Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 41


Saran Boye 41
Viral

_WASHE GARI_*

A gidan su Nu’aymah kuwa a safiyar yau bayan kammala breakfast ɗunguma sukai asibiti suka duba jikin ta, kamar ko yaushe basu duka aka bari suka shigaba. Baba malam ne kawai dasu Abba Musbahu. Sai hajjo da Ananah. Umm dama batajeba dan tanason zuwa gidan Gwaggo mahaifiyarta. Daga can zata biya asibitin tare da Gwaggon.
Basu jima a asibitinba suka dawo gidan, baba malam da ƙannensa uku da hajjo sai Ananah a falon hajjo suka yada zango domin tattaunawa. Sunyi zaman kusan awa guda sannan Abba Musbahu yay kiran Abdallah da Naser a waya. Ba a rufa mintuna biyarba kuwa sai gasu dan dama duk suna gida. Zama sukai inda Ananah ta nuna musu kowanne kansa na a ƙasa..
Fuskar baba malam a ɗaure ya dubi Abdallah, “Abdallah zan fara ta kanka, dan karka zata shirun da mukai maka kamar mun ƙyalekane bisa abinda ka aikata mana. Gani ga ƴan uwana ga Hajjo harma da Ananah. Inason ka faɗa mana dalilinka na aikata abinda ka aikata. Shin bamu da daraja a idanunka ne mu da muka baka auren yaranmu kokuwa raini ne dan kaga ka girma?”.
Cikin sauri Abdallah ya ɗago yana kallon baba malam ɗin da girgiza kansa. “Wlhy sam ba haka bane ba Abbah. Kuna da darajar da bayan MANZON ALLAH babu mai ita a idona a duk faɗin duniya sai ku”.
“Ban yarda ba Abdallah, inda ace munada wannan darajar da bazaka aikata abinda kayi ba. Mu aura maka yara ka sake mana su akan wani banzan dalilinka mara amfani”.
“Abba ku gafarceni, amma wlhy ina son Nu’aymah, son da zaku iya rasani idan kuka hanani mallakarta. dan ALLAH a wannan karon karkuce mani a’a”.
“Ba maganarta nai makaba ni ai, maganar yarana daka saki nake maka”.
Shiru Abdallah yay zuciyarsa na masa ƙuna da zafi mai raɗaɗi, sai faman haɗiyar zuciya yake kamar budiddigin ƙwaɗo. Ganin yaƙi cewa komai hajjo ta amshe zancen da cewa,
“In banda zancen banza taya dan kawai nayi maka magana zakaje ka aikatama yara wannan wautar, ina iliminka yake? Ina wayonka yake? Kaine fa babba a gidan nan, kuma ka tabbatar abinda ka aikata da shi na ƙasa da kai zasuyi koyi. Ta hakane zaka iya zama jagora uba garesu a randa ƙasa ta lulluɓe idanunmu mu da iyayen naka?”.
“Kiyi haƙuri hajjo”.
Ya faɗa muryarsa na zuga.
“Idanma banyi haƙuri ba dukan ka zanyi Abdullahi. Yanzu dai ka maida matanka, batun Zainabu kuma gaka ga Nasiru yanzun, sai ku sasanta kanku dan babu mai shiga a wannan karon. Duk wanda ya sameta a cikinku mu abin farinciki ne a garemu, kuma zamu saka albarka. Sai kuje ku nema yarda daga gareta, wanda duk ta zaɓa magana ta ƙare”.
Hukuncin hajjo yayma kowa dai-dai, sai dai banda Naser da Abdallah. Dan a kallo ɗaya zaka hango tsantsar tashin hankali cikin idanunsu. Lokacin da suke ficewa daga falon har tafiya suke kamar zasu kifa, musamman ma Abdallah.

*_ABUJA_*

Aɓangaren Yoohan kam yau da azumi ya tashi kasancewarta al-hamis. Azumin litinin da alhamis yana ɗaya daga cikin ibadar da tun bayan musulintarsa ta fara zame masa jiki. Bayan ya idar da sallar asubahi yay zaman yin azkar kamar yanda baba malam ya koyar da shi ta bidiyo kol da sukeyi a kullum. Sai dai kasancewar bai gama haddacesu ba sai yake karantasu a littafin. Sai da gari yay haske kamar yanda shari’a ta koyar sannan ya miƙe zuwa ɗakin motsa jikinsa.
Kamar yanda ya saba ya farayi yana haɗa uwar zufa, kasancewar kwana biyu bai samu damar yin na kirki ba a kano sai yau yaji jikinsa yay masa ɗan nauyi. Hakan ya sashi zarta lokaci kaɗan, dan har Solomon ya shigo masa da tatattun kayan itatuwa (fruit) bai kamalla ba.
“Good morning sir”
Solo ya faɗa yana ɗan risinar da kansa tire a hannunsa.
A taƙaice Yoohan dake ɗan hakki ya share zufar goshinsa da cewa “Same”. Da ga haka ya cigaba da abinda yakeyi. Shigowar Solo da kusan mintuna sha biyar sannan ya kammala, lokacin har an fara gudanar da program ɗinsa a NTA. zama yay Solo ya miƙo masa juice ɗin. Kai ya girgiza masa yana goge zufar dake tsiyaya masa da ƙaramin towel, yace, “Barsa kawai”.
Sosai Solomon yayi mamaki. dan a watan nan ya fara lura da wani abu daga ogan nasa. Duk monday and Thursday da wahala kaga yaci wani abu har yamma. Kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru. Shima Yoohan ɗin bai sake tankawa ba, sai ma maida hankalinsa da yayi ga television ɗin gaba ɗaya. Ana kammala program ɗin ya miƙe, anan yabar Solomon na kimtsa ɗakin.
Tsaf ya tadda ko’ina Solo ya gyara, sai ƙamshi da sanyin ac dake ratsa ko ina. Toilet ya nufa yay wanka, ya ɗan jima a ciki kafin ya fito. Bashi da sha’awar fita ko’ina yau ɗin nan, dan haka body spare kawai ya saka da boxer ya haye gadonsa ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya. Cikin mintuna kaɗan barci kuwa yay gaba da shi.

A falo kam koda su madam Chioma suka haɗu dan yin breakfast kakarsa data haifi papa ce ta saka Destiny wai taje ta kira Yoohan ɗin. Sosai Destiny ta waro idanu waje. cikin yare tace, “Granny inajin tsoro gaskiya. Brother John baya son mutane”. Harara mama ta zuba mata, cike dajin haushi ta duba Madam Chioma. “Ai ga wadda ta watsa shi nan bai ganin kowa da gashi sai ita data haifesu. Yaro sai masifar taurin kai”. Banza Momy tai mata, sai mamanta ce ta karɓe zancen da faɗin, “Inma a bauɗen yake ai ba ita kaɗai ta bauɗar da shiba harda ɗanki. Debora ki daina sakama yarinyata baki akan rayuwarta fa, ni dama nasan masiface ta kawoki ba komaiba. dan kawai kinga nazo, yanda kikejin gidan ɗankine nima gidan inlow ɗina nen ai”.
Ai kafin kace kwabo sun hargitse da cacar baki kamar wasu kaji. Su dai jikokin duk idanu suka zuba musu kawai suna kallo da ƙannen papan dama momy ɗin kanta. Abun nasu zattakaici da dariya. Basuyi shiru ba sai da papa ya fito yay musu magana cikin damuwa.
Daga haka suka koma harar juna suna huci kamar wasu zakuna. Daga ƙarshe basuci abincin a Dining ɗinba sai dai kowa masaukinta ta koma aka kai mata nata.

Yoohan da baisan sunayi ba kam sai wajen sha biyu ya farka. Wanka ya sakeyi yay shiri cikin ƙananun kaya. Blue jeans da t-shirt fara ƙal an rubuta HERO da kalar blue a gaba. Ya gyara sumarsa da sajensa yanata zabga ƙamshi. Slippers masu taushi ya saka dan ba nisa zaiyi ba. Ya ɗauka wayoyinsa ya fito.
Da sauri Favour ta ɗauki remot ta rage kiɗan da suka saka a sifiku kamar zai tsaga falon lokacin da yake sakkowa. Fuska a matuƙar tsuke ya dubesu, baiko amsa gaisuwar da suke jera masa ba yace, “Wannan kiɗan da kuka cikama mutane kunne da shi fa?”.
Cike da tsoro Victoria tace, “Brother sai da nacema Favour karta kunna bakason ƙara da yawa, amma tace sai……”. Wani irin zabura Favour tayi ta danne bakin Victoria dan karta ƙarasa faɗa. Ba komai ta tuna ba sai marin da ya taɓa kashe fuskarta da shi ranar X-max ɗin last year da sukaje a ƙauye ya iske ta samu ciki. Cikin rawar murya tace, “Ƙarya take Uncle John, na rantse bance komai ba”.
Shi baimabi takansu ba ya fice abinsa saboda jin kakarsu data haifi papa na ƙwala masa kira da alama sunansa dasu Victoria suke ambata ta jiyo.
Da ƙafa ya fice a gidan bayan ya gaisa da ma’aikatan gidan a tsaitsaye. Can bayan layinsu ya nufa, inda yake ganin wani masallaci. Acan ya gabatar da sallar azhar, koda aka idar ya dawo gidan garden ya wuce kai tsaye. Babu kowa a ciki, sai sassanyar iskar dake kaɗawa daga ni’imar itatuwan cikin garden ɗin. Anan yay zamansa har la’asar tayi, kasancewar yanada alwalarsa massallacin ya sake komawa yayo sallar la’asar, ya cigaba da zamansa a ciki har zuwa biyar sannan ya fito.
Daya dawo ma bai shiga ciki ba, duk da kuwa Solomon ya sanar masa Momy nata zuwa nemansa tun ɗazun. Aika solo ɗin yay ya ɗakko masa key ɗin mota a ciki. Tare suka dawo da Miracle. Koda ta gaishesa sau ɗaya ya amsa ya ɗauke kansa, cikin damuwa ganin zai shiga motar tai saurin fada masa Momy tace yazo yaci abinci. Bai amsata ba sai da ya shiga motar mazaunin driver, dan ya hana kowa binsa. Kallonta yay sau ɗaya ya ɗauke kansa. “Ki sanar mata ina azumi”. Daga haka yay reverse ya fice a gidan.
Koda ta koma ta sanar ma madam Chioma sosai sukaita mamakin azumin mi Yoohan ɗin keyi? dan sunsan dai su azuminsu yanada lokutansa a addininsu. Ganin basu da mai basu amsa suka haƙura harya dawo gidan.

Yoohan kam koda ya fita wajen Hamza Ibrahim ya nufa, can suka haɗu gidan wani haɗaɗɗen abinci daya gaji da ƙawatuwa. Sun ɗan zauna kusan na mintuna talatin kafin a kira sallar magriba. Zuwa sukai sukayo salla suka sake komawa gidan abincin, anan Yoohan yay musu order ɗin abincin buɗa baki dan shima manager axumin ya keyi. Da wannan damar sukai amfani wajen sake faɗaɗa hirar tasu da duk ta kasance akan abinda ya faru a kano, wadda dama duk ya sanar masa ta waya. Hasalima shine ya bashi shawarar kawai yacema baba malam zai auri Nu’aymah ɗin koda a yanzunne. Shi kuma aranar bai wani ja zancenba ya amince da shawarar duk da a idanunsa yana ganin Aymah tayi ƙanƙanta da aure.
A fahimtar manager dai anya dama Yoohan ɗin ba ya na son Nu’aymahn bane kuwa?. Da yake baida mai bashi amsa sai ya watsar da zancen.
Duk yanda ake gudanar da bikin aure a musulinci da hidimar da hausawa keyi a al-adance manager ya sanarma Yoohan, dan haka basu rabu ba sai kusan goma na dare.
Koda Yoohan ya dawo a harabar gidan ya iske papa nashan iska. Zama yay a wajen suka tattauna abinda ya shafesu. Sai kusan ɗaya saura suka shiga cikin gida. A hakanma Yoohan ɗinne ya nuna ya gaji.

*_BAYAN KWANAKI UKU_*

A kwanaki ukun nan kullum sai Yoohan dake a birnin ikko yanzun sai ya kira Dr Aysha yaji yanayin jikin Nu’aymah da suka maida sumammiya, dan tunda ya bar kano a yanayin barci take, sai dai drip da ake ƙara mata a koda yaushe da allurai a ciki. Haka suke buƙata ta sami isashen hutu. Allurar kuma daya sa aka kawo masa daga canada tun wadda akai mata randa aka kawo ba’a sakeba. Dan ƙa’idar allurar sai bayan sati ɗaɗɗaya za’ayita, hakan yasa bai bama kowa ba ya ajiyeta a office ɗinsa a waje mafi sirri. Dan daga Lagos nan kano yake fatan dawowa ya duba Nu’aymahn. Kamar yanda ya sabarma kansa kuma kullum sai ya kira baba malam sun gaisa safe da maraice.

A gidan su Nu’aymah kuwa shirye-shiryen biki ake babu kama hannun yaro, dan yau saura kwanaki shida kacal a ɗaura auren su Hajarah. Da Abban su Adawiya yace a ɗaga har sai Nu’aymah ta samu sauƙi. Amma sai baba malam ya hana hakan. Ya ce babu abinda za’a fasa ALLAH zai bata lafiya itama.
Yayinda aketa shirin biki Abdallah da Naser ƴar tsama a tsakaninsu kullum sake faɗi da tsauri takeyi akan Nu’aymah. Gashi sun maida asibiti wajen yininsu duk da ita wadda sukeyi domintama batasan sunayi ba ma. Duk sunbi sun tashi hankulansu akanta. Yayinda Adawiya ita nata hankalin yafi nasu tashi. Dan har yanzu Abdallah yaƙi maida auren nasu. Su baba malam kuma babu wanda ya sake cewa da shi komai akan hakan.
Sosai Adawiya ta rame, kamar ba itace suka dawo ta zama lukuceciya ba. Tabi ta ɓoye kanta a gidan babu mai ganinta sai ƴan sashensu. Ita kuma Addah tayi kamar bama tasan halin da Adawiya ke a ciki ba. Dan tun lallashin datai mata na farko taki saurarenta saita watsar da ita bayan ta babbanka mata zagi da yi mata kaca-kaca.
Ƴan uwantane kawai da Umm ke tausayinta, dan Hajarah tamafi kowa damuwa da halin da Adawiya ta jefa kanta. Har kwatance take mata da yanda Yusrah tai kamar komai bai dametaba tanata harkokinta ita. Hakama Nu’aymah lokacin da aka rabasu aka bashi aurensu. Amma sam Adawiya taƙi fahimta. Sai bin hanyoyin da zatai magana da Abdallah takeyi shi kuma ya toshesu ya hanata kowacce dama. Gaba ɗaya ya maida hankalinsa ga takarar neman yardar Nu’aymah da take a rabin duniya da barzahu.

A washe garin da Yoohan ya cika kwanaki huɗu da tafiya su Papa sukazo kano shida ƙannensa da abokansa uku. Babu wanda yasan abinda ya kawosu. Shi kuma baba malam bai faɗama kowa ba sai ƴan uwansa da Hajjo da Ananah kawai.
Amma yanda Papa da gayyarsa suka koma ransu a ɓace zai baka tabbacin zaman baiyi daɗi ba. Dan shima baba malam ɗin dai ranar yini yayi babu walwala tattare da shi.

★★★★

Ana saura kwanaki huɗu ɗaurin auren su Kubrah Yoohan dake a birnin ikko har yanzu ya kira Dr Sa’ad ya sanar masa su tsagaita da yima Nu’aymah allurar barci haka nan, idan ta farfaɗo a kowanne lokaci a kirasa a sanar masa.
Haka kuwa akayi, ƙarfe kusan sha biyu na daren rar Nu’aymah ta farfaɗo…………✍

_________________________

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

 

 

I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.

*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply