Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 5


Bibiyata Akeyi 5
Viral

Page 5

*
Baki tasake tana kallonsa jitayi yace
Rufe bakin,
Saurin rufe bakin tayi sannan takauda kai gefe,
Tareda jan dan siririn tsaki ahankali tafara magana damme dakabugeni a school,
Kuma kabini abaya haryanda nazo kuma kasake bibiyata
Tsaki takara ja
Gani tayi yazuba mata idoh kaman wani wanda yakeson gano wani abu atattare da itah, kara tamke rai tayi cikin tsafin murya tace mekuma kake kallo,
Wani abu nakeson ganowa shin wae kece kuwa ta dazun nan kallon gefe da gefenta yayi wadda hakan yasata itama bin yadda ya kalla da kallo

Kai bake bace,
rike havansa yayi cikin zolaya yace oh namanta ashe yanxu kinyi makeup ne wani kololon bakin cikine yatokareta,
Wato nufinsa dazu batayi kyau ba kome,
Gyaran murya yayi tareda cewa idan kagama shirmenka saikaban hanya nawuce,
Sosa kyeyansa yahauyi, yayah bafah shirme nakayi ba koma meye nidai bani hanya *hanna* wanda kunya tabi tacikata jin kiran mijin anty da yaya Wato shine kaninnasa Wato ba ita yabiyo ba oh sh*t tace tareda dan dukan goshinta da tafin hannunta, meyasa na aikata haka wayyo yanxu shikenan zaidauka tunaninsa nakeyi tafada acikin ranta,

Saurin juyawa tayi tashige daki, murmushi yayi sannan yafurta,
She’s amazing, ahankali yadda yah mahmood bazaijiyoshiba, abinda bai saniba shine tun tsayuwarsu yake kare musu kallo tass, daya Bayan daya. idankagama saikawuce mushiga cewar yah mahmood, Sosa kansa yayi sannan yashiga da sallama, antyne tafuto cikin fara’a tanamasa barka, yaude naga najeeb, dariya yayi sannan yadan waiga ko zaiga ta inda zata bullo amma shiru, yaya mahmood dake zaune gefensa yagane wanda yake nema dafashi yayi cikin sauri yajuyo daga masa gira yayi, mekake nema, bbu kawae inaduba yanayin gidanne ow kawae ya mahmood yace danyaga rainin hankalin najeeb yawuce yanda yake tsammani,

Waye najeeb??????
NAJEEB
najeeb kanin mijin antyne wanda yakasance shine autansu,
Su bakwae ne awajan mahaifinsu , iyayensu asalin yan bauchi ne wanda yanxu hakama anan suke zama babansu yarike mukamai da yawa a high court,
Sanda yakai matsayin Grand cady sannan yayi ritaya, matarshi tafarko itace hadiza, hadiza irin mutanan ne masu masifa,
Amma kuma tanada kirki sosai dasanin darajar dan adam, yaranta hudu da alhaji masa’ud babbar yarsu itace ikilma wanda yanxu tanada aure da yara shida sai aminu wanda shima yaransa hudu dakuma halima wacce ke aure acikin garin bauchi da yara shida itama, awajan haihuwar salima ne Allah yamata rasuwa, tarasu tabar yarta kyakkyawa maikama da ita, alhaji mas’ud yayi kuka narashin, mata mai nagarta, daga baya yafawwalawa Allah komai, yarungumi yayansa hudu databari hannu bibiyu, yaki jinin kallonsu cikin bacin rai,

Ana haka Allah yakawo wani wani justice, daga maiduguri, asalunsu shuwane dayarnsa mata da maza, lura yayida alhaji mas’ud baitaba Gani yayi maganar matarsa ba, adah yayi tunani koh danbasu saba sosai bane Amma yanxu abin yasha bambam dan wata rana yakirashi akan yazo gida yasameshi dan akwae wasu takardunda yakeso yazo yakarba yaje office yayi aiki akansu, sanda yakara kusan, hour biyu akan yadda ya umurceshi yazo, Bayan ya isoneh yake tambayrsa mayya zaunar dashi nan yake shaida masa cewa yatsaya shirya yaransane tambayarsa yayi ina matarsa nan yake shaida masa Ai Allah yamata rasuwa, hakuri yabashi sannan yace masa zama bbu mata banasa bane, yanemi wata ya aura domin yaransa, shaida masa yayi yanatsoron ya auro wanda zata musgunawa marayun yayansa neh shiyasa don yanxu samin mata tagari yayi karanci.

Shiru justice yayi wani tunani sannan yayi gyaran murya yace, to Ai bakazauna hakaba, gayata nan nabaka dan inada tabbacin baxata musgunawa yarankaba, amma kaje kayi tunani kafin kayanke hukunci, shiru yayi sannan yamasa godiya yatafi,
Bayan kwana biyu ya yanke hukuncin amincewa da auran, amma kuma akwae fargaba aransa don baisan wani irinzama dasuyiba Bayan haka gata dangin shuwa kuma masuji da dukiya da mulki amma kuma bazai iya duban fuskan justice yace bayason auran yarsaba, zuwa yayi yashaida masa ya amince, wanda tuntuni ita ba’asamu matsala tawajan tava danta kasance mai biyayya ga iyayenta, dangin mahaifiyarta ne suka fara magana akan za’adauki karamar yarinya akaita bauta wajan yara, dan wannan auren bautane, toshe kunnuwanta tayi dan ita tansan mijinta kuma tana respecting duk wani wish nasa. cikin kwanciyar hankali yaturo magabatansa akayanke rana wanda suma danginsa bakarin farin ciki sukayiba ganin shidakansa yace sujemasa tambaya, dansunyi akan yayi aure harsun gaji, andaura aure ba’ayi wani shagaliba walima kawae akayi akakai tadakinta, dafarko yayi zaton samun matsala daga wajanta amma hakan bata faruba dan tana kula da yaransa kamar ita ta haifesu, dalilin dayasa yadauko salima daga gun mahaifiyarsa kenan yadamka mata

ba’a dade dayin aurenba ciki ya bullo tahaifi yarta fara sol mekamada mahaifinta amma hasken mamanta, itada kanta tabukaci asawa yarta hadiza bakaramin dadi yajiba, Bayan tayaye halima wacce suke kira da maamaa ta haifi danta mahmood shima kammannin babansa sak sanda tadau shekaru kafinnan ta haifi najeeb wanda shikuma bbu abinda yabaro namahaifiyarsu sai ma ince yaso yafita kyau, ammashi kalan babansa yadauko dan bakine shi daganan bata sake haihuwa ba nan duk gidan suka daukiso suka daurawa najeeb tundaga kan iyayen har yayun bawanda yakeson laipyn autansu,

Najeeb dan kimanin shekaru ashirin da shida kykyawane baki yanada tsayi amma ba sosaiba yayi karatunshi tundaga secoundry har zuwa doctarin deegree dinshi akasar waje wanda yanxu dawowarsa kenan daga can kasar yayi gam da katar da zinariyarshi😍😍

Back to labari tashi anty tayi tanufii dining sannan tamusu Iso karasawa sukayi dukkansu kowa yakama kujera yazauna kwala mata kira anty tayi kan tafuto itada amal suci abinci sannan tadauko wa uncle dinsu yaganshi,

Futowa tayi daukeda bashir akafadanta sannan dayan hannun yana rikeda amal zuba mata idanuwa yayi tundaga nesa yakasa daukewa jiyayi an dafashi……..

Ur’s
Z33yyb3rw3r

BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writing by
Zaynab Bawa (z33iiyyb3rw3r)

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply