Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 24


Bibiyata Akeyi 24
Viral

Page 24

*

Juyowa yayi ya kalleshi sannan” da murmushin dake boye da damuwa acikinsa”.

Girgiza kai yayi yajuya daniyar futa” mai martaba ne yatsareshi” yareemah ” fadamun sunan surikata kaji”.

*”Hanna”* wow”😍 halima tace” hadeda hada yatsunta biyu waje daya sannan taware guda ukun amma sunan yayi “.

Murumushi yayi kawai sanna yajuya ya fuce.

Sojojinsa ne” suka rufa masa wasu na gaba” wasu na baya” suka sashi atsakiya, harzuwa wani tangamemen sashi wanda idan kagani, za’a iyacewa na mata hudu ne”, amma gefen MG ne wanda yake rayuwa shi kadai”.

Gefe daya gida ne mai hawa biyu” sainabiyun wanda suke jere amma shi plat ne mai matukar kyau duk yanda zan kwatanta muku kyawun wannan gida bamai yiyuwa bane, iya karshen kyau” gidan yayi kyau ” plat din ya nufa” wanda kofarsa duk ta glass ne’ irin glass din da ko bullet baya 6ulashi”.

Wasu lambobi aka danna ajikin kofar, da’alamu kofar mai sucurity ce “, kofar ne tabude inda wasu daga cikin sojojin suka fara shiga, sannan shima yashiga”, wani falo ne dan madaidaici mai kyawun gaske” komai na falon farine sol har daukan ido yakeyi”,

Daga dukkan alamu dai yafisan kalan farii”.

Har mamaki irin kyawun falon yakeban, amma nace bafa abin mamaki bane dan idanna yi la’akari da falon MG ne, kuma sanin kankune kunsan waye MG”.

Daki kai tsaye yawuce dan yin wanka “.

Can cikin falon mai martaba kuwa, farin ciki ne da kuma tausayin *yareemah* da yabarasu dashi, sa6anin kilishi da intisar Wanda bakin cikine fall a zuciyarsu, intisar jitakeyi kamar zuciyarta zai futa dan bakin ciki ga wata irin kishi daya lullubeta, har cikin ranta ba karamin so takeyiwa *Yareema* ba” ita kuwa kilishi zafin dukiya da mulki yakusan kubucewa ahannun su ” amma duk yanda za’ayi bazata bari ya auri wannan yarinyar ba” duk rintsi sai ta rabashi da itahh”.

================

*Hanna* sun gama exam lafiya”, inda se shirye shiryen zuwa kano, inda zuwansu yahadu da bikin anty samha da za’ayi sati biyu masu zuwa, inda soyayyarta da najeeb sai karuwa yakeyi kullum idan basa maqale a waya toh suna gidan anty suna zuba soyayya, abu daya dayake damunta shine yanda najeeb yayi shiru da zancen turowa gidansu kokadan yadaina mata maganan,

Yau sauran kwana biyu sutafi kano, yaya jalal ne zaizo yadaukesu, sai shirye shiryen tafiya sukeyi.

*Hanna* ce” tafito cikin sauri ” daga alamu wani waje takeson zuwa, ammah ce azaune acikin gida, lokacin hanna tafuto wayan tane tafara ringing, hankalinta baikai kan Ammah dake zaune acikin gidan ba, daukan wayan tayi tana cewa, myn gani fa ahanya inazuwa, gaban Ammah ne yafadi dan dagajin wayan da wani take” kuma da alamu saurayinta neh, me hakan yake nufii kenan???? Ta tambayi kanta”.

Fucewa tayi cikin sauri dan zuwa gidan anty dasu hadu da najeeb, yaso ace shizai kaisu Ammah yasan hakan ba mai yiwuwa bane, bbu yanda za’ayi iyaye subar yayansu yakaisu” yana matsayin saurayi ba muharramunsu ba”.

Bayan isarta gidan anty, tasamu najeeb ya dade dazuwa, sun dade suna hira, sweety” dagowa tayi ta kalleshi” kinji haryanzu bance komai gameda maganar turo manya ba ko???”

Sunkuyar da kanta kasa tayi”

Yaci gaba da cewa”!!!!!

Narasa mai yasa duk lokacin da zansamu abba da wannan maganar, sai wani abu yatsareni” kuma nakan dade bankara tunowa ba kuma akowani lokaci nayi tunanin zuwa hakanne take faruwa ” muringa yin addu’a dan jinakeyi kamar akwai wanda keson rabamu, narai narai yayi da ido” idan narasaki zan shiga wani hali, irin son da nake miki ni kaina bazan iya fadin sa ba”, wani irin tausayin kansu ne yakamata’.

Murmushi tayi, addu’a ne yakamta muyi dan babu abinda yafi karfin addu’a”.

Shima murmushin yayi zanyi kewarki” amma zanbiyoki kano, kinji sweety, umm lokaci yana tafiya, hameeda tana jirana zamu shiga kasuwa,” ok bari inkaiku” no kabari” kollon tuhuma yamata” wai meyasa haka” hah” nafarko idan na baki abu bakya karba” idannace ko makarantarku zanzo saikikii” dan bakyaso kishiga motata?? Eyehh??

Langa6ar da kanta tayi” hava myn tayaya zan karbi abu ahannunka” ace a’iinah nasamo?? Kaikanka kasani dole sai an tuhumeni”.

Sannan zancen zuwa makaranta kuma” kaikanka kasan zancen duniya baya buya idan akaje akasamu, babanmu akafada masa fah,” mai zai dauka yaturani karatu natafi soyayya??”

jikinsa ne yayi sanyi” yasan duk laipinsa ne, in sha Allah yakusan zuwa karshe kinji sweety,”

Murmushi kawai tayi amma aranta itama tana fatan faruwar hakan”.

Kallon agogon hannunsa yayi, yatashi yana fadin zantafi, abba zai aikeni” zanyi missing wannan kyakkyawar fuskar” rufe fuskanta tayi daa tafukan hannayentaa,” dariya yayi ya nufi kofar fita” bazakayiwa anty sallam ba??” eh kice mata na tafi” fita tayi da niyyar rakashi har bakin motarsa tarakashi” sannan yatafi”.

Dawowa tayi tayiwa anty sallama, sannan tafito da niyyar wucewa gida,

Turus tayi na ganin wayannan mutanen masu *bibiyarta* sunyi parking motarsu,” wata zuciya ce da tunkarota” yau ko kasheta za’suyi saita tunkaresu”.

Cikin karfin zuciya ta tunkaresu” gabanta sai faduwa yakeyi”.

Cikin wani irin mamaki mutanen suke kallonta ganin su take tunkarowa.”

To be continued

_Ur’s_
_Z33yyb3rw3r_

. *BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

_
*_Ina mika sakon ta’aziyata ga feedoh yar ficika marubuciyar (matata gimbyata)narashin mahaifiya Allah yajikanta”._*
*yakuma sa aljanna ce makomarta, idan namu yazo Allah yasa mucika da imanii” ameen*

*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply