Bakar Inuwa Hausa Novel Hausa Novels

Bakar Inuwa 52


Bakar Inuwa 52
Viral

Episode 52_*

……….Sai dai addu’ar tata bataci ba. Dan suna shigowa falon daya raba sashensa da nasu Anne sukai kiciɓus. Sai dai Ramadhan ya ɗauke kai kamar baiga Anne ba dan shima dai kunyar yaji. Ɗan murmushi Anne tai tana binsu da kallo kafin ta sauke ajiyar zuciya da numfashi tana mai binsu da addu’oin zaman lafiya da samun zuri’a masu albarka.
Har ya isa ƙayataccen bedroom ɗinsa da komai na ciki yake kalar royal blue and golden bata yarda ta buɗe idanunta ba. Ya direta a saman lallausan gadonsa da yaji shimfiɗu masu inganci, anan ma da runfa ta net white color mai kwalliyar blue kaɗan-kaɗan.
“ALLAH nauyine dake Ustazah, wannan ai sai kisa na rame”. Ya faɗa cikin kunenta tare da sumbatar kuncinta na haggu. Ita dai bata motsa ba balle ta buɗe ido, sai da ta ɓata fuska da tura baki yace tana da nauyi. Murmushi yayi da ɗallin lips ɗin a hankali.
“ALLAH da zafi Ya Ramadhan”.
“Ai dama dan kiji zafin nayi. Idan kuma wannan yayan bai fita bakinki ba ALLAH sai nazo na darje ciwon na banbanta miki tazarar dake tsakanin Yaya da ni”.
“Toni mizance dan ALLAH?”.
“Oho ya rage naki tashi kisha magani kisa kayan barci kar wannan towel ɗin yasa mura kamaki”.

Da ƙyar ya iya sakata tashin tasha magungunan da tun bayan sallar magrib aka kawo masa su. Dan tun da yaga yanda take tafiya ya yanke shawarar nemansu. Kayan barci ya ajiye mata ya shige toilet, hakan ya bata damar sakawa da sauri-sauri tai amfani da designers turarurrukansa masu ɗan karen ƙamshi ta haye gadon da sauri tai kwanciyar kai da kafafu tare da yin addu’a kafinma ya fito taja bargo har saman kanta. Dan tasan kaɗan daga aikinsa ya fito da towel babu kunya a gabanta.
Ilai kuwa hakan ya fito kansa tsaye, ya ƙaraso har gaban gadon saboda wayarsa dake ring. Kasancewar ata gefen can ɓangaren Raudha ta kwanta shi kuma sai ya zauna a gefen gadon ta ɓangaren data bari domin shi. Yana goge ruwan fuskarsa da jikinsa yana wayar da A.J dake kula masa da business ɗinsa a can America yanzun. Cikin harshen turanci suke maganar cike da ƙwarewa, dan haka Raudha ta shagala a saurarensa dan yanda harshensa ya karye bama zakace yasan wani yaren Africa ba. Wayar taɗan jashi lokaci dan harya miƙe ya koma gaban mirror. Yana gyara jikinsa yana cigaba da wayar harya shirya cikin tausasan kayan barci, kafin taji ya sake zama a gefen nata. Kaɗan ta ɗaga bargon ta leƙashi, sai tagansa da kofin tea daketa turiri sai kuma lap-top da yake ƙoƙarin kunnawa har sannan wayar na maƙale a kunensa. Shagala tai a kallonsa ƙasan zuciyarta na godema ALLAH daya azurtata da samunsa matsayin miji. Banda ƙaddara ita tasan ko a ƴar aiki bazata ishi Ramadhan kallo ba. Sai dai UBANGIJI shi mai rahamane mai kuma jinƙai. Sannan mai ƙaddara abinda yaso ga waɗanda yaso koda akwai tazarar nisa ta rayuwa ko yare ko addini ko yanki a tsakanin bayinsa.
Yaja lokaci yana aikin sai dai ya ajiye wayar tuni, har barci barawo yay tashiri kan Raudha saboda maganin data sha.

Ramadhan da idanunsa ke faman raɗaɗin barci, ya kai hannu bisa goshinsa ya murza da furzar da iska mai nauyi. Ya gaji matuƙa, gashi abinda yakeyin mai muhimmanci ne. Dan kayan da zasu fitarne a sabuwar shekara A.J ɗin keson ya duba abinda baiyiba su ajiyesa gefe wanda yayi su fara packaging ɗinsa yanda ya dace da mikashi ga yan talla kafin a fitar.
A hankali ya rufe lap-top ɗin bayan ya kashe yana ɗan danna gefen wuyansa alamar riƙewa. kofin daya sha lipton da lap-top ɗin ya sauke kasa. kafin ya koma toilet ya ɗauro alwalar barci sanna ya hawo gadon da danna wani abu net ɗin ta buɗe gaba ɗaya ta lulluɓesu. Sai ɗan hasken fitilar cikin gadon daya kunna ya kashe ta ɗakin gaba ɗaya. Bargon da Raudha take ƙudundune a ciki ya ɗage, sai yaga ashe kai da ƙafa take kwance. Kansa ya ɗan girgiza kawai, yasan tadata yanzu wani aikinne kuma, sai kawai ya kwashi piilos ɗin shima ya maida inda tasa kanta dan bazai iya yarda da kwanciyar kai da ƙafa ba shida matarsa. Gara ace ɗaki suka raba ko gadon. Dan lokaci Amnah ko faɗa sukai da ita bai yarda da raba ɗaki ba. Dole ta kwana tare da shi ko zata kwana masa kukan baƙin cikin daya tusa mata. Inma itace tai masa laifin duk zafin da yakeji a ransa ya gwammaci su kwana waje guda ɗin, shi kuma yasan a inda zai fanshe haushinsa ai (🤣😂mugu ɗan masa🙊).

Sai da ya janye bargo gaba ɗaya ya karemata kallon yanda kayan barcin sukai mata ƙyau kafin ya saki wani ɗan guntun murmushi da iya laɓɓa ya tsaya masa. jikin nata ya taɓa yaji zazzaɓin ya sauka, sai kaɗan da bai ida hucewa ba dai. Filon da take kai shima ya ɗaura kansa suna fuskantar juna. Ya sumbaci goshinta da laɓɓanta sannan yay musu addu’a yaja bargo tare da rungumeta yana sauke ajiyar zuciya.

Da asuba ya rigata farkawa, sai dai yana motsawa itama ta farka. Gaba ɗayanta a jikinsa take lafe da alama hakan ya mata matuƙar daɗi, sai dai suna haɗa ido tai saurin ƙoƙarin janye jikin nata kunya kamar zata nutse. Riƙota yay ya hanata damar juyawar. Cikin ɗan daburcewa take ƙoƙarin faɗin, “Kayi haƙuri ni ALLAH ban san ma….”
Ruf ya rufe mata baki da nashi batare daya bari ta ƙarasa faɗa ba (😜ƙazanta ko brush babu🤕🙄). Duk yanda taso kwatar kanta bata samu damar hakanba. Dole ta nutsu ta barshi ya gama yamutsata san ransa tsoro kamar ya kasheta. Dan a tunaninta za’a tafi next level ne😖. Da ƙyar ya iya yakar ƙansa ya barta jin an sake kiran salla na biyu, ya sauka a gadon da ɗan zafin nama ya faɗa toilet. Ruwa mai ɗumi ya sakarma kansa yana mai sauke nannauyan numfashi da rumtse idanu. Sunan ALLAH ya dinga ambata dan yasan lallai akwai matsalolima ba matsalaba. Gashi da alama Raudha tamkar Amnah take itama zatai shegen raki duk da ita daba sickler ɗin ba. Dole ya haɗa harda wankan lada. Koda ya fito yay mata maganar ta tashi bata motsaba dan kunya harya zura jallabiya yasa turare ya fice. Sai dai ya gargaɗeta karya dawo ya sameta a kwance bata tashi tayi salla ba, ta kuma sake shiga ruwan zafi inba hakaba ya dawo da kansa zai sake gasata.
Raudha da gaba ɗaya a firgice take da Ramadhan ta miƙe da sauri bayan ta leƙo ta bargo ta tabbatar ya fita. Toilet ɗin ta afka itama. Ta watsama jikinta ruwa da ƙara gasa ko’ina duk da dai Alhmdllhi garas ta tashi yau sai dai rashin jin karfi na sabo.
Koda ya dawo a saman sallaya ya sameta tana karatun alkur’ani. Hakan ya masa daɗi sosai, sai shima kawai ya zauna suka cigaba dayi tare. Duk da mamaki ya matuƙar ɗaure kan Raudha jin yanda yake karatu a nutse cikin daddaɗar muryarsa mai faɗi da amo da gaba ɗaya ta danne ƙarfin tata siririya mai zaƙi. Sunyi karatun da yawa sannan sukai addu’a. Kanta a ƙasa tace, “Ina kwana”.
Bai amsaba, sai dai ya kafeta da idanu, ɗan dagowa tai kaɗan sai suka haɗa ido, zata maida ya riƙo habarta da hanun damarsa. “Karki kuskura ki rufe idanun nan”. Ya faɗa da sauri ganin tana niyyar lumshesu kuwa. Yanda taji babu wasa a furucinsa ya sata dakatawa. Sai dai taƙi yarda su haɗa ido….
“Ni bana son irin wannan gaisuwar ga matata shiyyasa ban taɓa amsa miki ba”.
Duk yanda taso jurewa kasawa tai, sai da ta ɗago ido ta kallesa sai karaf a cikin nashi da launinsu ya canja. Ƙwayoyin cikinsu bakaƙe masu ƙyalli ya juya mata cike da tabbatarwa. Ta risinar da nata tsigar jikinta na tashi dan ta rasa abin cewa kuma. Zuciyarta na tunanin (Banda gulma irin tashi wace gaisuwace kuma bayan wannan da aka banbanta tsakanin mata da miji da sauran mutane? Ita dai tunda ta taso a gidansu irin wannan taga anama Abbansu).
A bazata kawai taji saukar lips ɗinsa saman goshinta. Kafin ta dire numfashi ya saukesu kan lips nata ya bata light k.. Harya janye kuma ya sake maidawa ya cafkesu da ƙyau yana matse hanunta dake cikin nashi tsam.
A gwame ta dinga fidda numfashi kamar yanda nashi ke fita a harɗe, har saida yayi yanda yake so sannan ya barta dan kansa. Cikin rufewar idanu ya lalubi kunenta.
“Wannan itace nake buƙata a kowacce safiya idan mun tashi, da kuma idan na dawo aiki shine sannu da zuwana”.
(Tabb ashe kuwa akwai tsallen baɗake) cewar Raudha a zuciya. A fili kam yanda yay maganar babu wasa a ciki ya sakata jinjina masa kanta kawai batare da tace komai ba. Mikewa yay shima ya mikar da ita batare da ya sake cewa komaiba. Dolenta tabi yanda yakeso suka koma gado bayan ya cire mata hijjab ɗin ya barta da abayarta dan shima yana son kauda kansa ga abinda zuciyarsa ke bijiro masa.
Fargaba ta hanata barci har sai da taji yana sauke numfashi a hankali alamar shi ya fara sannan tai nata itama tunda taga ba abinda take tsoron bane zai faru……….✍

*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*

 

*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*

*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_

 

Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261
__________________

*_JAMA’AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*

 

Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F

*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77

 

*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________

*_BAƘAR INUWA…👇🏻_*

Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_

*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*

*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742

_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*

 

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply