Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 35


Sakon So 35
Viral

Ciro wata Yar katuwan jakan Gwaggo Abee yayi daga motan tareda maida kofan yarufe yadan saci kallon fuskan Lujain, today is the first time daya fara ganin all set na cute white short teeth nata duka sabida how happy she is ga dimples dinta dake wani kalan lotsawa kaman ana operating nasu da remote, ta kankame Gwaggo gamgam tareda lumshe idanu kaman wani zai kwace mata ita, dan dauke kai yayi tareda gyaran murya hakan yasa Gwaggo dake murna sosai ta tureta tace “cikani Lulu mun tarema mijinki hanya” sakinta tayi ahankali tana komawa gefenta batare data kalli Abee ba daidai lokacin Hamza da Kausar sun karaso wajen cikeda girmamawa Hamza yace “ina kwana Gwaggo” washe baki Gwaggo tayi tace “kaga yaro mai tarbiya ba irin nawa jikokin ba basu rusunawa idan zasu gaidani” ahankali itama Kausar tadan rusuna tace “ina kwana Gwaggo” wani kalan washe baki Gwaggo tayi tace “ana ganin kwayar idanunki anga na Babanki yaya sunanki yammata” ahankali Kausar tace “Kausar sunana” Gwaggo tace “Masha Allah Kausar ina zaku haka keda Lulu kukaci hijabia kaman matan limamai” murmushi tadanyi ganin Gwaggo is so lively tace “Hadda zamu” dasauri Lujain amugun shagwabe tana kara kama hannun Gwaggo tace “Gwaggo ni barani ba” ba Hamza da Kausar kadai ba har Abee saida yadan kalleta jin yanda tai magana yadauke kai dasauri, irin Gwaggonta tazo din nan mai taremata, itama Kausar dasauri tadan kalli Abee dasauri taje wajenshi hannunshi takama kaman zatai kuka tace “Abee dan Allah muhuta gobe saimuje eh Abee tunda Gwaggo tazo” dasauri Gwaggo tace “da sunana zakuyi amfani kuyi sabon Allah badaniba” saikuma tadan kalli Abee tace “adan barsu suhuta yau ko Imrana” adan kunyace yace “to Gwaggo” yana maganan yawuce rikeda jakan Gwaggo a hannunshi Kausar da Lujain sukahau tsallen dadi Hamza yace “Allah shiryeku” Gwaggo ta tabe baki tace “tayani fadi dan nan yara kiri kiri suki karatu wanda yafi na yahudun dasuke zuwa amfani, nidai ku kaini cikin gida” tai maganan tana mikama Kausar Yar purse dinta tace “rikamin naira dubu uku da dari biyu da hamsin ne aciki dake na yarda nasan baraki cimin ba amman kinga wannan” tanuna Lujain tace “kuran kudi ce” dariya daga Hamza har Kausar sukayi Lujain ta daure fuska sukai cikin gida, daga Kausar har Hamza wani kalan dadin ganin Gwaggo sukaji, wani kalan uban sallama Gwaggo ta rangada afalo Hajiya dake zaune tareda Abee ta amsa tana murmushi tace “barka da zuwa Gwaggo” cikeda farinciki Gwaggo tace “nasameku lafiya ya Lula incedai bata tadaku da yunwan dare” wani kalan daure fuska Lujain tayi tasaki Gwaggo tawuce tasami waje akasa tazauna Gwahho ta kalleta tareda tabe baki tace “too danna fadi gaskiya shine zakiyi fushi dani aisai kiyi tayi” Gwaggo tai maganan tana zama akan 3 sitter daga Kausar da Hamza suka zazzauna kusada ita suna kallonta kaman sunga tV, Gwaggo tace “Hajiya kinga wannan jikan tawa fitinanniyan yarinya ce ga taurin kai da kafiya ina chan gidan dana amman ina tunanin halin dazata sakamini ku ciki” dan murmushi Hajiya tayi takalli Lujain dake kumbure kumbure tace “Lujain batada matsala bata taba daminmu ba gaskiya” dan dariya Gwaggo tayi tace “ai shine nan, bani jakata kagani Hamza” tashi yayi yadauko jakan yakawo gaban Gwaggo sauka tayi kasan carpet tashiga bude jakan dasauri Lujain dake fushi tazo wajen tace “mekika kawomini Gwaggo”? Hararanta Gwaggo tayi tace “yanzu kinga daman kulani” Gwaggo tai maganan tana ciro wani katon kwano data daka lafiyayyen yaji da bushashen nama da kayan kamshi tace “Hajiya ga yaji dakaina na dakashi kinga wayan nan gantalallun yara su Samira dazaran sunga zan fara aiki guduwa suke su labe hope ke baki kiwuya” tai maganan tana kallon Kausar dake kallonta dasauri Kausar ta girgiza mata kai tace “a’a banda kiwuya” baki Hajiya takama tace “Kausarrrr sannu da aiki” kwashewa da dariya Hamza yayi da Lujain harda kyalkyacewa Abee yadan saci kallonta yanda take kallon Kausar tana dariyan kasan tsokana ce, dan girgizakai kawai yayi yakai coffee shi baki yay sipping, Gwaggo cikeda lallashi tace “karki biyemusu ni ina ganinki nasan baki da kiwuya kin iya shan aduwa da goruba da magarya”? Dasauri Kausar ta gyada mata kai tace “eh” fito da ledojinsu Gwaggo tayi ga goruban duk an kankare jiki sunyi kyau tace “zoki debi naki kafin su wayan nan dake miki dariya” kaman Lujain zatai kuka tace “Gwaggo nifa” daga Abee har Hajiya dawowa yan kallo sukayi Gwaggo entertaining nasu kawai take agidan ana haka saiga Musty da Harun da Ibro da Anty Binta sun kawoma Lujain atampopinta da aka gama dinkawa haba dakin kachamewa yayi wawan goruba ake Musty da Harun harda Yar rige rigen dauka, sosai Musty ke lura da Abee yanda any magana da Lujain zatayi saiya kalleta kodan sabida bata taba magana da dariya irin na wanda takeyi yau ba ganin Gwaggo ta oho shi kanshi Musty kallonta kawai yake she’s so adorable and a very sweet and beautiful girl, he just wish abokinshi zaizo yarinyar nan and open up his heart da yanzun ne xaisan soyayya.

Dan yatsine fuskanta tayi jin maranta ya murda, tashi tayi ahankali Ibro yace “ina zaki ana hira mai dadi dake babu wanda yataba jin muryanki agidan nan haka” Musty yace “sai yau da Gwaggon ta kenan ba” Anty Binta tace “to kishi kuke yarinya da Gwaggonta” Gwaggo tace “ai tunda aka kawota nan gidan ku nahuta jibi yanda tai haske takara kyau ashe haka kikayi sa’an zuri’a dan Allah jibi yanda kansu yake ahade kowa nada kirki, babu yanda banyi da ubanta yakawoni nan nadubata ba yaki kunsan idan yafita sallan asuba baya kara dawowa sainai bacci sabida karnace yakaini, shinefa na kira Hadi dole nasashi yasaka mini number Imrana awaya ta nakira Samira tamini saving nasa kiramini shi, kira daya nama dan albarkan nan jiya da daddaren nan yace shikenan zaizo da safen nan ya daukoni, saiko gashi yazo aike Lulu kinyi miji” wani kalan kunya taji juyawa tayi tawuce stairs abinta tana tafiya ahankali Gwaggo kuma takara gyara zama tabude sabon chapter babu wanda baya dariya adakin nan sai Abee da kawai jinsu yake babu Uhm babu um um, Gwaggo sai zuba take ana dariya a falon harda hawaye.

 

Tashi ahankali Abee yayi Gwaggo tace “ina zaka Imrana” anatse yace “abu zan dauko a sama” dasauri tace “ayyooo tafi to abinka” stairs yayi Gwaggo tabishi da kallo saikuma takalli su Musty tareda rige murya kaman wacce zatai gulma tace “surukin nawa baida hayaniya kaman ku” haba mezasuyi banda dariya shi kanshi Abee dake stairs yana jinsu dan murmushi yayi yawuce abinshi Musty yace “ai Imrana Gwaggo tun muna yara haka yakeda miskilanci akwai shariya da rashin son magana” Gwaggo dake kallonsu tace “uhmmmm ba shakka” yanda tai maganan yasa suka kara kwashewa da dariya.

 

Karasawa sama yayi yana tafiya ahankali harya wuce kofan dakin Lujain saikuma yadawo baya ahankali ya tsaya chak gaban kofan yana sauraron sautin kukanta dayaji yakai kusan 1min tsaye awajen saikuma yasaka hannunshi ahankali yatura kofan batare daya shiga cikin dakin ba, tana tsugunne agaban bathroom na dakin da ledan pad da Kausar tabata a hannunta, dan dago kanta tayi tadan kalleshi shigowa cikin dakin yayi yana tafiya one one yakarasa inda take a tsaya akanta ahankali yace “what’s wrong with you”? Gently ta janye hannunta taboye pad din hannunta abayanta sannan takife kanta akan kafafunta murya chan kasa tace “cikina ke ciwo sosai” yana kallonta ahankali yace “stand up” girgixamai kai tayi batare data dago kanta ba, kana ganin yanda take kasan cikin bakaramin ciwo yake mata ba, juyawa yayi yafita daga dakin yanajin yanda kukanta ke karuwa yafito da wayanshi Anty Binta na zaune a falo suna dariyan Gwaggo wayanta yashiga ruri ganin Ya Imran ke kiranta yasa dasauri ta mike tsaye tareda daga wayan takai kunnen tace “Hello Yaya” anatse yace “go and check on that girl” yana maganan yana katse wayan, dasauri Anty Binta takarasa sama dakin Lujain tawuce datagani abude ganinta a tsugunne har yanzu takasa tashi tana kuka sosai yasa tai wajenta dasauri tace “Lujain menene what’s wrong” ganin pad a hannunta yasa tace “Subhanallahi maranki ciwo yakene”? Gyadamata kai tayi Anty Binta tace “tashi to ki kwanta kafin asayo miki magani” cikin wani kalan murya tace “kafana yarike ki kiramini Gwaggo na” dasauri Anty Binta tace “haka kafanki ke rikewa” Gyadamata kai tayi tana kuka, tashi Anty Binta tayi tafita dakin Abee tayi tai knocking tareda sallama, daga taciki yace “shigo” bude kofan tayi tashiga ahankali yana zaune gaban desktop dinshi, kusadashi tayi tace “Yaya she’s having MP cramps ne sosai yana rike mata kafa Ya Imran zaka kaita asibiti ne ko zaka kira Dr yamata prescribing magani asayo?” Batare daya kalleta ba yace “you can go” juyawa tayi tafita daga dakin batare data kara cewa komiba.

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply