Bakar Inuwa Hausa Novel Hausa Novels

Bakar Inuwa 67-68


Bakar Inuwa 67-68
Viral

_Episode 67-68_*

………..*_WASHE GARI_*

Washe gari babu kunya Gimbiya Su’adah tazo har sashen su Anne ta tuntuɓesu batun auren Aynah da Ramadhan. Dan Pa yaƙi bata haɗin kai kwata-kwata. Ramadhan ko taki cemasa komai duk da tasan yana cikin gidan. Hasalima har zuwa yay ya gaisheta. Yanda bata ɗaga masa maganar abinda ya faru ba a jiya shima baice komai ba. Yau ma bayan ya dawo sallar asuba yaje ya gaishetan. Nanma bataceba shima kumai bai ceba.
Koda Bappi ya gama saurarenta cewa yay taje zataji komi da suka yanke shi da su mai-martaba. Ranta ya ɓaci, amma ta danne ta tafi. Duk yanda sukai da Bappin ta kira Adda Asmah ta sanar mata. Itako daga can gurgun tunaninta bata yay aikin boka ya tabbata kenan. dan dama yace zai rufe bakin kowa ai. Shi kansa Ramadhan bai isa yin ko tari ba akan batun.

Hhh ALLAH sarki Addah Asmah. Batasan a yanzu matar Ramadhan da kakaninsa tsaye suke kansa ba. Dan a yau yini Raudha tai aikin karanta addu’oin warware sihiri dana kariyar ALLAH ita da Ramadhan suna tofawa a ruwa kamar yanda musulinci ya koyar damu. Suka kuma ajiye matsayin ruwan shansu. Yini guda suna a sashensu. Hatta abinci nan ake kawo musu. Yayinda Anne ta zaunar da shi ta sanar masa dokar Doctor akan Raudha na bedrest. Ya tabbatar mata babu damuwa zaiyi ƙoƙarinsa na kare hakan. Taji daɗi sosai tai masa nasiha ita da Bappi tare da addu’ar ALLAH ya kiyaye gaba.

Washe gari gida ya cika da baƙi taf tako ina. Bakajin komai sai hayaniya. Sai dai duk wannan hayaniya da gidan ya dauka babu mai ganin shugaban ƙasa da first lady. Dan suna can sashensu suna baje kolin shafukan soyayya kamar su kaɗaine a duniyar. Basu da aiki sai zaman garden ɗinsa dake matuƙar ɗaukar hankalin Raudha takeji kamar a wata sabuwar duniyar take. Abu mafi ɗaukar hankalinta tsuntsaye da ake kiwo a wajen da ruwan da aka kawata mai bulɓulowa cikin dutse kai kace ba tsarawa akai ba. Sau ɗaya ya barta ta shiga sukai wanka a pool ɗin wai bayaso Unborn ɗinsa ya ɗauka mura tun yanzun. Ita dai dariyama yake bata. Dan baida aiki saita idan ta haihu babynsa kaza kaza. Kokuma ya kwanta a cinyarta yayta hira da cikin da ko a jikinta bai nuna akwaishiba dan cikin a shafe yake kamar babu hanji balle ɗa.
A ɓangaren su Adda Asmah hankalinsu a tashe yake babu ango babu dalilinsa. Gashi har an fara event yau a cikin ukun kawai da mai-martaba ya basu izininyi tun a waccan ranar. Koda Fulani ta iso tasa a kira mata Ramadhan anƙi ganinsa. Gashi Bappi ya sashi kashe wayoyinsa duka sai mai muhimmanci kawai. Yo banda abin Fulani ma ganin shugaban ƙasa guda wasane kamar wani ganin Bilyn Abdull haka😏.
Aiko ta shaƙa. Tazo har sashen Anne amma ƙofar sashensa a rufe. Hakan yasata tunanin koma dai raina musu hankali ake baya gidan aka ajiye waɗanan zaratan securitys ɗin zagaye da anguwa kamar masu gadin wuta. to komadai miye Shugaban kasa Ramadhan ya zama gwal ma ya fisa arhar gani a garesu.
Dan ko kunshi da yace bilkisu ta kawo mai yiwa matarsa a sashen akai mata cikin garden, yayinda shi yake acan falon hutawarsa zaune shi da Ibrahim da A.J da sukazo biki suna shan hirarsu, dan Gimbiya Su’adah ta gama turama abokansa invitation kaf ta waya akan zaiyi amarya. Koda suka zo kuma baice da kowa komai ba akan hakan.

Koda aka kammala ƙunshin ya gani yayta santi. Kaɗan-kaɗan ya kamo ya sumbata. Harda labarta mata yanda ya dinga satar kallon kafafunta da hannayenta lokacin da akai mata na bikinsu. Aiko mi zatai inba dariya ba har saida ya ƙulu. Tako shiga masa gwalo da kiransa gulmamme.
Gyaran kai kam shi ya wanke mata da kansa ya gyara mata shi tsaf har taita mamaki. Yako tabbatar mata tsabar son da yakema gashine kawai ya sashi koya a wajen Anne. Harda cewa wataran zai mata kitso da sai tasha mamaki.
*_RANA BATA ƘARYA……_*

Lallai wannan zance haka yake. Dan kuwa a yau juma’a bayan sakkowa masallaci aka ɗaura aurarrakin yaran Taura Family har su biyar. Sai dai wanda suka kasa kunne suji da Ramadhan a ciki sukaji tsit. Sai da aka kammala a karshe aka ɗaura na Ayna’u Musaddiq da angonta Aminullahi Ashiru. Ɗa ga tsohon gwamnan jihar TANDAZA, ya jima yana sonta tana masa ikkanci, dan har kuɗi sun taɓa kawowa ta bijire. Da yake uban baida fus a gidan haka ya hakura duk da kuwa bokine garesa Alhaji Laminu Tandaza. Sai dai kuma masu iya magana sunce matar mutum kabarinsa. Gashi kuwa UBANGIJI ya tabbatar da hakan.

Gagarumar ƙurace ta tashi a gidan Adda Asmah jin sunan ango a bakin ƴan ɗaurin aure da ba haka suka saniba tun farko. A cikin kanƙanin lokaci ta hargitsa kowa. Zata taho Taura House ayi wacce za’ai ita da gimbiya Su’adah da take tunanin ta munafinceta Abban Aynah ya tabbatar mata ko gate ta tsallaka a bakin aurenta. Wannan tashin hankali ya saka Fulani hana Adda Asmah fita. Dan kowa yanda yaga Alhaji Musaddiq yau babu makawa zai tabbatar da abinda ya faɗa ɗin.
Amarya Aynah kuwa suma tayi a take sai da aka nemi likitan ceto ranta.

A Taura house kam babu wanda yasan mi ake ciki. Dan kuwa koda anguna suka shigo gaisuwa babu wanda yaji wani sabon abu da babu shugaban ƙasa Ramadhan da ganinsa dama bai zama lallai a idon kowanba.  Dan yanda ya fita tare da Bappi da mai-martaba wajen daurin aure haka suka dawo a mota ɗaya. Yana shigowa kuma ta ƙofar baya yabi zuwa sashensa dan ya tabbatarma Raudha kartaje ko’ina ana ɗaura aure gida zai dawo.
Duk da dai taji gargaɗinsa. Anne tazo da kanta ta tafi da ita ta gaisa da wasu aminanta na amana dan ba wani ganin Raudhan sukai sosai ba lokacin nasu auren. Komai cikin dauriya Raudha keyinsa. Amma jikinta a matukar sanyaye yake tunda tasan yau mijinta zai zama nasune su biyu. A kwanakin nan duka kullum sai ta buya tasha kukanta. Kuma tsaf Ramadhan na lure da ita batare data sani ba. Sai dai bai taɓa nuna mataba ya barta da lokaci kawai. Zai daibi duk hanyar data dace ya mantar da ita idan suna tare kafin ta sake samun dama.
Kasa ɗagowa tai ta kallesa lokacin daya shigo tana zaune ita da Basma da Rumaisa da Fadila a falo. Yayi kyau matuka cikin ɗanyar shadda data wadatu da jiƙaƙen ɗinki. Sai maiƙo da ɗaukar ido take gamai kallo. Gashi sosai babbar riga ke kawata adonsa da maidashi wani babban mutum. Sannu da zuwa su Basma sukai masa suna mikewa. Dama Anne ce tace suzo su ɗebe mata kewa kafin ya dawo tunda tasan babu mai shiga sashen nan da sunan yazo biki.
Bayan ficewarsu ya tako a hankali zuwa gabanta yakai dukunne. Hannayenta ya kamo cikin nasa tare da saka ɗayan ya ɗago habarta. Itama tayi ƙyau matuƙa cikin wani lass mai azabar kyau da nauyin kuɗi. Ga ɗinkin ya zauna mata ɗas a jiki saboda kibar da tayi da ƙara haske da fresh. Taci kayan ado na ɗan kunne da sarka da zabba da awarwaraye ga ɗauri daya amsa sunansa ɗauri kai kace itace amaryar.
Kukan da taketa riƙewa tun ɗazun ta sakar masa. Lumshe idanunsa yayi tare da mikewa ya ɗagata cak ya rungume a jikinsa yana murmushi.
“Haba ƴar aljanna. Kwantar min da hankalinki Ramadhan B. Hameed Taura na Ameenatu Dawood Hutawa ne ita jaɗai insha ALLAH. Badan bazan iya karawaba wataran idan kaddarar hakan ta shigo, sai dai ina fatan rayuwa dake ke ɗaya dan tun asali zama da mace ɗaya ne tsarin Ramadhan. Sai dai tsarin ALLAH yana gaba da nawa Ameenatu. Amma a yanzu nakine ke ɗaya babu wadda aka ɗaurama Ramadhan aure da ita”.
Ƙanƙamesa tai da sake fashewa da kukan da batasan na farin ciki bane kokuwa na minene. “I love you Noorullah”. Ta faɗa da ɗagowa lokaci ɗaya ta manne lips nata da nashi.
Tab humm, batasan kuka ta kawo gidan mutuwa ba. Dan kuwa bawan ALLAH caraf ya cafke tare da ɗaukarta cak sukai bedroom. Yako shiga yamutsata son ransa. Yama manta da wata kwalliyar biki. Sai da labarin ya canja salo kuma ta ruɗe. Sai dai batasan dama haƙuri yake yana ɗaga kafa ba dan dole. Aiko tilas ta bari ya rage zafi yanda ya kamata. Da ga karshe dole aka sake nemo su Basma suka kawo mai sake kwalliyar biki.

Uhhm andai ji kunya😣😮🚶🏻.

★Bayan sallar la’asar sai ga Aunty Hannah mata ga vice president da tawagarta sun iso gidan bikin. A ciki kuwa harda Asabe da Hajiyar Birni dasu Fatisa. Wayyo dadi kamar zai halaka Raudha. Ta rasa inda zata saka kanta taji daɗi. Ga Anne ta saka an musu kyaƙyƙyawan karamci da tarba ta musamman ta abinci. Su aunty Hannah anata faman ɗaga kai da hura hanci ana yatsine-yatsine kai kace itace ma firt lady ɗin tsabar yanda guards ke dogare a bayanta da mata ƴan siyasa.
Ina Raudha bata ita takeba. Farin cikin ganin Mummynta ya rufe mata ido ruff. Ko Hajiyar Birni da Hajiya mama sai da sukai mata tsogumi ta gaishesu. Anan suka kasance har bayan magrib. Da zasu wuce Anne ta haɗa musu shatara ta arziki musamman su Fatisa da sukaji kamar karsu rabu da ƴar uwarsu. Dan suma dai yanzu Alhmdllhi har sun kawo mazan aure ana shirin zuwa hutawa gaida Alhaji baba Dauda mai zamani surukin Mr president na ƙasar NAYA. Yaso zuwa daurin aure Inna ta tashi da amai da gudawa aka kwasheta asibiti a rikice tana can ana kara mata ruwa dole ya hakura. amma yasha takaici wai kallo ya wucesa daga shi har M. Gambo amininsa da shima ya gama saye zuciyar asabe batare data san shiɗin bane har yanzun. Dan yace bazai bayyana mata kansa ba sai ta yarda ya turo iyayensa. Itako tace su ba yaraba bata yarda da wannan ganganciba yazo gareta kawai su sasanta. To yanzu dai yace zaizo ɗin amma bai tsaida rana ba.

Bayan wucewar tasu ma zazzaɓi ne ya rufe Raudha. Koda aketa shirin tafiya dinner ita tana can duƙunkune a bargo. Dama kuma bata saka ran zuwan ba tunda tasan Ramadhan dai bazaije ba. Kuma babu tabbas zai barta taje itama.

★Kafin a tafi dinner gimbiya Su’adah ta cigaba da neman number Fulani da Addah Asmah kamar yanda taketa fama tun bayan dawowar ƴan ɗaurin aure hakan baiyu ba. Dan duk kashe wayoyinsu sukai. Taso su Safina su leƙa gidan suyi ALLAH ya sanya alkairi hakan bata yuwuba dan Taura house yayi matukar cika kasancewar duka matan gidan uku sun aurar da yara.
Ta turama Ramadhan gargaɗi sosai akan ya tabbatar yaje dinner ɗin nan amma sai dai baima gani ba dan yau yayi busy da yawa. Babu wanda yasan ainahin abinda ya faru sai fa da aka isa wajen dinner sai su Bilkisu Amare kawai da angunansu amma babu Aynah babu Ramadhan babu duk wani wanda ya shafi masarautar Bina dake a gidan Addah Asmah dan dama biyu aka rabu. Wasu sukayo nan Taura House wasu can gidan a cewarsu duk za’a haɗe wajen dinner da walima dakai amare.
A sannan gimbiya Su’adah takejin mummunan labarin cewa ai kiɗa ya canja bada Ramadhan aka ɗaura aure ba. Ta matuƙar gigicewa a haukace ta shiga neman number Ramadhan amma har sannan switch up. Ta nufi sashen Pa ta iskesa da baƙinsa da basu wuce ba. Tsabar yasan miya kawota kuma yay kememe yaki tasowa. Haka ta wayance ta fito. Maida akalar kiranta tai ga Mai-martaba, shikam ta samesa. Sai dai yaja mata gargaɗi akan idan har tace wani abu yana cikin Taura house sai ya mata hukunci mai muni, tabar koma minene za’a tattauna bayan biki.
Wannan al’amari ya matuƙar sake rikita gimbiya Su’adah, dan kuwa a daren nan jininta ba karamin hawa yayiba har sai da Safina ta taimaka mata da maganin barci.

★Wajen dinner kam bidirinsu suka sha kamar babu gobe. Dan gaba ɗaya anan aka haɗe amare da angwayen. An raƙashe an kwalle anci ansha sai dai Bily taji inama Raudha na wajen. Amma dai su Basma sun ɗauka komai a waya duk da anyi vedio recording. Su Ibrahim ne suka halarci wajen bisa wakilcin babban yayan amare shugaban ƙasa Ramadhan tare da cos. Hakama manyan mutane matan gwamnoni da ministers da ƴaƴansu duk sun halarta. Dan hatta da yaran su Alhaji yaro glass na nan anyi komai da su kamar babu wata a ƙasa. Karfe ɗaya aka tashi amare da tawagar jama’a yan biki sukayo gida. Masu gidaje a cikin Bingo suka nufi nasu muhalli anama angwaye da amare fatan alkairi da zaman lafiya da zuri’a masu albarka………✍

*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*

 

*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply