Bakar Inuwa Hausa Novel Hausa Novels

Bakar Inuwa 32


Bakar Inuwa 32
Viral

Episode 32_*

……….Buɗe ƙofar ya saka Raudha saurin juyowa dan batai tunanin ganin wani ba a wannan lokacin. Su Bilkisu ne dama dai ke shigo mata a kwana biyun nan, tasan kuma yanzu sunyi barci. A bazata ta ɗan waro idanu waje, domin ganin abinda batai zato ko tsammani ba. Tunda bai taɓa mata hakan ba…
Ɗauke kanta tai da ga garesa da sauri, ganin ya cigaba da takowa cikin ɗakin kuma idonsa a kanta ko ƙyaftawa bayayi. Kayan barci ne jikinsa farare tas, wandon har ƙasa, hakama rigar mai dogon hannu ce. Ko ba’a faɗaba kallo da ga nesa zaisa ka fahimci zasuyi taushi kayan. Duk da kasancewarsa farin mutum kuma badan kwalliya ba sai da suka masa ƙyau. Sai da ya ƙaraso gaban gadonta ya dauke idanunsa a kanta ya koma bin ɗakin da kallo kamar yau ya fara shigowa ciki, hannayensa dake zube cikin aljihun wandon pyjamas ɗin nasa ya zare sannan yakai zaune a bakin gadon.
Mamakine ya sake turnike Raudha, sai dai babu damar yin magana ko neman dalili. Sosai fuskarsa ke a cinkushe babu ɗigon fara’a, wanda yay masa ma farin sani yana ganinsa zai gane ransa a ɓace yake.
“Sannu da zuwa”.
Raudha ta faɗa a hankali kamar mai raɗa. Sai dai hakan bai hanashi jinta ba. Amma maimakon ya amsa mata sai jeho mata furucin data kasa jurewa sai da ta ɗago ta dube…
“Bani abinci”.
Shine abinda ya fito a bakinsa batare da ya damu da girman mamaki da maganar zata zo wa Raudhan ba. Bawai dan bai isaba, sai dan ba haka ya saba ba. Batama tunanin ya taɓa cin abinci a gidan kamar yanda kuku ya faɗa.
“Kallona zaki tsaya ko abincin zaki bani?”.
Tsam ta miƙe har tana bige ƙafa da gado. Ta matse ido raɗaɗin na ratsata ta fice zuciyarta na gudu-gudu fiye da takun kafafunta. Ita yanzu ina zata nemo abinci 1 harya gota? Tasan dai kuku yayi barci. Ƙwalla suka cika mata idanu, amma sai ta haɗiyesu tana ƙoƙarin sauka downstairs.
Turus ta ɗanyi ganin Bilkisu zaune a falon duk da dai babu haske mai yawa, iyakar lamp ne na gefen kujera kawai. Amma hakan bai hanata ganinta ba. Ta baje books da takardu saman centre table da taja gaban kujerar da take zaune. Itama Bilkisun a ɗan firgice ta ɗago, sai kuma taja ajiyar zuciya da ɗan shafa ƙirjinta. Da’alama da farko tsoro taji, farin glass ɗin idonta ta zare tana faɗin, “Aunty lafiya bakiyi barci ba?”.
Raudha ta ƙarasa takawa inda take, “Ke ya kamata na tambaya aunty Bilkisu, ko tsoro bakiji ke ɗaya anan?”.
“Karatu nakeyi aunty, cikin ɗaki Basma ta hanani yi a nutse da gurnanin barcinta. Shiyyasa na dawo falon. Kuma banji tsoro dan securitys ma ai gasu nan sunata kai kawo a compound”.
Kai kawai Raudha ta gyaɗa mata, dan tasan gsky aunty bilyn ta faɗa. Haka securitys ɗin gidan ke kwana tsaye kamar zasu iya tare mala’ikam mutuwa ɗaukar ran wani a gidan…..
“Aunty ko baki da lafiya ne?”.
Bily ta katse tunaninta.
“A’a lafiyata ƙalau. Abinci yace zaici shine zan duba. kitchen”.
Ɗan jimm Bilkisu tayi dan da farko bata gane wa Raudha ke nufi ba, sai kuma ta ce, “Oh ko Yaya ya dawo ne?”.
Kai Raudha ta jinjina mata cikin ɗanjin nauyi, dan Bilkisu ta girmi su Fatisa ma ba itaba. Bilkisu tai ƴar dariya. “Oh yanzu a daren nan kuma?. Amma bana tsammanin abinci a gidan nan. Ya kamata kema dakin ajiye masa tunda kinsan komi dare zai shigo”.
To kawai Raudha tace. Dan bayan hakan bata da abin faɗa. Taya zata zauna fadama Bilkisun ɗan uwansu bai taɓa cin abinci a gidanba. Ita huɗɗa makamanciyar wannan ma bata taɓa haɗasu ba.

Kitchen ɗin ta nufa, ganin hakan yasa Bilkisun bin bayanta. Komai sun buɗe babu wani abincin arziki da zasu bashi ya ci, dan haka Bilkisu ta bata shawarar su dafa masa wani abu kawai mai ɗan sauƙi. Ba musu Raudha ta amince, abinka da na’urorin dake sauƙaƙa aiki, cikin abinda bai ƙulla awa guda ba suka haɗa masa abinci mai sauƙi da Bilkisu tasan bazaiyi ƙorafi ba. Raudha ta haɗa komai a wani ɗan basket mai ƙyau ta ɗauka suka fito. Sama ta nufa, Bilkisu ma sai ta hau tattare komatsanta domin komawa ciki ta kwanta haka nan…

Saɓanin yanda ta barsa zaune yanzu a kwance ta samesa saman gadon, sai dai ƙafafunsa duka biyu na a ƙasa cikin tttausan slippers ɗinsa bakaƙe da suka sake haska ƙafar tasa. Yaja karamin filo ya saka kansa, amma duk da haka sai da ya tallafe kan da hanun haggunsa. Na damar kuma nakan cikinsa riƙe da hisinil Muslim ɗinta daya kifa saman cikin. Kamar yanda Raudha ta zarga barci ne ya fara figarsa, sai dai tana buɗe ƙofar ya farka dan dama bai nisa ba. Amma sai bai motsa ba harta ƙaraso gabansa taja table dake can gaban sofa ta ɗora basket, duk da bata da tabbacin anan ɗin zaiyi zaman ci.
Sai da ta kai durƙushe sannan tace, “Ga abincin”.
Shiru kamar bai jita ba, harta fara tunanin ko barcin nasa yayi nauyine. Tana shawarar yanda zata tadashi sai taga ya motsa hanunsa, littafin ya ajiye gefensa kafin ya tashi zaune da kyau. Fuskar ta ƙara tsukewa fiye da farko alamar dai yunwa nacin bawan ALLAH da ba wasa (😹🤭😝lol).
“A zuba?”.
Ta tambaya cike da taraddadi. Mai makon ya amsa mata sai ya zuba mata hararar da ta sakata fara buɗe bowl ɗin da suka zubo abincin babu shiri. Ya ɗauke kansa kamar bai lura da yanda hanunta ke ɗan rawa ba. Ji yake ma kamar ya mangareta, ga takaicin kansa ya ishesa. Dan sai yanzu yake ganin kamar ya zubar da ajinsa ne. (Malam shugaba da baka san da ajin ba sai da kaga girki a gabanka🙄😝😂?).
Yana ganin tanata zubawa bai tsaidata ba, sai dai ta zuba mai isarta da take zaton zai cinye sannan ta mike zuwa karamin fridge dake a ɗakin nata ta ɗakko bottle water ta buɗe ta tsiyaya a karamin glass cup data haɗo da shi ta ajiye masa ta miƙe. Shi dai tuni ya fara cin abincinsa ma.
Har ya kammala cin abincin natsuwa na saukar masa bai sakejin motson Raudha mai ƙarfi ba. Shi yama zata kwanciya tayi, sai da ya ɗan waiga ya ganta a inda ya shigo ya same tana cigaba da karatun Al-qur’aninta. Sai dai kuma harga ALLAH barci takeji, amma batasan taya zata kwanta yana a ɗakin ba.
Koda yaji uwar hanjinsa ta ɗauka baiyi yunƙurin barin ɗakin ba, sai da ya sake share kusan mintuna ashirin a zaune yana cigaba da karanta hisunil Muslim ɗinta da ya sake ɗauka. Hammar da yaga ta jera kusan sau uku a jere ya sashi mikewa riƙe da littafin. Ta bishi da kallo dan ko inda take bai kalla ba har yaje ƙofa. sai da ya kama handle ɗin zai murɗa ya furta kalmar “Thanks ”. Tamkar mai ciwon baki.
Ƙincewa komai tai itama, dan Raudha badai zuciya ba. Hakan ya sashi waigota lokacin da yake saka ƙafarsa ɗaya waje. A mamakinsa sai yaga kanta duƙufe akan Al-qur’anin duk da kafin ya waugo ɗin yana jin idanuntane a kansa. Lip ɗinsa na ƙasa ya kamo da haƙori ya tura cikin baki tare da cijeshi da ƙarfi, kafin ya galla mata hararan ‘Wannan abar ko’ ya fice yana ƙwafa.
Tanajin ya rufe ƙofar itama ta sake ɗaggowa ta dallama ƙofar harara da murguɗa bakinta. Kafin ta rufe Al-qur’anin ta cire hijjab ta haye gadonta bayan ta kashe filar ɗakin gaba ɗaya tabar lamp na gefe side drawer ɗaya kawai. Dan kayan da yaci abincin ma batabi takansu ba tunda tasan bata da ƙarfin kaisu kitchen.

★★

Tun da ga wannan ranar Raudha bata sake sakashi a idonta ba, sai dai ta gansa a television, kai ko ƙannensa dake a gidan bata tunanin yama san da zamansu. Oho ita ina ruwanta, a ganinta wannan matsalarsa ce shi da su.
Kamar ko yaushe tana yawanyin baƙi, dan yau data kasance alhamis ma ta samu baƙuncin wasu matan gwamnoni guda huɗu. Dukansu manyan mata ne da zasu iya haihuwarta koma yin jika da ita, amma yanda suke mata kalamai cikin girmamawa da kwantar dakai batasan ta dinga tsinewa da tsige mulki da siyasa a zuciyarta bama. Yo banda mulkin babu ta yanda waɗan nan natan zasu iya ko kallonta. ƴar aikisun ma sun fita shekaru, ilimi, wayewar rayuwa, da ma ta siyasar. Amma dan abun kunya sunzo gabanta suna damunta da wani your excellency da ranki ya daɗe. Taja tsaki a ranta tana ƙarajin takaici da bama inuwar muliki suna BAƘAR INUWA.

A ɓangaren shugaban ƙasa kuwa ya sake komawa matuƙar busy. Dan abubuwane birjik saman kansa musamman na talakawansa da suka zuba ido da kunen sauraren farajin naɗe-naɗen muƙamai, tunda sunsan wannan hanyarce kawai shimfiɗar fara musu aiki. Anan kuma cikin gida gasu tsohun shugaba ƙasa sun tasashi gaba akan tursasashi amincewa buƙatunsu kamar yanda god father’s nasu ke control nasu suma a bayan fage. Sai dai taurin kai da tsaurin ido na Ramadhan ya sashi jajircewa akan maganarsa ta farko na yarda da sharaɗin 50-50 amma ragamar zaɓin speaker na hannunsa. Sukuma sanin tasirin speaker ɗin a garesu yasa sukace sam bazata saɓuba. Ga list ɗin shugaban ƙasa na cabinet ɗin da suka kasance zaɓinsa duk yarane matasa da basu wuce talatin da biyar, arba’in zuwa ƙasa ba. Ma’ana duk sa’aninsa ne. Waɗan da zasu ɗara shekrunsa ƙalilanne.
Tabbas jayayyar ta fara gundurar manyan jam’iyyar, domin kuwa ta wani fanin a tsorace suke da dagiyarsa. Ba komai ya jawo hakan ba sai zuwansa ƙasar Nigeria. Dan bayan zaman tattaunawa da sauran shugabannin Africa da sukai a Nigeriar shugaban ƙasar Nigeria yayi zaman na musamman kuma na sirri da shugaban ƙasa Ramadhan ɗin. Kuma har zuwa yanzu babu wani bayani daya fita akan tattaunawar tasu ta ko wanne fannin na ƙasashen biyu.
Daga can bayan fage kuma god father’s nasu na cigaba da shirye-shiryen tsara ta yanda za’a halaka dattijon arziki alhaji Hameed Taura da suke kallon shike bada gudunmawar kafiyar Ramadhan kai tsaye.

To bayan dai an turza an kuma turzo dole su Alhaji Usama suka amince suka sakarma Ramadhan tashi jayayyar badan yafi ƙarfinsu ba, sai dan akwai wata a ƙasa. Bayyi wani farin ciki ba, dan yasan a yin hakan da sukai kwai manufa mai ƙarfi. A cikin kwanki uku kacal da amincewar tasu akai zaɓen fidda gwani a majalissa. Dan sai da sune za’a gabatar da jerin subayen cabinet na shugaban ƙasa dama duk wasu muƙamai daya shirya tsaf.
Duk da akwai ɓoyayyen zaɓi hakan bai hana bama ƴan majalissa damar yin zaɓen fidda gwani ba akan speaker ɗin ba, daga ƙarshe dai dole aka nuna zaɓin bayan fage badan hakan shine fatan wasu ƴan ƙasarba da ma wasu a cikin ƴan majalissar, musamman da ya kasance babu wanda yasan da ainahin speaker ɗin sai da akaga sunayensu. Dan haka zaɓin ya bama kowa matuƙar mamaki da sanya mafi yawan al’ummar ƙasar NAYA farin ciki da sake ganin kimarsa. Musamman matasa da aka ɗakko matasa ƴan uwansu da ko’a wajen zaɓe ma ba’ai tunanin zasu kai labari ba amma aka aza a kujerun guda biyu da bayan kujerar shugaban ƙasa sai su a faɗa ajin ƙasar, dan kuwa duk matasane suma masu ƙwazo da aka zaɓesu da yaƙini tun daga jihohinsu. A ɓangaren manyan kuma da shugabannin jam’iyya hakan yayi matuƙar ƙona ransu da sakejin tsanar Ramadhan. Taya zai ɗakko yara ƙanana ya ɗora kan shugabancin manya, bayan ga wanda ma suka haifi ubanninsu a wajen ba’a su ba. Wannan zaɓin speakers yasa a ranar sau kusan uku jam’iyyar da shugaban ƙasa ya fito suna zaman meeting wanda ko guda a ciki ba’a gayyaci wani na jikin shugaban ƙasar ba kuma.
Raudha kanta da basanin minene siyasa ko mulki tai ba zaɓin ya mata ɗari bisa ɗari. Ta kuma sakasu a cikin addu’ointa sosai akan ALLAH ya cigaba da tallafa musu wajen ɗaura mutanen kirki bisa muƙaman da dole sai dasu ne mulkinsa zai tafi cikin nasara da sauke hakki.

Bayan fidda speakers shugaban ƙasa ya cigaba da wasu naɗe-naɗe da suka shafi office nashi da suka sake bada mamaki, masu bashi shawara akan fanoni da dama na mulkinsa da sauransu akwai manyan dattijai da akasan su akasan jajircewarsu wajen faɗar gaskiya da yin gaskiya akan ayyukansu da ma tsaurinsu. A zaɓin nasa ya kasance akwai matasa masu jini a jika irinsa ya muƙar sake ɗaukar hankalin talakawan ƙasa a kansa, har yanda wasu ke nuna masa ƙauna ma sai ya baka tsoro. Yayinda dattijan ƙasar NAYA musamman waɗanda suka ƙwallafa rai a mulkin suka fara shaƙa daga takun na shugaban ƙasa, dan suna masa wani kallone kamar na TAKUN SAƘAr nuna kishin matasan ƙasar da mayar musu murtanin sun babake komai a baya suma. Hakan yasa ba ƴan jam’iyyarsa kawai ba, har wasu ƴan jam’iyyun da sarakunan gargajiya suna zaman yin meeting da tattauna take-taken Ramadhan ɗin.
Sarai yana jin wasu abubuwan dake faruwa, amm sai yay biris kamar kunnensa a toshe yake, idanunsa kuma a makance. Yay matuƙar maida hankali wajen tsara yanda yake buƙata a tantance masa cabinet nashi da taimakon mayan mutanen dake zagaye da shi na kirki duk da akwai masu fuska biyu kuma a cikinsu dai suma harma a matasan, kafin su amshi muƙaman da ake burin bama kowannensu..

_________★_________

A daren yau manyan dattijan nan, da al’amuransu ke keɓantattu ga al’ummar ƙasa sukai zaman tattaunawa na musamman a tsakaninsu, dan gane da ganin bayan Alhaji Hameed Taura, da zukatansu ke raya musu komai shugaban ƙasa Ramadhan yanayine bisa umarninsa. Wato a zahiri dai Ramadhan shine shugaban ƙasar NAYA, amma a baɗini Alhaji Hameed Taura shike mulki. kamar dai yanda suke ga sauran shuwagabanin baya, wanda shima Ramadhan ɗin haka suka tsara a kansa. Sai dai tun kan aje ko’ina ga komai na shirin sukurkurce musu.
A cikin tattaunawar tasu ne. Oga kwata-kwata ke ambaton “A wannan gaɓar ya kamata matar shugaban ƙasa ta nema office nata”.
Cikin mamaki sauran duk suka dubesa, dan sam basu fahimci muhimmancin yin hakan ba a garesu. Ɗan murmushi ya saki tare da ɗaukar kofin abinda ke gabansa ya zuƙa ya ajiye. Cikin ɗacin rai yace, “Na fahimci a yanzu da kujerar first lady kawai zamu iya fara yaƙar wannan yaron tunkan al’amarin nasa ya ƙara nisan kiwon da bola sai ta fimu daraja”.
“Amma ranka ya daɗe, ko ka manta first lady sweet seventeen ce. Sannan girman ƙawai, iyakar karatunta o level ne. Babu abinda ta taɓa sani a siyasa balle sha’anin mulki, rayuwarma yaushe ta gama fahimtarta?”.
“Duk wannan raunin nata ne ya sani tunanin a bata office”.
Shiru sukai suna sake ninƙaya a nazari, dan har yanzu basuga wani alfanun hakan ba a garesu sam sai tsagwaron kwamacala da shirmen da ƙasar tasu ke tunkara. To amma sun san halin oga da shegen zakule-zakule. Sai dai duk sanda ya zaƙulo abu zaka samu mai muhimmanci ne a garesu daga baya….

★★★

A lokacin da suke can suna tattauna yanda first lady Raudha Dauda Hutawa data koma *_Raudha Ramadhan Taura_* zata mallaki Office, anan Taura House Ramadhan dake ganawar sirri da kakansa ke zaune a keɓantaccen falon baƙi na Alhaji Hameed ɗin suna tattauna muhimman batutuwa. A cikin tattaunawar tasu ne kuma Alhaji Hameed Taura yay ma Ramadhan batun saka Raudha a makaranta ta cigaba da karatu, dan hakan nada matuƙar muhimmanci a mulkinsa da ita kanta.
Ramadhan dake kai yankan kilishi bakinsa yay wani ɗan guntun murmushi da baida maraba da takaici, kafin cikin tausasa harshe ya ce, “Bappi wannan shi naso nuna maka akan auren nan. Taya za’ai shugaban ƙasa da mata mai matakin o lavel a ilimi, sannan ƴar shekara sha takwas tayi yarinta da yawa?”.
“Wannan duk ba damuwa bane Ramadhan, sai ma kafi jin daɗin control nata yanda kakeso, zakace nina faɗa maka nan gaba idan idanunta suka buɗe akan abinda kake ganin kai bazata iya ba”.
“To amma Bappi ni a wannan gaɓar ma banga amfanin yin karatun nata ba, dan nidai yanzu bazan bari ta ƙetare ƙasar NAYA ƙaro ilimi ba, sannan bani da sha’awar iyalina shiga harkar siyasar nan”.
“Sosai tunaninka ya sani farin ciki, sai dai kuma baida nasaba da daƙile mata zancen cigaba da neman iliminta. Ba lallai saitaje ƙetaren NAYA ba. A cikin ƙasar nan dama ya kama tayi, kai kanka hakan kimace a gareka, da ƙara bama talakawa hope game da mulkinka. Zata iya shiga duk jami’ar da takeso a ƙasar nan, kokuma tayi online school na ƙasashen ketaren inma suke take so, amma zamanta babu karatu bazai yuwuba. Koda bazata shiga siyasa ba akwai abubuwa da yawa da suke bukatarta a mulkin koda kai da ita baƙwa buƙatar ta kasance a cikinsu”.
Ɗan jimm Ramadhan yayi, sai kuma yaɗan ɗage kafaɗa da cigaba da cin kilishinsa. “ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi”. Kawai ya faɗa ya tsuke bakinsa. Shima Bappi komai bai sake cewa akan hakan ba. Bayan murmushi da yay ma sai ya ɗakko masa wani zancen daya shafesu kuma……….✍
*_Typing📲_*

*_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_*

https://arewabooks.com/chapter?id=62b0ba6cf0deac225fe20185

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply