Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 26


Bibiyata Akeyi 26
Viral

Page 26

*

Washe gari da sassafe, Ammah tashirya da niyyar zuwa gidan malam,

Bayan ta shirya tafito, tawuce gidan kawarta hajiya larai, wanda duk wani tuggu da muggan abubuwa Ita take koya mata, ”

Bayanin duk wani abinda taji jiya tamata, sannan takara da cewa, hajiya konawa zankashe arabata dashi,” natabbata ba karamin mutum bane dan kinsan abinda malam yafada, har inde nayi sake asirin ya karye, toh mijin da zata aura samunsa nawuya, ”

Gaskiya bazan iya ganin zuwan wannan rana ba, wallahy yanda natsani uwarta haka natsaneta, intakaice miki hannafi tsanarta fiyeda uwarta,”

Wata yar shewa hajiya larai tasa, haba kekuwa hajiya banfa sanki da sarewa haka ba, duk kin wani bi kin rikice akan yarinya karama, ”

Ammah ne tace bazaki gane ba ne hajiya, har wani lokaci nadaban fa babansu yake ware mata wai najin damuwowinta, komu matansa bamu samu wannan lokacin ba,”

Wallahy tun lokacin da aka haifeta dana fahimci Irin son da yake mata nakejin tsanar yarinyar. ”

Kedai yanzu ki kwantar da hankalinki, halin malam saidai kifadawa wani dan shekara da shekaru yana miki aiki, baki taba Kallon ba dai-dai ba dan haka yanxu barina shirya saimu wuce,”

Aitsabar tashin hankali kanmuje har na kirashi, mukawai yake jira,”

Sai bayan tagama shirinta sannan tafito, a motar hajiya larai, suka shiga suka nufii kauyen,”

Banisa ne dashi sosai ba, idan aka d’an futa agari yake,

Bayan isarsu ne kaitsaya gidan malam suka nufa,”

Dama ya dade yana jiran zuwan su,”

Bayan sun shiga ne amma ta gama koro masa bayanai, ”

Shiru yayi nadan wani lokaci sannan yace, tabbas akwai wanda ke nemanata,” kicin kidima Ammah tace malam arabasu, dan yadda uwarta ta kuntata min na auren mijina itama saina kuntata mata na ganin yarta agaban ta ba aure har abada, ”

Shiru yayi sannan yace, hakan mai yiwuwa ne amma dole sai mun dakatar dasu da yawan addu’o in da sukayi, kullum Cikin addu’a suke bbu rana bbu dare,

Budar bakin hajiya larai sai cewa tayi alagafarta malama akaashesu kawai itada saurayin, nikuwa araina nace wannan katon bokan basajin kunyan kiransa da malam shikuma yayita yake baki yana amsawa.”

Ammah ne tayi saurin katseta, A’ah” baza’a kaahesu ba, idan nakasheta aiban cusawa uwarta bakin Ciki ba, tazauna arayende uwarta taci gaba da ganin bakin Ciki, shikuma idanna kasheshi ai ban cusa musu bakin cikiba, gwamma suganshi araye amma yaki, auranta. ”

Kinga daganan na bata mata suna nace ya lalata tane yaki auranta, hajiya larai ce tayi saurin karbewa yanzunma waya sani tunda kince binsa takeyi wajan sa, shi bai taba zuwa ba.”

Cikin gamsuwa da shawarar su malam yace” yanzu mufara raba tsakaninsu kafin muzo zuwa wannan stage din, ”

Wani dan magani yabata yace ta zuba masu a abinci, idan ta zuba kasala data sauka musu bbu mai iya tashi nafila acikinsu, acikn wannan daren yakeson yin aikin.”

Kar6a sukayi Cikin murna da ganin kaman burinsu yacika, suka zube masa kudi, suka koma gida,

Direct gida tasauke ta, sannan itama tawuce nata gidan, ”

Tana zuwa kuwa tasamu inna kaltu tad’auura miyar dare,”

Ko dar bata jiba ta aiki inna kaltu kasuwa, sannan tashiga tajuye, tarage kadan dan ta tabbata ba lallai su *hanna* da hameeda suci abincin darenba, dan saudayawa tana kallo da daddare abincinsu daban sukeyi,

Bata damu da duk wanda zaici abincin ba, tajuye aduka, itadai bazata bari ‘ya’yan ta suci ba, ”

Yamma likis yaya jalal ya iso, zuwa gobe da safe dasu wuce, da dddare bayan anzubo mishi abinci, ya kalli *hanna* da hameeda dasuke zaune, ku sauko muci abinci yace tareda kawar da idanunsa daga garesu *hanna* ta yatsine fuska yaya na koshi nikam,

Wani kallo daya wulla mata, aitabaaan lokacin data sauko ba tasa hannu a abuncin, hameeda batajira anmata nata Kallon ba, tayi saurin sakkowa,” Wani Irin dadi abincin ya musu wanda su kansu basusan dalilin hakan ba, kuma bawai abincin yawani hadu bane, amma ku masu karatu basai nafada muku abinda ke Ciki ba😭. ”

Sanda suka cinye abincin tass sannan hameeda, takwashe kanukan zuwa kicin, hanna uwarsan jiki kuwa tayi d’ai-d’ai.”

Basu dade da cin abincinba suka kwanta, bacci sosai sukayi, adaran boka yafara aikinsa.”

================

Wani mutumi magani gaban likita hankali tashe, da police guda biyu acikin office din. ”

Magana naji yafarayi yana cewa” tayaya za’ace ba’asamu Wani dalilin da zai nuna shaidan wanda sukayi hakanba, _jinayi kamar nasan muryan nan amma a’ina? 🤔 masu karatu kubiyoni dan musamo amsa amma nima nakasa tunawa_ police dinne yafara magana sir” duk wani bincike munyi yanuna mana ba accident yayi ba bigeshi akayi, dan munsami mashin _power bike_ dinsa akasa bbu alamun kokewar Wani abu ajiki, gakiya i _ _asaured u that_ wannan dasa hannu aciki munakan _inveatigeting_ duk wani mai hannu zaisamu _punishment_ mai tsaurin gaske. ”

Yaja Wani _deep breath_ sannan ya kalli doctor, doctor” _please_ yaushe zai farfado??? ”

_Sooner_ in sha Allah inji _doctor_ ,yar buguwa ce _and then_ ya razana _so_zuwa nan da _few hour’s_ zai iya farfadowa, fita yayi zuwa dakin da aka kwantar da yaron, sosai ransa yake bace, dan ya tabbata duk mai hannu sayya kasheshi,

Cikin yan minute’s yakira shugaba police ya shaida musu akan su duba CCTV camera dake layin sukawo masa _result_ Cikin hour’s suka gama hada komai suka kawo masa abinda yafaru alayin a wancen ranan.”

===============

Sai wajan 6:30 iyalan gidan alh muhammad suka tashi dawata Irin kasala, dakyar sukeyi sallah, kowa mamakin Irin wannan bacci yakeyi, dakyar su *hanna* suka samu suka fara shiri dan dawuri zasu wuce kano. ”

===============

MG ne zaune shida Abubakar a farfarjiyan sha shunsa , sojoji sai shawagi sukeyi,

MG ne yakara magana _in angry tonge_ , Wani Irin banzan zancen wannan har sai mun jira _sister’s_ kafun a shirya yanda za’ayi _event_ din, haba *yareemah* sunkussan zuwa dan yanzu inada tabbacin tasowarsa, mtswww Yaja tsaki tareda _hot n sexy eyes_ dinsa bai Kara cewa komaiba, dan
A rayuwar sa, _he hates_ acewai umarnin wasu zaibi, wayarsa ce tafara _ringing_ ganin kiran daga captain bala ne yasashi yin _picking_ abinda yadada masa ne yasa shi saurin mikewa zaune yarasa farinciki zaiyi ko akasin hakan,
Gabansa ne yahau dukan uku-uku.”

To be continued

_Ur’s_
_Z33yyb3rw3r_

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

*_Banida bakin yimuku godiya gaskiya naji dadin yanda kukeson littafinnan, da masu bina ta prvt nima inasonku kamar yadda kuke sona luv u all My fans_*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply