Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 1


Bibiyata Akeyi 1
Viral

Page 1

Zaune take acikin wajan amma hankalinta baya jikinta domin kana kallanta kasan tana cikin matsananciyar damuwa wanda hakan yagaza boyuwa sanda yanuna akyakyawar fuskarta,

Tunani take acikin zuciyarta shin ko tajene tasamesu taji dalilin wannan *bibiya* da takura dasuke mata ne, atake wata zuciyar tayi saurin gargadarta domin batasan mugaye bane,

Amma aida mugaye ne dasun dade da cutar dake, wata zuciyar tace da ita. Mtswww taja wani dan siririn tsaki, ni wallahi tsoronsuma nakeji tafada cikin muryar kuka tareda kifa kanta ajikn table dinda yake gabanta.

Tosu wayannan mutanen suwaye?? mesuke nema awajanta??? Wani laifin tamusu dasuke *bibiyar*rayuwarta?? dataga dai bata dayadda datasamu amsar tambayoyinta kawai tamike tare da zarar jakarta tayi hanyan fita daga restuarant din dake cikin school din zuwa hall na lectures dinsu tana kallo daya yayiwa daya mZ33yyb3rw3ramu nuna masa ita yayi akan tatashi subita koda taga haka wuff tafice daga cikin wajan batareda datsaya biyan kudiba dan damuwa bata barta tayi ordering komaiba

Koda tafita tayi noticing ana binta amma hakan be daga mata hankalinta dan abunyafara binjiknta direct hall dinda zasuyi lectures tawuce tasamu har malamin sunshiga sa’arta daya bame tsanani bane yasa tayi saurin shiga tasamu gefen kawarta amira tazauna

Amira rada tamata akunne ke inata kiran phone dinki ina kika shiga kikabari phone anata kira banza ainaso kiyi missing attendance,

Gabaki daya wannan surutun da amira takeyi batasan atakure dakeba kawae tatashi tacanja wajen zama tace kici kanki

Ana tashi kuwa ko takan amira batayi ba tafice dama shine last lecture dinsu na ranan, kodatafita batayi mamakin ganinsu ba don tasan za’a rina (wae miji ya saki mata ubansa yaje zauranci)
Fita tayi tawuce gida koda tana keke napep ma haka taga suna binta sanda tazo dab shiga gida kafin suka juya,

Tana shiga gida tasauke wata nauyayyan ajiyan zuciyarta,
Da sallama tashiga tasamu babansu harya dawo tatsuguna aladabce tamasa sannu da hutawa ya amsa cikin sakin fuska sannan tatashi zata tafi harta fara tafiya naji yace, *hanna*

*Hanna*ni unknown nakara maimata sunan araina nace amma sunan yayi saurin juyowa tayi cikin ladabi da nitsuwa tace na’am baba yace idankin shiga ciki kyakiramin mamanki toh tace tareda juyawa

Tacigaba da tafiya cikin nutsuwa giftawa tajeyi taji wani zancen daya hargitsa mata Tunani yakara gigitata tare da tsundumata cikin damuwa kunnenta takara kawowa kofar dakin taji hajiyah lami wacce suke kira da Amma tanacewa,

Ai aikin malam nakarangi yanakyau kiduba tun yarinyannan naarama danasa yatura mata aljani wadda ze hanata aure aizancen danake miki haryau bbu wanda yataba sallama da sunan yazo wajanta ga yan uwanta komai ya kankama biki kawae muke jira itakuwa shiru kikeji kamar an aiki bawa garinsu tana gama fadin haka suka tafa tareda shekewa da wata shedaniyar dariya aibata jira sunkara wata maganar dazata daga mata hankaliba tawuce jiri na ebar ta harshirin yasadda ita yakeyi

Tana shiga dakin mamansu kawae tafada kangado tasaki wani marayan kuka me tsuma ran me sauraro

Temakonta daya mama bata dakin yasa tayi kukanta mai isarta daganan tatashi tawanke idonta daganan taadauro alola tayi la’asar tayita addu’o in neman tsari daga sharrin mutum da aljani

Mamane itada inna kaltu mai aikinsu Zaune akicin tana dafawa baba ruwan shayi ni inna kaltu kuwa kinga diyarki tadawo daga makaranta

Najita shiru haryanxu batazo tacemin tadawoba inna kaltu take aikwa bangantaba inaga bata dawoba, to halan cewar mama dauke da gajeruwar damuwa aranta

Yarone dan kimanin shekaru 12 yayi sallama mama waekije inji baba yana falo yana jiranki toh kace masa ganinan zuwa

Fita tayi daukeda farantin ruwan shayi ahannunta tanufi falo anan tatarar da baba yana karanta jarida sallamarta ce tasashi ajiyewa tareda zare gilashin dake idonsa amsa sallamar yayi sannan takaraso ciki tazauna tazuba ruwan shayin tamika masa yakarba yadan kurba sannan yayi gyaran murya mama tajuya ta fuskanceshi dan da’alama maganar dayakesonyi mai mahimmanci ne

Shin waini halima meyake damun diyarkine gabaki daya ina lura da ita kwanannan batasakewa batada walwala shin meke damunta?? Hmm wani gauron numfashi taja wallahi alhaji nima kwanakinannan haka nake kallonta narasa meke damunta nifa alhaji inaji yarinyar nan dagaske fadan mutanenne halan aljanine ya aureta

Kul karnasake jin wannan zance abakinki baba yayi saurin gargadarta ni inaji aji kina wani alkhairi ne yake BIBIYAR RAYUWARTA kace mahaifiyarta keyakamata kije kiji damuwarta

Bayan ta idarda sallah ne taki shingida tafara gyangyadi tagakamar inuwar mutum akanta agigice tafarka ta…………

Shin wae wayake BIBIYAR rayuwar *hanna*??????????

Shin wae Su wayannnan mutane dasuke BIBIYAR yaruwarta ta suwayene???????

Shin dagaske Aljanin da aka turo mata ya sameta kuwa ko akwae wani boyayyen al’amari ne

Domin samun amsar wannan tambayoyi kubiyoni musamosu tare

Ur’s
Z33yyb3rw3r

BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writing by
_Zaynab Bawa (z33iiyyb3rw3r)_

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply