Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 39


Bibiyata Akeyi 39
Viral

Page 39

 

*
Bata nufi ko ina ba sai garden tazauna akan resting chairs, sai kuka takeyi, kamar wanda danshi aka aikota duniya. ”

Ganin yanda take yasa moddibbo nufan wajen, tsayawa yayi ya gama nazari akanta, dafa kanta yayi, daogowa tayi takalleshi farine soll tsoho mai farin gemu yanada tsayi madaidaicii,”
Sunkuyarda kanta tayi dan wani irin kwarjini yamata, “sunkuyawa yayi ya zauna da nishi alamun tsufa ta kamashi,”
Cikin sigar kwantarda hankali yafara magana irinnasu na dattawa,”
Jikata nasan kina Cikin damuwa amma kisani kuka ba shine mafita ba. ”
Akullum ki yawaita addu’a shine maslahar damuwarki, sunkuyarda kai tayi ta cigaba da wasa da yatsunta,”
Murmushi irinnasu na manya yayi sannan ya cigaba da cewa, mai nene dalilin da zaisa iyayenki su za6a miki miji amma ki bijre musu? ”
Sunkuyarda kai tayi hawaye d’aya nabin d’aya sai yanzu take danasanin maganganun data fad’a musu kuma agaban wa’yanda sukazo neman auranta.”
Baijira amsarta ba yaci gaba da cewa, ”
Kinsan cewa bbu wanda yake da mahimmanci a rayuwa irin mahaifa, kikasance Akullum mai san faranta musu,” girgiza kanta tafarayi hawaye d’aya nabin d’aya, ” ahankali ta furta ba haka bane,”
Toh menene Jikata?”
Yatambaya Cikin sigar lallashi, ”
Girgiza masa kai tayi, Murmushi yayi dan tabbas yasan akwai abunda take boyewa.”

 

 

 

 

To kifad’amun dalili har inde bakyaso nazargeki akan kin yiwa mahaifanki biyayya, ” bansan cutarda wanda yake tareda nine ko kadan banso wani yasake cutuwa kamar yadda najeeb yacutu,”
K’ura mata ido yayi nasan gaskanta abinda yake tinani,”
Cikin hikqma yace kidaukeni matsayin kakanki, danni nadaukeki ajikata kifada mun duk wani abinda yake faruwa da rayuwar ki karki boyemun komai, in sha Allah tare zamu nemo mafita, ”
Cikin yarda da tsohon tafara bashi labarin duk wani abinda yafaru har izuwa kwanciyar najeeb a asibiti, dogon numfashi yaja sannan yace mata, jikita tunda naganki nasan kina tareda sihiri ajkin ki saidai baida k’arfii dan atunanina yawan addu’a da kike ya ne yasa abin baiyi karfii ba amma in sha Allahu da addu’a zamu yakesu bbu wani abinda yafi karfin addu’a, ” _mutane musani bawai dan kinada damuwa sai jitafi wajen wani yace zai miki aiki awarware sihiri shine masalaha ba A’a akwai addu’oii dayawa acikin qur’anii mai girma wanda su kadai sukan iya samawa dan adam waraka dan Allah mukiyaye zuwa gun wasu malaman yawancinsu bokayene suke k’arya dasunan malamai Allah yakare_

 

 

Nasiha yamata sosai sannan yace ga addu’a kiringa karanta ta kartabace abakinki da yardar Allah duk wani mai nufan ki da sharri zai koma kamsa “`waraddal lahul lazina kafaruh bigaizihim lam yanalu khaira wakafal lahul mu’umininal qital wakanal laahu qawuyan azizan hakima“`
Wannan addu’a hakika tana maganin sharri dakuma mai nufinka da sharri ahaka yayita mata nasiha sannan yace taje tasamu mahaifanta tabasu hakuri, ”
Jikata d’agowa tayi tayi kalleshi, gobe kizo gidana ki kar6i sauran addu’oiin, sannan zansa ayita saukan alqur’anii,”
Sannan abu na karshe bawai danna fito a dangin abadallah ba yakasance yaro mai hankali, duk duniya banda mahaifanki banga wanda zaisoki sama dashi ba, ”
Yasoki tun baki mallaki hankalin kankii ba, yasokii tun bakisan kankii ba inatunanin duk wanda zaki aura abayansa yake amma inaso kiyita addu’an zabin alkhairii,”
Allah ya miki albarka amin ta amsa d’an hira suka ta6a sannan yatshi har bakin kofan tarakashi dake yatsufa ahankali yake tafiya sanda suka isah bakin falon taja tatsaya alamu yamata akan tashiga bbu musu tashigo shima yabi bayanta abakin kofa tatsaya ta durqusa guiwaowainta duka biyu sannan ta sunkuyarda kanta, ”
Cikin rawar murya ta ce abba dan Allah kuyafemun nayi kuskure amma in sha Allah bazankara maimaita kamarsaba.”
Mai martaba ne yayi magana wanda dama tun maganarta tafarko Bata 6ata masa raiba yasan dole da dalili, gashi yanzu yanda tatsuguna tana neman afuwarsu yasa yarinyar k’ara shiga aransa, Cikin sigar gamsuwa yace tashi kice d’iyata baki mana laipyn komai ba Allah yamiki albarka ahankali ta amsa sannan tatshi sum sum tafice, ” mai martaba suka fito sun tsaida zancen su na iyaye kowa ya amince amma sunaso yaran su dai-dai ta kansu, godiya mai martaba yayita musu Ganin haka yakarasa suka tabbatar lallai wannan al’amari nada mahimmancii.”

 

 

Karfe hud’u aka fara shirye shiryen d’aukan amarya Motoci ne nagani na fad’a akalla sun kai motoci ashirin kowacce baka ne wulik sunyi parking suna jiran fitowar amaryarsu,”
Itakuwa tana ciki ana mata nasiha sai kuka takeyi, kamar wanda akayiwa mutuwa dakyar aka fita da ita da matanda sukazo daukan amarya mamane riqeda ita suka shiga, ”
Fada suka wuce dan anan zata zauna zuwa gobe akaita gidanata,”
*Hanna* kuwa nad’aki iyakacin hameeda ne tabisu, iya karrama an karramasu, a shashin waziri umar iyayen abubakar aka ajijeta kafin agama biki, shashin yahad’u sosai, site d’in abubakar aka ajiye amare. ”
Sannan wa’yanda suka kawota suka koma gida.”

 

 

Karfe kusan 6 labba taga bbu *hanna* bbu dalilin zatajo gashi, bayan magrib za’a fara shirin dinner, ”
D’aukan motanta tayi ta nufi gidan dakyar ta lallashi *hanna* tabiyota dan itada tace bazata ba.”
Da’akazo wajen shiryawa ma sanda akayi rikici ce tace bazatayi kwalliya ba kuma su hud’unsu sanda ummii ta d’auko musu makeup artist,
Sanda suka addabeta ne yasa tayarda aka mata light makeup amma bakaramin kyau tayiba.”
9 aka fara tafiya wajen dinner, su *_hanna_* sune k’arshen tafiya alokacinda motarsu tatsaya a katafaren hotel d’in alokacin motocin MG suka danno hancinansu Cikin hotel d’in. ”

 

 

 

Fitowa sukayi amotan

_ Suka nufi ciki shima MG Fararen kaya yasa manya bakaramin amsarsa su kayi ba gabaki d’aya sai daukan idanuwa yakeyi, ”
Amfara gudanar da event kowa yana sha’aninsa banda hanna data takure agefe bayanda ba suya tafita ba amma tak’i.”
Shikuwa MG gabaki d’aya ya gundura da zaman wajen gashi ba kalli *hanna* ba kuma andameshi da kallo barin ‘yan matan dake wajen, ” duk da akayi akwai wasu daga Cikin sojojinsa a wajen amma hakan bai hanashi takura ba,”
Sanda event yakai tsakaiya aka kira k’annen amarya kowa yaje amma banda ita ganin yanda amaryar ta 6ata rai take kollonta yasa ta d’anji bbu dad’ii jakar kud’in tadauko ta nufi gun amaryar liki tafara mata sai alokacin MG yaganta yashagala da kallonta ga wanikyau da tayi sai dai fuskarta akwai alamun damuwa duk sai yaji bbu dad’ii ganin ta Cikin damuwa atunaninsa ko zancen auransa da aka mata ne yassata Cikin wannan damuwar. ”

 

 

Bata ankaraba sai ji tayi kawai anfara mata ruwan kud’ii na liki kamar itace amaryar.”

 

 

To be continued

Ur’s
*Z33yb3rw3r*
[12/2, 9:32 AM] Anty Jamila D Ili: *BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by

© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

My first novel

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply