Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 35


Bibiyata Akeyi 35
Viral

Page 35

 

 

*
Ahaka suka k’are meeting d’in, akan za’a nemo musu wacece ita?” kuma menene alaqarsu da ita? ”

Haka yau takasance ma, agun anty samha ta kwana, su amira sun bata hakuri amma kaman bada ita sukeyi ba.”
Haka yau ma takara mulke jikinta da had’i, sannan suka kwanta. ”
Amma kokadan bata bawa anty samha kofar da zata mata maganar najeeb ba. ”
Dasafe kuwa wani irin kyau tayi fiyeda najiya, kuma yau takasance ranar da za’afara event. ”
Mama kasa hakuri tayi sanda ta tanka.” ke wai mai kika fara shafawane kam?”
Turo bakinta tayi, ”
Zaki fad’amun ko saina bige wannan bakinkin?”
K’in mayarda bakin tayi tak’ara turoshi, ”
Tashi tayi da niyar bigeta, ganin haka yasa takwala ihu.”
Aikuwa dama umma nawajen, ”
Tashi d’aya tafara tahaukan Mama ta masifa,”
Ke banasan shashanci kina jina ko? ”
Ina ruwanki da kalar da tafanta tayi?”
Hava yaya kikalleta fa sai kace wata mai bleaching ki kalla yadda fatarta tayi haske? ”
Umma ce” tace yanzu ke aisha haryanzunki bazaki iya, bambamce farin bleaching, dana gyara ba? ”
Toh tare ake musu gyara itada samha.”
Jin hakane yasa hanklain Mama kwanciya,”
Hmm kawai Mama tace daganan bata sake cewa komai ba. ”
Shiga d’akin su amira tayi, duk d’insu sakewa sukayi kamar wanda bbu wani abu dan sukansu fushin da sukayi kowa yaji jiki, hira sukeyi sosai, can wayar ta tafara ringing ganin anty samha ce mai kiran yasata saurin amsawa.”
Hellow” anty, ”
Kuzo d’akina kedasu amira, bbu 6ata lokaci ta shaida musu kiranna anty samha Tashi sukayi suka nufi d’akinta.”
Shiga suka yi tana kan gado. ”
Dawasu kaya awajenta.”
Zama sukayi, harhad’a kayan tayi awata jaka mai kyau sannan ta d’ago ta dubesu, mikawa *hanna* jakar tayi, gashi dan Allah yanzu kukai fadah, fad’a baki sukeyi dukkansu suka ambaci fadahh?”
Eh ” kanwar sace yar gidan sarki tadawo daga school kuma duk wani ankonta awajena yake, kunsan zuwa jimawa zata buk’ace su.”
Ta6e baki amira tayi to ai anty sai abawa driver yakai mata danni wallhy bansan rainii takareshe maganar tana kawarda kanta gefe,”
*Hanna* kan wayarta tafara dannawa dan tasan wannan zancen bamai yiwuwa bane.”
To ke anty ita baza tazo ta kar6a da kanta bane? ”
Ko tsabar sarautar ne sai ankai mata?”
Dan Allah ni basaina tsaya magana ba idanna isa daku kukai mata. ”
Idan kuma bazaukai ba shikenan.”
Dan akwai abunda zata baku kuzomin dashi ne. ”
Haka badan ransu yasoba suka tashi danzuwa kaimata,
Kuma abinda yafi ci musu raima shine wai ba driver bane zai kaisu a taxi zasuhau futa sukayi kowa sai k’unk’uni yakeyi.”

 

 

 

 

MG ne zaune agaban mai martaba da’alamu bakinsa akwai magana sosai amma haryanzu yak’i cewa komai. ”
Ganin haka yasa mai martaba ya sallami duka ‘yan palace d’in.”
Juyawa yayi ya fuskanci MG, sannan yace ”
Yareemana da’ alamu bakinka akwai zance dayawa amma kayi shiru.”
Maza fad’amun damuwarka kasan idanba niba bbu typing wanda yadace ka fayya cewa damuwarka. ”
K’asa yayi da kansa yanad’an sosawa ganin haka yasa mai martaba murmusawq,”
Yanajin dad’i MG ya tambayeshi abu duk girman abun yana iya barmasa. ”
Ehem go ahead my son tell me, yafad’a a lokacin dayake ta6a kafad’arsa,”
Cikin alamun Jin kunya yace ”
Dama abba inaso aje nemamun auren *hanna* ne.”
Mai martaba bayyi tsammanin zancenda zaifuto abakinsa bakenan, baisan lokacin da ya mike ya zauna daga ki shine giden dayake. ”
Cikin zumudi yafara magana, son da gaske kake?”
Allah nagode maka daka nunamin wannan rana, ”
Nayi farinciki wanda nikadai nasan irinsa.”
Yareema akullum ganin nakeyi kawai kana fad’in kakusa aurene dan ka kwantar mana da hankali, dukda cewa hakan amma idan kafad’a hankalina yana kwanciya, amma yau Allah ne kad’ai yasan irin farinciki da nake ciki, Allah yamaka albarka kuma yasa Alabarka azamnatakewar auranku. ”
Cikin ransa ya amsa da amin.”
Fad’amun yar gidan waye, zuwa gobe nasa amin bincike, dukda nasan cewa bazaka ta6a za6ar macen da batada tarbiya ba amma hakiinane amatsayin mahaifinka nayi bincike akan ta da mahaifinta.”
Cikin ladabi yace Abba ai ‘yar gidan wan mahaifin matarda Abubakar zai aura ne. ”
Ikon Allah kenan wato duk wannan tsawon shekarunda muka dauka, kasanda cewa tanada kanin mahaifi anan?”
Gyad’a kansa yayi eh abba. ”
Rashin sanine aida lokacinda akaje tambayan na Abubakar da anhad’a duka.”
Amma yanzu komai da zafi zafi akeyi barina kira modiibo.”
MG ne yad’aga wayar yamasa dialing ring uku aka dauka. ”
Cikin girmamawa ya gaida middibbo, ya amsa Cikin kulawa.”

 

Moddibbo aminin mahaifin mai martaba ne tsoho mai farar aniya, kuma babban malami duk wata amanar da sarki abdallah yabar masa, sanda yatabbatar yacikasu. ”
Bayani mai martaba ya koro masa,”
Sosai ransa yayi fari dan murna har sujjudur shukur sanda yayi. ”
Cikin farin ciki yace”
Allah yacikaman burinmu dazafi zafi zamuyi komai,”
Ran auren Abubakar sai muyi magana. ”
Kannan muci gaba da addu’a Allah yacika masa burinsa dan idannasa yacika namu yacika.”
Ahaka sukayi sallama kowa ransa farii tass. ”
Nan da nan mai martaba yafara kiran dangi abunnema yasamu,” Cikin yan mintuna kowa sai kira yake dan gaskatawa. ”
Ummii dabatasan labarin mayyake faruwaba, kira kawai take gani ta ko’ina.”
Kashe wayar kawai tayi dan batasan surutu. ” ni saida abinma yabani mamaki sai kace wanda akace yau ne d’aurin auren.”

 

 

Su *hanna* ne tsaye a kofar shiga fadahh, rigima sukeyi dan sunce bbu wanda ya’isa yasa Su cire takalmi, sunkai kusan 30 minute a kofar wajen har takai ga yanzu wasu dogarawa sunzo da niyar korasu. ”
Tana kallo captain bala dake biye dasu tundaga gida.”
Wajen dogarawa taga yanufa, ”
Magana yamusu sai gasu sun nufo wajanta,”
Suna zuwa aikuwa hakuri suka fara basu, kamar wanda zasu tsugunna. ”
Sannan suka umurci d’aya daya musu iso.”
Hakan kuwa akayi.” Suna shiga nan kallo yakoma sama ai basu ta6a tunanin fadan babban gari bane acikinta. ” sanda sukayi tafiya mai nisan gaske kafinnan suka isa wani sashi mai d’an karan kyau.”
Adai-dai lokacin MG yafito daga kofar mai martaba. ”
Gabantane taji yayi wani mugun fad’uwa sakamakon had’a ido dasukayi.”
Saurin komawa baya tayi tariqe hameeda gam. ”
Shikuwa d’auke idonsa yayi kamar baita6a kallonta ba.”
Gani tayi daga fitowarsa sojoji sun masa runfa, tunani dama wato agidan sarauta yake, yatsine fuska tayi Sannan tace shiyasa yafiya girman kai. ”
Tsaki taja mtsww wanda har yafito fili Suka juya Suna kallonta.”
Ganin ko’ajikinta batamasan tayiba yasasu juyawa sukaci gaba da tafiya. ”
Shikuwa anasa 6angaren baiyi mamakin gainta anan ba dan yanada tabbacin aikota akayi.”
Wani plat suka nufa mai shegen kyau, dan tsarin baiyi kama da tsarin gidan bahausheba. ”
Sak yanda larabawa sukeyin gidansu duk glass.”
Tsayawa yayi abakin k’ofar sannan yayiwa wata kuyanga magana akan tayi musu issoh. ”
Wani falo tashigar dasu falon bbu tarkace dan mai shashin batacikason yawan kayaba,”
Sai dai komai na falon classical ne. ”
Juyawa tayi zata wuce, Saurin tsayarda ita amira tayi sannan tace wurin labba mukazo.”
Amsawa tayi da kayi sannan tashige wani sashi.
Kafin d’an wani lokaci anchika gabansu da kayan marmari dasu drinks,
Ko kallon wanda takawo basuyiba balle sannu ransu yakai kololuwa gun baci, dan rainin hankali tawani shanyasu. ”

 

Aiko ba komai sai tazo takar6i aikanta dansu bazama sukazoyiba. ”

 

 

Can kusan tak’ara ten minute akai sai gatanan tafito.”
Dan lokacin har amira tamike da niyyar fita, ” ganin bazatafi sa’arsuba yasa ransu k’ara baci,
Karasowa tayi Cikin sakin fuska, binsu d’aya bayan d’aya tayi tana hugging nasu Cikin murna, nan tafara magana, dan Allah ku gafarceni nashiga wankane, ita kuma tatsaya jirana batazo ta sanar da Ummii ba ku gafarceni. ”
Duk cikinsu bbu wanda jikinta baiyi sanyi ba ganin yadda sukayi tsammani ba haka suka sameta ba.”
Hanna ce tace wallhy bbu komai dama sak’one, anty samha ta bayar akawo miki,
Cikin fara’a tasa hannu takar6i aikan godiya take surfawa, duk da cewa wannan bawani abu bane, amma tayi appreciating sosai. ”
*_Hanna_* ce take satan kallonta ko tabbas kama sukeyi sosai da wannan mutumin,
Itama kyakkyawace ta ajin k’arshe .”
Saidai MG yafita kyau😜. ” hameeda ce ta mintsini amira ta niyyar tatashi, amira tashi tayi,
Hava dan Allah badai tafiya ba?”
Eh wallhy muna sauri ne inji hameeda, to muje ku gaisa da Ummii, da kin gaisheta kawai daganan aika zamuje,
No aibazataji dad’i ba idanna fad’a mata, badan ransu yasoba suka nufi wani shashi, afalo suka sameta, wata kyakkyawar balarabiya suka gani mai kmada labba, tana kallonsu tasake fuska,
Sannan suka k’araso gaisheta sukayi, ta amsa Cikin sakin fuska,
Ummii kinga abinda suka kawomun, a’ah😃 to angode Allah yasaka, ta fad’a tana kallon *hanna* wanda tun shigowarsu yarinyar ta d’auki hankalinta, kuma tarasa dalili,
Tashi sukayi suka mata sallama,
Hava my doughters kujira zuwa jimawa mana, dan har Cikin ranta batasan tafiyar *Hanna* jitakeyi kamarta dad’e da saninta, kud’i ta d’auko mai yawa tabasu amma bayadda batayiba sukak’i kar6a. ”
Ganin hakanne yasa tayiwa labba magana, sai labba tajuya samun kanta tayi ta riqe hannun *hanna* dasuke niyyar fita, lallausan hanu mai taushi ne taji ya riqeta, saurin juyawa tayi sukayi idoh hud’u dana Ummii, saurin yin k’asa da kanta tayi dan haka kawai takejin nauyin matar, had’a idonda sukayi kuma yasa tajii wani iri kamar wanda tataba kallon kwayar idanun awani waje. ”
K’ara damk’e hannun ta tayi my doughters, dagowa tayi tasake kallon ta sannan tak’ara sadda kanta k’asa,
Menene sunanki?”
Ita kanta batasan lokacin da tamabayar ta fito abakin taba,
*Hanna* tfad’a Cikin girmamawa da jin nauyin wanda akeyiwa magana,
Alhmdllh tafad’a a zuciya a fili kuma tace, sunanki da dad’i, nagode tafada ahankali,
Juyawa tayi gunsu, amira nan ma ta tambaya kowa ya fad’a mata, albarka ta samusu, anahaka labba tafito, itada wasu kuyangi da ledoji a hannunsu, har lokacin hannunta na riqe dana *Hanna* nan ma dakyar suka kar6a saida sukaga ranta ya6aci. ”
Dakyar tasaki hannun ta hakan ba karamin mamaki yabawa Hanna ba,
Direba akasa yakaisu har gida, anan akayi tamusu fad’an kar6an kayan da sukayi.”

 

 

Shirye shiryen fita event suka fara, mai kwalliya tazo Har ta fara shirya amarya sai a lokacin, su *hanna* suka fara shiryawa suma. ”

 

To be continued

 

Ur’s
~Z33yyb3rw3r~
[12/2, 9:30 AM] Anty Jamila D Ili: *BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by

© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

My first novel

_
_This Page is dedicated to Hon Bawa Alabura’s family. “zaynab bawa loves u dearest, ina alfahari daku.”_

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply