Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 45


Bibiyata Akeyi 45
Viral

Page 45

*
Yau juma’ a baba yatashi da zazza6i sosai, ”
Hakanne yasa mama takira Abba ta shaida masa.”
Baid’auki tsawon lokaciba yashirya dan zuwa duba d’an uwannasa dan umma batamasan da tafiyar ba. ”
Sai bayan ya shirya ne yake shaida mata Aikuwa itama tace saita bishi,”
Nan ne yace shikuma bazasuyi tafiya subar yara mata kad’ai agida ba. ”
To ai saisu shirya mutafii,”
To tace sannan taje tafad’awa su *hanna* akan su shirya su tafii bauchi zuwa gobe dasu dawo. ”
Basu d’auki ko baba ne ba lpy ba sund’auka kawai tafiyace tataso.”
Shiryawa sukayi, ”
Sannan umma tace ma Abba ya tuntubii su jalal idandasu wce sai su biyosu abaya,”
Zuwa gobenne bazasu iya zamaba?”
Ai bawai hakan bane dan su dubo babansu ne, ”
Ok toh kiramin jalaluddeen d’in, takirashi Abba yashaida masa cewa su sun wuce bauchi duba baba idan zakuje kaida saleem da salman sai ku taho mukam muntafii,”
Toh ya amsawa Abba dashi, sukuma su Abba suka d’auki hanya, ”
K’arfe uku tamusu agarin bauchi, direct federal lowcost suka wuce gidan baba dasukaje sun samu jikin nasa da d’an saukii dan haryacii abincii,”
Abba ne yakaishi asitibitin AMSAD nan ake shaida masa kawai zazza6i ne sai asannan hankalin Abba ya kwanta, ”
Maganii suka rubuta masa awajen yaje yabiya kud’ii suka koma gida,
Suna komawa yasha maganii,”ya samu bacci kafin magrib daya tashi jikin yayi sauki dan har masallacin sukaje tareda Abba.” Aikuwa k’arfe 7 saigasu ya jalal sun iso, ”
Kuma bbu wanda suka fad’awa suna hanya,”
Wayar *hanna* ce tafara ringing tana dubawa taga labba dauka tayi sannan tace,”
Antyna nai takiran wyarki d’azu bata shiga. ”
Eh lokacin muna hanya ne,”
Hanyan ina? ”
Labba ta tambaya
Bauchi” tace atakaice, ”
Cikin k’in gaskanta zance tace bauchi kuma?”
Eh bauchi babane baida lafiya, ”
Subhanallah Allah yabashi lpy.”
Ameen *hanna* tace, ”
Sannan sukayi sallama.”
Labba na tashi bata wuce ko’ina ba sai shashin affan tana zuwa tace yaaa affan *hanna* tabar garii, ”
Garii ya tambaya eh tace ta je bauchi mahaifinta babu lpy,”.
Subhanallah yace Sannan yace Allah yabshi lpy da ameen Labba ta amsa, ”
Shiru tayi sannan tace ya affan yanzu yaya zamuyi?”
Shine kuma d’azu naje nagama shirya komai. ”
Nasan abunyi kinsandai kwana biyu ne kuma gobe kwana biyu zai ciki.”
Idan ya cika bamuda wani Excuse dole mudauki na annabawa yin hakan kuma yana nufin saka yaa yareema awani hali, ”
Shiru sukayi na ‘yan wasu sakanii,
Affan ne yayi Saurin tashi yace i got an idea,”
Wat idea ya affan? ”
Mubar komai kawai mu sauka agarin bauchi, zuwa 9am tomorro kowa ya hallara garin bauchi.” dat means munyi asarar komai nanan kenan? ”
Labba asarar kud’ii kikeji?”
Damuyi asarar damukesonyi yanzu ba gwara munyi asarar komaiba.”
Bari kiganii zan kira abdul muyi magana zuwa jimawa nasan zai kama mana kinjii, zomuje wajen yaa yareema. ”
Futa sukayi suka nufii shashin MG koda sukajee afalo suka sameshi, yana zauna a lokacin ssau 3 yana kiran layin amma taki dauka daga k’arshe ta danna busy,”
Duk yanda yakeson jin muryarta abinya faskara dan takii d’auka, shigowar su affan ne yasa shi ajiye wayan. ”
Waje suka samu suka zauna sannan affan yace yaaa yareema munason army d’inka guda talatin 30,”
Talatin mai zakuyi dasu ya fad’a yana had’e rai, ”
Yayaa idan baka bada way’annan army d’inba kuma kaima ka shirya muyi garin bauchi ba daga gobe,” you will loose her forever i mean it forever, ”
Kollonsu yayi kallonda fassarashi yakanyi wuya,”
Yaa yareema idan bakasan asamu matsala, duk abinda mukace kar ayi musu, ”
Kuje suna Waje sannan zanbasu order, kafin kufita,”
Yana fad’in haka ya lumshe idanuwansa, fita sukayi Aikuwa kafin su fita har yakira yagaya musu,”
Suna zuwa suka za6i sojoji talatin wanda ko wace k’asa sanda suka za6i biyar acikinta, ”
Adaren sojojin suka kama hanyar bauchi.” Sanda sukaga tashinsa sannan suka k’ara shiga shashinsa lokacin yana shirin fita sallar isha ganinsu yasa yatsaya yana sauraronsu, ”
Labba ne tace yaa munaso mudakai gobe da sassafe muwuce bauchi,”
Sai mubi morning flight,
Ok d’aga waya yayi zaiyi kira, ”
affan ne yace yaa yareema wazaka kira?”
Zankirane a shiryamun prvt jet ne kafin safiya, ”
No yaa yareema it has to be personal idan kayi wannan kiran duk k’asa zata d’auki zuwanka,”
Ko’iina za’a shirya maka tar6a mukuma ba haka mukeso ba, ”
Munfiso yakasance zuwan kanka kayii.”
Kallon affan yayi sannan yace kana nufin nashigawa, Governor da sarki gari batareda na sanar musu ba? ”
Eh yaya labba ta amshe,”
Har inde zakaje amatsayin MG to dole ka sanar amma wannan shigan zaka shigane amatsayin ka na mai neman aure,” ba amatsayinka na MG kokuma d’an sarkii ba iyakacii muda kai da zumuje, ”
U knw itz imposslbe bana tafiya da sojoji k’asa da goma hakan yana nufin na karya doka kuma kunsan ba abinda natsana kamar in karya doka,”
Ok tom amma yaya zuwa jimawa zumuje muyi booking, ”
Ok kuje kuyi nida sojoji 10 hadda Ahmed cikon na gomansu,”
Toh sukace sannaan suka fita danyin booking, ”
Zuwa k’arfe taran dare komai ya kammala,”
Sai a sannan yasamu lokacin kiran abdul yana d’aukaa yace ya buddy yakake? ”
Lpy klau ya bauchi?”
Bauchi klau,
Sanda suka gama gaisawa yace ”
Buddy akwai wani taimako nake nema,” Daga d’aya can bangaren abdul yace haba buddy yanzu dan zaka nemi abuu awajena saika kirashi da taimako? ”
Ka fad’an mun kawai ina jinka,”
Nan yakoro masa abunda yakeso, ”
Can abdul yad’an nisa yace buddy kasan yanayin wajennan fa zaiyi wuya ace ba’asamu wanda yakamashi ba,”
Affan ne yace ka k’o’karta buddy kasan ya yareema ne yakeson wajen, nan ya zayyano masa labari ai alokacin abdul yamike, ”
Yace dole ma wannan wajen yasamu barina fita,”
Saikusan 10:30 yqkirashi y shaida masa ansamu wajen, ”
Labba ne tayiwa ummii da kanwar ummii bayanin abunda zasujeyi nan tagama Had’a komai sannan taje daki.”
K’arfe biyar bayan sunyi sallah suka gama had’a komai,
Nan MG ya shiga yiwa ummii sallama,”
Albarka tasa masa sosai sannaan tamasa addu’a akan Allah yabashi abunda yaje nema,
Zuwa 7am sunsauka garin bauchin yakubu.”
A jameel guest palace suka sauka dashi da sojoji goma da affan da labba idan sunsami abunda sukeso aranar dasu koma”

 

 

Kiran hameeda labba tayi bayan tad’aga take tambayanta jikin baba cemata tayi jiki yayi sauki sosai dama zazza6i ne, ”
Nan take ce mata sis bamu fasa wannan shirin bafa yanzu gamu mun iso tun safe.”
Yanzu yaya kenan sis gashi nabar wannan aikan a kano, ”
Cewar hameeda.”
Ok yanzu yaya za’ayi? ”
Kisameni a jufatu zan wuce sai mu zabo toh tace sannaan sukayi sallama.”
Kiran amira tayi tace tazo tarakata bata barii *hanna* taganta ba tafuce suka had’u da amira bata wani tsaya yiwa amira Bayani ba suka wuce jufatu anan suka had’u da labba sukayi sayayyarsu sannaan suka juyo, ”
Sun koma gida tasamu anty maryam da anty maman amal sunzo,”
Kiran anty amira tayi sannan tamata bayanin komai, murna acikin anty kamar tazuba ruwa tasha, ”
Mama da umma suka kira nan ma aka koro musu bayanii,”
Umma da mamane suka harzuqa wana irin shashanci ne wannan keda labban kukeyi kwana biyu fa kuka bata kuma idan yau bata aminceba kenan kuna nufin ita tacii wannan karan, umma ne ta k’ar6e zancen sannaan tace aiko bata yarda yauba bbu wani kwana biyu a haka ma saita amince, ”
Hameeda ne tace ni yanzu ma ba wannan ba akan yanda za’ayi zuwa jimawa taje wajen,”
Zama taje inji umma, ”
In sha Allah idan taje duk wani fitina ya k’are ko zuciyar dutsi takeda shi saita amince ayau d’in nan in sha Allah.”
Ok toh Allah yayarda Cewar Mama yarinyarda agaban iyayensa ta budii baki tace batasonsa bansa akaba. ”
Ni inbanda abun so bama banga mai zanyi da ita ba,”
Yafita komai da komai nesa ba kusa ba. ”
Anty maman amal ne tace haba mama wannan wace irin magana ce, koda ace bata kaishi komai ba mace daraja ce da ita kuma ni aganina hakan da take yi kanta take kwatawa yanci.”
Yanzu burinmu kawai yau ta amince. ”
K’arfe uku na yamma *hanna* tafito awanka sanda tajira aka kira sallah sannaan tayi ta d’an shafe jikinta da turare,”
Wata arniyar arabian gown designer hameeda ta ajiye kusada *hanna* baki da hancii *hanna* tasake tana kallon rigar dan bakaramin kyau tayiba mata ba kai ba ita kadai ba duk wanda ya kalli rigan yasan ya had’u light pink ce rigar kalan da hanna ce mutuwarso, ”
Kisa muje anguwa hameeda tace ai abbu musu hanna tasa rigar dan tamata kyau,”
Kai sis a’iina kika saya wannan rigar? ”
Tayi masifar kyau,”
Kiyi light makeup mufita kawai hameeda tace bbu musu tayi light makeup daya k’ar6i face dinta, ”
Bata bata lokacii ba ta shirya rigar ta matukar karbanta,”
Takalmii hameeda ta ajiye mata farii mai kyau da kuma kuma d’an karamin veil shima fari soll. ”
Gyara gashin ta tayi yayi acucii mai kyau,”
Sannan tasa veil d’in tafito kamar wata balarabiya sakk, saidai batada haskensu. ”
Amira taganii tace beb yaushe kikazo?”
Yanzu nan taga shigansu irin d’aya da hameeda amma bata kawo komai ba.”
Fita sukayi zasu tafii, a lokacin mama da umma suka kirata, ”
Mama ne tace *hanna* kizama mai tausayi rayuwarki, sannan umma tace a kullum kisowa d’an uwanki abunda kikesowa kankii.”
Jikintane yayi sunyi nan sukayi musu sallama suka tashi suka fita suna fita hameeda taturawa labba taxt tace mata Suna hanya. ”
Ganin sun nufi GRA villa garden yasa *hanna* cewa ke mezamuyi kuma a villa garden?”
Amira madai tambayar dake ranta kenan amma tayi shiru,”
Ke kinfaya saurii ne kitsaya ki gani mana hameeda tace, ”
Suna isa alamu yagawadawa hameeda cewa sun iso dan motocii ne awajen dayawa irii daya kuma dukansu marsedeze benz ce,” guda daya ce taraba kala ita farasol ce kodaganan abun zai bada sha’awa, ”
Shiga sukayi dama already ansan dazuwansu ba’ataresuba suka shige,”
Tun daga waje waje akafara decorating da pink an white na flawers sai ratsin jaa, ”
Hameeda ce tafara ciran matane tana cewa su shiga intagram zata fara daukan live video yanzu,”
Takira matane samada ashirin nan amira taga itamafa baza’a barta abaya ba nan tafara kira itama tana cewa ayi joining. ”
Tun daga bakin wajen suka fara shooting live video a insta,”
Dan wajen bakaramin kyau yayiba kan su k’arasa Cikin wajen kowacce tasamu views samada talatin, ”
Dan yanda wajen ya tsaru bazaka iya kallo ka wuce ba shi yasa aka fara views nan likes yafara biyowa baya.”
Shiga wajen sukayi ainan kallo yakoma sama wani irin kyau waje yayi wanda fad’arsa bata lokacii ne ko shugaban k’asane zaizo wajen iya kacii. ” Suna shiga wajen bbu kowa sai flawers da aka jera tako ina, ”
Batasan lokacinda tak’arasa Cikin wajena tana k’are masa kallo ba, juyawa takeyi tako ina tana kallo.”
Jitayi kamar ana kallonta juyawa tayi kawai taga MG daga nesa yana tsaye ya hard’e hannuwansa yazuba mata ido, ”
Ganinsa yasa fara’ar fuskanta yakau ta tamke fuska kamar wanda bata ta6a dariya ba.”
Sake hannunsa yayi yafara takowa wajenda take, baya ta rungayi jikuma yana matsota sai jinta tayi kawai ta fad’a a kujera da6as,”
Sanda yamatso kusa sannan ya durqusa akan gwuiwowinsa yace, ”
Ina sonki,” Ina sonki, ”
Zanje ko ina na maimaita wannan kalmar zan fad’a alokacinda idamuwana suke arufe kuma zanfad’a alokacinda idamuwana suke abude zan fad’a a yayinda nake bacci,” kuma zan fad’a agaban kowa i will tell d hole world dat i love u.”
Inasonki sosai, ”
Akanki nafara sanin menene so kuma akanki nakeson k’are so, bana fatan ganin ranar da zan futawa wata mace wannan kalmar ba.”
I love u plz marry me I promise to make u d happiest women on earth. ”
I promise to be honest, to be loyal, to be Your frnd ur brother,
I promise to Luv u forever nd am gonna be the best husband ever,”
Ciro dan karamin kit d’in dake aljihunsa yayi, diamond ring d’inne ya bayyana, sai kyqlli yakeyi, ”
Akanki yace,
Will u marry me?”
Shiru tayi tana kallonsa. ”
Ranga6ar da kai yayi sannan yace plz marry me.”
Girgiza masa kai tayi tatashi tana niyyar fucewa labba ce tayi Saurin k’arasowa wajen, da sauri itama ta zube gwuiwowinta, wanda hakan sanda yasa *hanna* riqe baki ahankali kamar me shirin yin kuka tace ”
Labba plz kitashi,
Girgiza kai tayi tace nop am nilling here untill u agreed to marry my brother,”
Hanna plz marry him, ”
U’r gonna be the luckies Girl ever,”
An I promise u b d best 6ta inlaw plz👏ta had’e hannayanta, ”
Girgiza kai *hanna* tahau yi alamun fa bata amince ba.”
Can kuma su hameeda, sai dabii aketa bugawa a insta, ”
Anty hindu da take Can kano itama sai kallo takeyi ji takeyi kamar ta futo ta wayan ta wankawa *hanna* marii baresu anty samha da bakin Cikin *hanna* yacikata.”
Amirace taqaraso wajen amma bataje dab suba dalilin d’aukanda takeyi, ahankali kamar rad’a tace beb say yes, ya tayi kamar bata jiba kuma sarai tajita,
Affan ne yak’araso wajen gwiwansa d’aya yasa ak’asa yace plz marry him,
I promise to be d best brother inlaw, plz say yes shiru tayi ta tsaya tana kallonsu jikinta yafara yin sanyii, ”
Amma fa gaskiya bazata iya ba.”
Ana haka captain Ahmad ma ya fito, ”
Yasa kafafunsa akasa yace Plz say yes, wasu zafafan hawayene suka fito mata ta runtse idanuwanta,”
Ahaka da d’ai-d’ai sojojin suga runga fitowa sun fito kowanne da wandon kakin soja ajikinsa da jan polo abayan anrubuta, plz say yes da fariin rubutu, sukuwa amira labba da hameeda, jan gown sukasa da bakin d’an kwali. ”
Sai Affan shima jan t-shirt da bakin wandone ajikina.”
Wayan labba ne tad’auki k’ara tana dubawa taga taga anty afeeya, a hans free tasa, tana d’auka tace plz say yes dear, ”
Aikuwa Can halima takira wayan itama ana d’auka abinda ta fad’a kenan.”
Can wayan MG ta d’auka itama yana dubawa yaga ummii d’agawa yayi alokacin tace, ”
Ahankali tace habiby tell her dat am gonna be d best n sweet mother inlaw that is hardest to find.”
D’agowa yayi ya kalleta alamun taji mai ummii tace. ”
Kuka ne yakwace mata dasauri tasa hannuwanta biyu ta rufe bakinta,”
Kamar wanda suka Had’a baki dashi da soldiers d’in, dasu affan da yan Cikin wayoyin sukace, ”
Zamu zame miki d best family ever,”
Wayan amira da hameeda ne suka fara ringiing kamar me mutane daban daban sai kira a keyi daga masu cewa ta amince kai kusan duk wanda yakira hakane. ”
Hameeda ne tace hava beb say yes mana,”
Runtse idanuwanta tayi sannan ta miqa masa hannunta ttsayawa yayi kallonta,
Labba ce tace *hanna* baki amsa bafa, ”
D’aga kanta tayi ahankali tace na amince,”
Cikin murna yasamat zobben ahannunta data miqo masa, ai yanasa zobben wajen ya d’auki ihu. ”

 

 

_Yaukam abar *hanna* tasha ruwa danta amince da auren MG_ _z33yyb3rw3r ma tasha ruwa_

_Saura kuma naji nace Page yayi kad’an sai nayi suburbud’a_😜

To be continued

 

Ur’s
Z33yyb3rw3r
*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by

© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply