Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 22


Bibiyata Akeyi 22
Viral

Page 22

*
Mama ta fuskanci kalu bale da yawa” awajan Ammah, kuma Har gobe tana kara fuskantar wani kalu balen.

Farko tafara Mata da makirci da yawa” inda saita ebeh abinci da siyar, sannan kuma tace mama ne ta ebe, lokacin da suke su kadai, hakan bata faruwa Sai bayan ya auri mama, hakanne yasa yafara yarda cewa mama tana eba masa abinci gakuma satar kudi da ake yawan yimasa.

Sosai suka fara samun matsala” inda ita mama batasan meye laifin ta ba amma baba ya canja kwarai da gaske, Dan ko maganar ta ba sosai yake amsawa ba.
Alokacin tanada cikin anty hajja, dake mama macece mai “sirri” yasa bawanda ta taba fadawa, duk yataru wani abinda take gani bata magana, kuma iya kyauta tawa tana kokari wajan yiwa baba biyayya” dan tabbas mama tafi umma hakuri.

Ana Haka Har Allah yasa *Wata* *rana* yadawo lokacin dawowarsa baiyiba, yadawo Dan yayi mantuwa ne, daga bakin kofa yahadu da Ahmad da kayan abinci niki niki, yana futa dasu,
Ga mai abin hawa yana jiransa Ana loda masa kaya, zai dashi yayi ya tambayeshi Ina zaikai kayan??? Cewa yayi zai Kai gidansu goggo ne (gidansu kakaninsa), baba yayi matukar mamaki cikin hikima ya tambayeshi ko yaune farko, aikuwa kunsan yaro” kuma bawai yasan meyake faruwa bane. Atake ya shaida masa ai yadade yana kaiwa.
Betsare yaron ba, Amma cikin zafin zuciya ya nufi dakin Ammah, abinda yaji ne ya matukar birkita zuciyarsa. Wato Ammah yaji suna tadi tadi da kawarta irin makircin da suke shukawa, Anan yaji shirin satar da take shirin yi masa na makudan kudi, kuma su daurawa mama Alokacin tace ta tabbata dole Sai ya saketa.

Wani irin tausayin mama ne yakamshi, da tuno irin abubuwan da yayi ta Mata, Har zai juya yaga Idan be tabbatar wa da Ammah yajita ba” toh wannan sace sacen da takeyi bazata daina ba, bude dakin yayi ya shiga da Sallama, amsawa sukayi, cikin kid’ima Dan basuyi tsammanin ganinsa yanzu ba.
Neman waje yayi ya zauna, tareda fuskantar su.
Kiji tsoron Allah halima duk wannan abunda kikeyi dan kikori Aisha Wanda ita ta daukeki amtsayin yar uwa.
Wannan abinda kikeyi bashi zaisani rabuwa da “itaba” mai yasa bazaki riki kaddara ki dauketa amtsayin yar uwarki ba’ shiru tayi yayi ta mata magana mai sanyaya jiki hadeda wa’azi.
Alokacin jikin Ammah yayi sanyi, amma cikin zuciyarata, haryanzu son ta kori mama yana nan.

Sai bayan yafita kawarta ta kara zugata, Kan yacimata mutumci akan kishiya, Ana tadaura Mata aniyar zuwa gun boka, dan takori mama.

Mama taga sauyi sosai awajan baba, Dan wancen lokacin ma tabari akan sauyin yanayi, yasashi canja Mata.

Sosai baba yake nuna Mata kulawa, dan mama cikin ta bai hana Mata kula dashi ba yanda mama takasan ce, mace mai tsafta.

Wannan kulawa ba karamin cin ran Ammah yakeyi ba, ko lokacin suna su kadai bata samu wannan kulawa bah.

Bayan Wata biyu, ta haifi yarta mace, akasa Mata sunan umma, wato khadija Ana kiranta da (hajja), sosai baba ke nuna Mata soyayya, ma yarinyar dayake duk yaran Ammah maza neh, guda uku.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya, lokacin inda yaran Ammah shida” uku maza uku Mata, yaya Ahmad shine babba yana aiki a lagos yanzu da matansa biyu da yara hudu. Sai yaya jabir da yaya unais da anty Maryam duk rana daya akayi auransu, Sai rabi ‘ ah da hafsat.

Yaran mama uku tanada cikin na hudu, Anty hajja itace babba tanada yara uku, Muhammad shine babba Sai Aisha (mamii) karamin shine aslam, Sai maman amal itama yaranta biyu, Anty hundatu ne Wanda bata dade dayin aure ba, ta auri babban dan umma.

Alokacin da aka haifi *hanna* ne kuma Ammah tadauki tsana ta daura Mata.
Alokacin ne tamata asiri, aka tura Mata aljanu Wanda bbu tabbacin akwai su ajikinta.
Sai saleem da abba.
Nisa wa yayi sannan yace kutashi kuje ku kwanta, dare yayi, tashi sukayi duk jikinsu yayi sanyi, danjin hali irinna Ammah.

Dakin mama suka nufa, da Sallama suka shiga ganin momy sukayi zaune akan kujera, harara ta watsa musu daga Ina kuke??? Mama daga dakin yaya jalal muke, sauke ajiyan zuciya tasauke, shine zaku Kai dare Haka??? , kallon agogo sukayi, shadaya nadare 11:00, mama wallahy bamusan dare yayi Haka ba, kuwuce ku kwanta,

Bamusu sum-sum suka wuce daki.

Bayan sun shiga ne” *hanna* tadauki wayarta ganin misscalls din najeeb tayi kusan 10, ganin dare yayi ne kawai yahana ta kiransa dan rabonta da muryarsa tun safe,
Kwanciya tayi cikeda kewarsa aranta.

Jarabawa suka fara sosai, kanta yayi zafi, kokadan bata da lokaci duk tarame.

Gashi ansa ranar auran Anty samha yarinyar umma.

A ranar yaune MG yake shirin dirowa kasar sa ta haihuwa.
Jirgi guda kasar Dubai ta bashi Dan tafiya da duk sojojinsa. Sai dai sukansu sunsan dasuyi rashin masu tsaro sosai, tareda Ummii da intisar da affan.

================

*Masarautar* *kano*

Shirye Shirye akeyi sosai na tarban *yareema* abdallah, kota Ina gyara masarautar akeyi, hatta garin kano sanda tasan da sunada bako inda, Har shugaban kasane yazo” dan taryansa,

Karfe uku 30:00 dai-dai jirginsu ya dira a Nigeria, garin kano.

Dumbin taron jama’a ne suka zo taryansa, inda daga masarautarsu ma gayya gudane. Sannan ga governor da sauran Manya, hadda shugaban sojoji wato chief wanda afuska Sai farin ciki yakeyi sosai, azuciyar sa kuma da dadama daya kasheshi a wajan.

Gabaki daya suka dugun zuma sukayi, masarauta.

To be continued

_Ur’s_
_z33yyb3rw3r_

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply