Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 2


Bibiyata Akeyi 2
Viral

Page 2
*
Gani tayi kamarda inuwar mutum akanta agigice tafarka lokaci daya kuma tasauke ajiyar zuciya ganin mama dake tsaye akanta,

Sunkuyar da kanta tayi sannan tace sannu dashigowa Mama batareda ta amsa taba tasamu waje tazauna sannan tace *hanna* ta dago takalleta cikin sanyin murya tace na’am mama,

Meyake damunki kifadamin dan banasan kallonki cikin damuwa murmushin yake ta kirkiro sannan tace bbu komaifa mama mekika Gani shiru mama tayi tazuba mata ido tana nazarin yanayinta ta kunsan uwa da danta koyaya dah yakai da boye damuwarsa takan gane yana cikin damuwa

*hanna* sunanta da mama takira ne yasata dago kanta daga sunkuyen da take sannan tace na’am mama tadaura da cewa nimahaifiyar kice kina tunani idan baki fadamun damuwarkiba akwae wanda yacancanta kifadawa bayanni

Murmushin yake takara kwakulowa sannan tace Allah mama bbu komai kainane yakemin ciwo kuma gashi samester yazo tsakiya karatu yafara zafi

To Allah yasauwake kisha magani saikihuta mama tafadi hakane bawae danta yarda cewa yartata bata da wata damuwa ba, kuma bawae dan tanada tabbacin datasha maganinba

Mama nafita tasauke ajiyan zuciya tareda jawo alqur’ani taci gaba da karantawa nantake taji kashi tamanin daga cikin dari na damuwarta ya gushe damuwarta ta batafi saura kalilanba

Rufe qur’anin tayi sannan tanade pray mate din cikin natsuwa tanufi kofar Fita daga dakin

================

katafaran masarautace mai girman gaske
Wanda ko bantsaya muku bayaniba kunsan yanayin girman masarautar kano dan tana daya daga cikin masarautu masu girman gaske
A wannan kasa tamu masarautace mai yawon jama’a

Da dumbin alkhaire atattare acikinta wanda kuma tasamu adali jajirtaccen sarki dattijon arziki mai farar aniya

*Sarki*Abdulaziz lamido

Wata mata nahango zaune akatafaren falon sarki wanda yasha kayan alatu dana more rayuwa matar dake zaune afalon kana kallonta koba’afada ba kasan itace matar sarki domin ko daga yanayin kayan dayake jikintama zainuna hakan balle azo zuwa yanayin fatar jikinta

Dukda dai bawata walwala atare da ita amma hakan baihana kyawun fatarta futowa kallo daya daka mata kagane damuwar dake tattare afuskarta

Ahankali tasa gefen gyalenta tamatso kwalla sannan tace mai martaba badai kanaso kagwadamin bani na haifeshiba shiyasa kaki amincewa da kudurina amma kasan yanda nake sansa araina koh yayan dana haifa bana sonsu haka

Kasan yadda nake jinsa araina kuwa tafada cikin muryar kuka inajin ciwo acewae shekara 35 amma haryanxu yagagara yin aure kuma munzuba masa idoh muna kallonsa

Nifa wannan yarinyar daya damu da ita atunanina aljanace ba mutum ba, mai martaba yakura mata ido kawae domin bayaso yatsaida ita saita dasa aya

Sannan taci gabada cewa tayaya xa’ace shekara tara kenan kullum zancensa mutum daya bamusanta bamutaba kallontaba

Mai martaba baza’aduba wannan zance ba idan da’abi shawarata atara malamai kawae suyita masa rokon Allah har adace wannan aljana tarabu dashi

Gyaran murya mai martaba yayi sannan yace bawae naki tatakiba amma yakamata mujira harsai shekatunda ya eba mana suncika kafin muyanke masa hukunci

Ainida ba se anjira ba dan wannan ba mutum bace ga yar uwarsa intisar aisai ahadasu

Kilishi Kilishi Kilishi mai martaba yakira sunanta tareda hadaerai sannan yace

Nafada miki alkawari na dauka zanbarshi yacika wannan lokacinda ya eba donhaka banasan sake jin tashin maganar nan

Toh tace amma bawae dan ranta yasoba sannan tatashi tawuce zuwa shashinta

Tana Fita fadawa sukafara kwasan gaisuwa amma ko kollonsu batayiba tawuce dayake Kilishi Allah yayita mace mai girman kai dakuma nuna isah

================

Zaman cikin gidanne yasoma gagararta domin sai habaice habaice kawae akeyi

Koda Mama taji abinda Su Amma sukeyi hakan baisa tatanka musu ba dan inda sabo tasaba kuma Allah yayita mace mai hakuri wanda gane fushinta abune mai wuya

Juyarda kanta tayi wajan inna kaltu sukacigaba da aikinsu domin yau itace mai girki domin bata taba bari mai aiki tayi ma mijinta abinci itata keyin kayanta

*Hanna* tashi tayi tayi da niyar shiga daki Hafsat da rabi’ah wanda suke yayu a wajanta ne suka tafa tareda shekewa da dariya Hafsat tace dama wasukam Ai saidai Zaman daki domin ba mashin shini suka kara tafawa yoh saima kunbata bakinkune kewar amma aixaman daki yanxu akaafarashi

Zuruf *hanna* tashige daki domin itama kanta abunyana damunta wani irin bakin jinine dani tafada tareda fashewa da matsanancin kuka

Amma yau tasamowa kanta amsar tambaya tada dade tana addabarta aranta, aljanine dagaske ya aureta tunda da kunnan ta taji bawani bane yajimata

Toh sukuma wayannnan masu *bibiyarata* suwaye shin ko suma aljanune??? ta tambayi kanta

Wannan tambayarne haryanxu takasa samun amsar ta kuma batasan wazata nema ya amsa mataba

Saidai takudirta aranta bawanda zaiji wannan zancen
Ai idan aljani yafi karfinta Toh itama akwae wanda zata kai karansu wajan sa

Tadauki alkawarin yin tsayiwar dare tahana idanta barci harsai Allah yamata sakayya da wayannan azzalumai masu BIBIYAR rayuwar ta.

Shin wae waye itah wannan hanna?????

Shikuma wannan wanda iyayansa suke tunanin aljana ta aureshi wayeshi????

To be continue

Ur’s
Z33iiyyb3rw3r
BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writing by
Zaynab Bawa (z33iiyyb3rw3r)

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply