Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 20


Bibiyata Akeyi 20
Viral

Page 20

*

Isowar mai martaba ne yaje yasamu likitocin, danjin kwakkwaran bayani, aikuma sun samu labari mai dad`i dan an tabbatar musu da cewa Har ya farka, inda mai martaba ya nuna rashin gamsuwa da maganarsu, TV suka jona, nadakin dayake, aka nuno musu tundaga kaishi dakin harzuwa farkawarsa.

Ba’afi awah d`aya da kwantar dashi, yafarka, harzuwa shigan likitannan, Ya fita yadawo da wasu likitocin suka zo dakyar suka samu, suka masa allurar bacci.
Kasancewar maganin bai ratsa jikinsa ba. Kuma alluran da “aka masa jininsa nada karfi yasa basu dad`e suna” aiki ajikinsa ba ya farka.

Gashi kuma, gubar haryanzu bata gama sake jikinsa ba, Kodaa lokacin daya farka bawai yagama sanin “a’inah yake ba.

Wannan labarin ne yasa hankalin danginsa ya kwanta.
Gida suka wuce, Dan mai martaba ya fahimci Ummii tun jiya bbu komai acikin ta.

Dakyar ya lalabata suka bar aaibitin suka nufi gida, affan kadai suka bari acan, duk da intyy taso zama Amma, kilishi dake ranta abace yake tayi kirmushi shi tahanata.

Suna isah gida mai martaba yaja hannun Ummii, Har kofar bandaki yaraka ta yace tashiga tayi wanka, ba gardama ta shiga, dan itama jikinta baya Mata dad`i ahaka.

Bata d`auki tsawon lokaci ba ta futo.

Nan ta samu Har ya had`a Mata tea mai katuro, zama tayi agefen gado, Mika Mata kafin tea d`in yayi nan ma bbu musu ta karba, tafasha sanda takai rabi kafin yadaga Kai, karasa mana yafada Mata, dagowa tayi ta kalleshi, tayi narai narai da idoh, hawaye yacika idon tapp, girgiza Mata Kai yayi, “ya kar6i kofin ya kara Mata abakinta, ba musu takarasa shanye sauran.

Ajiye kofin yayi, sannan yajuyo da ita suna fuskantar juna, magana yafara Mata cikin harshen da tafi ji” Amina kisan cewa wannan abun da yafaru da yaron nan bawai, rashin tsaro kokuma kulawa bane, yasa faruwar hakan.
“A’a Sai dan Haka Allah ya kaddara, karki manta kowani dan adam da tasa kaddarar.
Nisawa yayi sannan yaci gaba da cewa, ai mu abin alfaharinmu ne ace” yaranmu duk duniya Ana alfahari da shi.
Ba’irin taimakon da bayayi kingani kuwa ai addu’ar mutane ma kariya ce agareshi.
A yau akace dannan ya mutu, mu iyayansa zamu zama abin alfahari ga duniya, mun haifi da kuma munbashi ingattaciyar tarbiya, Wanda hakan yasa yatashi da tausayi da kuma taimakon al’ummah aransa.

Haka ya zauna adakin yayita kwantar Mata da hankali.

Ganin sun shiga daki, sun dad`e ne yasa ran kilishi mummunan 6aci, dakyar ta “iya yin break fast tawuce daki, bata bi takan kowa ba.
Koda sukazo komawa asibiti, cewa tayi kanta yana ciwo, sannu suka Mata cikin tausaya wa, sukace _afeeyah_ tazauna kodata bukaci wani Abu, cemusu tayi suje kawai bbu matsala da saketa,
Sai hararan intisar takeyi takasan idoh, akan tazauna, kirmushishi tayi kaman bata ganta ba, dan jitakeyi kamar baza su “isa asibitin taganshi ba,

Haka suka futo, suka dugunzuma Zuwa asibitin.

Satinsu daya acan, MG yasamu lapya, Ya warware, Sai yar rama dayayi, yayi fari dama gashi bbu bambanci da larabawa, Sai yakara yin wani kyau sosai, Wanda yasa intisar kara yin kololuwa acikin soyayyarsa,

Duk wani Abu datasan zatayi yafaranta masa rai takanyishi, Amma ko kallan arziki bata samu daga gareshi.
Inda captain Ahmed ranshi baci yakeyi, irin yanda intisar ke shigewa ogan nasa, yasan akwai Wanda yakeso bayasan wannan kyautatawar da takeyi masa, bayason iyayen oganna shi su canja ra’ayi na jiran lokacin da suka eba masa,

Kuma hakanne tafaru, dan ransu mai martaba da Ummii yana faran tuwa da irin kaunar da take nuna ma dannasu, shikuwa captain Ahmed ya yatqbbata tanayi ne dan riya.

Gashi batada kunya kokadan bata dace da ogan saba, Dan ranan saida yaso marinta.

Kusan watansu daya “a” asibiti kuma acikin satin sukesa ran komawa Nigeria, dan umarnin mai martaba ne hakan, inda su sun dade da komawa.

Affan da intisar ne kawai suka saura da intisar taki yadda tabisu.

MG ne zaune adakinsa, shida captain Ahmed.

Daga idoh yayi ya kalli captain Ahmed, motsa lips dinshi yafarayi wanda sukaci pink harsunfara kaman red, lokacin dana eba yakusan cika kuma bana tunanin za’akara min wani lokacin, captain ahmad tattaro hankalinsa yayi gabaki daya dan yasan yana wuya furta kalmomi musu yawa abakin oganna shi, Har inde kuwa yafara magana mai tsayi to maganar nada mahimmanci.

” Iska ya furzar, tareda shafa sumar kansa ya lumshe idoh, ya cikaba da cewa, ka tabbatar ka kira captain bala ya tabbatar ba’asamu matsala ba.

================

*Hanna* ce suka fito a lectures, kowa ya gaji likis.
Amira ce ta fara magana ” inbanda jaraba irin na wannan malami ace monday za’afara exam Amma haryanzu yaki gama lectures, hmm ni wallahi nagaji nema, Ina gama exam kano zanbi yar uwata Sai Dan fara IT zandawo, bade tafiya zakiyi ki barni ba????? Amira ta amshe zancen, ahap Sai kuma kiyi, hameeda Wanda duk haushin su yacikata, itaba da karatu ba Sai shan wahaala, taama kasa tanka musu,

Harsunzo tsallaka titin wajen school din Wata mota tatsaya agabansu.

To be continued

Ur’s
_z33yyb3rw3r_
*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

Wannan shafin nakune yan uwana, nakaina Allah yabarmunku, *Anty* *rashida* *Anty* *ummi* da kuma *Anty* *sadiya*
Zaynab bawa na matukar kaunar ku

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply