kasa gaban Hajiya yazo yace “Hajiya natafi yau ina azumi bazanyi breakfast ba” yakalli Lujain da kanta ke kasa yace “good morning Anty Lujain” dago kanta Lujain tayi ahankali tadan kalli Abdallah dake kallonta yana murmushi sauke kanta kasa tayi tama rasa mezatace itane wannan babban yakira da Anty, Haiiya dake murmushi tace “Antynku Lujain badai kunya ba” murmushi yayi yace “natafi” “Allah bada sa’a Abdallah” Hajiya tafadi tana hararan Kausar datazo ta zauna gefen kujeran da Babanta ke zama rikeda plate na chips itama ta shirya makaranta hijabi kawai zata saka tafita, fitowa daga kitchen Anty Binta tayi itada Maman Aneesarh ganin Lujain yasa tai wani kalan murmushi tazo wajen suka ajiye kuloli tashafa kumatun Lujain hakan yasa tadago kanta dan murmushi tama Anty Binta tace “good morning Anty” morning Lujain bari nahada miki tea” tea tahada mata a big cup this time sannan tazuba mata chips a plate da fried egg da pepper soup, ahankali tafaracin chips din tanashan tea ahankali dan yanada zafi ba kaman wanda Gwaggo kemata ba, kamshin turaren Abee da yacika falon yasa tasan yasauko ne dan ko kadan bakajin footsteps nashi, zama yayi Anty Binta tace “Ya Imran coffee ko shayi Wanne kakeso”? “Coffee” yafadi ahankali yana duba agogon hannunshi, Hajiya dake kallonshi tace “zubamai da chips da farfesu Binta ni bantaba ganin makiyin abinci irin Imrana ba saisa gashinan Abdallah kaiya dauko” Baice komiba kawo mishi Anty Binta tayi a tray tadaura kan table dake gabanshi coffee yadauka yafara sha daidai nan Kausar tagama tamike takalli Abee shima kallonta yayi yanashan Coffee, kaman zatai kuka tace “Abee ban iya assignment dina ba” wani mugun kallo yamata yace “and u are telling me now” sauke kanta kasa tayi sabida mugun kallon dayamata ahankali tace “Abee kayakuri baran karaba” Hajiya dake jinsu tace “ke wlh fitinanniyan yarinya ce Kausar, ke kinci abincinki kin koshi saida shi yafaracin nashi shine zakimai batun assignment salon karyaci, tunda aka haifeki Babanki yadainacin abinci yakoshi” kaman zatai kuka tace “ai nace sorry ko Abee” ijiye coffee yayi ahankali yamika mata hannu alamun tabashi book din dawani kalan sauri tabude jakanta tadauko book din takawomai maths ne kan probability ne, ahankali yace “come here” kusadashi tazo cikin 2min yanunnuna mata yanda zatayi yamata solving daya yabata second question din yace tayi yagani zama tayi tafara shikuma yacigaba da breakfsat nan da nan tayi takawomai dubawa yayi yaga tayi daidai hakan yasa “now get ready, Hamza na jiranki a car” hada jakan tayi tasa hijabi tafita dagudu, saida yagama breakfast dinshi sannan yatashi yadan kalli Lujain data gama itama amman kanta akasa hakan yasa Anty Binta dake kallonsu tace “tashi kutafi Lujain” tashi Lujain tayi tadan kalli Anty Binta saikuma takalli Abee dake tsaye, juyawa Abee yayi yay kofa yace “Hajiya natafi” Hajiya tace “Allah bada sa’a bishi Lujain” binshi Lujain tayi itama tabude kofa tafito waje duk su Hajiya suka bita da kallo, wajen wata mota daban yayi bmw baka ba jeep din jiyaba budewa yayi yashiga gaba hakan yasa takarasa wajen kirjinta bugawa yake kawai to ina zasuje baya tabude ahankali zata shiga suka hada ido wani mugun kallo daya mata yasa tamaida kofan tarufe tadawo gaba tabude gently tashiga cikin motan gabanta nawani kalan fadi, motan kamshi kaman ba mota ba, ganin credentials nata a motan yasa tadan bude idanunta takalli file din datasan Gwaggo kadai ke boyemata dan awajen Gwaggo suke acikin katon akwatin bununta taboyesu, ga birth certificate dinta, primary certificate dana JSS Ce dakuma na indigen da Nin dinta duka awajen, dan juyawa tayi takalli cikin gidan to Gwaggo tazone batasani ba, bude musu gate akayi suka fice dudda motan tinted ne gani take kaman zaa ganta hakan yasa ta sauke kanta kasa, sun danyi tafiya mai nisa wani hadadden school yakaita da baida wani nisa sosai da company shi yasan mai school din sosai childhood friend nashi ne, kashe motanshi yayi a parking space yasa hannu yadauki file nata yabude kofa yafito, kasa bude kofan tafita tayi sai kallon cikin school din take da student keciki gabanta nafaduwa yanzu nan ma za’a faracemata Yar iska ne dan yanzu ko’ina ansanta hawaye ne yacika mata idanu, juyowa Abee yayi ganin bata bude kofaba har lokacin yasa yazo ta wajen bude mata kofan yayi dasauri takalleshi lips nata har rawa suke murya chan kasa tace “ni……banason school, dan Allah kada kasani, wlh banaso” tai maganan hawaye na zubomata daga idanu dasauri takai hannu tashare yana wani kalan kallonta yace “why?” Dan kallonshi tayi saikuma tasauke kanta ahankali tace “nan ma zasuce ni yar iska ce maibin maza, everybody will be looking at me ana nunani ana cewa nice a video nan” fashewa da kuka tayi yace “don’t you dare cry for me anan” dasauri tahadiye kukan tana goge fuskanta da bayan hannunta, cikin kakkausan murya yace “akwai wanda yadaukeki yakaiki sama ne when all the rest of the students na reception akasa? Akwai wayanda yakaiki bayin maza ne?” Girgixamai kai tayi wani abu na tokaremata zuciya, wani kalan dan tsaki yaja yace “kin zaci inason Auren nan da akamin dakene kokuma I fancy you one bit?” Shiru tayi yace “the way I am dealing with you dudda I don’t consider or regard you matata kema haka zaki shiga school din nan deal with anything that comes ur way and study hard” gyadamai kai tayi ahankali tanaji kaman tafashe da kuka danji tayi tabama kanta tausayi, anatse yace “futo” fitowa tayi daga motan ahankali ta matsa gefe maida kofan motan yayi yarufe sannan yakalleta yace “ke” kallonshi tayi kaman yanda shima ke kallonta, calmly yace “karki dauki Auren nan da akamin dake as anything, ke ba matata bace and bazaki taba zama dayaba, as far as Imran is concern I don’t have a wife! Dan haka do whatever you want, idan kinga wanda kikeso talk to him, mingle with your fellow students, dazaran komi settle down zan rabu dakene u will be back to your parents house cus babu abinda zanyi dake” yakarashe maganan yana tabe baki ahankali yace “kin gane”? Gyadamai kai tayi ahankali sotake tayi kuka amman yahanata gaba yayi yace “let’s go” binshi tayi tana tafiya ahankali, gaidasu masu gadi sukayi sannan suka shiga ciki ga mamakinta kusan rabi da kwatan student na makarantan turawa ne kadan daga cikinsu ne yan nigeria, sama sukaje wani babban office yabude yashiga wani babban mutum ne zaune yana ganin Abee yatashi yana bashi hannu yace “welcome Soja, ga waje ku zauna” zama duk sukayi yakalli Abee yace “itane student din”? Gyadamai kai Abee yayi yace “bani file nata” bashi Abee yayi yadudduba sannan yakira secretary nashi yabata tamai photocopy documents nata duka yabaama Abee original, agabanta tanaji Abee yabiya 5.7M school fees nata da kudin textbooks nata da kudin Waec da neco dan yace yanaso tayi a SS2 din nan idan taci shikenan, secretary aka kira ta tafi da ita changing room dan saka uniform shikuma mutumin yacigaba da magana da Abee yace “I assure you this babu wanda zaiyi bullying nata a school dina, her image will be well protected, sannan kaman yanda kamin bayani awaya last night zata dinga special lesson din 4 idan ta tashi saikazo kawuce da ita gida, and lunch dinta will be given to her, kabata one week zakaga tasake jikinta tashiga student da kyau without fear na being bullied ko kirata names, Ya guy din ankamoshi kuwa?” Daidai lokacin secretary tashigo tareda Lujain data saka kayan makaranta skirt ne dark blue da Riga sky blue long sleeve sai jacket dinshi dark blue, dakaramin farin hijab sai farin safa da black shoes, uniform din sun mata wani kalan kyau she looks chubby and sooo cute, tashi mai makarantan yayi yace “Soja muje mu kaita ajinsu tare” raurau tayida idanu tana kallon Abee daya dauke kanshi daga kanta yamike shida mutumin sukai gaba itakuma abaya wani class mai kyau SS2 suka tafi ajin duka turawa ne mutun 3 ne Nigeria sai ita yanzu ta hudu ga teacher a ajin shiga mai makarantan yayi yasa aka mata warm welcome sannan yakaita sit nata agaba tazauna ahankali tasake dagakai takalli Abee dashima kallonta yake wani kalan lankwashe kai tayi ashagwabe hawaye yacika idanunta tam har kyalli suke dawani kalan sauri Abee yabar wajen mai makarantan yasallami ajin yafito yasameshi agaban office suka karasa magana sannan yawuce yafita daga school din yashiga motanshi yawuce company shi that is just few blocks away.

Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;

Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply