Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 44


Bibiyata Akeyi 44
Viral

Page 44

*
Abaya tabi MG dagudu taratsa tacikin sojojinsa ta kutsa tawuceh har gaban sa taje ta tsaidashi sannan ta tsugunna tana maida numfashii. ”
Shafa gashin kansa yayi sannan yad’an furzarda iska, cikin sanyi yace menene?”
Yaa yareema gudansu *hanna*. ”
D’an tsaki yaja ahankali sannan yace ki gaidata yara6a yana shirin wucewa, riqo hannunsa tayi sannan tace yaya dama wani xobbe ne nakeso kazaba,”
Inza6a?” yatambaya, ”
Eh ma *hanna*
Tsaki yad’an k’ara ja sannan yace wasu irin ring ne?”
Diomond ring, ”
Diamond ring, yayi exclaiming,” eh tace atakaice to me zatayi dashii? ”
Lokaciin zaizo nidai kawai kaza6a.”
Ok muje ciki, shashinsa suka nufa, ”
Suka zauna tafara nuna masa,”
Baitsaya bin kyau ba kawai yad’auki wanda yafii kowanne tsada. ”
Aikuwa readers kumsan basaina 😜.”
Fad’a ba kunsan yanda kyawun ring d’in zai kasace.” Zaroo ido 😳 hanna tayi, ” Yaa yareema kasan kud’insa kuwa?”
D’aga kafad’ansa yayi🤷‍♂ sannan yace,”
Nikuma shii nakeso, kuma kinsan kud’ii badamuwa bane,”
Tashi tayi sannan tace gobe anty hibba zata iso (k’anwar ummii ce) 🤷‍
Yau da daddare jirginsu zai taso, ”
Kabani kud’in natura mata,”
Jingina yayi da kujerar sannan yad’aura k’afansa d’aya kan d’aya ya lumshe idanuwansa kamar wanda baisan magana yace kije zantura mata. ”
Kallonsa tayi aranta tace kamar bashine mace take wahalarwa ba,” sai wani shan kamshii yake mata. ”
Yaa yareema akwai abinda nakeson yi da atm dinka d’inne fa tafad’a tana turo bakii.”
Miko mata yayi batareda ya bud’e idanuwansa ba, ”
K’ar6a tayi sannan ahankali cikin k’unk’uni tace kuma sai nayi abinda naga dama dashi.”
Inajinki yace saurii tayi tarufe bakinta tayi waje aguje. ”
Mirmushi yayi sannan yace labba kenan.”
Tana futa bata tsaya ko’inaba sai gidan su hameeda wucewa tayi ta gaida umma sannan tawuce falo yandasu *hanna* suke zaune, ”
Zuwa tayi itama tazauna sannan tasa hannu agyda soyayya plate dasukeci.”
Kallonta sukayi ko ajikinta gabaki d’aya sai wata irin kunyar labba ta lulli6eta tasan koba komai zataji bbu dad’i ace batason yayanta. ”
Sake jiki tayi kamar bbu abinda yafaru dan ita batama nunawa hanna tasan amma faruba aamma itakam *hanna* sai wani sunne kai takeyi,”
Hameedace ganin yanda *hanna* takeyinyada yasata jan tsaki, juyawa sukayi suka kalleta rai abace tace, ”
Kinsan kinada kunya aibazaki aikata abinda kika aikataba.”
Kallonta labba tayi taksan ido dan taga reaction d’inta. ”
Harara ta wullawa hameeda tace me kuma nayi?”
Ta6e baki hameeda tayi sannan tace ohow gashi yasa kinata sunne kai, ”
Tsaki *hanna* taja daganan bata kara cewa komaiba, itakuwa labba tana jinsu batace musu k’ala ba sai gyadan ta takeci kamar batsan ma sunayi ba.”
Kallonsu tayi sannan tace antyna nazofa arakani nashiga kasuwa ne.” hararan wasa *hanna* ta gallah mata harara sannan tace waye kuma antynki.”
Ke mana aiko kink’ii saina kirakibda anty kuma dole ki amsa. ”
*Hanna* yaya nasanki sosai wanda inada tabbacin babu wani namiji da zaisoki fiyeda yadda yakesonki,”
Tun ina ‘yar shekara goma yake zancenki har izuwa yanzu baitaba daga ido yakallibwata mace da sunan so ba. ”
Kuma na tabbata idan ba keba bazqiso wata mace ba kuma bazai ta6a aureba idanba keba.” maiyasa bazaki taudayawa wannan bawan Allah ba, shuru tayi ta sunkuyarda kai dan batajin zata iya bata amsa dan haryanzu bata fara son yayanta ba kuma bataji zata faraba.”
Tashi sukayi d’akin umma sukayi suka tambayeta, adawo lpy kawai tace musu, ”
Shiryawa sukayi sannan suka saka kai suka fice.”
Ashe ba kasuwa dasuje ba gidan afeeyah tawuce dasu wanda ke anguwar taraunii, ”
Gidane mai kyan gaske, horn tayi mai gadii yabud’e tashige cikin gidan, bbu wanda yatambayeta wajenda zasuje,”
Tana tsayawa tajuya ta kalli hanna sannnan tace anty muje koh, ”
Harara ta 6alla mata sannan tace sunannan bazai futa abakinki bako,”
Fita sukayi suka shige gidan iya tsaruwa gidan ya tsaru sosai sallama sukayi afeeyah dake zaune afalonta tana bawa d’anta d’an kimanin shekara biyu abincii, sallamraune yasa ta juya sannan ta amsa ganin sune dasauri ta nufesu tana zuwa ta rungume *hanna* yau yayabtace agidannan? ”
Janta tayi zuwa ciki tama manta dasu labba koma ince bata lura dasuba.” Muda ba’a damu damu ba saimu koma tunda sharemu kikayi, ”
Juyawa anty tayi sai asannan ta lurada hameeda ruqo mata hannu tayi sannan tajuya takalli labba tace saiki koma toh,” au haka kikace? ”
To bazan komaba tana fad’in haka tayi ciki tazauna kusa da hanna tazauna,”
Zaunawa anty afeeya tayi kusada *hanna* a kunyace *hanna* tagaisheta amsawa tayi cikin fara’a sannan tajuya ga hameeda itama suka gaisa cikin fara’a sosai. ”
Cikin tsolaya tacewa hameeda, gaskiya kina kama da sis d’ina sosai,”
Hameedane tayi dariya sannan tace aidole, maman mu yaya da kanwa hakama babanmu suma yaya da kanii ne, ”
Jijjiga kai anty afeeyah tayi sannan tace gaskiya kam dole ayi kama,”
House girl d’inta ta kira ta sata ta kawo musu abun motsa baki, ”
Sosai takejan ta da hira,”
Abin har mamaki yaba labba dan tasn anty afeeya bata kasance daga cikin masu sake fuska ba bata sakan jiki da mutum da sauri amma gashi nan tasake da *hanna* tabbas *hannace* tadace da yayansu tasan koda wata ya aura bazasu sota kamar yadda sukeson *hanna* , tabbas son *hanna* ajininsu yake daga mahaifiyarsu da mahaifinsu zuwa kan uban gayyan MG harzuwa kansu wata irin k’auna sukeyiwa *hanna* bata misaltuwa,
Haka Allah ya haliccesu da sonta azuciyoyinsu, ”
Sosai anty afeeyah ke hidima dasu kamar. Mai shriin goyonta dan so,”
Hameeda kuwa ganin yanda sukeson hanna yasa acikin ranta tad’au alwashin saita juyarda *hanna* zuwaga MG dan ba kowane family bane zakace bakasan d’an uwansu kuma suyita lalla6aka , jin dad’in irin soyayyar da suke nunawa hanna takeyi dan koba komai tasan ‘yar uwarta baza tayi dana sanii ba. ”
Sai bayan sunyi sallar azhahar sannan suka fita da niyyar tafiya,”
Anty afeeyah lokacinda sukazo fita rike hannun *hanna* tayi ji takeyi kamar karta futa, ”
Ahanyane labba,
Basu wuce ko’iina ba sai gida.”
Koda sukaje sanda labba ta dad’e sosai agidan kafinnan ta tashi tatafi,
Kollon hameeda tayi sannan tace sis mud’anje can muyi magana mana, toh hameeda tace tabita suka je wani waje yanda *hanna* bazata jiyosu ba, ”
Sun d’an dade suna magana wanda ni kaina banj mai sukace ba balle *hanna* abinda naji kawai ak’arshe ne hameeda tace in sha Allah haka za’ayi, sai labba tace tam shikenan gobe zan aiko dan bazan samu damar shigowa ba,”
Suna gamawa taje wajan *hanna* sukayi sallama tatafi bata damuba dan tasan maganarsu bazata wuce itada MG shiyasa aranta kuwa tace zakuyi ku barii mah, ”
Kusan k’arfe goma lokacin *hanna* tagama chttn tana kwance tad’auko wayarta bud’e hoton najeeb tayi tana kallo tana kuka,”
Dan haryanzu tanajin sonsa aranta barin yanzu daya dameta da kira kullum yana bata hakurii, ”
Jitakeyi idan bata aureshiba zaata cucii kanta kuma shima ta cuceshi,”
Alokacinne irin soyayyar da ‘yan uwan MG ke nuna mata tabbas idan ta ce bazata aureahiba tayi butulcii kuma ta kauce maganar iyayenta kuma gashi ita haryanzu zuciyarta najeeb takeso kamar tayi hauka.”
Kuka tafashe dashi mai cike da k’unar rai gawani irin zazzabi dake niyar rufeta, ”
Ahaka hameeda tashigo tasameta, zama tayi kusa da ita batama sanii ba saijin muryarta tayi tana cewa,”
Haba *hanna* wannan wani irin damuwa kikasawa kanki wai? ”
Karfa ki manta cewa kullum da daddare inajin ki kina kuka akan najeeb waishin najeeb d’innan shine autan maza da bazaki iya rabuwa dshiba?”
So kike kisawa kanki ciwon zuciya? ”
Toni gaskiya wannan abun ya ishenii zanje nagayawa umma hala ita kiji maganar ta, me najeeb yafi MG da kika za6i najeeb akan MG eyeh?”
Hasalima bbubabinda yakai MG, yamasa fintinkau yawuceshi nesa ba kusa ba yawu ceshi wucewarda bazai kamoshiba haba *hanna* maiyasa bazakiso mutumin dayake sonki tun bakisan kanikiba?”
mayyasa bazakiso wanda shine kad’ai zai soki har k’arshen rayuwarsaba?”
Karki manta bashi yasawa kansa sonkiba kuma kisan cewa zafin da kikeji nasonda kikeyiwa najeeb to baikai kashi d’aya acikin ashirin daga cikin wanda MG yake miki ba, ”
Kekuwa wani irin laipy MG yamiki ni natabbata idan akace kifad’a bbu wani uzurinda zaki kawo.”
Kiyi tunani kada kije kiyi abinda zaisa kiyi danasani bana fatan hakan arayuwata, ”
Jikin hanna ne yayai sanyi jin magan ganin hameeda,
Juyawabtayibta rungumeta tace hameeda narsa yanda zanyi,”
Ni nasan abin yi inji hameeda, dasauri hanna tad’ago kai tace menen shi? ” Sa hannu tayi ta share hawayen dake gangarowa afuskan *hanna* sanda tagama share mata sannan tarike hannuwanta duk biyu ta damqe tace kibani nanda kwana biyu idan baki amince da auran MG ba toh ki yanke ko wani irin shawari,”
*Hanna* ce tace kwana biyu fa kikace? ”
Eh kwana biyu nace wata yar dariyavtayi sannan tace hameeda kina wasa danii nine kike tunanin zaki juya acikin kwana biyu?”
Lallai hameeda haryanzu baki gama sanina ba, ”
Nop mu zamu juyaki,”
Keda suwa? ”
Kedai tunda kin yarda kawai shikenan nayarda tafad’a batareda damuwa ba dan tasan ba yadda za’ayi ta amince acikin kwana biyu.”
Hira suka d’an ta6a sannan suka kwanta. ”

 

 

Washegari k’arfe sha d’aya sukaje gidan anty samha,”
Dama tunda akayi auren basuje gidanta ba dake rijyar zaki, ”
Aikuwa sunsami abubakar agidan sun zauna sukasha hira sosai amma anty samha bataji dad’in yanda taga *hanna* tarame ba,”
Suna zaune su hud’u ana hira anty samh ne takalii *hanna* tace habibty kinrame dayawa meya sameki? ”
Hameeda ne tayi saurin kar6e zancen tace anty tsawa kanta damuwar wannan najeeb d’inne,”
Tamke rai anty tayi tace ke wato haryanzu baki fitarda wannan najeeb d’inba ko? ”
Abbakar ne yace A’a kyaleta ai ba’ayiwa soyayya haka,”
Hameeda ne tace hmm dan bakasan wanda yake sonta take masa wulakancii bane da sauriii anty samha tace waye? ”
Cikin zumud’ii hameeda tace anty wani sojane naji ance duk kasarnan bbu kamarsa kumafa tun ba yanzuba yake sonta tun tana y’ar k’arama itama shaidace akan hakan
Dan gidan sarkii ne ance wai yareemane, yawwa yaa abubakar shinefa yamaka babban aboki, abubakarbsake baki kawai yayi yana kallonta dan ya tabbatar cewa itace *hannan* yareema, ”
Zaroo ido😳 anty samha tayi tace badai yareema ba?”
Shidai kuwa inji hameeda, ”
Riqe baki anty samha tayi tace aina fad’a miki *hanna* cewa wa’yannan masu *bibiyarki* alkhairine Allah yatabbatar da wannan al’amarii, ba aminba *hanna* tace.” hameeda nr tasake cewa kuma baki kalli yanda family dinshi ke sonta kamar zasu cinyeta,”
Abubakar ne yace tabbas yareema na ganin jarabawa dan banta6a tunani akwai wanda yarima zaice yanso yasamu matsalaba, ”
Tabbas Allah shine mai d’aurawa bawansa duk wata jarabawa,”
*Hanna* bawai dan yareema yana d’an uwana ba A’a saidan inason fad’a miki gaskiya Allah yarima mutum ne wanda samun irinsa yayi wahala,”
Mutim ne daysan darajar dan adam mutum ne mai kare talakawa da dukiyarsu,”
Idan kika sameshi natabbata kinyi sa’a har karshen rayuwarki, ”
Ahqka sukayita bata shawara tashiga tad’ayan kunnen tafita tad’aya sai magrib tukunna abubakar ya maidasu gida.”

 

 

To be countinued

 

Ur’s
_Z33yyb3rw3r_

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by

© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

My first novel

_Wannan shafin nakune yan uwah ‘yan nijar, saudat nijar, nafii nijar_halima lawali nijar,”_Kai da duk wasu_yan nijar wannan shafin_ nakune,”
Nagode da_ BIBIYAYAR labarina da kuke yi.
Ina sonku kamar yadda kuke sona_ 😍😘

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply