Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 4


Bibiyata Akeyi 4
Viral

Page 4
*
Suna Fita daga lecture taji wani irin yunwa takamata, wanda bazata iya jira bah harsai tanemi wani abu tasa acikinta,
bawani kudin kirki bane a hannunta yasa kawae tashiga wani dan shop a skull din tasaya malt da biscuit

Juyowar dazatayi gam tayi karo da mutum,
baya tayi zata fadi
Cikin tsafinnama dakuma jarumta,yayi
saurin tarota ,yadaidaita mata tsayuwa, dagowa tayi da niyyar kollon ko waye wannan fuskarta cike damasifa,
lokacin daya kuma ida nuwansu yasauka cikinna juna, wani irin faduwar gabane taziyarci zuwa tanufa,
Zubawa junansu ido sukayi na yan dakiku,
Wani irin shock ne yafara bin tundaga kafarsu zuwa kokon kansu gabaki daya wani yanayi suka tsinci kansu mai wuyar fassarawa,

Saurin dauke kwayar idonta tayi daga cikinnasa, dakyar ya tattaro nutsuwarsa waje daya, sannan kwakwalwarsa ta iya tattaro masa kalma daya yace SORRY, yayinda yakafeta da ido, awani irin salon murya irin na mayaudaran mazannan yayi wannan magana,
Wanda idan sunyi sukan sace zuciyar mace, koya takai dajin kanta,
Amma anashi wajan bawae yayi dan yaudaraba saidan besan lokacin yayi wannan salon ba ,
Aikuwa hakanne tafaru da ita domin wannan murya tagama tafiya da imaninta gabaki daya gabanta ne yahau bugawa dasauri da sauri, cikin dakewa tace is ok tawuce batareda ta kara waiwayowa ta kalleshiba,
bawae kuma dan batasan sake kallonsa ba,
Saidan bataso yamata wannan kallo mai kashe mata jiki.

Matsallaci tawuce Kaitsaye,
dan tasamu tasa wani abu acikinta donko karywa batayiba amma takasa,
abu kamar wasa yanason zama gaske, tunanin wannan bawan Allah yahanata sake,
Zuruf tamike, bata wuce ko inaba sai bakin titi tanemi abin hawa,
Domin yafi mata tawuce gida, bazata iya jure irin wannann sabon yanayi datacinci kanta, acikinta.

================

Wacece ita abinda yake tambayan kansa kenan dukda dai yayi soyayya da mata daban daban amma wannan yanayi daban yake, komade Wacece ita saina samota yafada afili,
wannan itace tadace dani dama inason nace maikyau da tarbiya wannan ko yanayinta yanuna daga gidan tarbiya take,
Numfashi mai zafi ya furzar sannan ya cigaba da driving cikin kwanciyar hankali da nishadi waka yasa yana mamin sayya shafa gashin kansa cikin kwaciyar hankali, yadan daki sitiyari yana kada kai, kana kallonsa kasan akwai nishadi atattare dashi.

================

Mai adaidaita dan Allah juya kamaidani GRA
federal lowcost mukayi zankaiikifa eh nafasa kajuya nace
Kaitsaye GRA suka nufa yasauketa tabiyashi yajuya abinsa,
wani dan madaidaicin gida nagani mai kyan gaske nan tanufa cikin nutsuwa takwankwasa gate din gidan wani dan dattijoneh ya budeh washe baki yayi cikin fara’a yar baba dama kinanan inanan baba ina wuni lpy klau yar baba yakaratu Alhmdllhy tace atakaice tareda wucewa cikin Kaitsaye wata kofa tanufa
Bude kofan kenan amal tajuyo Ai aguje tazo ayoyo ummah(yawanci akan kira kanwar uwa da umma ) anty anty anty aibashiri anty tafuto Lafiya amal irin wannan kira
Tsayawa tayi turuss sakamakon ganin *hanna* anty yayar hannace uwa daya uba daya tanada aure da yara biyu amal da bashir, *hanna* takanyi wata uku bata leka gidan sister dinta ba saboda Allah yayita mai maqon uwa nan dacan taje sai tafara cewar mamanta shiyasa batacika futaba yanxu haka, halinda ake ciki yau *hanna* watanta biyu rabonta da gidan antynta kunga kuwa hanna mai laipy ceh sosai.

Saurin sauke amal tayi
Kama kunnunwanta tayi da hanna yenta biyu alamunna tuba nake,
Folding hanneyanta tayi irin banhakuraba rausayarda kanta tayi tace pleassssssse ok amma da sharadi ehem inaji karkira yin sati baki zoba nayadda tace cikin sauri karasowa tayi suka rungume junansu jin amal sukayi tanacewa nibanda ni jawota *hanna* tayi suka hada suka rungume

Yawwa ainaji dadin zuwanki dama aiki yamin yawa narasa yadda zanyi yanxu saiki canja kaya mushiga kicin,
Gaskiya anty ninagaji kiyi kayanki kawae, yawwa waeni meya hana baby amal zuwa makaranta,
Kedai bari wae uncle dinsune yadawo daga karatu shine wae yau saidai abatta daizo ganinsu, aikuwa yanxu kusan 12:00 harmafa dataje tadawo

Wallahi abbansu amal dinnanma
Agaisheshi dan kaninsa zaizo sai ahanata zuwa maaranta yajira ran weekend mana kafinya gansu mtsww taja guntun tsaki,
Aibaki saniba duk abinda yarannan yafada yazaune
Nibari wannan bamai karewa bane tashi kidauramin abinci.

Tashi tayi cikin azama tafara girkawa dama ita ba bayaba wajen iya girki bawani abinci mai yawa tayiba dan ita aganinta yin abinci kala kala masuci kalilan almubazzarancine.

Fried rice tayii mai raida lpy wadda tasha kayan lambu kala da iri dakuma hanta wanda akayankata kananu sannan tahada coslow wadda yasha dafaffen koyi bama kamar zeyi magana., zobo tahada wadda yasha kayan kamshi sannan tayi kunun aya tahada ayan da dabino da kwakwa ta markada,
daidai cikinsu tayi wadda babu barna aciki, jan nama tasoya tazuba akan abincin tarufe zuwa 1:30 tagama komai tajereshi adaining ta kimtsa ko ina ta wanke kwanukan da akayi amfani dasu,

Fitowa tayi tagyra ko ina nagidan sannan ta jona burner tazuba turare mai dadin kamshi kamkace meh gidan gabaki daya yadauki kamshi mai sanyin dadi.

Wanka tashiga adakin amal daganan tadauro alwola tayi sallah ta idar lokacin anty harta gama shiryasu amal da bashir itama tayi wanka tashirya,

Fita tayi zuwa dakin anty kibani kaya nasa bude wadrop kidauka mana to Ai naga duk kintaba sawane kajimin yarinya wanda bantaba sawaba kikeso nabaki hava anty yanxu ya mahmood yaga kaya ajikinki nima kuma yagani ajikina haba Ai abunda kunya uhm kyaji dashi bude akwati kidauka to anty tank u

Simple makeup tayi dama ita bama’abociya san kwalliya barkatai bane,
Jan swiss less tadauko dinkin riga da siket tasa,
Ya matukar amsar kalan fatarta, dayake farace amma batacika haske sosae ba saidai kuma baza’a kirata da baka ko chacolate ba,
Tayi mamakin yanda kayan yazauna mata chif chif kaman angwada,
Anty kuma tadan Fita kiba kadan.

Fotowa tayi daga dakin tanacewa anty amma kayannan bama kanki kika dinkawa bako????
Fitowa tayi daga dakinsu amal tana rikeda rigar bashir ahannu, wanda tacire masa ranan kewa,
Au dama wannan kika dauka Toh kinyiwa kanki dama dinkin sallah namiki kuma bazan sakeba, hava anty nidin kinefa,
Eh kedin tawa😏, kantarufe baki sukaji karan door bell, jeki duba barin futoda Su amal, juyawa anty tayi ciki itakuma danufi kofa bude kofan tayi tajuya tanayiwa anty magana, alamu taji kaman Ana kallonta, Juyowar dazatayi daga mutum abakin kofa yakafeta da idoh yajingina ajikin kofa tareda harde hanneyanta,

Baki tabude tana kollonsa jitayi yace……

To be continue

Ur’s
Z33yyb3rw3r

BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writing by
Zaynab Bawa (z33iiyyb3rw3r)

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply