Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 18


Bibiyata Akeyi 18
Viral

Page 18

*
Wata irin faduwar gaba ne yake damunta ayau, kuma tarasa dalili.
Hakanne yasa ko waje batayi sha’awan fita ba.
kasan cewar ranar asabar ce, bbu lectures, zama tayi kawai tana tunanin dalilin wannan faduwar gaban tata
Can zancen mutanen na shekaran jiya yafado Mata.
Addu’a tasamu kanta da kara yimasa na Allah yakareshi.
Dakyar taya kice damuwaar aranta, domin kar hameeda ta fahimci wani Abu.

Cigaba sukayi da hidimominsu kamar bbu abinda yake damunta,
Amma Can cikin zuciyarta damuwa ce sosai.
Kusan karfe shadaya 11:00
Tashiga falon babansu dake yana gida bbu office.
Da Sallama Tashiga ya amsa Mata cikin farin ciki,
Nadauka yar tawa yau baza tazo taya abbanta hira bane, saboda akwai yar uwarta kusa da itah.

Murmushi tayi sannan takarasa shigowa ciki, tazauna akasa kusada kafar sa.
Dama wannan ka’ida ne duk ran asabar tana tareda mahaifinta tana tayashi hira “sannu da hutawa baba, yawwa sannu *hannatun* baba.
Murmushi tayi najin dadin sunan da baba ke kiranta dashi.
Tad’i suka fara yi “irin” na d’iya da mahaifinta, cikin farin ciki da annashuwa.

Aljazeerah! Yake kallo, Amma hankalinsu gabaki daya yanakan tad’insu, tunda ta shigo yamaida hankalinsa kanta, danjin ko akwai Wata damuwa atattare da ita.

Saurin daukan remote yayi “yana kara sauti, subhanallahi, Kai mutane babu Imani, wato duk wani mai gaskiya Sai sunga bayansa.

TV take kallo haikam.
wanda tagama tabbatar wa wannan da yanxu ake fadin an harbeshi, A Aljazeerah”
Shine Wanda ranar sukaji Ana zancen kasheshi,
Batasan lokacin da hawaye yafara bin fustan taba, tsan tsan tausayin sane ya cika Mata ruhi,
Lallai wa ‘yan nan mutane sun ciki azzalumai marassa imani.

Juyawa baba yayi gunta dan yimata magana,
Tsintar ta yayi hawaye daya nabin daya.
Juyawa yayi yaga yanda take kallo.
TV takurawa idoh, sanin zancen da’ akeyi a tv din yasa yayi tsammanin tausayi,
Yabata.

Dan yasan itah! Mutum ce” mai tausayi.
Lallashinta yashiga yi” sannan yace taje daki ta kwanta ,
Tashi tayi ta fita, yabita da kallon tausayi,

Shiga d’aki tayi, takwanta rub da ciki akan gado, Sai zullumin wayannan mutane takeyi aranta.

Hameedah ce” tashigo daka Mata duka tayi, ke Ina kika shiga inata nemanki, saida ta’iso kusa talura da halin da ‘yar uwar tata tashiga.
Zaunawa tayi kusa da ita!! Taci gaba da Lallashinta, dan ganinta awannan yanayin tasan ambata Mata rai ne.

================

Koda zuwan su Ummii basusha wahalan shigaba.
Dan akwai abinda sojoinsa suke d’ aurawa adam tsen hannunsu.
Ganin haka yasa bbu bata lokaci suka cika cikin asibitin.

Cikin dakin Theatre kuwa,,
Angano dayan harsashin rigar bullet proof dake jikinsa ta tare,
Inda dayan na gefen cikin sa ” harsashin bulawa yayi ya fice.
Amma dayake ba Kowani irin harsashi bane, anyi shine na musamman mai hade da guba yasa yaratsa jikinsa sosai.
Gubar mai karfi ce.
Koda kirjinsa da yake da riga Amma sanda wajan yayi shatin baki.

Sun dauki akalla awah hudu akansa.

Kafin sukayi iya kokarin na ganin sun kashe karfin Gubar.

Saida suka kammala komai. lokacin awansu hudu da rabi da shiga theatre.

Inda haryanzu maganin bai fara aiki ba, Sai yayi 1hour ajikinsa kafin yafara kashe Gubar.

Lokaci daya suka gama aka futo dashi, ko numfashi bayayi.

Aka kaishi zuwa wani d`aki mai tsaron gaske.

C I D camera ne takowani sako na dakin.

Nan aka ajiyeshi.

Dan zuwa nan da 2hours numfashinsa zai iya dawowa.

Yanxu roban numfashi ne amaqale a hancinsa.
Wajen dakin kuwa sojojine masu tsaransa birjik, tundaga gate din asibitin.
Ummii kuma na kofar dakin da yake, addu’a kawai takeyi, kokadan tunaninta bai kawo ta “khira mahaifin sa ba.

================

Mai mar taba ne zaune a faadaa.
Wayar sa da ke hannun wani bafade ne, tadauki ruri.
Kallon sa sarki yayi alamun ya amsa, amsa kiran yayi tareda karawa mai martaba akunne.

Sallama akayi ya amsa.
Meh????? Yaushe???? A’inah?? Shine abinda sarki yace, inna lillahi wa’inna ilaihi ra’ji’un kawai yake nana tawa, wanda hakan yaja hankalin fadan.
Rike kansa yayi dayake wani irin sara masa.
Lokaci daya kuma yafara ganin duhu.

To be continued

_Ur’s_
_z33yyb3rw3r_

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

 

_Wannan_ _shafin_ _nakine_ *nafii* _nagode_ _da_ _yadda_ _kike_ _nunawa_ _liittafina_ _soyayya_
_Kodan_ _ke_ _Sai_ _na_ _kara_ _yawan_ _pages_ 😜

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply