Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 25


Bibiyata Akeyi 25
Viral

Page 25

*
Cikin mamaki suka tsaya kallonta,” na ganin su take nufowa “.

Har takai tsakiyan titin wani mummunan tsoro ya dira a zuciyarta”.

Juyawa tayi da sauri, da niyyar komawa”.

Tsayuwa sukayi suna kallonta,” su kansu sunsan tayi kokari,” shekara da shekaru, suna *bibiyarta* kuma sun dade da gane cewa ta fahimci ana binta amma ko sau daya bata ta6a tunkararsu ba,”

Sun sani tabbas yau sotakeyi tasan kosu suwaye??”

Wata zuciyar ce takara tunzurota” shinke haka zaki zauna ana *bibiyarki* bakisan kosu suwaye ba?? ”

Ko dalilin *bibiyarki* dasukeyi yakamata ki sani wata zuciyar ta kara tunzura ta.”

Kara juyawa tayi ta nufesu, alokacin zuciyarata sai dar-dar takeyi.”

Ganin yanda suma suka zuba mata idanuwa ne” yasata tsayawa cak,”

Alokacin wani mai mashin ya karyo kwata.”

Kasancewar anguwar bamai jama’a bane yasa abun hawa basu cika wucewa ta layin ba,”

Irin ‘yan isakan yara masuji da tashen girma ne, wanda suna kallon kowa suka kade bbu mai Iya daukan mataki, dan suna kallon iyayensu sunada kudi. ”

Ganinta atsaye a tsakiyar titin dake GRA kano road, yasa ya Kara karfin gudun _power bike_ din dan aganinsa rainin hankali ne ta tsaya atsakiyar titin,”

Kanta ya nufa gadan-gadan da wani mugun gudu kamar me shirin tashi sama, ”

Hankalinta kwata kwata baya jikinta, wanda Ita batamasan da zuwansa ba,”

Gani kawai tayi daya daga Cikin, wayannan mutanen yabude motar ya nufeta gadan-gadan Cikin sauri, ”

Wani Irin razana tayi,” ganinsa ya nufota gashi takasa motsawa konan da can, ”

Gani tayi yana matsowa kusa da Ita, ya daga kafanshi kaman mai shirin yin naushi,” sa hannu wanta biyu tayi ta kare kanta tana jiran saukan naushi kawai.”

Rufe idonta tayi Ruf!! Jin shiru yasa tabude idanuwanta, budesu yayi dai-dai da lokacin da yasa kafa ya naushi mai mashin din dayazo dapp da Ita da niyyar kadeta,

“iyah! Kacin razana ta razana, ganin mai mashin din da yake shirin kadeta, yayi gefe mashin din yayi gefe,”

Wani Irin buguwa yayi, ganin hakan yayi” sanadiyar da yasa ta kwala Wani raza nenen ihuu!!

Sosai tarazana ganin mutumin ko motsi bayayi alamun ya bugu, dayawa, ”

Juyawa tayi afusace wajan wannan mutumi,”

Cikin tsiwa tafara magana.”

Aibashi yakamata kakasahe ba ” nizaka kashe, dan bashi ne wanda kukayi tsawon shekaru kuna neman hallakawa ba”

Cikin kuka tace menayi muku ne kam da baza kubarni nayi rayuwata ba??”

Wai kusuwaye mah??”

Ganin yayi shiru yana kallon ta ne yasa tace”

Au nagane dan ku bakowa bane face azzalumai masu maida rayuwar mutum kamar ta dabba,

Meye ka tsaya kana kallo na , ka kasheni mana, tafada Cikin karaji,”

Cikin nuna girmamawa ga wanda akeyiwa magana da ladabi, kamar wanda yake wajan wanda yagirmeshi, yafara magana.”

Kiyi hakuri “mam” hakkinmu ne kare lafiyarki, iya tsawon lokutan da akadauka mana. ”

Duk Wani amsosin tambayoyin ki” k’ijiyesu kina gab da samun amsoshinsu, dan lokaci kalilan ne yarage” tabbas nasan kinada tarin tambayoyi amma ki ajiyesu saura kiris” mutumin dazai amsa miki yana tafe.”

Ina so kisa aganinsa muka masu cutar dake bane.”

Yana fadin haka yajuya” zuwaga dayan, har lokacin ta na tsaye ko motsawa batayi ba” sai magan ganunsa ne suke mata yawo a kwakwalwanta,”

Magana sukeyi amma batasan mai sukace ba taga ya tsaida adai-daita, ya nufota,

Alama yamata da ta shiga bbu musu tashiga.

Tana kallo yayi wajan wannan na kwancen itakuma mai adai-daita yaja suka tafi dayan ya biyo bayanta.”

Suna isa tacire five hundret, kojiran change batayi ba tashige gida da sauri-sauri gudu – gudu, ko sallama batayi ba ta bude kofan dake jikin gate din tawuce ciki.”

Direct d’akin mama tawuce, hameeda tasamu zaune tafad`aa jikin ta tafashe da kuka, Cikin kidima take tambayarta maiya faru??? ”

Bata iya bata amsaba sanda tayi kukanta mai isarta sai by buga bayan ta hameeda takeyi”

Dakyar tad’ado ta fada mata duk abinda yafaru, Cikin sigar lallashi tace Kiyi hakuri natabbata bamasu cutarwa bane, kamar yanda suka fada, ”

Amma kikara kiyayewa, dan banji dadin tunkararsu da kikayi ba, ke kanki kinsan mahakurci mawadaci ne, tun da sunce lokaci kalilan yarage, muci gaba da addu’a har tsawon lokacin,”

Sau da yawa nakanji ajikina tabbas ba masu cutarwa bane yasa hankalina ya kwanta Kiyi hakuri. ”

Haka tayita lallashinta har tayi shiru” kuma ki canja mood dinki kar mama ta fahimta. ”

Juyawa tayi da niyyar daukan jakarta dan nunawa hameeda tsarabar da anty tabayar abata,”

Karaf!!” idanuwanta yasauka akan mama wanda da alamu tadade awajan. ”

Kallon tuhuma take binsu dashi,”

Lokaci daya idanuwansu yayi zuru-zuru alamun rashin gaskiya ya bayyana tattare dasuu”

Shigowa tayi tazauna ta fuskancesu,”

Mekuke zance akai?? ” ta tambayesu, mutsu- mutsu sukafarayi alamun basasan fadin abinda aka tambayesu” shiru sukayi nadan lokaci sannan tace” ba daku nakeyiba ne??”

Mama daga najeeb ne “nan takwashe duka yanda sukayi dashi tafada musu,”

Shiru mama tayi sannan tace Allah yakyauta ” muci gaba da addu’a, tabbas wannan jarabawa ce ta ubangiji Allah yabamu ikon cinyeta”

Su duka suka amsa da ameen. ”

Sannan mama tatahi tafuta” bayan tafita ne tajuyo ta kalli kofar dakin,”

Bawai bata yarda da abinda tafad’a ba” amma tanada tabbacin ba zancen da sukeyi ba kenann,”

Hasalima tun shigowar ta tabiyota ganin tashigo ahargitse ko lura da Ita datake zaune afalo batayiba, haknne yasa tabiyota danjin maiyafaru? Zancen da dataji ne yadau hankalinta yasa taki shiga. ”

Tadaura niyyar bazata gwada mata tajiba amma zata tsananta addu’a, kan Allah yakare mata d’iyarta daga kowani irin sharri.”

Ganin mama tafita yasa ta sauke ajiyan zuciya, hameeda ne takalleta sannan tace” sis bakya Kallon yakamata mufadawa mama?”

Um Um ba yanzu ba dan kokadan banasan tashin hankalinta ”

Ok amma ki Kara kiyayewa, in sha Allah”

Tashi sukayi suka nufi falo.”

Hameeda ce tace” mama kin kira momynsu amiran?? Nakirata amma kushirya kuje kukara tambayar ta da kanku. ”

Cikin sauri suka shirya suka nufi gidansu amiran.”

Dakyar momy ta amince data barta tazo amma sai satin bikin.”

Haka suka nufi gida bayaan da sukaso ba, dan sunso abarsu sutafi da Ita tare, ”

================

MG ne zaune afalonsa wayane sakale a kunnensa, kana Kallon sa za’a hango bacin rai karara a fuskarsa, ji nayi yana cewa” Mekuke nufi da hakan kenan??”

Cikin karaji naji yakuma cewa!!”

Captain bala!!

Karka yarda Irin haka takara faruwa??”

Cikin rawar murya wanda ake waya dashi naji ya amsa da” yess sir,” tsaki yaja ya kashe wayar, hadeda cillata a daya kujerar,

Ya kishin gid’a a jikin kujerar hadeda lumshe ido, jiyayi an tabashi, a hankali ya bude idon yasaukesu akan Abubakar amininsa, tashi yayi ya zauna, sannan shima yasamu waje ya zauna.”

Abubakar ne yakara cewa” Wato dabazaka dawo aurena ba kenan ko mai kake nufi?? ”

Eh!!” yanzun ma dan antakuarni ne da sai lokacin yacika, ”

Dakuwa anga dan iskan aminin ango” Abubakar yace”

Kaikasan dan kai nayita jawa iyayen yarunyar nan rai. ”

To ai gani nadawo, haka sukayita shirye shiryen yanda zasu tsara bikin Abubakar dan gidan waziri wanda za’ayi satin sama,

===+============

Amma ce gaban malam nakaranki hankali tashe

_Kuyi hakuri da jina shiru kwana biyu sai jiya nadawo amma in sha Allah yanzu kullum zaku ringa ganina_

To be continued

_Ur’s_
_Z33yyb3rw3r_

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply