Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 3


Bibiyata Akeyi 3
Viral

Page 3
*
DUBAI

Wani tangameman gida nahango, wanda fadin girmansama tsayawa bata bakine, kyawunsa kuwa kokadan baya misaltuwa domin bansan dawani yare zanmuku bayanin da har zakugane kyau tsaruwar wannan gida ba, hatta tsaron gidan ma, sojojine masu tsaran gidan sunza gayeshi , tako wani sako da lungu gaba da baya,
Azatona tunda kasar larabawa ne nadauka sojajin larabawa zangani amma inah zancen yasha bam bam,

Sojojine kala kala wanda kowace kasa sanda suka bada gudumawa wajen kare lafiyar wannan bawa nasa, kowani soja yana sanyene da kakin kasarsu sojojine bila adadin wanda irga yawansuma bamai yiwuwa bane,

Mamaki da alja’abi suncikani waishin waye wannan dan adam dinda ake gadin rayuwarsa haka. ko sucurities dasuke gidan shugaban kasa basukai natsaron wannan bawan Allah yawaba,

MAJOR GENERAL (MG) Abudullahi kukeji daya tamkarda dubu, gwarzon namiji wanda kallonsa kadae ke razana makiyah, ba country dinsa ba kadai
hatta da sauran kasashen sunaji dashi shiyasa suke bada gudumawa wajen kare lafiyarsa, domin shi mai sadaukarwa al’ummah rai da lafiyarsa ne,

Zaune yake kankujerar tangameman falonsa kafanshi daya akan daya ya jingina da kujera karkada kafansa yakeyi ahankali cikin nutsuwah da solon birgewa,

Farineh tass kyakkyawan gaske wanda kana kollonsa dakaga kamanninsa da larabawa dogo neh sambal mai faffadan kirji, gwarzon namiji, subhanallah kyawun wannan bawan Allah, abin ba’acewa komai, saidaai hamdala. idanuwansa farare tass kwayar cikin kuwa bakikirin shape dinsu oval ne masu kyawun gaske, gashin kansa bakine sidik, with his cute pink lips, OMG he’s damn cute, i don’t even knw how to describe him, he’s so muah👄

Rurinda wayarsa tadaukane yasashi bude idoh ahankali cikin nutsuwa daukan wayar yayi tareda karata akunnensa.

Amsa sallama yayi sannan yayi hade dayin murmushi subhanallah kyawunsa baisake bayyana ba saida both side na face dinsa suka lotsa (beauty point)
Abin al’jabin baizoba sanda yafara magana da hausa wadda hakan ba karamin abin mamaki bane
Amsawa yayi da toh abba ammafa akwae abinda nakeyi wadda haryanxu bankarasaba yana maganane cikin natsuwa abba ba halin tafowane cewarsa dadahali danazo cikin week dinnan saboda nima nayi kewarka ina bukatar ganinka to
Call u later baejira mai za’aceba kit yakashe wayan

Wata nauyayyar ajiyar zuciya yasauke kokadan bayason abinda zaisa yaje gida yanxu

Danbaxai iya jira lokaci yacika kafin ya cika kudurinsaba yafi masa sauki yajira lokacin kafin yashiga kasarsa tahaihuwa

Karar saukowar takalmintane yakatse masa tunanin dayakeyi
Wata farar matace wacce bazatafi shekaru hamsin da biyar ba kana kallonta ko tantama bbu dakasan itace mahaifiyar MG Abudullahi balarabiyace
Kyakkyawar gaske
Ko banfada ba kunsan yanayin yanda kyawun larabawan Dubai yake
Karasowa tayi dauke da murmushin dake kara fitoda kamanninsu da MG Abudullahi zama tayi kusa dashi tadafa shi sannan tafara magana cikin harshen larabci

Meyake dmunka haka naga gabaki daya yanayinka yachanja lokuta da dama nakan fada maka kacire wata fargaba bbu wata wacce xatasamu miji kamarka tace bataso kanada kyau da mulki da kuma dukiya bbu wata mahalukiayar da zata kika

Shiru yayi nayan wasu dakika sannan yace ummee bana so asoni dankyawu na ko kudi kowani mulki danake tattare dashi

Mutane dayawa bawae sunasona bane wasu tsoro nane yakesawa sununamin so wasu kuma dan dukiya da mulki yasa suke sona bawai har zuciyah ba wani zafaffen huci yafitar yakara damke hannun ummi dayake rike dashi ummee tajawoshi jikinta ahankali tafara shafa kansa batareda tace komaiba

Aranta kuma tanace Allah kasaukakawa wannan bawa naka wannan jarabawar da ya tsinci kanshi aciki tana tausayin danta ace yakamu dasan wanda basumasan ko tana existing ba

================

Yauma kamar kullum shiri tayi tsab nazuwa makaranta doguwar rigane ajikinta ta yane kanta da gyalen rigar wadda hakan yafito da sihirtaccen kyawunta wanda ba lokaci daya kake kollonta kagano wannan kyawunba

Jakarta ta zara direct dakin babansu tanufa dasallama tashiga sanda ya amsa sannan tashiga tagaisheshi ya amsa da fara’arsa kinfuto kenen eh baba yanxu zanwuce dari biyar yaciro yabata godiya tayi masa sannan tatashi yafibata dakyakkyawar addu’a wadda yakamata duk wani mahaifi yayiwa diyarsa lokacin da zataje wani waje nadaban

Fitowa tayi zuwa bakin titi domin samun abun dazatahau tawuce makaranta duk da chanja mata dasukayi hakan baihanata fahimtar suwaye acikin motar ba adaidata tayi saurin tsara tahau batayi mamakin binta da motar takeyiba har zuwa makaranta sannan ta sallami mai adaidata tayi cikin school din

Sanda suka shiga lectures 80:30 tayi basu suka fitaba basai 11:30 dayake 3hour lectures ne sunafita taji wani irin……..

To be continue

Ur’s
Z33iiyyb3rw3r

BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writing by
Zaynab Bawa (z33iiyyb3rw3r )

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply