Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 13


Bibiyata Akeyi 13
Viral

Page 13

*

Haka kawai ta tsinci kanta da masa addu’ar kariya daga sharrin su

Haka amira tayita kwantar Mata da hankali Dan tasan Abu kadan ke dagawa kawar tata hankali gata dasa damuwa,,,,,,,, bata barta ba sanda taga tadan sake!!!!!! ,,,,,,,
Ni wallahi amira abinda yadaga mun hankali Sai kace abinda yake faruwa a film bantaba dauka yana faruwa a zahiri ba,,,,,,,,
Yanzu deh mubar wannan maganan barin duba mana abinda zamuci Fita tayi zuwa kitchen Dan dafa musu indomie Dan shi yafi komai sauki,,,,,,,,

================

Ina labarin najeeb ne??????

Yana katse wayan ya nufi falo a guje Dan fadawa mahaifinsu yaje nema masa aure,,,,,,,,,
Turus yayi tundaga bakin kofan falon zumudi yasa gabaki daya ya manta da babansu yayi tafiya,,,,,,

Murmushi yayi tareda sosa keyarsa yajuya Amma ya kudirta duk randa akace dad yadawo maganar da zaifara masa kenan,,,,

Haka yashare sukayi tacin soyayya awaya shida sweety dinsa duk da rashin ganinta yana damunsa Amma,,,,, yakudurta gobe saiya sata a idanunsa,,,,,,,,,

Babban abinda ke damunsa dukda a’ido tana nuna masa tana sansa Amma abaki bata taba furta masa ba
Ya alakanta Hakan da kunyan da take dashi

Duk bata kasance bafula tana ba,,,,,
amma tanada matukar kunya,,,,,,,,,,,,,, ita cikakkiyar bahaushiya ce Wanda kana kallonta zakaga cikar zatinta na hausawa,,,,,,,
Da asalin kyawu irinna hausawa ya bayyana ajikinta

================

Wayan da take gefen sane ta dauki ruri!!!!,,,,, Koda ba’a fada ba yasan wayan da ke kiransa,,,
Wani irin faduwar gaba ne yake damunsa kuma yarasa dalili,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,
Hakanne yasa kallon yanayinsa captain Ahmad yafita daga office din zaiba shi privacy,,,,,
Dan MG Idan yana cikin wani yanayi baya bukatar kowa kusa sanin halinsa ne yasa Idan suna tare dashi suka ganshi a wannan yanayi suke bashi waje shi kadai??????

Captain Ahmad yazo Fita ya umurceshi da ya ajiye masa phone dinsa guda biyu,,
Da Wanda mahaifinsa ke samunsa da kuma Wanda yake talakawa masu complain suke samun sa,,,,,,,,
Sai akayi rashin sa’a dake phones din iri daya ne ya’ajiye Wanda manyan mutane suke nemansa,,,,
Ringing din da wayarsa keyi ne ya tabbatar masa da ba phone din dayace a ajiye aka ajiye bah,,,,,

Tsaki yaja sanda wayan tayi rurin ta tagaji bai dauka ba,,,,,,,,,
Sai da aka sake kirane sannan cikin nutsuwa yadauki phone din tare da picking din call din
Dan kiran daga mr presdent na Nigeria ne,,,,,,
Gaisawa sukayi cikin mutun tawa sannan yake fada masa sunada meeting da zasuyi a Dubai a burj al_arab kuma suna gayyatarsa tareda bukatan matakan tsoro

Haka kawae ya tsinci kansa da rashin son zuwa wajen Amma zaije kodan kare lafiyar al’umma

================

Sai karfe uku sannan amira takira driver yakaisu taraka *_hanna_* gida
Suka fito sannan sukayiwa Ammin su amira sallama har kofar gida suka kaita,, sannan suka juya

Bayan shigar ta gida tayita kokari ta danne damuwarta, dan ko mama bata fahimta ba
Tun karfe tara najeeb yakira ta Dan hatta mance da abunda yafaru da rana hira sukasha sosai daga nan Sai kusan 10:30 sukayi sallama Dan anty hajja ta hanata wayan dare sosae.

Wayanta tasauka tahau bincike a iya bincikenta bata samu wata masaniya akan wannan mutumin da akeson kashewa ba,,, Haka bacci yadauketa da taradda din wayannan mutane

Baccine mai cike da mafarkai kala kala,,,,
Akarshe ne tayi mafarkin wannan mutumi wanda awancen lokacin tayi mafarki ya harbi najeeb,,,,
Ya gurfana agabanta yana kuka amma takasa jin abinda yake fada
Ahaka tafarka cikin tsoro Amma hankalinta baikai na wancen karan tashi ba waigawa gefe tayi taga anty hajja nata sharar bacci itada yaranta Mata biyu Aisha (mammii) mai sunan mama Sai halima Wanda taci sunan yayar babanta
Sauka tayi tanufi toilet tadauro al’wala salla taringa yi tana neman zabin Allah saikusan uku bacci yadauketa akan sallayan

Kiran sallan farko ne yatasheta tatashi takara dauro al’wala taga batar da sallah
Sannan tatashi anty Dan itama ta gabatar da nata sallan,,,,,,, koma wa tayi ta kwanta nan da nan wani bacci mai dadin gaske yayi awon gaba da ita

Kamar a afarki taringa jin muryarsa a cikin bacci komadda idanuwanta takarayi tarufe can kaman Wanda tatuno wani tayi saurin mikewa tayi cikin falo aguje tana ihu,,,,,

To be continued

_Ur’s_
_Z33yyb3rw3r_

BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply