Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 49


Saran Boye 49
Viral

No. 49

…………Kusan duk falon sai da kowa ya miƙe saboda uban ihun da Miracle ta ƙwallo. Hannunta ɗaya riƙe da baki ɗaya riƙe da ƙafarta data bugi kujera. Duk kanta suka nufa cike da tashin hankali.
Banda Aymah data wani ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tamkar ba itace ta aikata tsiyar ba. Cikin mintuna ƙalilan bakin Miracle ya suntume, gashi an ɗagata ta kasa taka ƙafar sai faman ihu take tana kiran Jesus. Tayi yare tayi turanci hawaye shaɓe-shaɓe da fuska.
Abu kamar wasa sai ga jikin Miracle ya rine da zazzɓi dan harga ALLAH taji faɗuwar musamman data kasance a bazata tazo mata. Gata masha ALLAH tanada jiki. Ko a kwalar rigar Nu’aymah, dan saida ta gama shan ƙamshinta sannan ta ɗan matsa gab da Mira da aka kwantar a doguwar kujera dake kusa da inda Aymah take zaune ana jiran Doctor yazo ya dubata. Da wani salon iskanci tace, “Ayyah Aunty Orrobo sorry yeah, wannan baki haka kamar shantu? Gobe kam ya sake yin tsaki batare da ya tantance inda zaiyi ba”. Babu wanda yaji mita faɗa a maganarta ta ƙarshe bayan sannu da taima Mira. Dan kuwa da hausa tayi, yanda kuma ta kwaɓe fuska sai ka ɗauka duk tausayin Mira ɗinne takeyi.
A gefe kuma suna ganin Aymah ba wani turancin kirki takeji ba shiyyasa ta ƙarasa sannu wa Miracle ɗin da hausa. Haka suka cigaba da zama har isowar Doctor, ya duba Miracle ɗin sai ga sakamakon targaɗe a ƙafar data buge. Dole yace su shirya a kaita asibiti dan a duba ƙafar da ƙyau, a kuma yimata ɗinki a gefen bakinta da ya shafce.

Tun bayan wucewar su Miracle da Gebrail da Joy suka tafi rakawa asibiti Aymah ta koma sama dan lokacin sallar zuhur yayi. Dariya ta dinga sheƙawa tunda ta shigo kamar wata zararriya. Sai da tayi mai isarta sannan ta ɗauro alwala tana faɗin, ‘Duk wanda ya shirya match dani ai ya sani nima da shirina nake. Babu ta yanda za’ayi na zauna mushirikai su hau kaina suci tuwo. Wasa kam yanzu aka fara a wanga gida dan na kula basusan wacece Zainabu jikar Hajjo ɗiyar baba malam ba’.
Sallarta ta gabatar a nutse, tana idarwa ta ɗauki Al-qur’ani ta hau karatu cikin zazzaƙar muryarta. Blessing ce ta shigo kawo mata lunch, sai dai a falo ta ajiye bata shigoba. Ta matso jikin ƙofar danta sanar mata ga abinci nan kunnenta ya jiye mata zazzaƙar muryar Nu’aymah na raira karatun littafi mai tsarki. Tsayawa cak tayi daga yunƙurin knocking ɗin tana sake matsar da kunnenta dan taji sosai. Kamar wasa sai gashi ta share mintuna kusan goma tana saurarenta. Sai da taji tsoron kar wanu ya shigo ya ganta ne sannan tai saurin barin sashen.
Oho, Aymah batasan tanayiba. Karatunta ta sha na kusan awa ɗaya sannan tai addu’a ta miƙe. Sosai takejin kewar ahalinta, musamman ma Muhammad abokin dambenta. Gudun kar damuwa taima ranta yawa yasa ta fito falon danta ɗanyi ko kallo ne. Sai da ta fara duba abincin da Blessing ta ajiye, duk da taga shinkafa da miya hakan bai sata jin zataci ba. Itafa gaskiya bazata jura cin abincinsu ba. Ya dawo zata faɗa masa ita zatana girkintane kawai. Da wannan tunanin ta maida kulolin ta rufe. Saurarrakin biscuits ɗin data ci ɗazun ta ɗebo. ta dawo cikin kujera ta kunna tv a ranta tana mamakin yanda koda yaushe suke cikin wutar nepa. A maimakon kallon ma sai tai ta Searching tashoshi tana duba masu amfanin da riƙe Numbers ɗinsu a kanta. Hakan ya jata lokaci mai tsayi har aka kira la’asar. Salla taje tayi, ta sake wanka. Tsaf ta fito tana baza ƙamshi ta sauka ƙasa.
Yanzunma duk a falin ta iskesu an dawo da Mira data sha ɗauri a ƙafa da hannunta data kulje, kunburin bakin kam ya ƙara faɗi dan ya kusa shanye rabin kumatunta. Batare da Nu’aymah ta duba ko inda take ba tacema su Destiny suzo su rakata taga gidan. Harara mama debora ta zuba musu da musu gargaɗi da idanu. Amma duk sai suka maƙe kafaɗa suka miƙe. Tsaf Aymah na lura da komai, dan haka tai murmushi kawai (Mama debo karfa kizama next level🤣lol).
Suna fita Joy tace, “Yarinyar nan na kula da rawan kai ta shigo gidan nan, wlhy ni sai nagama kamar itace ta sama Mira ƙafa ta faɗi fa?”.
Gebrail da ya bi Aymah da kallo kamar idanun zasu zubo ƙasa yay saurin waigowa yana duban Joy ɗin. “Hy madam banda ƙarya fa, dan kawai tana rayuwanta kai tsaye sai ace tana rawan kai?. Kufa ɗazun kuke gulman hausawa bagidadawa ne. Sai kuma gashi ita ta ƙaryataku yanzun tunda ta nuna kanta a buɗe yake. Da kun sone ta ƙunshe kanta a ɗaki komi? Mtsoww amebo girl”.
Zumbur Joy ta miƙe kansa, Momy ta daka musu tsawa. Dan ciwon kai suke neman ƙara mata bayan wanda take ciki. Saboda akan idonta Aymah ta sakama Miracle ƙafa. Amma tai shiru saboda wani dalilinta. Tsaki Joy taja da yima Gebrail alamar zasu haɗune da yatsunta. Shima sai ya ɗage kafaɗa da taɓe baki irin na I don’t care ɗin nan.
Wani irin tafasa zuciyar mira ta ringayi, ga abin faɗa a bakinta amma babu damar cewa. Ita kanta yanzu maganar Joy ta sakata ƙara tariyo a yanda ta faɗin. Tunda tasan lafiyar ALLAH take tafiya babu kuma komai a gabanta. Aiko tabbas saita damalmala kan yarinyar nan bisa tiles ɗin gidan nan bara ta warke dai.
Su mama debora nata cancana maganar da Joy ta faɗa akan tunanin Aymah ce ta kada Mira. Yayin da su Maman Favour keta ƙoƙarin kare Nu’aymah ɗin akan Joy ɗin ta faɗi dai son zuciyarta ne kawai.
Oho, Nu’aymah batasan sunayi ba, tana can sunata zagaya lungu da saƙo na gidan ita da su Victoria. A ƙarshe suka yada zango cikin garden ɗin gidan da yay mugun tafiya da tunanin Aymah. Musamman ma swimming pool ɗin da ruwan cikinsa sky Blue da keta ɗaukar idanun mai kallo. Sun ɓata lokaci sosai a garden ɗin, dan har sai da duhun magriba ya fara rufa sannan suka fito.
Yanzun kam babu kowa a falon kowa ya shige, sai masu aiki biyu maza dake gyarawa. Sashenta tai wucewarta suma su Favour suka nufi ɗakinsu.

___________★★★__________

A kano kam shiru kakeji babu wani abu daya sake faruwa bayan jin labarin inda su Abdallah suke. Ashe Abdallah saudia yay komawarsa, Naseer kuwa yana anan cikin garin kano sai a yau yazo gidan. Kowa yayi mamakin ganinsa hankali kwance saɓanin yanda sukayi tunanin samunsa.
Dominma ya ƙara tabbatar musu da hankalin nasa a kwance yake sai da ya shiga kowanne sashe yay musu bangajiyar biki. Da yamma su Abba Musbahu zasu koma Lagos harda shi cikin ƴan rakkiya airport.
Bayan ya dawo ne shi da malam ƙarami da suka kaisu ya samu gaisawa da baba malam daya shigo. Yanda babu wanda ya tambayesa ina yaje cikin su hajjo haka baba malam ma baice masa komaiba. Sai dai a ƙasan ransa mamakin yanda babu wata damuwa tattare da Naseer ɗin yakeyi. ‘To mi hakan ke nufi?’ ya tambayi kansa acan ƙasan zuciya. babu mai basa amsa, dan haka yaja bakinsa ya tsuke ko Umm baima wannan maganaba. Bai san itama abinda Naseer ɗin yayi yana cikin ranta ba, tayi shiru ne kamar yanda kowa yayi ne kawai itama.

___________★★★★__________

Lafiya lau Nu’aymah tai barcinta a sashen ita kaɗai batare dajin ko ɗar ba na tsoro. Dan haka sam dama ba ɗabi’arta bace ba kowa ya sani. Abinda kawai yayta cimata rai shine kaɗaici da kewar ahalinta. Gashi bata da ko ƴar waya balle ta kirasu taji koda muryarsu. Sai damuwa akan waɗan nan mutanen gidan data fahimci sam babu mai ƙaunarta a cikinsu. Sai dai kowa da nasa salon kallon data lura yana mata. Yaran nan su Victoria ne kawai babu ruwansu, sai su maman Destiny. Amma har masu aikin gidan tana fahimtar kallon ƙyama da suke binta da shi duk da kuwa duk suna mata gaisuwa da girmamawa. Lallai kuwa dolene ta ɗaura ɗammarar zama mara jin magana, inba hakaba wahala zata sha tunda ta fahimci shi daya ajiyeta bamai zama bane. Yazama lallai kenan itace zataima kanta yaƙi da kanta basai ta jira daga wurinsa ba. Da waɗan nan tunane-tunanen tai barci a wannan daren, hakan yasa washe gari bata fita a sashen nata ba sai bayan sallar zuhur.
Yau kam babu kowa a falon sai Abraham kawai yana kallon cartoon, yanda yaron bai tanka mata ba haka itama bata kulashi ba tai ficewarta. Kai tsaye garden ta nufa abinta. Shiru wajen babu komai sai kukan tsuntsaye da iska mai daɗi dake kaɗawa. Ta zauna a bakin pool ɗin tare da zira ƙafafunta ciki tana lumshe idanu saboda sanyin ruwan. Haka ta zauna tsahon lokaci a wajen rabin hankalinta duk yana ga tunani, kamar ance ta waiga sai idanunta caraf akan Gebrail da ita kanta batasan adadin lokacin daya ɗauka a wajenba. Kanta ta ɗauke daga dubansa tana sake tsuke fuska. Yayinda shi kuma ya shiga takowa inda take yana wani rangaji irin na gayu marasa jin magana. A mamakinta sai kawai ganinsa tai ya zauna daf da ita shima ya zura ƙafafunsa cikin ruwan.
Kallonsa tai da wani irin takaici, shiko ya saki murmushi. Kafin ya furta maganar dake bashinsa taja baya ta fidda ƙafafunta tana jan wani shegen tsaki…….. Da sauri yace, “Ayya sorry my aunty, i……”
Wani shegen kallon da tai masa ne ya sakashi haɗiye abinda ke bakinsa. Ta zira takalmanta ta fice daga garden ɗin gaba ɗaya. Ta kula yaron nan yana son shigar mata hanci, to lallai zata fyatoshi kuwa da gaggawa tunda shi ɗan bunsuru ne.
Gebrail kam da kallo ya bita a wani irin yanayi yana lashe laɓɓansa, harga ALLAH tun ganin Aymah a wajen dinner ya rikice, dan yarinyar da shekarunsa ta dace bawai yayansa ba.

Takaicin da take ciki na Gebrail yasata ko ganin hanya batayi take tafiya kawai ta bayan garden ɗin. Dan jitai sam batama buƙatar shiga cikin gidan balle ta sake karo da wani takaicin kuma. Cak ta tsaya saboda jin ana magana ƙasa-ƙasa kamar cikin tashin hankali. Tai saurin komawa baya kaɗan ta maƙe jikin rassan flowers ɗin da suka sarƙe wayar garden ɗin. Ƙafafunsu kawai take gani banda fuska saboda karewa da bishiyan ayaba tayi, saboda da turanci suke haɗawa a maganar ya bata damar jin wani abu a ciki.
Wanda ke maganar yace, “Boss! Nima ganin hoton nan ya matuƙar tadamin hankali, dan bamu saniba koma bashi kaɗai baneba, tunda wannan ma a tsakkiyar file ɗin nan na companyn na samesa”. Cikin tsananin tashin hankali taji wanda aka kira boss ɗin ya fara magana da yare, kafin ya kuma dawo yi da turanci kamar zai haɗiye harshensa. “Tabbas akwai damuwa idan hoton nan ya shiga idon wani, dan zai iya zama silar buɗewar ɓoyayyen sirrina da babu wani mahaluki daya sanshi bayan mutum huɗu, suma ɗin ba komai suka saniba akai sai abinda na sanar musu. SB kayi gaggawar ɓatar da hoton nan, sannan dolene a cikin watannan mubi kaf takardun nan mu bincikesu dama gidan gaba ɗaya, sai mun tabbatar da babu wani makamancin irin wannan hoton sannan hankalina zai kwanta, zan shigo Lagos ɗin nima amma bari sai tafiya mai tsaho ta sam….”. Sai kuma ya sake komawa yin maganar da yare wancan na amsa masa.
Gani tai ɗaya na takowa alamar zai fito. Tai azamar sake maƙewa a wajen dan taɗau alwashin sai taga kosu ɗin su wanene?.
Har yayo nisa taji wancan ya tsaidashi, da turanci yace, “Kaga bani hoton nan kar a sami kuskure, zan ƙonashi ni da kaina kawai”. Batare da wancan ɗin yayi musu ba ya miƙa masa yana faɗin, “Okay sir”. Daga haka ya juyo zai fita.
Da kallo Aymah ta bisa harya ɓacema idanunta, bata sanshiba, dan babushi a cikin duk waɗanda aka nuna mata a cikin gidan. Jin ana takowa za’a fito ya sata sake komawa da sauri ta maƙe. Wani irin waro idanu tayi ganin Papa ne ya fito. Ta bisa da kallo zuciyarta na wani irin motsi a ƙirjinta. Sai da ta hangi ya shige cikin falon gidan sannan ta sauke ajiyar zuciya ta fito a wajen zuciyarta na mamakin wane sirrine yake iƙirarin babu wani mahalukin daya sani sai mutane huɗu?. Miyasa yace sanin zai iya zama sanadin buɗewar sirrinsa? ‘Sirrin mi to?’ ta ayyana a fili cikin jimami.
Wata zuciyace tace, ‘Ke ko Aymah ina ruwanki, ko shishshigi da son asani. Hakane fa’. ta sakke ayyanawa a ranta tana barin wajen. Daga nan ma sai ta koma cikin gidan itama.

Kamar wasa sai ga tattaunawar papa da baƙonsa ta kasa barin ranta. Duk yanda taso yakicewa abin sai sake tisa kansa yake a zuciyarta. Haka kawai takejin ƙwaɗayin son ganin hoton nan. Sai dai idan tacema zata gani a ina zata gansan? Tunda yace ƙonawa zaiyi. Koma bai ƙonaba tayaya zata iya shiga ɗakinsa binciken hoto?.
Waɗan nan tambayoyi sunta mata kaikawo a zuciya har lokacin Yoohan ya shigo gidan bata sani ba.

Yoohan da ƙarfe takwas na dare da wasu mintuna jirginsu ya sauka sun iske guards ɗinsa na jiransu a airport, basu wani ɓata lokaci ba suka nufo gidan. Lokacin da suka shigo basu iske kowa ba a falon sai Blessing dake shirya dinner. Itace ke sanar musu ai su Momy duk sunje church. Baice komaiba yay gaba Solomon na biye da shi har ƙofar sashensa. Cikin in-ina da rawar harshe Solomon yace, “Sir! Ga kayan inaga ni basai na shiga ba?”. Da ɗan mamaki Yoohan ɗin yay masa kallo ɗaya ya ɗauke fuska a tsuke, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru yana miƙa masa hannu alamar ya bashi kayansa dake a hannunsa. Saurin miƙa masa yay da faɗin, “Am sorry sir ba laifina bane dokar madam ce hakan”. Shi dai Yoohan baice masa komaiba ya amsa ya rufe ƙofar. Harga ALLAH shi Solomon ma dariya yaso bashi. jin ko ina shiru yayi tunanin kota kwanta ne? Ya ɗan kalli ɗakin sai ya wuce nasa kawai. Wanka kawai yayi ya fito dan sai da yayi salla tunkan su taho. Abincin dake kan dining ɗin ya nufa ya buɗe, shinkafa ce dafa duka da taji haɗin kayan lanbu tanata ƙamshi, sai gasashshen nama kaza da haɗin salad a gefenta. Zama yay ya zuba abincin kaɗan yasa salad ɗin da yanka ɗaya na naman dan yunwa yakeji, rabonsa da abinci tun breakfast saboda aikin daya sha masa kai.
Baifi lauma uku ba aka turo ƙofar aka shigo babu ko knocking. Yasan Momy ce kawai ke masa wannan halin a gidan, ilai kuwa itace sanye cikin skirt da riga na lass, taci uban gashin Attachment da kallo ɗaya zai baka tabbacin mai tsadane dan sai walƙiya yake da ƙyalli. Bible ɗin hannunta ta ajiye saman tebirin taja kujerar kusa da shi ta zauna tana shafa masa kai. “My Boy duk yunwarce tasa ko kallon mutane ba’ayi?”. Tun shigowarta sai yanzu ya ɗago ya dubeta yana wani sake ɓata fuska. “Momy ai ke ɗince sam baƙyama mutane knocking sai dai ki….” Da sauri ta katsesa da faɗin, “To naji sarkin ƴan ƙorafi, kai kullum magana ɗaya baka gajiya zan gyara”.
Haka kullum take faɗa masa idan yayi magana, kuma bazata gyara ɗinba. Hannunta data ɗora saman sajensa tana shafawa da faɗin, “To kayi murmushi mana” ya janye da cewa “Niba fushi nayi ba yunwa nakeji”. Jin yace yunwa yakeji duk sai ta rikice kamar ba abincin ta samu yana ci ba. Amsar spoon ɗin tayi daga hannunsa ta ɗiba takai bakinsa. Zaiyi magana tai saurin faɗin, “Hahh! Kona maka ɗura na rantse”. Yasan idan baiyi yanda take so ɗinba ba barinsa zatai ba. Dan haka kawai ya shiga buɗe bakin tana bashi. Data kai hannu saman jikinsa kuma zai ture.
Nu’aymah da tun shigowar madam Chioma surutunta yaja hankalinta ta fito ta kuma ƙyaɓe baki a karo na babu adadi. Barin jikin ƙofar tayi ta fito tsakkiyar falon sosai tana wani ɗan munafikin tari data ƙirƙiro.
Da sauri duk suka juyo suna kallonta, ganin ta cigaba da tarin Yoohan ya zare hannunsa dake cikin na Momy ya ɗauki glass cup ɗin dake cike da ruwa ya nufota. Yanda madam Chioma ta tsuke fuskane murmushi yaso suɓucema Aymah, sai ko yawu ya sarƙeta ta shiga yin tari na gaskiya. Tuni Yoohan ya manta da Momynsa dake a falon, ya riƙota da sauri ya zaunar bisa centre table da ke kusa da su. A gabanta ya durƙusa ya saka mata kofin a baki. Da sauri ta ɗora hannayenta duka biyu a saman nasa da ke riƙe da ruwan suka karasa da kofin bakinta a tare. jikinta sai rawa yake hawaye na zirara dan taji sarƙewar sosai. Ɗayan hannunsa ya ɗora a gadon bayanta yana shafawa. Kusan rabin ruwan tasha sannan ta janye, ta maida hannayen nata ta riƙe kumatunta tana ɗan murzawa da sauke wahalallen numfashi irin na wanda ya sarƙe. Cigaba yay da shafa mata bayan yana jera mata sannu.
Kanta a duƙe ta tokare gwiwar hannunta da cinyoyinta ufan bata iya cemasa har tsahon mintuna kusan biyu. Sai a sannan ne madam Chioma ta taso inda suke. Hannunta ta ɗora akan nasa dake shafa bayan Aymah ta ɗan bubbuga ta wuce batare da tacema Nu’aymah sannu ba. Binta yay da kallo harta fice. Haka kawai ya samu kansa dajin haushin abinda tayin. A ganinsa ya dace ace tama matarsa sannu tunda a gabanta komai ya faru ai. Wannan halin na Momynsa ya fara damunsa shi kam. Ya kula batason kowace mace ta raɓesa a rayuwa daga ita sai ƙannensa. Kai su kansu ƙannen nasa wani lokacin fuskarta nuna ɓacin rai takeyi……..
Hannunsa da Nu’aymah ta janye a bayanta ne ya maidosa hankalinsa, saurin riƙota yay ganin zata tashi. “Ina kuma zakije?”.
Cikin ɗan sanyin muryar da sarƙewar taja mata tace, “Zanje in kwanta barci nakeji”.
“Da miya fito dake nan ɗin?”.
Baki ta tunzira masa da faɗin, “To bahar na kwanta ba surutunku kai da Momynka ya tasheni”.
“K ba momynki bace?”.
“Bayan bata sona”. Ta faɗa da iya gaskiyarta.
Tsatstsare ta yayi kawai da idanu ya kasa cewa komai. Ganin zata miƙe ya sake ruƙota, “Kinga muje kici abinci kafin kije ki kwanta ɗin”.
“A’a ni na ƙoshi”.
“Mi kika ci?”.
“Babu komai, kawai dai na ƙoshi”.
“Silly girl, kodai sauran kayana kika tattare kika cinye?”.
A yanda yay maganar sai yaso bata dariya, amma saita gimtse abinta batayi ba, ta zare hannunta kawai daga cikin nasa tana miƙewa, “ALLAH ni barci nakeji ka barni na kwanta”.
Bai sake ce mata komai ba ta raɓa ta gefensa ta wuce. Kallo ya bita da shi harta shige ta maida ƙofar ta rufe. Idanunsa yaɗan lumshe da sauke ajiyar zuciya sannan ya miƙe. Shima jiyay baya buƙatar cigaba dacin abincin, dan haka yay kiran Blessing ta telephone ya sanar mata tazo ta kwashe. Yana cikin haɗa tea a kofi Blessing ɗin ta shigo, ta tattare komai ta fice da shi, shi kuma ya nufi ɗakin Aymah da kofin shayin da biscuit guda ɗaya. Zaune ya sameta a gaban mirror tana ɗaure gashinta, ta canja kaya zuwa wando da riga na barci. Wandon ɗan fit ko cinya bai gama rufe mata ba, sai rigar itama dai babu wani girma da siririn hannu. Rikicewa tayi sosai dan batayi zaton shigowar tasa ba. Yanda taketa budum-budum ɗin neman hijjab ne ya bashi damar kallon abinda take ƙoƙarin son rufewar.
Sosai ƙirjinsa ya harba. Ya ajiye shayin a kan mirror da biscuit ɗin yana faɗin “Gashi nan kisha kafin ki kwanta”. Daga haka yay ficewarsa dai-dai da ita kuma taja hijjab ɗin sallarta data samu nasarar gani a yanzu ta ƙudundune jikinta.

Koda Yoohan ya fita da sassarfa ya rufe ƙofar falon ya kashe komai ya nufi nasa ɗakin shima. Ƙofar ya maida ya rufe ya jingina a jikinta da rumtse ido da ƙarfi. Tsaf Nu’aymah ta shiga dawo masa cikin idanu. ‘Ƴar 17years ce da wannan surar?, ko ina ya kai yanda ya kamata?’. Ya ayyana a ransa tsigar jikinsa na wani yamutsawa…………….✍

😜Ƴar yarinyace fa Dafta, ka bari sai ta girma kawai🤣🙄.

_______________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

 

*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

No. 50

____________

_Ina ma’abota karance karance littafin hausa? Wanda ke nishadantar wa ya fadakar? Kana ya tsunduma ku a kogin lobayyar kauna..?_

_*REAL FEEDO* hazikar marubuciyar nan ta zo muku da wani gangariyar littafi mai suna: *BA AMO…!* *BA AMO* wani nazartaccen littafi ne daya zo da wani irin salo na daban…_

_Labarin *BA AMO* ya faru akan wata yarinya da d’an sarkin garin su, yarinyar gidan su gidan yawa ne…Baban su yana auri saki ya tara ‘ya’ya da mata da yawa. Tirqashi! To ita yarinya sunan ta KHAIRAT… Tun farko dangin mahaifin su sun tsani mahaifiyar tasu,Bayan ya auro ta, Ta haifi yara mata zallah suna kiran ta da uwar mata kuma kwata-kwata basa kaunar ita da ‘ya’yan nata. To ita yarinya ta gama karatun ta…. wato KHAIRAT.. shekarun ta 22 matan gidan nasu suna mata gorin tayi kwantai tak’i aure. Kwatsam wata rana yarinyar ta samu labarin d’an sarkin garin su ya bude sabon company ya fara daukan sabbin ma’aikata, 🧚🏻‍♂️😍cikin ikon Allah ta zuwa ta samu aiki. Ta fara zuwa aikin ta, a karshe su kansu da suka fahimci kwazan ta da nutsuwar ta samu karin matsayi. To a lokacin ne kuma Yarima da PA dinsa suka sami matsala aka kore ta a ma’aikata sai aka daura ita Khairat d’in a matsayin P.A dinsa. Tafiyar tasu batama yi nisa ba! Aka yi makiya suka yi masu sharrin wai karuwar sa ce, har labarin yaje gun mai martaba. Itama Khairat d’in labarin yaje ga mahaifin ta har ya nemi korar ta daga gidan sa, da kyar aka lallashe shi ya hakura.._

_Tab rungutsumi din fa kenan🤮Ya zata kaya ne ga YAREEMAH GA KHAIRAT..a roof d’aya? Ya rabbi😢 labarin kauna yayi.. Amma fa Za’a sha rikici.. Karku manta khairat daga gidan yawa tafito🥺Ga basuda wani hali.. Shin sarki zai yadda da Khairat amatsayin personal assistant din yareemah ko kuwa.? Duk wannan ruguntsumi n REAL FEEDO ce kadai zata iya warware mana.._

_BA AMO::::: (Ba Labari…)_

_DOMIN MALLAKAR NAKI/‘NAKA TUNTUBE MU TA:_ +227 81 73 10 21

________________

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply