Bakar Inuwa Hausa Novel Hausa Novels

Bakar Inuwa 75


Bakar Inuwa 75
Viral

*_Episode 75_*

………..Alhmdllhi a wani dare na juma’a da yay dai-dai da cikarta watanni goma cif ta farka da gigitacciyar naƙuda. Rikicewa Ramadhan yayi, da ƙyar ya iya control ɗin kansa ya saka jallabiya sannan ya fito kiran Aunty Zuhrah. Da taimakonta suka ɗauki Raudha zuwa clinic ɗin gidan, yayinda tuni su Basma sun sanar ma Anne. Babu bata lokaci a daren Anne da Dr Hauwa suka nufo gidan, inda suka samu har wata Dr ta shiga da ita ɗakin haihuwar. Babu ɓata lokaci Momyn Jafar ta rufa musu baya itama, aiko ta tarar Dr Ingoze na niyyar halaka yaro dama uwar. wata irin muguwar bangaza takai mata tare da sauke mata tagwayen maruka, daga haka ta hankaɗota waje ta koma kan Raudha.
Kowa yayi mamakin yanda aka hankaɗo Dr Ingoze waje. Gashi Dr Hauwa tace security su rike mata ita har saita fito. Hakan kuwa akai zuciyar su Anne fal wasuwasi. Dama shi Ramadhan suna kawota ya koma ciki kamar yanda Aunty Zuhrah ta bashi umarni. Maimakon zama sai yay alwala ya fara nafilfili da nemawa matarsa sauƙin naƙuda da fatan sauka lafiya.
Tabbas Dr ingoze tama Raudha lahani, sai dai cikin amincin ALLAH an samu damar ciro jaririn ta hanyar theatre kamar yanda Dr Hauwa ta yanke shawara. Dan ƙarfin Raudha ya nema karewa saboda yanda Dr ingoze ta dinga danna kan yaron yana ƙoƙarin fitowa kafin zuwa Momyn Jafar.
Sai gabanin asuba suka fito, anci nasarar ciro santalelen yaro gashi ƙato alamar uwarsa taci ta ƙoshi. Sai dai babu damar ganin Raudha har sai ta samu isashen hutu kamar yanda Dr Hauwa tace. Atake murna ta gauraye gidan na gwamnati, kowa kuma nama Raudha fatan samun lafiya. Lokacin da jariri yaje hanun uban gayya Ramadhan hawaye yaji sun cika masa ido. Ya sumbacesa tare da rungume abinsa yana maijin kaunarsa na ratsashi. Wannan shine karo na biyu da ALLAH yay masa ƙyautar da kuɗi basa badata, hakama mulki da ɗaukaka. Ya bukaci ganin Raudha duk da Dr Hauwa taso dakatar dashi ya bata haƙuri, dole aka ƙyalesa ya shiga shi kaɗai ya dubata. Tausayinta ya kamashi, ya dinga jera mata tagwayen kiss’s da addu’oi.

Zuwa wayewar gari labari ya karaɗe lungu da sako na ƙasar NAYA akan shugaban ƙasa ya samu ƙaruwa. Ga hoton Baby nata yawo saboda su Basma da sukaita turawa ƴan uwa da abokan arziki. Sai yazam kowa ƙoƙarin ɗorawa yake a shafinsa, wasu idan sun gani suma sai su ɗauka daga haka ya karaɗe wayoyin mutane. Yaro yasha addu’oi yayinda ƴammata da yawa suka koka dajin kishin inama daga jikinsu ya fita. Sultana dake ƙasar America kam harda kwanciya ciwo dan har yanzu ciwon son Ramadhan na zagaye da ita. Kawai dai babu yanda zatai ne tunda ya faɗa mata iya gaskiyarsa shi baya ra’ayinta tayi haƙuri ta samu mai sonta..
Karo na farko, lokaci kuma na farko da Gimbiya Su’adah ta kira waya tasa aka haɗata da Raudha data farka a washe gari da rana. Yajiki tai mata da fatan samun lafiya. Ita dai Raudha abun ma har hawaye ya sakata. Ramadhan dake gefenta yasa hannu yana share mata fuskarsa ɗauke da murmushi.
Ɗansa dake hanunsa yanata barci ya kalla. Ya shafi lips yaron jajaye yana faɗin, “Ba kuka zakiyi ba Partner. ALLAH zaki godemawa a wannan gabar, ni shaida ne Maah ta jima dayin nadamar abinda tai miki, ta shanye a cikintane kawai saboda nauyin tunkararki. A yanzu kam koda abinda ke faruwa da Lubnah a gidan miji ya isa sake tsoratata”.
Da mamaki Raudha ta dubesa. “Aunty Lubnah kuma?”.
Kai ya jinjina mata batare da ya kalletaba ya cigaba da wasa da sumar yaron. “Eh Lubnah. Tun satin da aka kai Lubnah gidan aure bata sake farin ciki ba. Kuskure kaɗan miji zai lakaɗa mata duka tare da ƙanensa. Ke hatta da uwar mijinma ba ƙyaleta taiba itama dukan nata take. Duk da dukiya irin ta gidan su Mansur ƙiri-ƙiri suka sallami kaso ɗaya bisa biyun ƴan aikinsu aikin ya koma kan Lubnah. Cikin ƙanƙanin lokaci ta fita hayyacinta saboda azaba. Ameenatu, tun sanda Lubnah ta kawo Mansur garemu matsayin miji na nuna ƙin amincewata, saboda na jima dajin labarin mahaifiyarsa bata zama da sutukai. Hakama kanensa basu da isashen tarbiya. Amma sai Maah taƙi saurarena saboda Lubnah tace tana son sa akace ai nima wadda nake aure bata dace dani amma suka amsa. Dan haka Lubnah zata auresa ko ina so ko banaso. To ga sakamakonan sun gani, dan yanzu a dalilin dukan da surukar mijinne tai mata tai ɓarin cikin jikinta, maimakon Mansur ɗin yaji tausayinta sai ya maidota gida da takardar saki har uku wai yana zarginta da tarayya da drivernsu kiji sharri. Koda nai bincike uwarsace duk ta tsara hakan kamar yanda take koran matan ƴaƴan itama tai sanadin da za’a korota”.
Sosai abun ya taɓa zuciyar Raudha duk da zaluncin da su Lubnah suka dinga mata a baya. Ta jingina kanta da kafaɗar Ramadhan tana kallon babynsu hawaye na zubo mata. Shima rungumita yay da hanunsa cikin son kore mata damuwarta yace,
“Ustazah dawa yaron nan ke kama?”.
“Dani mana”
Ta bashi amsa tana share hawaye. Ƙeyarta ya ɗan tallara kaɗan. “Son kanki yayi yawa madam. Kowa yaga Abdull-Hameed Ramadhan Taura yasan gida ya ɗakko, mufa jininmu ƙarfine da shi yarinya”.
Murmushi tayi mai ƙayatarwa da cewa, “Uhm nidai basan cika baki. Dama da Pa kace yana kama ko Bappi sai na yarda”.
Dariya yay yana mai sumbatar kumatunta. Hakama babyn ya sumbaci goshinsa. “Bakice komai akan sunan dana kirashi da shi ba”.
Murmushi tayi mai kyatarwa da shafa kumatunsa. “Saboda shine ra’ayina shiyyasa nima”.
“Woow sweetheart inajin daɗi idan muka kasance bisa tarayyar abu guda”.
“Noorullah! Idan duk yarana zasu kasance da sunan Bappi ko Pa ko Anne ko Maah ko kai bazan taɓa baƙinciki ba. Fatana dai ALLAH ya bani ikon sauke nauyinka dake kaina ka kuma zamemin miji har a gidan aljanna. ALLAH ya raya Abdull-Hameed Ramadhan Taura ya albarkaci rayuwarsa. Yasa yay gadon ƙyawawan halayen Bappin da Pa da kai kanka”.
“AMin ya rabbi sweetheart. ALLAH yay miki albarka ya ƙara miki lafiya. Yasa nan da wata shekarar mu sake dawowa labour room…..”
Da sauri ta rufe masa baki ƙwalla na ciko mata ido. “Wannan ai fatan tsiyane”.
Dariya ya kyaƙyale da ita yana ture hanunta. Miye na wani fatan tsiya anan ai nasan zaki iya Mrs Taura.
Haka suka kasance cikin nishaɗi har saida Aunty Zuhrah tazo ta korashi ɗakinsa sannan.

★Sai da Raudha ta warke sosai aka fara shirye-shiryen taron suna, amma kowa dai yasan sunan yaron Abdul-Hameed anma Bappi takwara. Ramadhan yaso ayi suna a Taura house Bappi ya hana yace ayi a government house kawai. Badan yaso ba dole hakan aka shirya. Taron sunane daya haɗa manyan mutanen ƙasar NAYA lungu da saƙo, inda amaryar jego da baby sukaci ƙyau har suka gaji. Shi kansa angon jegon yayi tsaf dashi kamar yana shirin yin sabon aure. Anci ansha an kumayi bishasha, inda yaro ya samu ƙyaututtuka masu ban mamaki wasuma dan riya sukai badan ALLAH ba. Dan kawai wane yayi kar ace su basuyiba.. Hatta M. Dauda ba’a barsa a bayaba ya haɗo kayansa na jego harda saitin robobin wanka da saƙe saƙin wanka na icce da ƙatuwar garwarsa ya kawo. Wannan abu yasa su Aunty Hannah takaici duk da ba’a wajen taron ya bayarba. Sai dai ita Raudha farin ciki tai ita da Ramadhan.
A zahiri taro ya tashi lafiya, sai dai a baɗini wasu sun iso wajen taron ransu da ƙulli. Ba su kowa bane sai su Alhaji Yaro glass da ko Aunty Hannah yanzu batajin sirrinsu. Bayan taro ya tashi lafiya wajen ƙarfe biyar na yamma a tsakanin government house zuwa Taura house aka buɗema motar Alhaji Hameed Taura wuta. Harbi ne irin na kwararrun maharba da ko a nesa suka harbo harsashi sai ya isa ga wanda suka hara ɗin. Sai dai in ALLAH ya kaddara da kwananka a gaba ka tsalle domin ikonsa.

Tabbas masu harin sunyi nasarar kaima motar hari sai dai basu taki sa’a ba, amma duk da haka ɓarnarsu ta shafi Taura house. Bayan kammala walima Alhaji Hameed ya shiga mota shi da Anne da su Yafendo domin komawa gida. Sai dai kiran Daddyn Aynah ya riskesu akan rikicewar jikin Adda Asmah gashi ya kira Gimbiya Su’adah bata amsa ba. Hakanne yasa suna ɗan gota government house Bappi da Anne suka fita amotar suka shiga wata harda Yafendo, Inna kuma dake fama da ƙafa tunkan su tafi wajen walimar dama danta dagene Bappi yace a wuce da ita gida. Kasancewar motar da su Muneera ke ciki suka amsa ɗin yasa Muneera dawowa wajen Inna ita kuma. Su Alhaji yaro glass basu san da wannan canji da aka samuba suka sanarma yaransu tahowar Bappi da sanar dasu motar da yake ciki su shirya.
Idan UBANGIJI bai ƙaddara mutuwarka ga makiyiba, komai wahalar mai wahala sai dai ya dawwama cikin wahalar farautar zafin rana data ɗacin zuciya babu nasara.

*_ALLAH ka shiga tsakaninmu da maƙiyanmu😭🙏🏻._*

Take a wajen ma ALLAH yay ma Inna Rasuwa, dan sai gawarta aka nufi asibiti da ita. Driver da Muneera ne kawai ke numfashi. Shima driver ko mintuna biyar basu cikaba ya rasu.
Karaɗewar labarin wannan hari da aka kaima Alhaji Hameed Taura cikin kanƙanin lokaci yasa ko zama basuyi a gidan Adda Asmah dake a mawuyacin hali itama suka taho. Hakama Raudha da Ramadhan da su Aunty Zuhrah duk sun rikice a government house. Dan kuwa babu abinda kake gani a yanzu akowane gidan tv sai harin da aka kaiwa Alhaji Hameed Taura. Amma abinda yaba mutane mamaki kamar yanda yan jarida ke faman shelantawa babu shi a motar duk da kuma daga government house kowa yaga motar ya shiga har shugaban ƙasa yay masa rakiya.
Zamu iya cewa a wannan dare gaba ɗaya NAYA a hargitse ta kasance. Dan ba’a samu damar bizne gawar Inna ba saboda jami’an tsaro sun rike. Kuka Raudha take tana sambatu da ambaton “Su din azzalumai ne. Dama sun ce sai sun kashemu, miyay musu, mi kai musu kaima mijina?. Na tsanesu, da ace sun samu nasara kan Bappi yau da kaina zan kashesu, amma ko yanzu karka ƙyalesu Ya Ramadhan. Na rokeka karka barsu suma su dukansu”.
Kalaman Raudha sun girgiza Ramadhan, dan haka ya tsareta ta sanar masa suwaye? Mita sani? Mi take boye musu. Shi tun sanda ta karema Bappi hari ya tabbatar tasan wani abu.
Cikin kuka ta shiga girgiza masa kanta. “Wlhy bansan komai a sannanba Ya Ramadhan, sannan bansan su wanene ba. Nayi hakane saboda shima ya taimaki wani tsohon daya fisa shekaru a filin idi. Amma badan na sanshi ba. Badan nasan komai daga garesaba. Sai dai zan faɗa maka abinda na sani nima, amma wlhy ka yarda dani, ban yarda da aurenka saboda su ba. Nayine kawai dan yima mahaifina biyayya da gujema mahaifiyata tsinuwa da Gwaggo tace zatai mata inhar ban yarda da aurenka ba………..”✍

 

*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply