Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 4


Saran Boye 4
Viral

No. 4

WAIWAYE ADON TAFIYA.

Malam Hashim musa shine asalin mai gidan. Babban malami mai tarin ilimi daya taka rawar gani a duniyar musulunci. Yasha gwagwarmaya ƙwarai da gaske na ganin ilimi ya yaɗu da faɗaɗa cikin al’ummarmu ta nagartattun hanyoyi.
Kasancewar yayi gwagwarmayar rayuwarsa ta neman ilimi lokacin ƙuruciya a garin Jibiya ta jihar katsina sai ake kiransa da suna ɗan jibiya.
Matan Malam Hashim ɗan Jibiya biyu kacal a duniya. Zainabu (Hajjo) sai Zulaiha.
Ƴaƴansa Huɗu duk maza, kuma dukansu Hajjo ce ta haifesu, dan har Zulaiha ta koma ga ALLAH bata taɓa ko ɓatan wataba.
Sooraj mahaifin su Nu’aymah da ake kira da Baba Malam shine babban ɗansa. Sai Rudwan mahifin Abdallah wanda shima yanada iliminsa sosai, amma shi yana kasuwanci ne, duk da suma su Baba malam suna kasuwancin. Sai Mustapha Mahaifin su Adawiya, shima dai malamine dan tare da Baba Malam suketa ƙoƙarin cigaba da ginin da mahaifinsu ya bari na yaɗa ilimi. Sai auta Musbahu, shine mahaifin su Yusrah, shima dai malamine, yanama addini hidima yana kuma business.
Kamar yanda kukaji a farko gidansu Nu’aymah gidan manyan malamaine sananne, sannan kuma ƴan kasuwane na gaske, dan har sunada kamfanin dake sarrafa Mangyaɗa da kuma sabulu, suna kuma sufurin kayan masarufi sosai ta hanyoyi daban-daban cikin farashi mai sauƙi duk daga kamfaninsu mai suna ƊAN JIBIYA FAMILY.
Kamfaninsu sanannen kamfanine dake da haja a lungu da saƙo na ƙasarnan sabida sauƙin kayansu. Sannan kuma sanannun malamaine da duniyar musulinci ke alfahari dasu a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sunada manyan makarantun da ake koya ilimin addini zallah a cikin kano dama wasu jihohi maƙwafta, suna kuma da gidan marayu nasu na kansu da suka assasa domin ladan ya ringa isa zuwa ga mahaifinsu da ALLAH yayma rasuwa kusan shekaru ashirin da suka shuɗe.
Family ne da alkairansu a bayyane yake wa duniya duk da suna ƙoƙarin ɓoye kansu dan kar asan sune keyi. To amma masu iya magana kance alkairi dankone baya faɗuwa ƙasa banza.

Sooraj (Baba Malam) shine ya zame musu tamkar mahaifi bayan rasuwar Malam Hashim, ya kama ƴan uwansa ya dunƙule kansu waje ɗaya babu mai jin kansu sai ALLAH. Suna ƙaunar junansu matuƙa da mutunta juna. Komai nasu sai sun nema shawararsa kamar yanda shima idan zaiyi wani abu sai ya tarasu ya nema tasu duk da suna a ƙasa dashi.
Tun mahaifinsu nada rai suka gina wannan gida daya kasance gari guda, dan malam Hashim ya mallaki filin ne tun anguwar babu wasu gine-gine kirki, da farkoma noma yakeyi a filin, sai da yaransa suka fara tasawa ya zagayesa yay massallaci da islamiyya, ya kumayi ƙaramin gida a ciki yana zaune da iyalansa. Bayan rasuwarsa arziƙin kasuwancinsu ya ƙara haɓaka sai suka gyarashi aka faɗaɗa massallacin da Islamiyyar, suka kuma ginama kowa sashensa inda zai zauna da iyalansa. A hankali harkoki na ƙara haɓaka musu suna sake gyara gidan har ALLAH ya kaisu ga wannan matsayin suka kasance cikin tsakkiyar birnin kano.

Sooraj (Baba Malam) ya jima baiyi aure ba, dan sai da takai har Hajjo na nuna masa ɓacin ranta akan hakan, sannan yay auren zuminci da wata ƴar ƙanwarta mai suna Salamatu. Rana ɗaya aka ɗaura musu aure su Uku, shi da ƙannensa biyu. Mustapha (Abban Adawiya) da Rudwan (Abban Abdallah) Bayan aurensa da Salamatu ta haifa masa yara uku duk maza. Yayinda shima Rudwan matarsa keda yara uku a lokacin, Maza biyu mace ɗaya. Abdallah shine babba, sai Omar, sai Aysha. Amma Mustapha matarsa bata haihuba.
Shekarar da Musbahu zaiyi aure a shekarar ne Matar Baba malam Salamatu da ƴaƴanta uku, sai matar Mustapha sukai haɗari a hanyarsu ta zuwa Jigawa suka rasu. Lokacin shi Rudwan matarsa na fama da laulayin ciki bata bisuba, sai yaran kawai. Dukansu ALLAH yay musu rasuwa a motar, Abdallah ne kawai keda sauran kwana a duniya. Shima dai ya bugu, dan yasha doguwar jinya kamar bazai rayuwaba ALLAH dai ya raya kayansa bayan yasha wahala. Gida ya koma babu yara ko ɗaya sai Abdallah kawai, sai kuma cikin jikin Momynsa.
Ba ƙaramin tashin hankali suka shigaba a wannan lokacin, dan Hajjo yitai kamar ta zare dan kiɗima, gawarwakin jikokinta biyar da surukanta biyu da driver aka sallata a rana ɗaya kolaci ɗaya, haka aka jera kabirburansu abin tashin hankali😭. (Ya rabbi ka gafartama iyayenmu damu baki ɗaya😭🙏🏻).

Bayan rasuwar matan su Baba malam basu sake maganar aureba har Momyn Abdallah ta haifi cikinta namiji, wanda aka maidama suna Omar, bayan kamar wata biyu da haihuwarta amaryar Musbahu ma ta haihu mace, ita kuma taci suna Jameela.
Hajjo nasan su Baba malam su ƙara aure, amma kuma tausayinsu yasa ta kasa takura musu, sai dai ta cigaba da binsu da addur fatan samun mata nagari da zasu maye musu gurbin matansu. Ansha kawo musu matan aure har gida, musamman kasancewarsu malamai kuma masu kuɗi Alhmdllh. Sai dai basu taɓa amsaba, dan basu farfaɗo daga magagin rashin family ɗinsu ba.
Bayan shekaru biyu da rasa iyalansu ƙwatsam ALLAH ya haɗa Baba malam da Firdausi (Umm) a wajen wani walimar yaye ɗaliban makarantar BUK. Tunda ya ƙyalla ido akanta bai ɗaukeba, duk inda ta shiga ta fita idanunsa a kanta, gashi babu damar mata magana saboda sune manyan baƙi a wajen, hasalima shine yay lecture wa ɗaliban mai ratsa jiki. Inda itama anan Umm ta mutu ason wanda tasan ko kallo batama ishesaba, amma kasancewarta mace miskila ta gaske, kuma mara son yawan magana sai ko a fuska bata nunaba.
Kamar yanda Firdausi (Umm) ta mutu akan son Malam Sooraj Hashim haka babbar ƙawarta, aminiyarta Fauza (Addah) itama ta mutu akansa lokaci guda, sai dai itama ɗin dai bakinta bai furtaba, sai dai kasancewarta mace mai faranfaran da barkwanci dason jama’a sai taita yabashi har Firdausi ta gaji tai mata ƙorafin ta isheta. Dariya tayi a wancan lokacin, dan itace kaɗai ta iya zama da Umm kasancewarta mace mai bahagon hali, ga rashin son wasa, dan sam Umm bata da fara’a, bakuma tason yawan wasa kamar ƙawarta Fauza (Addah).
Ahaka taro ya tashi lafiya Fauza da Firdausi na begen abinda basa tunanin zasu samu a zukatansu, sai dai kuma abinda basu saniba shine Malam Sooraj tunkam yabar makarantar yasa ake bibiyar masa Umm, har aka tashi kowa ya kama gabansa ana binsu a baya har gida anguwarsu. Mai bin nasu yana ganin inda suka shiga ya koma da baya yaje ya sanarma Malam Sooraj Hashim. Baba malam yaji daɗi matuƙa, bai kumayi ƙasa a gwiwa ba ya sake sakawa aka bincika masa mahaifin Firdausi (Umm).

Firdausi (Umm) da Fauza (Addah) ƙawayene konace aminai. Anguwarsu ɗaya, hasalima katangarsu ɗaya, sannan iyayensu Aminaine tun zamanin ƙuruciya. Hakanne ya saka iyayensu matama zama ƙawaye na ƙut da ƙut da babu maijin kansu. A taiƙace ma dai sun zama ƴan uwa. Umm itace ta sakama Fauza suna Addah, saboda sunan babbar yayarsu kenan itama, suna kiranta Addah, shine itama sai take cema ƙawarta Fauza Addah, ahankali suma sauran ƴan gidan suka koma kiranta Addah.
Mahaifin Fauza (Addah) yafi na Firdausi (Umm) arziƙi, dan yana ɗaya daga cikin ƴan kasuwar leda da akeji dasu a cikin kano a wancan lokacin, sannan kuma ɗan boko ne sosai. Mahaifin Fauza (Addah) shike ɗauke da nauyin karatun Umm tun daga firamare har zuwa jami’a. Dan yayun Umm duk iya aji shida na firamare babansu ya ciresu yay musu aure. Itako tana bala’in son karatu, musamman da taga Fauza (Addah) zata cigaba dayi, tata roƙon baban ya barta amma yaƙi, yace itama aure zai mata kamar yayunta. Hankalinta ya tashi, dan haka ta nufi mahaifin Addah ta sanar masa. Shine ya lallasheta, ya kumace ta kwantar ta hankalinta indai karatune zatayi insha ALLAH, shinema zai ɗauki nauyin komai na karatun nata har sai iya inda ta gaji ita da Addah.
Taji daɗi sosai, dan tasan indai yayama babanta magana bazai musaba saboda ƙaunar da sukema juna. Ilai kuwa, baban Addah nama baban Umm magana ya amince, atare aka kaisu makarantar sakandire, bayan sun kammala kuma suka nufi jami’a duk da Mahaifin Umm baiso hakaba, amma kunyar amininsa ta hanashi yin magana ya zuba ido.
To da yake komai aka sakama rana zaizo ƙarahe sai gashi cikin hukuncin ALLAH sun kammala, a randa suka kammala ɗin kuma Umm tai gamo da mijin aure.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

____________________________

Bayan kwana biyu da haɗuwar Umm da Malam Sooraj Hashim Jibiya yazo har gida da kansa wajen babanta ya nema izinin yin magana da ita, tare da tambayar ko an mata mijine?.
Baban Umm yaji daɗi sosai, dan babu wani mahaluki dazaiƙi jinin gidan Malam Hashim Jibiya, nagartaccen gidan dake cike da nagartattun mutane, manyan malamai da ake alfahari dasu a ciki da wajen ƙasarma gaba ɗaya.
A take babu wani jan zance ya amsa masa da ya nema so wajenta, inhar tana sonsa shikuma yayi alƙawarin aura masa ita. Malam Sooraj (Baba Malam) yayi farin ciki da wannan karamci, haka ya koma gida cike da ɗokin wannan al’amari, da tarin godiyar UBANGIJI kuma. A ranar baiyi magana da Umm ba, sai bayan kamar kwanaki biyu ya sake dawowa gareta. Inda akai masa masauki a gidan su Addah, a falon babansu.
Duk da Addah tayi murnar ganinsa a gidansu sai bata zaƙeba har saida taji dalilin zuwan nasa. Jikinta yayi sanyi hartasha kuka jin ba wajenta yazo ba. Dan tun ran walimar yayesu zuciyarta sam bata huta daga begensaba, tanason faɗama ƴar uwarta Firdausi (Umm) amma takasa furtawa, duk sanda ta tunkareta da zancen sai taji gabanta na faɗuwa.
A yau da taji ƴar uwarta yake so saita godema ALLAH da bata furta mata zancenba, ta kumayi alƙawarin mantawa da Malam Sooraj Hashim jibiya a ranta har abada, dan tafi ƙauna da farin cikin ƴar uwarta ta samesa fiye da ita. Haka ta cire komai a ranta taita ƙoƙarin mantawa da shi, ta kuma cigaba dama ƴar uwarta addu’a da murnar samunsa matsayin mijin aure.
Tun daga wannan ranar Addah bata sake zama tayi koda tunanin Malam Sooraj ba har aka ɗaura musu aure da Umm. A ranar da aka kai Umn gidan Malam Sooraj Hashim Jibiya, aranar Addah tai gamo da Malam Mustapha ƙaninsa da yazo ɗaukar amarya. A take shima soyayyar Addah ta shigesa, baiyi ƙasa a gwiwa ba kuma ya sanarma ɗan uwansa. Kamar yanda yabi nasa neman auren bisa matakin shari’a haka ya bima ƙaninsa har iyayen Addah suka amince suma.
Kwatanta muku kalar farin cikin da Addah da Umm suka shiga a wannan lokacin ɓatama lokacine, sunyi kuka sunyi murna har basu san adadiba, ba ƙaramin godiya sukaima UBANGIJI ba daya sake dunƙulesu a gida ɗaya matsayin matan yaya da ƙani. Itama Addah ba’aja wani dogon lokaci ba aka ɗaura aurenta da Mustapha aka kawota.
Da farko ganin kan Addah da Umm a haɗe yake ya saka Momyn Abdallah jin haushinsu, ta ware kanta bata shiga cikinsu duk da ɗanta Abdallah kullum yana wajen Umm. Dan tunda tazo gidan yazama ɗan ɗakin amarya, ahankalima ya dinga zare kayansa yana komawa dasu sashen Umm. Tun Momynsa na faɗa harta haƙura ta zuba masa ido kawai. Daga baya kuma ma saita kwantar da hankalinta suka ƙulle kansu su huɗu ganin Addah da Umm basu da damuwa. Ita dama matar Abba Musbahu babu ruwanta, dukansu tana girmamasu da mutintasu kasancewarsu matan yayun mijinta. Duk da kuwa bazasu girmetaba sai dai suyi sa’anni ma. Ita kanta Momyn Abdallah ba girmarsu zataiba, kawai dai an mata auren wurine saɓanin su da duk sunyi karatu.

Addah ta samu ciki da zuwanta gidan, amma Umm shiru kakeji. Sunyi murna sosai da cikin Addah, har ALLAH ya sauketa lafiya ta haifo ɗanta Namiji santalele. Wanda yaci suna Hashim, amma suna kiransa da malam ƙarami. Babu jimawa matar Musbahu ta haifo nata cikin itama Namiji, yaci suna Ahmad. Itama tsakaninsu babu nisa da Momyn Abdallah datai haihuwa ta biyar, itama ta haifo mace aka sake maida mata Aysha.
Sosai su Baba malam sukai farin ciki family ɗinsu ya dawo kamar da. Inda sukema Umm Addu’ar itama ALLAH ta kawo mai albarka. Haka haihuwar matan gidan ta cigaba da tafiya a jajjere. Sai da sukai haihuwa hurhuɗu kafin ALLAH ya bama Umm ciki itama. Kowa ya tayata farin ciki sosai, musamman ma Addah da ayanzu takeda yara huɗu, Ɗaya namiji Uku mata. Sai Momyn Abdallah nada huɗu, maza biyu mata biyu. Matar Abba Musbahu nada huɗu itama duk maza.
Umm ta haihu Namiji sannan su Addah duk suna fama da laulayi ƙananun ciki, sai dai kuma kwanan jaririn Uku ya koma. Sosai Umm tasha kuka, amma daga ƙarshe saita share hawayenta dan tasan ALLAHn daya bata ya karɓa ya fita sonsa. sannan ma yaran gidan babu wanda kemata shamaki da nasa, faɗi tashinsu sukeyi a sashenta kamar nata, musamman ma Abdallah da ƴaƴan Addah da inba faɗa maka akaiba bazaka taɓa sanin ba nata baneba.
Cikin amincin ALLAH bata rufa wata uku da haihuwa ba saiga wani cikin, inda shima Baba malam yay murna matuƙa fiye ma dana farko. Su Addah sun rigata haihuwa. Matar Abbah Musbahu ce ta fara haihuwar ƴarta mace da taci suna Yusrah, sai Addah ta haihu itama mace, aka saka mata Adawiya, sai Momyn Abdallah ta haihu itama dai mace, aka saka Safiyya sunan mahaifiyarta, sai dai ana mata alkunya da Amal. Bayan haihuwarsu da watanni itama Umm ta sake haifo ƴarta mace mai kama da ita. Wadda taci suna Zainab, da yake sunan hajjo ne sai ake mata alkunya da Nu’aymah.
Bayan haihuwar Nu’aymah da kusan shekara biyar Umm ta sake haihuwar yaro ɗaya namiji Muhammad, daga nan kuma shiru kakeji bata sake ko ɓatan wata ba. A lokacin Addah ta sake haihuwa uku, mata biyu da namiji ɗaya. Sai yazam tana da yara bakwai. Mata shidda maza biyu. Itama Momyn Abdallah ta ƙara biyu ƴammata tagwaye, tanada mata huɗu maza uku itama. matar Abbah Musbahu ko ɗaya ta ƙara shima namiji, tanada maza biyar mace ɗaya kenan. Daga haka haihuwar ta tsaya musu su duka babu wanda ya ƙarayi.

Rayuwar gidan tacigaba da gudana cike da birgewa da ban sha’awa, inda ALLAH keta ƙara ɗaga darajar mazajensu ta ɓangaren yaɗa da’awa da ilmantar da bayin ALLAH da taimakonsu ta hanyoyi da dama. Suma kuma ba’a barsu a bayaba wajen yima addini hidima. Ƴaƴansu sun tashi kansu a haɗe cike da tarbiyya kula. Komai tare ake musu.
Akwai shaƙuwa sosai tsakanin Abdallah da Nu’aymah, dan tunda aka haifeta ya kasa ya tsare. Komai yaci sai ya ragema Nu’aymah duk da alokacin yayi girma sosai, dan harma ya kammala firamare yana shirin shiga sakandire. Babu mai dukan Nu’aymah ya kwana lafiya a gidan. Umm ce kawai yake ma ɗan kawaici, itama zaita fushi da itane koda bazaiyi maganaba. Komai ma Abdallah na Nu’aymah ne, firarsa Nu’aymah, fushinsa sai an taɓa Nu’aymah, kukansa sai Nu’aymah na kuka.
Itama kamar tasan abinda yake yi, tanama kowa ƙiwa a gidan amma banda Yah Ab, duk abinda ta samu saita rage ta ajiye masa. Tun kowa na ɗaukar lamarin nasu wasa har aka fahimci yafi ƙarfin wasan aka koma binsu da addu’a.

Nu’aymah nada shekaru tara a duniya su Baba malam suka buɗe kamfanin mangyaɗa a garin Lagos, hakan yasa dole Malam Rudwan Hashim Jibiya (Abban Abdallah) ya koma can da iyalansa dan ya dinga kula da shi. Lokacin komawar tasu kam anga tashin hankali wajen Abdallah saboda rabuwa da Nu’aymah. Da ƙyar aka yakicesa daga jikinta, danfa shi yace inhar zaije sai dai da ita, kokuma a barsa anan wajensu. Ganin yanda yay matuƙar ɗaga hankalinsa yasa Hajjo sakawa a barsa nan gida badan Momynsa tasoba. Idan anyi hutu ya ringa zuwa musu, idan kuma sunzo shikenan.
Haka yana gani iyayensa suka lula Lagos aka barsa a kano saboda Nu’aymah. Bayan tafiyarsu Abban Abdallah da shekar biyu shima Abba Musbahu daya ƙara auren mata ta biyu ya bisa tare da Ammin Ahmad, yabar amaryarsa anan gidan yana zuwa weekend, dan aiki yayma Abban Abdallah yawa acan shi kaɗai, ga harkar Addini gata kasuwanci, ga nashi kuma yanayi shima.
Gida sai ya koma daga hajjo sai Umm da Addah da Ummah amaryar Abba Musbahu. Iyalan Baba Malam dana Abba Mustapha kenan. Sai idan sun sami hutune matan kanzo da yaran nan suyi, sukuma su Abbah sai suke zuwa weekend idan matan nasu sunzo nan.
Haka rayuwar ta cigaba da tafiya, shaƙuwa na sake ƙulluwa tsakanin Nu’aymah da Abdallah, hakama tsakanin Adawiya da Nu’aymah, dan sun taso sa’anni su biyu tunda su Yusrah suna Lagos.
Komansu tare ake musu, babu maijin kansu, Hassana da Hussaina ma ake kiransu saboda shaƙuwa. A hankali Adawiya ta kwaso kayanta ta dawo ɗakin Nu’aymah dake sashensu, suka zama a ɗaki guda, makaranarsu ɗaya, ajinsu ɗaya. Kai komaima nasu ɗayane. Gefe ga soyayyar Nu’aymah da Abdallah, inda itama Adawiya son Abdallah keta mata saƙa a zuciya batare da kowa ya saniba har ita kanta. Bata tashi farga dason da take masaba sai da yay mata babbar illa a jini da zuciya, har takai bazata iya haƙura ta barma Nu’aymah ba.

Tunda Abdallah ya kai minzalin aure bayan kammala karatunsa na degree aketa fama da shi yayi aure amma yaƙi, acewarsa Nu’aymah yake so. An lallaɓashi akan ya auri wata idan Nu’aymah ta isa saiya ƙara da ita, amma sam yace bazata saɓuba, zai jirata ko shekara nawane. Abin ya bama kowa mamaki, dan lokacinma fa Nu’aymah da Adawiya suna firamare aji shidda ne. Haka kowa ya haƙura aka zuba masa ido, sai ma ya koma karatu da kasuwancinsa na kansa daya ƙirƙira, ya duƙufa wajen faɗaɗa karatunsa na addini kuma tamkar iyayensa.
A wannan shekarar Abban Abdallah ya sake komawa Abuja da zama inda canma suka buɗe reshen Company ɗinsu na mangyaɗa, sai aka bar Abba Musbahu a Lagos. Tunda suka dawo Abuja Momyn Abdallah ta fara jan yaronta jikinta sosai, a hankali ta janye ra’ayinsa ya koma Abuja da zama wajensu, inda harkokin kasuwancinsa suka fara faɗaɗa daga Nigeria zuwa ƙasar Saudia. Lokacin kuma Adawiya da Nu’aymah sun shiga sakandire.
Suna aji uku a secondary Abdallah ya koma kara faɗaɗa iliminsa na addini a ƙasar Saudia inda yake kasuwancinsa yanzu, sai yazam baya zuwa sai dai aiko da kaya Nigeria Omar da Ahmad na kulawa dasu suma suna aika masa na Nigeria can.

Nu’aymah yarinyace ƙyaƙyƙyawa fara masha ALLAH, dan tana kama da mahaifiyarta sosai, yarinyace mai shegen wayo ga rashin tsoro ga tsiwa. Tsula tsiyarsu suke ita da Adawiya fiye da zato, kullum cikin jan faɗa suke a makaranta daga boko har islamiyya. Duk da rashin jinsu yarane masu kaifin basira da hazaƙa musamman ma Nu’aymah, tana da matuƙar ƙoƙari, dan tun tana aji biyu na secondary tayi saukar Qur’ani, bayan tayi da shekara ɗaya itama Adawiya tayi. Bayan duk sunyi sauka suka juya hadda, tare da karatun sauran littatafai kuma.
Hazaƙar Nu’aymah a makaranta yasa suna aji biyar wani malami ya bada shawarar a barta kawai ta zana ssce a wannan shekarar, koba komai zata kammala jami’a da ƙarancin shekaru. Baba malam ya amshi wannan shawarar, musamman daya duba maganar auren Nu’aymah da Abdallah da kowa ke jira, ya yanke shawarar tana zana ssce za’ayi auren sai taje ta cigaba da karatunta a ɗakin mijinta kawai. amma saiya sa suyi ssce ɗin tare da Adawiya. Wannan shine ya sakasu gama makaranta a wannan shekarar. Adawiya dasu Amal nada shekaru sha bakwai cif, Nu’aymah kuwa bata cikaba har yanzu, tana sha shida da wasu watanni dan su Adawiya sun girmeta……………✍

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
*_Typing📲_*

*_SARAN ƁOYE!!_*

 

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

Free page😋

_Daga yau free pages sun ƙare masoya. Ku garzayo domin samun waɗanan littatafai guda biyar akan farashi mai sauƙi. Dan girman ALLAH kibi ta hanyar data dace ki mallaki naki😅, karki zama cikin masoya masu mana SARAN ƁOYE akan kasuwancinmu😢🙏, muna alfahari daku aduk inda kuke. Muna godiya kuma da ƙaunar da kuke nuna mana irin trillions ɗin nan. Idan nace ku na dabanne ina nufin na daban har cikin raina😘😘🤝🏻_.

*_Masu buƙatar mu saka musu tallar kayan sana’arsu zasu iya zuwa suyi magana damu domin tayasu tallata hajojinsu a yanar gizo😘🤝🏻_*.

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply