Bakar Inuwa Hausa Novel Hausa Novels

Bakar Inuwa 22


Bakar Inuwa 22
Viral

Episode 22_*

 

………..Ganin taƙi cin komai Anne ta kira sunanta. Ta ɗago domin amsawa taci karo da wata wulaƙantacciyar harara data saka zuciyarta da hanjin cikinta tsargawa da ga gimbiya Su’adah. Saurin maida kanta tai tana amsawa Anne da rawar murya. Babu wanda ya lura da hararar sai Pa da Hajiya Shuwa. Dan haka Pa shima yay ɗan gyaran murya da sakin murmushi yana faɗin, “Ɗiyata ki saki jiki kici abinci kinji, munan family nakine na biyu insha ALLAH. Dan haka kar kiji komai kici duk abinda kike buƙata, kema mai baiwa wanine”.
Kai Raudha ta jinjina. Muryarta a risine ta ce, “To Abba nagode”.
Kiran da Ramadhan yayma Bilkisu ya hana kowa sake magana, ta miƙe tana amsa masa. Babu jimawa ta dawo ta fara zuba kunun gyaɗa a kofi. Anne ce tace mizatai da shi.
Cikin ɗan tura baki tace, “Yayane yace na haɗa masa nakai masa can”.
“Kunun kawai?”.
“Eh Anne shi kaɗai yace”.
“Bazai yuwu ba haɗa masa abinci, ni bansan mike damunsa ba yanzu bai son cin abinci duk ƙaunar dake tsakaninsu ada, yanzu babu ita.”
Bappi da tun ɗazun baice komaiba ya ɗan kalli can cikin falon inda Ramadhan yake yana faɗin, “Wannan hayaniyarce kawai ba wani abu ba, bara kiga ya samu nutsuwa zai koma cin kayansa.”
“Hakane”
Anne ta faɗa cikin tausayawa.
Raudha kam duk abinda ake tanaji kamar kowa, sai dai tana tsakurar abincinne da satar kallon yanda aka loda masa uwar madara a cikin kunun da bai gaza rabin kofi ba. A ranta take gulmar kunu zai sha ko madara?. Bata da mai bata amsa dan haka ta haɗiye gulmarta a ciki.
Koda Bilkisu takai masa kunun kawai ya ɗauka da farfesun kan rago, sauran kuwa ta dawo dasu. Adalilin dawo da kayanne take jin Yafendo na faɗin, “Ai kunga dai bazai cin ba, amma ya ɗauka masoyinsa Nama da madara, dan wancan kunu dai madarace kawai ba kunu ba”.
Dariya suka sanya, yaran nayi ƙasa-ƙasa. Anne tace, “Ai Ramadhan da nama sai kace wani kure, shi dai yaci nama. Bansan irin wannan ƙauna ba. Ko rai aka ɓata masa baya ƙin cin nama saboda son shi da yakeyi”.
Nan ma dariyar suka ɗanyi, ita dai Raudha nata murmushi ne kawai.

★★★

Da zasu koma batare da shi da Pa da Bappi ba, su sun wuce cikin masarauta ne, su kuma direct airport. Hakan ya saka Raudha jin daɗin komawar, dan sai ita kaɗai a vip ɗin. Sai dai tanata kallon tarkacensa daya bari a wajen da shaƙar ƙamshinsa tamkar yana nan, ta sake rimtse agogonsa dake cikin hannunta wanda da zasu fito daga falo a Taura Anne ta lura da shi ya manta a inda ya zauna, shine ta sata ta dakkosa. Koda ta ɗakko ta bama Anne cewa tai ta ajiye a wajenta ta bashi da kanta. Wannan shine dalilin tahowa da agogon har cikin jirgi tunda bata gansaba har suka baro Taura, yanzu kuma sai take ganin kamar bai dace ta ajiye anan ba gara ta bari ta bashi hannu da hannu. Sai dai kuma a ina? Yaushe kuma?. shine ke mata kaikawo a zuciya har jirginsu ya iso Bingo city batare da ta yanke kwakwarar shawara ba. Daga ƙarshe ma sai ta turashi cikin bag ɗinta batare da tasan dalilin yin hakan ba..
Koda suka sauka Anne sawa tai a maidata gida direct. Tai godiya batare data iya kallon kowa ba. har mota su Fadila suka mata rakkiya da nacin ta basu number ɗinta. Fuskarta ɗauke da murmushi tace musu itafa bata da waya.
A tare suka waro idanu waje. Rumaisa tace, “Kamarki matar Yaya guda baki da waya? To miyasa? Dami kuke gaisawa da Yaya kuma?”.
Cikin son kauda musu zargi tace, “Dokar Abbanmu ne sai kayi aure zaka riƙe waya”.
“Woow imagine! Dama akwai masu biyayya irinku har yanzu game da waya?”.
Basma ta faɗa da mamaki, dan su tun suna jss 1 ma sunada wayoyi, koda Ramadhan ya ƙwace a wancan lokacin basu ƙulla wata gudaba iyayensu mata suka saya musu wasu sukace su dinga ɓoyewa kar Ramadhan ɗin ya gani. Kuma haka akai har suka shiga ss 1 bai san sunada waya ba. Sai da ya saya da kansa ya basu.
Murmushi kawai Raudha tayi, yayinda Rufaidah ke faɗin, “Ai yanzu an saka miki ranar aure ya kamata Abba ya barki ki riƙe, zan faɗama Yaya kuwa”.
Kafin Raudha tayi magana har sun ɗaga mata hannu sun bar wajen saboda kiran da Sumayya ta ƙwala musu.

_______________________

Alhmdllhi an kammala zaɓen shugaban ƙasa, duk da dai a wasu sassa an samu ƙananun hatsaniya na matasa da kuma sace akwatin zaɓe. Sai dai Alhmdllh abun bai tsamari ba jami’an tsaro suka tsawatar. Zuwa yanzu babban fatan kowa shine hayewar wanda ya zaɓa. Inda wasu ko barcin kirki basayi musamman ga ƴan takarar idonsu kyam a tv, wasu kuma a redio ana sauraren sakamakon zaɓuƙan jihohi.
Sai dai abin zai baka mamaki idan nace ga Ramadhan ba haka bane, dan shi tamkar ma an basa lokacin samun damar yin barci ne. Ko sau ɗaya bai taɓa zama kallon sakamakon zaɓe ba balle damuwa da yaya komai ke tafiya. Lokaci-lokaci dai yakanji ihun yaran gidansu na faɗin Yayanmu ya haye jihar kaza. Daga haka bazai iya ƙaras da komaiba kuma.

A randa ake tsumayen jin sakamakon zaɓen kuwa ƙasar tayi tsitt kowa ya kasa kunne, inda masu shirin kota kwana ke shirye tsaf na tada tarzoma ta kowanne sashe. Dan dayawan sauran ƴan takarar sunfa fahimci wanda zai iya kai labari kai tsaye. Dan haka suka shirya sai dai kowa ya rasa. A sashen su Alhaji Yaro glass duk da sunga alamun nasararsu hakan bai hanasu shirya nasu ƴan tada zaune tsayen ba suma, dan a cewarsu ko da zata kwaɓe sun shirya.
To suma dai jami’an tsaro sun shirya tsaf dan bada kariya ga al’umma kamar yanda Ramadhan yasa Bappi kiran I.G da General da sauran manyan shugabannin hukumomin tsaron ya nema alfarmar su tsaya da ƙarfinsu wajen ganin wani harmutsu bai tashiba dan ALLAH…

★A ranar talata ƙarfe huɗu da mintuna talatin da bakwai na yamma shugaban zaɓe prof. Rabilu S Barde ya sanar da sakamakon zaɓe ga wanda ya lashe kujerar shugaban ƙasar NAYA.
Sabon shugaban ƙasa da komai nasa yazo da mamaki da sabon sauyi. Matashi na matasa, *Barr Ramadhan B. Hameed Taura*.

A hankali kofin fura dake hanun Ramadhan da fitowarsa kenan daga kitchen ɗin Anne yaje ya ɗebo furan dan yasha saboda barci daya tashi a makare yay sallar la’asar a ɗaki ya sulale ƙasa ya tarwatse saman Mable’s ɗin da aka ƙawata falon da shi. Babu zato babu tsammani jikinsa ya kama rawa, dan harga ALLAH sakamakon zaɓen yazo masa a bazata, bai taɓa saka ran zaici ba dan yasan akwai manya a gabansa, duk da shike da ɗaurin gindin masu mulkin ƙasar da manya. Wasu irin hawayene masu ɗumi suka silalo masa a saman kumatu, ƙafafunsa da suka nema gaza ɗaukar gangar jikinsa sukai ƙasa ya durƙushe akan gwiwoyin sa biyu har ɓallin ƙofi na ji masa ciwo. Amma sai bai kulaba duk da zafin daya ratsasa sai ya tafi sujdah.
Anne da Bappi, Yafendo, Inna, Pa Siyama, Bilkisu ma dake falon duk Sujudan suka tafi kamar yanda yayi. Kafin su ɗago su bilkisu su cika falon da ihu saboda shigowar sauran ƴammatan gidan da gudu suna ihun murnar yaya ya haye.
Duk wannan ihu dake faruwa Ramadhan ya kasa ɗagowa daga sujida sai da Pa yazo da kansa ya kamashi ya ɗago da shi. Sai kawai ya fashe da kuka ya rungume Pa ɗin.
Pa dake murmushi shima idonsa cike da ƙwalla ya shiga shafa bayansa a hankali. Tsit falon yayi suna kallon yayan nasu, dan da yawansu zasu iya rantsuwar basu taɓa ganin kukansa ba kamar haka. Garama irinsu Mardiyya dake bimasa a yanzu kuma duk suna gidan aurensu.
Taɓa kafaɗarsa da Bappi yayi ya sakashi sakin Pa ya juyo ya rungume Bappin. Anne sai tazo dukansu ta rungumesu. Hakan yasa yaran gidan duka zuwa suka rungumesu su duka suma.

A ɓangaren gimbiya Su’adah kam ai tsabar farin cikin ta zama uwar shugaban ƙasa jitai tamkar ta ciji uwawunta. A take ta fara amsa wayoyin taya murna ga ƴan uwa da abokan arziƙi. Yau sam babu ɗaure fuska sai farin ciki.

A ɓangaren Raudha ma shujuda tayi lokacin da aka sanar da Ramadhan matsayin wanda yay nasara. Batayi domin shiɗinne taso yaci ba dan dole. Tayine saboda fatan ace shine ahugaba na garin da suketa fatan samuwar mulki a hannunsa.
Su aunty Hannah kam gidan suka cika da ihu ita da ma’aikata. Ganin haka su Yasmin suka tayata suma. Farin cikinta uku ne a yau. A gobe za’a maida aurenta da Alhaji yaro glass kamar yanda sukai mata alƙawari. Na biyu zata zama matar vice president, na uku nan da shekar biyu itace matar president ɗin.

A fadar shugaban ƙasa ma da duk wani dake tare dasu ransa fal farin ciki. Hakama jama’ar gari magoya bayan jam’iyya da Ramadhan. Dan tuni an fara bikin murna ta ko ina saboda jami’an tsaro sun taka rawar gani na hana kowacce irin fitina yin tasiri. Yaran su Alhaji Audi ƙaura duk wanda ya fito ram ake da shi. Ta ko’ina ka zaga kiɗe-kiɗe da bushe-buahe ke tashi a ƙasar NAYA birni da ƙauye.

A lokacin da wasu ke murna wasu kuka sukeyi, dan da gaske irinsu alhaji Audi ƙaura ƴan takara wasunsu suma suka dingayi sai da aka zuba musu ruwa. Yayinda magoya bayansu da iyalansu ke cikin tsantsar baƙin ciki. Baƙin cikinsu bai sake ninkuwa ba sai jin cewar Jami’an tsaro sun kafa sun tsare ko’ina domin hana kowacce irin tarzoma tashi. Idan ma tsautsayi ya fiddo mutum kamesa sukeyi.

★★-★★

Bazamuce hankali ya kwanta a ko’ina ba. Sai dai Alhmdllhi masu tada tarzomar basu sami yanda suke so ba. Jami’an tsaro ta kowanne fanni kuma sunyi ƙoƙari, sai dai ALLAH ya saka musu da alkairi. Shi kansa shugaban ƙasa duk da akwai manufarsa ta ɗora Ramadhan akan mulkin yayi ƙoƙari sosai wajen jadadama jami’an tsaro harkar tsaron. Shine ya fara kiran Ramadhan ya tayasa murna. Sai kuma alhaji Yaro glass dake matsayin vice president a yanzu.
Alhaji Audi ƙaura ne na huɗu bayan mai-martaba kakansa, saboda shawarar da god father ɗinsa ya bashi na kiran Ramadhan ya tayasa murna. dan shine babban abokin hammaya dake bi masa a ƙuri’a, ido zai fi yawa a kansa fiye da sauran ƴan takarar.
Hakan kuwa akai, ya kira Ramadhan ya tayasa murna. Ramadhan dake kwance a doguwar kujera ya ɗora kansa bisa cinyar Anne an lulluɓesa da bargo saboda sanyi da yace yanaji ya amsa masa cikin muryar dake nuna rauninsa a yanzun. Duk da halin da yake a ciki ya cigaba da amsa kiraye-kirayen waya har sallar magrib, koda aka idar ma bai huta ba. Dan duk da zazzaɓi daya rufesa har kusan sha biyun dare yana amsa wayoyin taya murna daga sassa daban daban na duniya.
Abokai, yan uwa. Da iyaye, ƴan siyasa da shugabanin gargajiya. Wasuma bai sansu ba sai a yau.

Duk yanda Ramadhan dai yaso samun nutsuwa a ranar bata samu ba. Hasalima da zazzaɓi ya kwana da ciwon kai mai tsanani. Da safe har sai da doctor yazo ya duba shi. Duk da halin da yake ciki dole ya cigaba da amsa kiraye-kirayen taya murna a wannan yinin ma..

********

Kwanaki huɗu bayan faɗar sakamakon zaɓe ƙura ta lafa, sai shirye-shiryen zaɓen gwamnoni kuma da akeyi ta ko ina. Dan tsakaninsa dana shugaban ƙasa sati biyu ne. A kuma wannan tsakanin su Bappi suka sake zuwa Hutawa aka tsaida ranar ɗaurin auren Ramadhan da Raudha. Suka kuma ajiye komai har sadaki.
Mal. dauda baki har kunne ya zama surikin shugaban ƙasa. Dama tunda ya dawo da ƴan kuɗaɗensa sai ya zaɓi dawa zaiyi magana yanzun. An bige gidansa ana sabon gini, gefe kuma yana neman aure batare da sanin su baba Nafi ba. Dan Larai anata hura hanci sune da gida yanzu, duk da ta shiga ɗunbin baƙin cikin jin daga inda tushen kuɗin suka fito. Sai dai abinda malaminta ya faɗa mata game da watsa auren na Raudha da Ramadhan yasata shiga walwala ta maida komai ba komai ba. Yanzu sakamako kawai take jira na fasuwar auren a haukarta (😹😹).

*____________★_____________*

SANNU-SANNU bata hana zuwa, a na gobe zaɓen gomnoni aka maida auren Alhaji yaro glass da aunty Hannah. Duk da ba wani taro sukaiba aure kawai aka ɗaura ƙawayen aunty Hannah sun ɗan haɗu a gidan, ciki kuwa harda first lady. Wadda a ranar kowa ya sake tabbatar da alaƙarta da Aunty Hannah ɗin. Su Asabe ma dai nan gidan sukazo suka kwana, hakan yasa Raudha da mominta samun damar keɓewa da ƴan uwanta. Kuka ta dinga rusa musu akan wlhy bata son auren nan dan mutanen nan sunfi ƙarfinta. Duk da wasu sun nuna soyayyarsu gareta wasu ƙuru-ƙuru a ƙannensa da wata babbar mace da take ƙyautata zaton mahaifiyarsa ce saboda kamanni da suke ɗanyi suka nuna mata tsana da gargaɗi. Nan dai duk ta basu labarin abinda ya faru ranar zaɓen shugaban ƙasa.
Hankalin Asabe ya tashi, ta shiga yima Raudha faɗa akan miyasa ta amsa a wancan karon, dama irin wannan take guje mata tun farko. Maba danginsa ba ko shi bata ƙyautata zaton zai so ta. Mutumin da tun yana ciki ake ajiye masa kuɗi a asusun banki, ya girma yasamu ingantaccen ilimi, babu kalar ƙasar da bai zagaba yaga mata ƙyawawa ƴaƴan manya irinsa, amma tai tunanin zai iya dubanta matsayin mace. Kawai dai kakansa ke son wannan haɗin saboda alkairin datai musu.
Lallashinta su Fatisa suka dingayi da bata baki harma da shawarwari, dan harga ALLAH suma suna son ƴar uwar tasu ta auri shugaban ƙasa. Koba komai zasu fantama matsayin yayyen matar shugaban ƙasa. Zasu huce gajiyar wahalar da sukasha a hutawa a baya.
Sosai Asabe ta kasa zaune ta kasa tsaye, ji take kamar ta gudu da ƴaƴanta daga Bingo. Dama tasan idon Gwaggo idan yaranta sai wanu abu ya biyo baya. Dama wannan taita fargaba tun farko. Tunanin inda zataje da su ne ya sakata sake shiga damuwa. Har aka ɗaura auren aunty Hannah bata da wata walwala. Kowa tunaninsa aunty Hannah zata tare ne acan gidan Alhaji yaro kamar auren farko, sai sukaji saɓanin haka wai anan zata cigaba da zama tukunna. Hankalin Asabe ya sake tashi, dan tasan kuma babu danar sace Raudha kenan.
A ranar dai ko leƙe ango bai leƙo gidan ba, washe gari akai zaɓen gwamnoni. Wannan karon babu inda Raudha taje, hasalima wuni tai murƙususun ciwon mara har sai da suka dangane da asibiti. A asibitin ta kwana, washe gari suka dawo gida. Haka kwanakin suka cigaba da shuɗawa batare da Raudha ta ko sake jin labarin wani Ramadhan ba sai a tv kawai idan an ambaci sunansa ko an nunasa. Sannan Asabe ta kasa samo mafita game da auren na Raudha. Sai da auren aunty Hannah da Alhaji yaro ya cika wata guda cif suka fara ganinsa a gidan. Dan zuwa yanzu an kammala duk wasu zaɓuka sai jiran rantsarwa kuma. A ranar gyaran da ma’aikatan sukaima gidan ma na musamman ne, bai isoba kuma sai wajen tara na dare.
Raudha ta haɗo kan su Yasmin sukazo suka gaishesa. Baki ya saki da hanci yana kallon Raudha ɗin yana haɗiyar yawu. Dan harga ALLAH baisan haka yarinyar take ba. Bai taɓa ganinta ba sai a hoto, sai dai kuma a yanzu canji waje data samu ya sake fiddo mata da ƙyawunta da cikar budurci. Dan tana akan shekarunta ne na girma.
Harga ALLAH Raudha ta tsargu da kallon da tsohon ke mata, dan haka ta shiga ambaton sunayen ALLAH da jifansa da addu’oi. Tunda ta samu ta gudu ɗaki kuwa bata sake leƙo waje ba harda safe. Tanaji Yasmin tazo tana tashinta wai tazo a karya inji sabon Abba tai mata banza. Dole ta koma tace barci take.
Har Alhaji Yaro yace Yasmin ta koma ta tasota Aunty Hannah ta hana cikin kissa. Acewarta a barta tai barcin batajin daɗi, kuma anjima sunada wani trianing akan Raudhan. Badan yasoba dole ya haƙura, sai dai a ransa yana fatan ALLAH yasa kafin yabar gidan ta fito. Sai kuma akai rashin sa’a addu’arsa bata karɓu ba harya fitan batako leƙo waje ba………✍

*_BAƘAR INUWA…👇🏻_*

Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_A AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_

*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

*Recharge* – inda ake shiga domin saka kudi cikin account.

*Balance* – Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.

*Credit/Debit Card* – Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.

A inda (Enter your amount) za’a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba “Proceed”. Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).

——–

Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:

*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*

Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za’a gansa a Balance.

*Bank Transfer* – kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks.

_Account No_ – *1220077999*
_Account Name_ – *Arewa Books Publishers*
_Bank_ – *Zenith Bank*

Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din:

Amount Paid: – Nawa aka tura?

Name used for transfer: – sunan da aka saka wajan turowa

Transferred time: – lokacin da aka turo

Name of bank: – sunan bankin da aka turo dashi

Deposit date: – ranar da aka turo

Sai ayi SUBMIT.

*Airtime Transfer* – muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar:

MTN,
9Mobile
Glo
Airtel

Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance.

*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*

*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742

_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*

 

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply