Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 17


Bibiyata Akeyi 17
Viral

Page *17*

*
Fita yayi cikin sauri dan amsa wayar da mahaifin sa ke kira.
Ga baki d’ayan sojojin suka bi bayan sa cikin sauri. d’aga musu hannu yayi alamun su koma. Bbu musu suka jah suka tsaya a inda suke.
Captain Ahmed ne ya bi bayan sa
Dan ya san hatsari ne barin shi yafi ta shi daya.

Amsa wayar ya yi sannan suka gai sa. tambayar sa ya keyi da cewa.
Yareemah…!!! Kana lafiya?” cikin murya mai cike da da muwa yace “lapya na klau abba, wani abin ne ya faru?”
A’a bbu babu komai ka kula da kan ka kaji ko?
Kuma na kira mahaifiyar ka tace mun bata san lokacin fitar kaba.
Ya kama ta Karin ga sanar da ita, ai addu’ar mahaifiyar ma yana da Amfani kaji ni?”

Yareemah yace “In sha Allah.”

“To Allah ya kare ka daga sharrin ko wani irin halitta.”
Ameen yace sannan ya kashe kiran.

Juya wa yayi zai tafi Sai ya ga daniel tsaye yana murmushi tare da sosa kyeya kaman Wanda yake neman wani alfarma.
Kallon sa yayi sannan ya kawar da Kai yana kokarin mai da wayar sa cikin aljihu.

“Sir MG please ina son magana da kai.”
Kallon sa yayi tare da cewa “Ehem! ina jin ka.”

Yace “Sir Idan ba zaka damu ba mudan matsa tacan? ya nuna wani waje da bbu mutane ta cikin hotel d’in.

Kallon sa yayi batare da wani tunani a ransa ba ya nufi wajan.
Sanda suka isah MG ya d’an jin gina ya lumshe idanuwan sa ba tare da ya kalle shi ba yace “Kai nake sauraro.”

Duk wani abin da yake faruwa akan idon captain Ahmed ne.
Amma da yake Shima ba abin da ya kawo a ransa yasa ya tsaya nesa dasu sosai.
Ganin daniel na shirin ciro Abu daga cikin aljihun sa ne kuma ya nada tabbacin bindiga ne ya sashi fara shan jinin jikin sa.
Ga shi Kuma idon MG a rufe yake. Da sauri ya fara kara sawa wajan da suke a tsaye.

Amma dake da rata a tsaka nin su kafin yayi rabi harya karasa fitowa da bindigan. magana ya farayi cikin garaji Wanda hakan ne yayi sanadin bud’e idon MG amma kafin ya bud’e ido Sai sau kan harbi kawai yaji a gefen cikin sa.

Karar har binne ya jawo hankalin jami’an tsaron da ke wajan.
Bud’e idanuwan sa tarr yayi ya zuba su akan na daniel. Wanda ke wani irin dariyar mugun ta. A lokacin Idan kaga MG baza ayi tsammanin a kwai harbi a jikin sa ba. Sai dai Idan ka lura da yadda jinin kebin jikn sa.
Wani irin huci yake fita da shi Wanda duk d’auri yar mutum a wannan lokaci Idan ya gan shi sai ya razana. Dan idanuwan sa sun sauya kala sunyi jawur.

Wani irin shaqa ya kai wa daniel. Kan wani Dan lokaci idanun daniel ya fara zazza rowa. ganin yana shirin hallaka shine ya sa ya kara d’aga bindigan ya sake masa a gefen kirjin sa.
Ganin Haka yasa captain Ahmed cira bindigan sa Kan ya ‘iso ya sakewa daniel ita a goshi.

A lokacin jami’an tsaro suka isoh wajan a kayi saurin rirreke MG da jikin sa gaba ki d’aya ya 6aci da jini. captain Ahmed ne ya kara so ya tallafe shi.

Ga baki d’aya gun ya cika da sojoji. kai kace wani taron sojoji akayi. ga baki d’aya hankulan su a tashe yake Ganin shugaban su cikin wannan ya nayin.

Motar tai makon gaggawa ne tazo in da yan jaridu sun cika wajan makil. kowa koka rin d’aukan abun da ke faruwa ya keyi.
Nan da nan a kayi dashi babban asibiti dake cikin dubai. inda moto cin sojojin dake gaban su da Wanda ke bayan su sun Kai akalla mota sha biyu.

Kai tsaye *_(mass general hospital bostoon International)_* aka nufa da shi.
Manya man yan likitoci ne suka shiga theatre dashi. kokari su keyi na ganin sun ciro harsashan dake cikin jikin sa.

Ummii ne zaune a falo ita da wata ‘yar aikin ta tana matsa Mata kafa. ji tayi ga baki d’aya ba ta cikin nutsuwar ta.
Hakan yasa ta umarci d’aya ‘yar aikin da take yan ka mata friut data kunna Mata TV.
Hankalin ta baya Kan tv d’in Amma labaran da taji a nayi ne yayi saurin jawo hankalinta wajan.

Idan ba kunnuwan ta karya suka Mata ba, taji a na cewa an harbi MG Abdullahi Abdul-Aziz lamido. Wanda a halin yanxu ba’a san yana raye koh yana maceh ba.
Hawaye ne ya fara bin fustan ta bbu abin da take nana tawa Sai inna lillahi wa’innah ilaihi raji’un.! Wanda hakan ne yaja hankalin yan aikin ta suma ju yawa su kayi Dan kallon abin da ya razana ta. ihu d’aya daga cikin su Wanda ya jawo hankalin sojojin dake bakin gate da cikin harabar gidan shigowa.

A razene suka yiyo cikin gidan, dan ganin abun da yake faruwa. Kan Wanda tasa hanu akayi tana kwalla ihu su kayi suna tambayar ta abunda ya faru dan basu lura da ummi data dade da zama mutum mutumi ba a kwance. Wanda bata gane komai a lokacin. TV ta nuna musu da ga baki daya hankalin su ya Kai kololuwa wajan tashi.
Ihu da sambatun sojojin ne ya dawo da Ummii han kalin ta tashi cikin tashin hankali ta musu umarni da su kaita a sibitin. Dan kuka yaki zuwa Mata gani ta keyi kaman karya ne.

Fita suka yi Dan rakata asibitin motoci uku ne suka cika da sojojin Sai Wanda Ummii take a cikin d’aya. Kai tsaye asibitin suka nufa dan ganin abun da yake waka na….

To be continued

_Ur’s_
_Z33yyb3rw3r_

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

*Dedicated* *to* *_ummi_* *_aysha_* (haske Writter )

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply