Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 100


Bibiyata Akeyi 100
Viral

Page 100*

 

Jikin kilishi dai abun ba’acewa komai dan sai k’ara gaba abuu. yakeyi.”
Yaranta gabaki d’aya hankalinsu atashe yake kana kallOKnsu gabaki d’aya sunfita hayyacinsu, away’anna ranaku suna kallon tashin hankali, kokadan basuyi zaton haka daga wajan mahaifiyarsu ba.” ahalin yanzuma kilishi tbii shawarar kawqce, tabbas acikin kawaye baduka aka taru aka zama d’ayaba, akwai 6ata garii Acikin su, kamar yadda akwai nagarii cikinsu, akwai masu bada mummunan shawara akwai kuma masu bada kyakkaywan shawara, sannan bakowace irin shawara bace yakamata ana baka kadauketa, bakuma kowacce shawara bace zaka yada ita, aduk lokacinda akace anbaka shawara toh ana bukatar ka nutsu, kayi amfani da kwakwalwarka wajan taceta, haiqaqq akwai bata garin kawaye wanda, afuska zasu numa suna sonka amma azuciya kuma, suna kinka da’ace wani abun farinciki zai sameka cikin zuciyarsu suna bakin ciki.” tabbbas kilishi tahad’u da irin wannan kawaye, wanda ayanzu waye garii yawaya, tana cikin wani mumuunan hali duk ta dalilin munannniyar abota.”
Kasancewarta abaya mace mai tsoron Allah, saukinsu daya shine duk cikin masarautar bbu wanda yasan cewa kilishi batada lpy, hatta da kuyangu da jakadai an dakatar dasu dag shiga shashinta, wanda yaranta ne kwai sukayi hakan, babban tashin hankalinsu shine shirun da mai martaba yayi.”
Tun ranarda yashigo yaganta sannnan yajii irin magan ganunda take fad’i bai kara komawa ba, kuma har yanzu baice komai akan wannan al’amarin ba, yaran kilishi harsunyi zarya sun gajii,”
Zai zauna dasu suyi mgana amma daga zaran sun d’auko masa zancen mahaifiyarsu zai 6ata rai sannan kuma bazai kara cewa komai ba, harsu tashi subar wajan, abun yana matuk’ar damunsu ga abuu sai gaba yakeyi.” awannan lokacii su affan suka fara tunanin naimo mai maganii tunda sunjura harsun gaji.”
Ranarda kilishi tacika satii d’aya da fara rashin lpy, aranar duka yaranta suna zaune afalo yayinda ita kuma kilishi ke kulle ad’aki, shashekan kukan intisar ne yacika falon, yayinda mafii yawqncii haushinta sukeji, dan dasaka hannunta mahaifiyar su tashiga wannan hali, tsaki affan yaja sannan yace, nifa gaskiya nasamo mafita wadda hakanne kawai zaiyi mana kyau sannnan yayiwa umman ma kyau, zama shirun mufa bazai haifar da komai ba, sai abunda yake gaba ma.”
Yaya khadija ce ta amshe maganar ea cewa eh nima fa haka naganii, dan yanzu haka basa anyi mun magana damai maganii, affan ne yayi saurin cewa a’a yaya, nazauna nayi tunani kan hakan fa, baidaceba ace mun shigoda wani mai magani cikin wannan masaurauta bada sanin abba ba, ikilima tayi saurin katseshi da kai dallah rufe mana baki ni ahalin yanzu bansan wani dacewa ba, lapiyar mahaifiyarmu kawai nasanii, shii abban yayi shiru yak’i cewa komai, karfa ka manta duk mugun halinta ita ta haifemu, kuma duk cikinmu bbu wanda yau zaice tata6a daurashi wata mumminar hanya, nasan da wannan arfan yace sannan yakara da cewa” yaya koda aynzu ace umma tasamu lpy, wallhy aikin banza mukayi idan har bamu nema mata lahirarta ba.”
Kamar yaya suka tambaya, gyara zamansa yayi sannnan yace abunda bake nufii, yanzu duk cikinmu bbu wanda abunda tayi yadawo kanta ba, dabakinta tafad’i dan haka ita wacce akayiwa abun zamuje munema mata gafara agunta, sannan ayi zancen neman magani,”
Kana ganin hakane nafita, kuma ita hanna zata yarda ta yafee mata?” hava yaya wallhy nasan *hanna* sosai tanada tausayi sqnnan ga hakurii, duk hakurin yaya yariima da kike kallo Allah tafishi.”
Gabaki d’aya batada riqo arayuwarta, jijjiga kai sukayi sannnan sukai na’am da cewar sa.”
K’arfe takwas na dare 8:00pm su affan suka nufii shashin ummmiii.”
Tunda aka gama suna *hanna* takeson tafiya gida, ean tafiso saitayi arba’inn sannan tadawo, da tasamu marshall da maganan yakii fiirr ganin haka yasakata, samun ummii tasanar da ita, ummii bataki mata ba, amma har cikin ranta bawai tanason tafiyanta bane.” halin yanzu irin shaquwarda tayi da *hanna* ta dabance, balle yaronda kullum yana gunta, idan kaganshi wajan mahqifiyarsa to tabbas yunwa yakeji, gashi yanada hakurii saiya ini currr ma baiyi kuka ba.”
Ummii tasamu mai martaba da zancen tafiyan *hanna* gida, amma shii bai k’ii ba baikuma ce tatafii ba.”
Zaune suke ummii da *hanna* a falo, sai labba dake d’aki dauke da jariri, suna cikin zaune marshall yashigo, dan tunda yafita dasafe dawwarsa kenan, ummii ne tayi masa sannu dadawowa sannan tashige ciki, *hanna* ganin ummii tatashi dasaurii tanufii fridge tadauko mai ruwa mai sanyii 6arewa tayi sannnan tabashi ruwan yaja.” ajiyar zuciya yasauke sannan yace aikuwa kamar kinsan da ishin ruwa nadawo, nasanii mana tafad’a takaice, ina tare dakaiifa, murmushi kawai yayi bai kara furta komai ba su affan suka shigo da sallama, cikin sakewar fuska suka amsa musu,”
Zama sukayi sannnan suka ta6a hira kad’an, sannan yayya khadija tashiga zayyane musu abunda ke faruwa kafin sugama bayani hanna hawaye ya wanke mata fuska,” nan suka had’a da nemanan gafara, kokadan *hanna* bata riqeta ba, alokacin tashaida musu tayafe mata, godiya suka runga yi tareda matsanancin kunyarta data kamasu.”
Shikuwa marshall baice komaiba tunda har wanda akayiwa tace tayafe, baiga dalilin dayasa shii zai dauki zafii ba.”
Cikin nuna al’ajqbi marshall yace yanzu wayake yimata nagani, bbuu suka bashi amsa atakaice, dan haryanzu abba baice komaiba,” aikuwa yakamata yace, marshall yafad’a dan zama hakan ba mafita bane yana gana fad’in haka yajuya ya kallii *hanna* sannnan yace jeki sqnarwa ummii sannnan tafito mutafii baki d’aya muje duba cikin ummma dasauri ta miqe tajeta tasanarda ita abun yacika ummii da al’ajabii, amma haka tafito suka fice, koda suka isa *hanna* kuka tarinka yii ganin jikin kilishi har ummii sanda ta zubda hawaye.” dagudu *hanna* tafice bata tsayya ko inaba sai shashin mai martaba, tsugunnawa tayi kan guiwowinta tana kuka tana cewa, abbba mun tuba kamana raii wallhy abba umma najin jiki, kayi hakurii kanema mata wanda zai mata magani, nikam abba nayafe mata, har indai dannii kaki cewa komai.”
Tsayawa kawai yayi yana
Kalllon *hanna* , wannan yarinya wace irin zuciya gareta haka, duk wanda zaiyi mata sharrii ita da alkhairii zata bita, ajiyar zuciya yasauke sannan yace” *hannatu* diyata share hawayenki, kinjii kidaina kuka, wannan abuu baiyi dadii bakam nikaina ina neman gafararki, ni abbab bakayimun komaiba itama har cikin zuciyata na yafe mata.”
In sha Allahu daga yau za’a fara yimata magqnii zan sanarda madibboo, amin ta amsa sannnan tatashi tafice.”
Aikuwa kwanan kilishi biyu dafara magani, tasamu lpy aikuwa tana kuka tanemi gafarar *hanna* kamar yadda hanna tashaida wa kowa tayafe, haka itama ta shaida mata.”
Zama sosai akayi agidan yadda mai martaba zafff yayiWa kilishi Sannan yashaida mata dalilin dayasa bazai saketa ba dalilin yaranta ne, anan kuma yasaka intisar ta fiddo da miji.”
Aikuwa bata dad’e ba tafito dashi, cikin kwana biyu akayi auran, mijinnata yanada mata d’aya da yara hudu, yanada dukiyarsa, bai nuna bambamcii tsakanin ta da matarsa, zaman lpy sukeyi sosai.”
*Hanna* kuwa tatafi gida saita tayi kwanaki arba’in 40 curr acan dan saida akayi auran najeeb da karima kafin tadawo.” har tagama kwana arba’in dinta bata ta6a tad’awa wani Kan abunda kilishi tayi ba.”
Aranarda zata dawo marshall da kansa yazo d’aukanta,”

*BAYAN SHEKARA BIYU*

 

*Hanna* tagama karatunta, alokacin kuwa amiira ra yaya jalal shekaransu d’aya da yin aure sannnan tanada tsohon ciki, lokacin labba itama tayi aure dan dangin mahaifiyarsu ta aura, dan haka vatama kasaar.”
Hemeeda tahaihu yarinyarta kykkyawa, yayinda hafsat ma tahaihu tahaifii yaro,”
Itakuwa rabi’a haryanzu shiru da zaran saurayi yazo anacewa yafito zai gudu, tun abun yana damun amma har tadaina damuwa dan ta tabbata abunda tashukane ke bibibyarta.”

Saukan *hanna* kenan daga k’asar india daga wajan d’aurin auren abiid da fariisa wanda ya aurii matar shahid, matarsane da kanta tasaka ya aurii matar abokinnasa bayan rasuwarsa, dan tana tunanin wanda zai riqeta tsakni da Allah, da mijinta kawai ta yarda shiyasa ta roqeshi, ita kuwa fariisa dafarko ansamu matsala daga wajanta, dan tana kallo kamar tacii amanar mijinta da kuma kawarta ne, sai dakyar kafin ta amince.”

Agajiye sosai *hanna* take dan dakyar ta iya k’arasawa falonta nakasa tayi shame-shame, dakinta ma sai marshall ne yak’arasarda ita, aikuwa nan tashiga zazza6i mai zafin gaske gwajin farko yanuna tana d’auke da cikin wata uku, murna wajan dangin marshall baya misaltuwa, bayan wata tara ta haifo yarinyarta mai kamada ita sakk, gar rashin hasken fatarsu ma d’ayane.”
Ansha suna sosai yayinda tacii sunan mahaifiyar *hanna* suna kiranta da ainihin sunanta har su inne sunzo sunan tareda isshaq da matarsa wacce ya aura, itakuwa hussentu vata samu damar zuwa ba, sakamakon ciki da takedashi tsoho haka akayi suna aka gama cikin kwanciyar hankali.”

*BAYAN SHEKARA BIYAR*

*Hanna* na hango tazama mtashiyar mata wacce bazata wuce shekara ashirin da bakwai ba.”
Sai Abdulaziz yaronta nafari dakuma amina mai sunan mama, sai kuma hindu itace ta ukun sannann najeeb d’an karamun yaronda yake d’auke ahannunta.”
Dasaurii tashige gidansu bayan tafaka motarta, yaran suka bita abaya, gida naganii acike damm da alamu biki akeyi, Cikin saurii *hanna* tashige d’akin amma tana cewa,” hava yaya rabi’a kuyi saurii fa ku fito, ke kince bazakiyi komai ba sai walima, walimar ma yanzu lokacii yanata k’urewa, owwhh *hanna* idan kikayi hakurii yanzu zamu tafii cewar hafsat dake shirin fitowa, aigaradai dabata amsa, ita kuwa *hanna* dakin mama takora yaranta, tawuce wajan walima, washe garii kuwa da sassafe aka d’aura auran isshaq da rabiat bayan kwana biyu kuwa aka wuce da ita cameroon, *hanna* kuwa bataje ba dan marshall bai barta ba, washe garii bayan en biki sun watse kuwa, *hanna* nazaune dakin mama tana shirya kayansu dan gobe zasu wuce, amma tashigo, dafara’a *hanna* ta amsa sallamar sannan tace ammah bakiyi baccii ba?
Banyiba *hanna* ammah tabata amsa atakaice, zama kusada ita tayi sannan takamo hanunnunta tace, *hanna* nagode nagode,
Kwace hannunta tayi sannan tace haba ammah wannan abun fa duka yiwa kaine, eh dai *hanna* nasan rabiah er uwarkice ammafa sharrii na nemeki dashi sannann yakoma kaina, baki saduda ba sanda kika kallii er uwarki samu mijin aure duk ta dalilinki.”
Murmushi tayi sannnan tace ammah kije ki kwanta, dare yayi, Allah yamiki albarka tace sannnan tasaka kai tafice, amin *hanna* ta amsa sannnan takarasa shirya kayanta, ta kwanta, washe garii kuwa sasafe jirgin marshall yasauk’a bai dad’e da zuwwa ba kuwa suka koma.”

 

Zaune suke afalo marshall da *hanna* yayinda yaran dukansu sunyi baccii, kwance take ajikinsa, saurin d’agowa marshall yayi cikin farinciki yana cewa cutie yanaga kamar ciki kike dashi?” ciki kuma? Tafad’a sannnan taturo baki tace, Habadaii honey kayimun fatan sauk’ii mana, ai fatan saukinda zanyi miki kenan, tabb nikam hud’u sun ishenii, hudu fahh? aii saikinyii sha biyu.” shabiyu faa kace! Sai kace kaza, tabb, au haka kikace koh toh zamu ganii,”
Sai mu gani tafad’a hadeda daukan pillow na gujera tana maka masa, riqe filon yayi cikin wata irin murya yace,” u knw wat cwrtheart?” girgiza masa kai tayi, cikin wata irin siiga yace,” i forget to say that i love you yesterday cwrthear, and now i love you, inasonki irin sossai dinnan faa, love you muchest more tafad’a tanayi masa plash kiss akan lips dinsa,” sannna. Tazare pillow d’inta taci gaba da dukansa ahankali yana karewa yana dariya.”
~Hanna and marshall lives a happly ever after~.”

 

Alhmdllhy all possible things done with succes.”

Anan nakawo karshen wannna labari nawa na *hanna* da Abdullahii sai kunjini daukeda sabon littafina na *husna* ……..😜saidai kunjii labarin.”

Yanzu dai *hanna* da marshalł sunhuta zainab bawa ma tahuta, reader’s kuma kun huta.”

Am gonna miss yhou marshall and *hanna*😭

 

Takuce mai k’aunarku mai k’aunar sanyaku cikin farin ciki zeeiiyybawa❤😍

Ur’s

Z33iiyyb3rw3r

مشا الله
[8/27, 6:38 PM] 6ta Abuh: *BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

مشا الله لقد انتهت

*NOTE* “`banyi wannan littafin nawa dan cin zarafin wani ko wata ba, daga fara littafina zuwa yanzu plz inda akwai wanda na ta6a 6atawa raii ya yafeni,انا اسيف dan adam ajiiziineh, akwai lokuta dayawa da zaka 6atawa mutum kai batareda kasani ba.”
Nayi wannan rubutune dan fad’akarwa badan munanawa wani ba, Allah ina roqonka kasaka sak’ondaa nakeson isarwa ya isaga bayinka, Ya Allah ina roqonka kuskurenda nayi wajan wannan rubutu nawa ya Allah ka yafemun,اغفرلي ياربي ya hayyu ya kayyum ya zill jalalu wal ikram.“`

*GODIYA*

_Godiya ta gareki ta dabance *my Hajja* fatana Allah yabarmu tare, yaraya mana ihsan_انتي كل شيء

_Godiya gareki gwanata *Ayusher* hakika kin bani karfin guiwa sosai ina godiya ga hakan Allah yaraya mana husna da little baby انا سعدان بي لقاء اليك_

_Godiya gareki kawar arziki *Asmy b aliyu* ina matuk’ar k’aunarki_انتي صديقتي الحميم.

_Godiya gareki *pherty zarah* danuna soyayyarki gareni da kulawa شكران اكتر.”_
_Godiya gareki sadnaf شكران اليك *Sadnaf* Allah yaraya mana affan da ikram.”_
_Godiya gareki antyna tafii takowa *an2y rash* Karfafa guiwarki gareni ta dabance hakama soyayyyarki ta dabance_.”انتي كل شيء

*JINJINA*

*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*
Ayushert muh’d
Hajja ceh
Asmy b Aliyu
Pherty zarah
Kai da duk wani wanda yake cikin gidan haske ina sonku sosai.” Allah yabarmu tare Amin.” احبكم كثران.

 

*REAL HAUSA FULANI WRITTERS*
*Sadnaf* jinjina gareki

*REAL HAUSA FULANI WRITTERS*

*Rahiinat mahmoudou* Ahalin yanzu kintashi daga matsayin k’awa kin dawo er uwa gareni. اختي”

 

*KAINUWA WRITTERS ASSOCIATION*
*Anty fauzah er amana* nayi farin ciki sosai da nuna kulawarki gareni.” ina alfahari da hakan.”

 

*DA BAZARMU WRITTERS ASSOCIATION*
*MUNIIRAT* kawar arzikin ba munyi missing naki kiyi ki dawo fa.”لقد ءاشتقيتا عليك كثران

 

*BIBIYATA AKEYI FANS*
gaisuwarku ta dabance, ahalin yanzu kunzama jinin jikina ban had’aku da kowa.” انا احبكم كثرن

*HAJJACE NOVELS GROUP*

*ZAYNAB BAWA NOVELS*

*ASMY B ALIYU NOVELS*

*PHERTY NOVELS*

*HAUWA SARKI NOVELS*

*MAMAN USMAN NOVELS*

*DA DUK WASU GROUP DIN DA NAKE CIKI INA ALFAHARI DAKU*

 

الحمدلله

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply