Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 55


Saran Boye 55
Viral

No. 55

………….Sai da ya dire zip ɗin har ƙasa sannan ya maidata ya kwantar, hannun rigar ya kama ya cire, ɗayanma haka. Sannan ya cire rigar gaba ɗaya ya ajiye gefe. Idanu Aymah ta rumtse da ƙarfi jin zai zame skirt ɗinma. Bata da ƙarfin iya koda magana balle tace zata hanashi yin abinda taji yana ƙoƙarin aikata mata. Tanaji tana gani ya barta daga ita sai B&P. Ji take inama ƙasa ta tsage kawai ta zurma ciki. Sai dai tasan hakan bamai yuwuwa bane. Ta na sauraren ya idasa abinda ya fara sai taji baiyinba. Saima towel ɗin daya jiƙo da ruwan ɗumin nan ya fara goge mata jiki da shi a hakan batare daya cire sauran suturar tata ba. Taji daɗin hakan har cikin ranta. Sai kuma ya ƙara mata girma a zuciya. Ta tabbata shi ɗin ba mutum banza bane. Dan inda wanine duk da bata da lafiyarnan hakan wata damace a garesa. Amma shi tana kallonsa ta ƙasan ido aikin gabansa kawai yakeyi ko kallon ƙurilla bai tsaya mata ba…….
Ajiyar zuciya ta saki a hankali lokacin daya ɗagota ya saka a jikinsa. Bayanta ya goge tsaf sannan ya ɓalle bra ɗinta. Batare daya ɗagota ba ya zare ya ajiye, a haka ya goge mata ƙirjinta tana a kife. Ɗagota yay zai kwantar ta ƙara narke masa alamar batason ɗagowar. Yoohan ya fahimci inda ta dosa. Dan haka yaɗan murmusa kaɗan cike da ƙarfin hali. “I’m sorry bazan kallaba na miki alƙawari”. Duk da tana jinsa taƙi yarda ya ɗagotan. Dole ya barta a yanda take son. Ya jawo bargo a haka ya lulluɓa mata sannan ta yarda ya kwantar da ita. Ta cikin bargon ya zare mata sauran kayan ya goge wajajen. Ya tattare kayan da kansa ya maida toilet. A washing machine ya saka ya wankesu. Ya shanya mata su bra ɗinta, kayan kuma ya barsu a boket idan Uwaliya ta shigo sai taje waje ta shanyo su.
Sake dawowa ɗakin yayi ya ɗauka mata kaya. Rigace mara nauyi da kayan ciki waɗanda dai bazasu takura mata ba. Bai damu da yanda taƙi sake buɗe idanunba. Ya bita a yanda takeso ya saka mata kayan. Sannan ya yaye bargon daga jikinta yana sauke numfashi a hankali. gyara mata abinda baiyiba yayi ya ɗauketa cak zuwa bayi yana faɗin, “Muje kiyi fitsari nasan kinaji ko?”.
Kanta taɗan girgiza masa alamar a’a. Bai saurareta ba ya kaita, da taimakonsa tayi fitsarin da brush. Yana dawo da ita Uwaliya nayin knocking. Buɗe mata ƙofar yay ta shigo. Tana ajiye kunun gyaɗa data damo da soyayyan ƙwai dan aɗan zaman da tai da Aymah ta fahimci tana san soyayyen ƙwai.
Zama yay da kansa ya bata cikin lallashi kamar ba shi ba. Da farko taso ƙinsha amma lallaɓatan da yake yine ya sakata daurewa tasha. Dan yanda takejin muryarsa duk sai taji babu daɗi..
Idanun nata ta buɗe a hankali tana kallonsa. Yanda yaketa yawan kai hannunsa yana murza goshinsa ne yasata tunanin shima kamar baida lafiyan. Ga jijiyar kansa tayi ruɗu-ruɗu. A bazata yaji hannunta bisa goshinsa.
Saurin ɗago idanunsa yay yana kallonta. Daɗi yaji a ransa ganin ta ƙara buɗe idon harma yafi na ɗazun. Ya ɗora hannunsa shima akan nata data aza bisa goshinsa. “Kina buƙatar wani abu ne?”. Yay maganar a hankali yana kwantar da kanta a jikinsa.
Kai ta girgiza masa. sai kuma ta sake ɗagowa tana kallonsa ƙasa-ƙasa sosai, da alama batason buɗe idanun saboda ciwon kai da ke addabarta. Cikin magana ƙasa-ƙasa sosai da shi kaɗai ke iya jinta tace, “Kaima kanka na ciwo ko?”.
A bazata murmushi ya subuce masa. Ya sumbaci goshinta tare da sake maida kanta ya kwantar a ƙirjinsa yana shafa damtsen hannunta a hankali batare da ya bata amsar tambayar tata ba.
Ƙare lafewa tai bata sake magana ba itama. Sai ma barci daya sake ɗaukarta a haka saboda allurar bata gama sakinta yanda ya kamata ba.

Idanu ya tsura mata na kusan mintuna goma, a zahiri kallonta ya keyi. a baɗini kuwa ya tafi duniyar tunani mai zurfi. Ganin ta koma barcinne ya sakashi sauke ajiyar zuciya da sake maidata ya kwantar ya lulluɓeta. Fita yay dan yana son shirya abinda ya dace, ya kumayi sallama da jama’ar gidan. Dama ya kira Papa tun ɗazun sunyi magana. Papan ma yace zai samesu acan ƙasar Austria ɗin shima a randa za’aymata aikin.

________★★★_______

Dukkan abinda ya dace Yoohan ya kimtsa akan tafiayarsu ya tattara. Yayi sallama da kowa na gidan. Momy dai nata baƙin rai dan tace zata bisu yace a’a. Ta bari idan papa ya dawo sai suzo tare.
Bayan la’asar ƴan gidan su Abba suka iso, har dasu Adawiya. Duk ƙiyayyar da Adawiya kema Aymah yau sai da tai hawayen tausayinta kamar yanda su Yusrah keyi suma. Ƙarfe biyar dai-dai Ambulance da zata ɗauki Aymah ta shigo gidan tare da Dr Shikurah.
Yoohan ya ƙara duba komai na sashen nasu, ya tabbatar ya kashe duk wani kayan wuta, an kuma fidda duk abincin da zai iya lalacewa. Da kansa ya kulle ko’ina ya saka keys ɗin a jikkarsa. Duk ƴan gidan sun fito compound, babu dai wanda ke nuna jin daɗinsa da halin da Nu’aymahn ke ciki a zahiri. Sai dai a zuciya ALLAH kaɗai yasan karatun kurma.
Duk waɗanda zasu musu rakkiya airport sun shiga mota, harda Uwaliya da zata koma da zama gidan Abba sai su Aymah sun dawo. Haka motocin suka fita a jere waɗanda aka bari na binsu da addu’ar ALLAH yasa a dace.
Tafiyar mintuna kaɗan ce ta kaisu airport. kasancewar jirgin nasu na gab da tashi aka shiga da Aymah cikin jirgin, kafin suma su Yoohan da sauran passengers su shishshiga. su Abbah na binsu da addu’a kafin suma su taho. Basu bar airport ɗinba sai da jirgin ya ɗaga a samaniya ƙarfe biyar da rabi dai-dai.
Sun sauka a Dubai, daga can suka shiga jirgin kaisu Austria.

________★★★_______

Tun jiya Nu’aymah keta zuwama Umm a rai. Ta kira wayarta kusan sau uku kuma a kashe. Gudun karta saka abin yay mata tasiri a rai sai ta barshi akan Aymah bata da cajine maybe. Ko kuma ta kashe wayar a wajen shiriritan ta.
Haka taita juriya har washe gari da baba malam ya dawo daga tafiya. Shine ya lura da yanayinta. Cike da kulawa ya shiga tambayarta ko lafiya?. Duk yanda taso dannewa kartace komai saita gaza. Muryanta a sanyaye tace, “Haka kawai taketa zuwamin a zuciya tun jiya. Na kirata kuma wayan nata a kashe. Na nema Uwaliya mun gaisa nace ta bata tace min wai barci takeyi. dana sake kira daga baya kuma itama wayan tata a kashe. sai nakeji a raina kamar ba lafiya ba”.
Ɗan jimm baba malam yay yana kallonta. Dan Abbah ya kirashi bayan sallar magriba ya masa bayanin cewar jikin Nu’aymah ya motsa sosai harma sun wuce Austria yau da yamma. Murmushin ƙarfin hali yayi dason kwantar mata da hankali. Yace, “Babu komai insha ALLAH sai alkairi. Kimata addu’a kawai nasan zata kiraki idan ta kunna wayar. Nima tun jiya da safe bamu sake waya da itaba ma. Karki damu Jannat, ALLAH na tare da Zainab a duk inda take”.
Yanda ya ambaci ainahin sunan Nu’aymah ya sake sakata jin wani iri. Amma sai ta danne dan karta sake ɗaga masa hankali shima.
Daga haka suka bar maganar, sai dai daren ranar daga farkonsa har ƙarshe akan sallaya Umm da Baba malam suka kwana suna mikama UBANGIJI kukansu akan lafiyar yarinyarsu. Duk da ita dai Umm batasan ainahin abinda ke faruwarba.

____________********___________

Jirgin su ya sauka lafiya a babban birinin ƙasar Austria, Vienna International airport. ananma dai Ambulance ce tazo ta ɗauki Nu’aymah, Yoohan da Richard & Solomon kuma suka shiga taxi. Tafiyar mintuna kalilan ta kaisu katafaren babban asibitin Vienna daya haɗu harya gaji. Babu ta yanda za’ai ka ɗauka asibiti ne na gwamnati inba faɗa maka akaiba. Sannan abun zai matuƙar birgeka a yanda suka samu tarba. Ko hakan yanada nasaba ne da sanin Yoohan ɗin oho.
Ɗaki na musamman inda sam babu hayaniya aka kai Nu’aymah. Da alama ma an tanajesane domin irin masu matsalarta. Wajen koda takalmi mai ƙara ba’a shiga. Kai ko key ƙaramin alhaki ba’a buƙata. Duk wani abinda ke’a sashen na amfani zaka samu na robane saboda tsabar sanin makamar aiki. (a raina nace hummm ya kaga irin haka a 9ja😁).
Gaba ɗaya Aymah batasan a inda kanta yake ba, dan tun daga 9ja aka yo mata allurar data sakata doguwar suma saboda ba’a buƙatar duk wani motse-motse a kusa da ita.
Sai da Yoohan ya tabbatar an ɗorata akan matakin farko sannan suka bar asibitin. Hotel ɗin da Yoohan yafi sauka idan ya shigo ƙasar suka nufa. Acan suka kama masauki. A kallo ɗaya zaka fahimci shima yana buƙatar kulawar, dan haka Rich ya matsa masa akan yay wanka yaɗan kwanta koda bazaiyi barcinba zai huta.
Bai musaba yabi shawararsa. Shi kuma Rich ya fita zuwa nasa ɗakin. Bayan ya fito a wankan gorar ruwan addu’oin da Abba ya bashi ya fiddo, yay bismilla ya sha tare da shafe fuskarsa zuwa kansa sannan ya kwanta yana ambaton sunayen ALLAH da tuni ya gama haddacesu a kansa. Tun yanayi laɓɓansa na motsawa har ya komayi a zuciya. Cikin amincin UBANGIJI gagara misali sai gashi nannauyan barci yayi gaba da shi cikin lokaci ƙanƙani. Sai dai yayisa ne cike da mafarkin Nu’aymah. Hakan yasa bai wuce awanni uku ba ya farka. Alhmdllh ko yaya dai yaji sassauci ba kamar ɗazun ba. Ganinma lokacin salla yayi sai kawai yayo alwala yazo ya kabbara salla. Ko raka’ar farko bai ƙulla ba Richard ya shigo ɗakin domin son dubashi.
A wani irin mugun shock yace, “Jesus!! Yoohan!! Salla ka komayi?”.
Bai samu amsa daga Yoohan ba dan shi gaba ɗaya ma hankalinsa baya a nan kusa. ya nutsu sosai wajen bautar ALLAH.
Ruɗani iya ruɗani Rich ya shiga. Dan a take gumi ya jiƙesa sharaf ya nata kaikawo da surutai kamar wani zararre.
Shi dai Yoohan bai katse sallarsa ba, sai da ya idar a tsanake yay addu’oin fatan samun lafiya ga matarsa sannan ya dubi Richard da ya kasa zaune ya kasa tsaye. A daƙile yace, “Lafiyarka kuwa?”.
“Kai zan tambaya kana lafiya kuwa Yoohan?!. Salla fa naga kanayi?!”.
Idanu kawai Yoohan ya tsurama Rich dake maganar da yare tamkar zai haɗiye harshensa.
Ganin kallon da yake masa ne ya sake harzuƙa Richard ɗin, ya hayayyaƙo ma Yoohan da iya masifarsa, “Yanzu wannan ƴar yarinyar har takai ta canja ka ka bar addininka na gaskiya ka koma nata. John What’s wrong with you? Are you mad? Are you…………?”.
Saurin katsesa Yoohan yayi ta hanyar ɗaga masa hannu.
“please Richard!!. Ni ƙaramin yaro ne da zaka zauna kana min ihu a kai? Karka manta shekarata ɗai-ɗai har talatin da biyu. Kasan kuwa inada right ɗin zaɓama kaina abinda nasan ya dace dani ko?…….”
“Yes! Kanada zaɓi, kuma shekarunka sun kai. Amma tabbas alamu sun nuna baka a cikin hankalinka ne. Shin ƙyawunta ne ya ruɗeka kokuwa kuɗin da mahaifinta ya mallaka? Sunan da yay? Kokuwa asiri sukai maka?”.
A kanran farko Yoohan yay wani malalacin murmushi, sai kuma ya tsuke fuska tare da jan tsaƙi yana bin Rich da wani irin shegen kallon ɓacin rai da fusata. “Richard! Mubar wannan maganar dan ni ta shafa…….”
“Nima ta shafeni Yoohan. Dan ka wucemin aboki kai ɗan uwana ne jinina da zan iya bama kariya a kowanne irin yanayi a kuma kowanne irin hali”.
“Tunda kasan hakane sai ka bani lokaci dan ka fahimceni”.
Baki Rich ya buɗe zai ƙara yin magana Yoohan yay azamar ɗaga masa hannu.
“Please Rich, kana ƙaramin headache. Ka bani lokaci zamuyi magana”.
Zama kawai Richard yayi batare da ya sake magana ba. Dan yasan Yoohan ɗin ya kai maƙura kenan. Idan ya cigaba da jan maganar komai zai iya faruwa a tsakaninsu. A ganinsa kuma yanzu na lokacin samun matsala bane. Kamata yay ya taimakama Yoohan ɗin ya dawo cikin hankalinsa dan ya fahimci an gusar masa da hankaline kawai ta hanyar asiri. Shiru ɗakin ya ɗauka har zuwa wasu mintuna kusan ashirin. Kafin Yoohan ɗin ya fara miƙewa ya ɗauka jacket ya ɗora saman ƙananun kayansa. Batare da yayi magana ba ya nufi ƙofar fita. Shima Richard ɗin miƙewa yay yabi bayansa suka fice daga hotel ɗin. a waje suka tari taxi dan komawa asibitin.

__________★★★★___________

*_WASHE GARI_*

A yau data kama ranar da za’aima Nu’aymah aiki su baba malam sukaso tahowa shi da Abban Abdallah. Sai dai a bisa dalilin wani ɗan tsaiko hakan ya gagara. Tafiyar tasu ma ta tabbata sai zuwa jibi idan ALLAH ya kaimu.
Hakan baisa sun sare zaman jigum-jigum ba. Sai sukai zaman yin addu’oin samun nasara a aiki dan yanda Yoohan keta maimaita a tayasu da addu’a yana ƙara saka tsoro a zukatansu. Shi kansa sun fahimci a tsoratan yake. Saboda bai ɓoye musu ba game da haɗarin da aikin da za’ai mata ke da shi tun farko. Sai dai idan ALLAH ya amince sai ayi kaga kamarma bata taɓa shiga makamancin matsalar ba.
Hajjo har abincin sadaka tasa akayi, aka kuma sayi abubuwan wasan yara da makamantansu aka rabama yaran gidan marayunsu don suyi farin ciki suma. Maybe darajar hakan ALLAH ya saka musu hannu a lamarinsu suma.

*_ƘASAR AUSTRIA*

A nan kuwa Yoohan cike yake da fargaba. Sai dai yanata ƙoƙarin dannewa saboda kwarin gwiwa da Dr Liam Ke basa akan aikin. Dan shi da Rich sai a hankali. Ya ɗauki fushi dashi babu gaira babu sabar. Shi kuma sai hakan yay masa zafi ya tattarashi ya watsar. Ko game da harkar asibitin ya daina tuntuɓarsa da komai. Idan abu yake buƙata zaisa Solomon ne kawai yayi masa. Kai a yau ma gaba ɗaya baisa Richard ɗin cikin idanunsa ba har yanzun da suke shirin shiga da Nu’aymah ɗakin da za’ayi aikin.
Baya buƙatar haɗama kansa damuwa da yawa. Shiyyasa ya ɗauki lamarin Rich ya ajiyesa gefe. Dan shi dai abinda ya sani bazai taɓa komawa abinda Richard ɗin ke buƙataba dan ALLAH ya nuna masa ƙyaƙyƙyawar hanya a yanzu mai cike da ɗumbin haske. Ai ko papa dake matsayin mahaifinsa bai isa sashi komawa kafiri ba balle Richard duk da kuwa yana sonsa har cikin ranshi.

Sai da ya kammala shiryawa tsaf cikin kayan da zasuyi aikin. Ya gabatar da salla raka’a biyu sannan ya fito ya ƙarasa kimtsawa. Kasa shiga yay ɗakin da Aymah take domin fiddota zuwa ɗakin theatre ɗin.
Sai su Dr Sophia suka fiddota yana tsaye a ƙofar ɗakin. Cike da rauni ya bita da kallo samɓal akan gadon da aka turota tamkar gawa. Dan sun mata wata allura ne tun awa biyu da suka wuce. Wannan allura kuwa itace wasu da yawa masu irin matsalarta daga an musu ita suka tafi doguwar sumarnan shikenan har abadan. Ko an kammala aikin basa farfaɗowa. Wasu kuma koda sun farfaɗo sukan kasance komai sun manta na rayuwarsu ta baya. Sai an sake koya musu komai tamkar jinjiraye. Wasu kuma akan dace su tashi cikin rahamar UBANGIJI.
Wannan shine fatan su Yoohan akan Nu’aymah. Har aka shigar da ita hankalinsa yayi nisan kiwo wajen tafiya a dogon tunani. Sai da Dr Liam Yazo ya kama hannunsa ne ya kawo nannauyan numfashi. Lumshe idanunsa yayi ya buɗe a hankali akan ɗakin, Dole ne ya dawo da jarumtarsa jikinsa inhar yana son samun nutsuwa akan aikin nan duk da bashi kaɗaine zai gudanarba.
Ya cija lip ɗinsa na ƙasa. Cike da ƙarfin hali da ƙarfafa kai ya nufi ɗakin zuciyarsa na wani irin bugu dai-dai da takunsa.
“ALLAH ya bada nasara”.
Yaji an faɗa a bayansa. Cak ya tsaya tare da lumahe idanunsa ya buɗesu kafin ya juyo dan yasan Richard ne. Kallonsa yay kusan na sakon biyar cike da rauni. Sai kuma ya tako inda yake ya zo ya rungumesa idanunsa cike da ƙwalla.
Bayansa Rich ya shafa cike da kulawa. “Zakayi nasara X-man, Please ka yarda da kanka”.
Ɗagowa Yoohan yayi suna kallon juna. Rich ya jinjina masa kai yana murmushi. “Ka yarda da ni, inaji a raina matarka zata tashi da yarda ALLAH, kodan taimakon mutane da yawa da kayi a rayuwarka a dalilin wannan aikin. Kaima ALLAH zai baka farin ciki akan matarka yau”.
Yoohan yaji daɗin maganar Richard, dan haka ya sake rungumesa yana faɗin, “Thanks you Rich, I proud of you”.
Sake shafa bayansa Richard yayi shima yana murmushi, dan har cikin ransa yana ƙaunar Yoohan, ba kuma zai iya dogon fushi da shiba komi ya zama, kai koda kuwa criminal ne shi zai iya cigaba da sonsa da taimakonsa. Yasan wanene Yoohan tun ƙuruciya. Ya tabbatar kuma bazaiyi abu kansa tsaye ba sai da dalili. shiyyasa yaga ya dace ya ajiye fushin da yake yi da shi ya bashi ƙwarin gwiwa akan abinda ya kawosu har komai ya dai-daita. Ya tabbatar zai masa bayanin dalilinsa na komawa mai salla. Wannan shine dalilin dawowarsa. amma da har masauki ya canja tun a daren jiya. Proud of you too”. Ya faɗa shima sunama juna murmushi.

Koda Yoohan yazo shiga ɗakinma sai da yayi addu’a sannan ya shiga. Duk Doctors ɗin da zasu gudanar da aikin sun hallara, da alama ma shine kawai bai shigoba. Handglove ya cira ya sakama hannunsa. Ya zari Norse mask ma ya saka, duk abinda yakeyi idanunsa na akan ƙyaƙyƙyawar fuskar Aymah ne. Tayi wani irin ƙyawu fiye da wanda ya santa dashi. Fuskarta tayi fayau ɗan bakin tsiwarnan yana a tsuke. Ƙoƙarin maida ƙwallar data cika masa idanu yayi yana Murmushin tuno tsiwa-tsiwar data ringa masa tun daga haɗuwarsu har zuwa rayuwar aurensu ta ƴan kwanaki. Bai taɓa jin haushiba dan tana masa tsiwa. Hasalima wani lokacin yana takalarta ne dan kawai tayi masan. Saboda tsiwarta dake burgesa ko son ganinta shiru-shiru bayayi sam. Ya ƙarasa gaban gadon ya durƙusa a saitin fuskarta. Hannunta ya kamo cikin nashi ya riƙe, ɗayan kuma ya aza bisa kucinta na dama. Ya kafeta da kallo idanunsa na sake bayyana jan damuwa. Baice komaiba har tsahon mintuna biyu kafin ya miƙe yana haɗiyar zuciya da murmushin da baisan dalilinsaba shima.

Tunda suka fara aikin kuma sai jarumta ta baibaye Yoohan. Duk wani rauninsa da fargaba suka gudu. Ya maida hankali sosai akan abinda sukeyi da yaƙini da fatan samun nasara. Ko sau ɗaya baiyi saken addu’a ta ƙuɓucema zuciyarsa da harshensaba. Ambaton ALLAH yake tayi gwargwadon abinda ALLAH ya bashi ikon sani.
Sun shafe tsahon awanni a cikin ɗakin. Solomon da Richard na zaune a waje idanunsa nakan ƙwan lantarkin dake a waje. Fatansu kawai suga ja ya koma green. Sai dai tun suna saran hakan a kusa har suka fara sarewa. Dan ba ƙaramin daɗewa su Yoohan sukai ba basu fito ba..

(Ya rabbi ka bamu ikon cinye jarabawa😭🙏🏻).

★★★★

Kamar yanda su Rich ke cike da fargaba acan Austria, anan gida Nigeria mas baba malam cike suke da fargaban. Sai dai sun miƙa lamuransu ga UBANGIJI akan koda rasa Nu’aymah sukayi haka ALLAH ya ƙaddara. Kuma sun tabbatar hakan shine mafi alkairi a gareta. Sai dai fatan ALLAH ya basu haƙurin hakan.
Idan kuma ALLAH ya ƙara ƙaddara mata cigaba da wata rayuwar a gaba suna fatan nasara akan wannan aiki. ALLAH kuma ya hana samuwar loosing memory a gareta darajar Al-qur’ani izifi sittin dake haddace a cikin kanta da ƙirjinta.

Duk bayan wasu awa guda baba malam kan kira wayar Yoohan yaji ko sun fito. sai dai ba’a ɗagawa. Hakan ke sakashi fahimtar basu fito ɗinba kenan. Ko yace ya haƙura bazai sake kira ba har sai Yoohan ya kirashi sai ya kasa haƙurin bayan shuɗewar lokaci sai ya ɗauka wayar ya sake kira ɗin. Tunfa yana saka ran ganin kiran Yoohan a kusa-kusa har lokaci mai tsayi ya shuɗe. Yana son shiga gida amma ya kasa dan bayason zuwa yaga halin da Umm take a ciki itama. Yasan suna tsananin son Nu’aymah, da wannan damarma maƙiyansu keyin amfani wajen azabtar da su, saboda sun gama fahimtar itace tarkonsu. Sai dai hakan bashi ke nufin bazasu iya haƙuri ba idan ALLAH ya amsheta. Dan dama ai shine ya basu batare da yayi shawara da su ba.

****
A tare Richard da Solomon suka miƙe tsaye ganin jar wuta ta mutu blue ta kawo. Suka kafe ƙwayeyen uku da ido cike da tashin hankali. Rich likitane, yasan mi blue ɗin wuta ke nufi saɓanin green da sukai fatan gani. Shi kansa Solomon kasancewarsa tare da Yoohan a koda yaushe yasan ma’anar hakan. Cike da rauni suka kalli juna sai dai babu wanda ya iya furta komai.
A hankali ƙofar ta zuge, wani irin mummunan faɗuwar gaba ta riski Solomon da Richard a lokaci ɗaya saboda ganin an fito da Yoohan a gadon da aka shiga da Aymah alamar dai suma yayi. Daɓar Richard ya koma ya zauna kansa na juya masa. dan fito da Yoohan a wannan halin kawai shine amsar dukan tambayoyinsu akan rasa Nu’aymah……………✍

*_Inason naja hankalin masu karatu anan. Wlhy kasancewar Nu’aymah matsayin jarumar littafin SARAN ƁOYE bashi ke tabbatar da bazata iya rasa ranta ba. Dan haka kar mu saduda akan wai dole labarin bazai tafi yanda ake buƙata ba sai tana raye. Wannan gurɓataccen tunani ne. Mutane nawane masu muhimmanci a rayuwarmu suka fita kuma gamu namu LABARAN basu daina tafiya bisa ƙaddararmu ba😭. Rayuwar Nu’aymah ba itace tabbacin fiddo da aynahin saƙon da SARAN ƁOYE keson isarwa ba. Dan haka Please karku saka rai, kar kuma ku sare, dan SARAN ƁOYE yazo muku ne da sabon salo da gasken gaske, dan haka mu daure wajen amsar salon da yazo mana da shi dan ALLAH😔😭🙏🏻🚶🏼‍♀️._*

ALLAH ka gafarta mana😭🙏🏻.

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply