Bakar Inuwa Hausa Novel Hausa Novels

Bakar Inuwa 74


Bakar Inuwa 74
Viral

*_Episode 74_*

……….Faɗuwar Addah Asmah ta jawo mata shanyewar ɓarin jiki, yayinda lokacin da Aminu ya kawo Aynah har gida da takardar saki uku bayan dukan daya lakaɗa mata ya sake ruɗar da jikin na Adda Asmah har sai da takai Zulfah ta kira gimbiya Su’adah tana kuka akan tazo ta taimakesu Mom ɗinsu zata mutu.
Jini ba wasa bane, dan duk yanda gimbiya Su’adah taso ignoring al’amari ya gagara gareta, har hawaye tayi itama ganin video na Aynah hawan jininta ya nema tashi. Tanda halayen banza ta wani fanin, amma tanada zuciya mai ƙyau kuma. Dama can zugar Addah Asmah ɗin ce da fulani ke sake kangarar da ita wani lokacin. Haka ta shirya Safina na roƙonta kartaje dan ALLAH Mardiyya tace danmi? Ita rayuwa ai ba’a maida sharri da sharri. Koba komai ai ALLAH ya nunama Adda Asmah ita ba komai bace ba, sannan duk makircinta a karƙashin hukuncin ƙaddara da jarabawa yake. Idan Maah taje gareta a yanzu Ai sake tabbatar mata zakaran da ALLAH ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi ne. Sannan babu hanun daya isa canja ƙaddarar ALLAH sai dai kai wahalarka ka ƙare a wahale wanda kakeyi dominsa yana ƙara zama sama da kai.
Da wannan zantuka na Mardiyya suka ɗunguma gidan Addah Asmah, inda suka isketa ita kwance Aynah kwance cikin jini na dukan da taci hanun Aminu. Da taimakonsu aka wuce da su asibiti, a kuma daren mai-martaba da fulani suka iso suma. Sunji daɗin ganin Su’adah da yaranta a wajen, suka shiga sanya musu albarka. A daren shima Daddyn Aynah ya iso, bai kumayi zaman ɓata lokaci ba akai shirin fita da su waje dan jikunan nasu su duka yayi tsamari sosai.
Da Fulani suka tafi, gimbiya Su’adah tai kememe tace babu inda zataje hakama ƴaƴanta. Babu wanda yaga laifinta anan, dan ansan an cutar da ita…

___________________________

Wannan hatsaniya na cigaba da yaɗuwa cikin Raudha na ƙara girma. Komai nata ya canja, idan kaganta sai kace ba ita bace. Auren su Fatisa hanata zuwa hutawa Ramadhan yayi, iyakarta nan Bingo sabon gidan Mummynsu da yake anan akai yinin biki kamar yanda Alhaji Sageer Dogarai ya roƙa. Anyi yinin biki laraba Raudah ma a kwance ta yini da zazzaɓi, amma dan jaraba tana a gidan ɓoye. Da dare Alhaji Sageer Dogarai da kansa ya maidata government house duk da kuwa anzo daukarta, kuma dama tana tare da guards nata. Ba kowa yasan Raudha na gidan ba ƴan biki, sai da zata wuce gida. Aiko abin ya bama kowa mamaki kodan yanda Aunty Hannah tazo ita tana baza mulki kaikace itace matar shugaban ƙasar ma. Washe gari Alhamis ƴan biki suka ɗunguma Hutawa, inda akai musu tarba ta mutunci dan yanzu M. Dauda Alhmdllhi, duk da dai ginin shagunansa ko muce super market bai gama kammaluwa ba har yanzun. Amm kuɗaɗen daya samu ba ƙaramin barje guminsa yake ba. Kujerar makka kuwa ya rike sirrin a ransa shi da Inna da Baba Nafi zasu.
Ranar Juma’a aka daura auren su Fatisa da mazajensu. Auren daya bada mamaki kasancewar shugaban ƙasa Ramadhan ya halarta tare da wasu gwamnoni da ministers. Hakama Alhaji Hameed Taura da Alhaji Basheer Hameed Taura. Ga Alhaji Sageer Dogarai da tasa tawagar dan a cewarsa su Fatisa shima ƴaƴansa ne. Saboda Asabe ta riƙe masa nasa da amana, duk da kalubalen data ɗan fuskanta ga yaran a farkon auren, sai dai halin kirki data dinga nuna musu da nuna rashin damuwa da abinda suke matan ita da Yasmin sai suma suka risina suka bata haƙuri ta haɗa ta rungume ta zame musu uwa.

Sam Raudha bata san Ramadhan zaije ɗaurin auren ba sai gani tai alabarai da aka nuna dalilin zuwansa wajen. Jitai fushin da take da shi ya kwaranye. Dan tunda yace bazatajeba take haushi da shi, ta kama matsar kwalla Basma na lallaahinta. Koda ya dawo gidan bayan la’asar kasancewar a helicopter yaje ya dawo saita rungumesa tana kuka da jera masa tagwayen godiya.
Murmushi yay kawai ya kama hanunta suka shige ɗakinsa. Ya zauna akan sofa tare da ɗoraya bisa cinyarsa duk da ƙaton cikinta bai damu ba.
Sai da ya ɗan sumbaci lips nata yake faɗin, “Partner yanzu kin lalace wlhy, komai kuka komai fushi kamar ba Ustazah ɗina mai haƙuri da juriya ba. Anya kuwa ranar shiga labour room ba akwai aiki gagarumi a gabana ba?”.
Kwanciya tai jikinsa tana murmushi da hawaye. “ALLAH Noorullah dan baka san wahalar bane. Cikin nan ya isheni ji nake kamar na cire na huta”.
Murmushi yayi mai kayatarwa, ya ɗaura hanunsa a saman cikin nata yana shafawa. “Kiyi haƙuri jarumata saura ƙiris insha ALLAHU. Kedai kawai mu cigaba da addu’a ALLAH ya saukeki lafiya ok”.
Kanta ta ɗaga masa da sumbatar kumatunsa. Kafin tace, “Shine ka tafi Hutawa ɗaurin aure koma ka sanar min”.
“Hhh haba ƙawata, ina sanar miki rigima zaki sakamin da shagwaɓa, ni banjeba ke bakije ba”.
“To amma tunda kasan zaka basai kaje dani ba da an ɗaura auren sai mu dawo tare”.
“Ke ɗin ce zaki yarda muje mu dawo a ƙanƙanin lokacin nan. Yi haƙuri ai dakin haihu insha ALLAH zakije ki kai musu baby su gani. Kimma san ya mukai da Anne?”.
“A’a”.
Ta faɗa tana girgiza masa kai.
“Wai Taura house zaki koma da zama har ki haihu yaro yay ƙwari. Cikin farin ciki ta miƙe zaune sosai a jikinsa. “Kai amma naji daɗi ALLAH, koba ko….”
Baima bari ta ƙarasa ba ya mangare mata kai yana hararta. “Oh kinmaji daɗi kenan. To ai a take nace mata ban yardaba sai dai ita ta dawo nan”.
Baki ta tura masa gaba. “ALLAH wannan buƙulune kawai zakamin”.
Dariya ya ƙyalƙyale da shi mai kayatarwa. “Naji gara hakan, nida aka shirya yima buƙulun barina gaurofa. Muna nan tare ki haihu muyi rainon babynmu kamar yanda mukai na cikin”.
“Uhmm kaji wai mukayi, nadaiyi abina”.
Gira ya ɗage sama, yana mai kai bakinsa saitin kunenta. “To amma wake ƙarama babyn ƙarfi bani ba”.
Kansa ta ture da sauri tana ƙoƙarin tashi ya hanata. Haka ya cigaba da tsokanarta yana kunnata tana masa shagwaɓa. Daga ƙarshe suka koma gado sannan sukai wanka tare kamar yanda suka sabarma kansu a yanzu musamman irin wannan wankan na lada.
Kamar koda yaushe langyare masa tai, dan ba karamin jigata take ba a duk sanda hakan ta faru, sai takai ya mata tausa da lallaɓata tayi barci ake rabuwa lafiya. Yanzun ma bayan tayi barcin fita yay zuwa dinig yayi lunch dan yunwa yakeji sosai.

 

*____________________________*

A kwana a tashi babu wuya wajen UBANGIJI. Raudha ta cigaba da rainon cikinta cikin kulawar ALLAH da Ramadhan, duk da nauyin Al’umma dake a kansa yana iyakar ƙoƙarinsa gareta itama. Ga gimbiya Su’adah kadaran kadahan tsakaninsu, ba gallazawa babu nuna damuwa. Dan ko Taura House taje zata gaisheta ta amsa ba kamar da ba sai dai iyakar gaisuwarce. Bazata kulataba bazata kuma hantareta ba. Hakama tsakaninta da Aunty Hannah, takan leƙo gidan lokaci-lokaci su gaisa, wani lokacin da mutanenta ƴan siyasa, wani lokacin ita kaɗai sai guards nata. Sau uku tana zuwa gidan Mummynta Asabe. Hakama gidan su Bilkisu dake nan Bingo duk taje. Su Fatisa ne dai har yanzu bata leƙaba saboda ba’anan Bingo suke ba.
A haka cikinta ya shiga watan haihuwa raki da shagwaɓa ya ƙaru, dole kuma Aunty Zuhrah ɗiyar Yafendo ta dawo nan government House da zama dan Anne dai taƙi hakan duk da kuwa Ramadhan jikane. Tunda watan ya shiga kwanakin haihuwa ta daina zuwa makaranta, sai ta dai su Basma suzo su mata bayanin abinda akayi. Randa takejinta da lafiya ta fahimta, saɓanin hakan tace su barta karatunma baza’ayiba. Sukan mata dariya da tausayinta. Dan hatta uban gayyar idan ta birkice masa da rikici dariyarsa yake kwasa kafin ya koma lallashinta a shirya da ƙyar.
Tun dai ana saka ran haihuwar har kwanakin da aka bata a sibiti suka gota, koda Ramadhan ya nuna damuwarsa Dr Hauwa tace karya damu ana samun irin hakan ai ba komai bane. Adai cigaba da mata addu’ar sauka lafiya ……….✍

*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply