Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 51


Bibiyata Akeyi 51
Viral

Page 51

*
Shirye shiryen bikine yafara kankama daga kowanne bangare,”
Kokad’an yanzu su *hanna* bbu zama yau Suna chan gobe Suna chan, ”
Koda ita bamai yawan k’awaye bane amma tanashan mamakin irin mutanen da amira ke gayyata takeyi,”
Acikin week d’in hameeda tatafi kano dan itama akwai abunda takeso tayi acahn d’in, kuma baza’a rasa mutanen da zata gayyata ba. ”
Acikin satin su amira da *hanna* akayi resuming skull,”
Alokacin abubuwa sukayi musu zafii,
Yanda abun yazo dasauki ma dake IT zasu tafii, ”
Kuma *hanna* komai na IT d’inta agarin bauchi tacika,”
A accnt d’in da yabada atm su amira suka cire kud’ii mai yawan gaske, aka fidda anko masu kyau da tsada,”
Kala uku-uku, kowacce k’awa aika mata da nata akayi,”
Aikuwa murna wajen k’awayen ba’a tonawa, ”
Sai satiin biki za’a kawo lefe,”
Ana biki sauran satii biyu, ”
Kawai ranar saiga ummii ta aiko larabawa guda biyu masu gyaran jiki,”
Abun yabawa su mama da Ammah mamaki, ” Dan aganinsu su yakamata su nemi mai gyara musu yarinya sai ga, mahaifiyar ango nan taturo,”
Ba’ad’auki tsawon lokacii ba aka ware musu d’aki ashashin Ammah, ”
Nan da nan suka fara gyarata ba’a barin kowa yashiga ganinta ko MG ma sun hanata d’aukan wayqrsa duk yanda yaso kiranta akashe kullum wayanta, abun ba k’aramun damunsa yayi ba,” yaso yazo amma shima nashi hidin dumin ya masa yawa, ”
Har IV na bikin su amira ne suke rabawa hameeda ta dawo tare suke fita,”
Idan sunfita tun 11 basu dawowa sai dap magrib, ”
Yanzu gabaki d’aya amira ta dawo gidansu *hanna* dazama,”
Dayake aabubuwa sunyi yawa,”
Cikin kwana biyar *hanna* tadawo itada larabawan babbancin kad’anne dan bakaramin kyau tayiba, ”
Dakyar su amira ke samun ganinta sau biyu ko uku arana, da abin yafara yawa suka nemii mama ta acanja musu gida,”
Da farko mama tak’ii amma daga baya umma da amma suka ce su kansu amaren zasufii sakewa, har indai suka samu privacy, ”
Gidan Anty maman amal suka koma dayake ita ma ta koma gida tun da bikin ya matso kuma mijinta yayi tafiya,”
Sosai sukaji dad’in gidan dan yanzu Suna d’an samun sakewa, ita kanta *hanna* yanzu tafijin dad’i Suna tareda su amira yanzu ana barinsu su zauna waje d’aya tunda gidan a Rufe yake,”
Ko abu *hanna* taruqe sai yayi sassanyar kamshinda takeyi balle wajanda ta zauna, ko tawuce, ”
Itada hafsat hameeda amira ne sai hafsat da kuma way’annan larabawan,”
Abida da Aisha, ”
D’aya matar tad’an manyanta d’aya kuma matashiyace dabazata wuce shekaru 30 ba.”
Sa’ii Sa’ii umma na mata aika. ”

Su labba kuwa iyayen biki ko ganuwa ba’ayi duk wani hidin dimu itace akan gaba,
Hatta anko da suka cire ma sanda suka tura mata taganii sannan suka fitar.” da hameeda zata tafii sai tatafii mata dashi. ”
Suma chan sunyi nasu anko dun,”
Duk da cewa nasu classical ne, ”
Dan swiss k’arshen tsada sukayi order d’insa,”
Suna son sufita daban Suna shiga agane cewa dangin ango sunzo wannan na ranar diner kenan, ”
Sauran ranakun kuwa shirin da sukayi saisu Kansu dan bamai fad’uwa bane.”
Idan kaga intisar zakaceq ba ita bane,”
Dan ta kwantarda hankalinta, kokad’an yanzu bbu damuwar komai atattare da ita, ”
TA ware abunta shiirye shiryen biki kawai takeyi, itama barnarda kud’ii takeyi wajen bikin, kilishi har mamakinta takeyi,”
Hakanne yasa takirata d’aki zaunarda ita tayi ta dafa kafad’unta, sannan tace”
Intee kin daina son yareema ne?? ”
Girgiza kai tayi tace haba umma ya kike wannan zancen kinsan bazan ta6a daina sonsa ba.”
Kilishi ne ta nisa sannan tace mai hakan yake nufii kenan? ”
Kinfasa burinki na auransa?”
Nan ma Girgiza kai tayi tace wallhy umma ina nan akan baka na, bazan ta6a hutawa ba harsaina aureshi. ”
Nisawa umma tak’arayi tace tom wannan wani irin rawar k’afa kikeyi a auransa?”
Intisar ne tace oh umma duk way’annan tambayoyi ki ajiyesu amsosunsu sunqnan zuwa. ”
Tana fad’in haka tatashi tafice tabar kilishi da zullumi Tunani takeyi to menene yasa ta farin ciki haka bayan tana sonsa?”
Haka dai kawai tayi hakuri da way’annan tambayoyi. ”
Gashi wani k’arin abun haushin ma bai wuce yanda ‘ya’yanta suke narkarda naira akan wannan bikin ba.”
Da intisar taso ya aura. ”

*Ina labarinn najeeb*
====
Najeeb tun lokacin dayaga *hanna* ta amince da auran MG yazama k’aramin mahaukacii yabar suma tayi wani buzu buzu a kullum da ciwon son *hanna* yake kwana a kullum yatuna abun da yamata laifin kansa yake kallo,”.
Yayi kuka har yagajii kamar ba babban saurayi ba ya fawwalawa Allah komai, dan yanzu magana ma wahala take masa,”
Kokad’an bai shiga harkokin jama’a yafii ganewa kullum yana d’akii dan yanzu ya tabbatar *hanna* tamasa nisa, ”

MG ga baki d’aya yau yanajin sa kamar me, yatashi da sonjin muryar *hanna* Gashi ya kira wayarta a kashe.”
Massage yashiga rubutawa kamar duk wani lokacin da ya kira yaji wayan akashe sai yatura massage, ”
Massages d’insa sunfii ak’irga acikin wayar amma ita batsanma ya turo ba.”
*Hanna* ce zaune afalo su hameeda sun fita, itakuma zaman kad’aici ya isheta, kawai ta tsuncii kanta da son kunna wayarta, ”
Jakarta ta nufa ta d’auko wayan, tayi plugging din cherger sannan ta kunna wayan, sanda tagama ta kunnu tafara kallon Massages d’in MG atake tajii wani tausayinsa yakamata,”
Danna numb d’insa tayi zata kira, haryana shaurin yin ringing tayi saurin katsewa, ”
Aikuwa kamar yasan ta kunna a tym d’in yasake trying numb d’in sai gashi yashiga,”
Kallon phn d’in tatsaya yi har yakatse bata d’aga ba sanda, wani call d’in yasake shigowa ne ta d’aga,
Ajiyar zuciya yasauke wanda har cikin waya sanda tajii, ”
Cikin worried voice yace, sweety I miss u,”
Batasan lokacin da bakinta ya furta I miss u mor,,,,, saurin Rufe bakinta tayi bata k’arasa ba.”
Dad’ii yaji jin shima tayi missing d’insa. ”
Sweety zanzo yau da daddare,”
Rufe baki tayi tace no karkazo, ”
Meyasa?” yatambaya, ”
Bazasu bari kaganni ba.”
Nidai zanzo kisan yanda zakiyi yana fad’in haka ya kashe wayar baijira cewarta ba. ”
K’arfe shida su amira suka dawo itada hameeda da kuma hafsat.”
Suna zuwa dukansu suka zube jikin *hanna* ihuu tasa tana turesu ni da’allah menene hakan kutashi, ”
Hameeda ce ta d’ago tace beb kinga lefenki?”
Wallhy ko atarihi banta6a ji ko ganin wanda yasamu lefe kamarkiba, amirace ta nisa tace beb akwatunan talatin kamar amafarki, ”
Beb duk kayan ciki kyawunsu bayi fad’uwa, beb ko rabin akwatin ba’@bude ba kowa yagaji,”
Hafsat ce tace kud’in kan akwatii kinsan nawane? ”
Rufe mata baki tayi tace banson jii,”
Ganin zasu dameta da surutu ga lokacin magrib yayi yasata tashi tabarsu kamar wanda sukayi gamoo, ”
Sallah tayi tazauna akan pray mat tana jiran ayi sallan isha azao akwa6a mata abun ajikinta,”
Wayanta ce tafara ringing dan tunda ta kunna bata kashe ba, tana dubawa taga MG ne. ”
Tana d’auka yace mata yana waje,”
Futa tayi ta na sand’a har tafice agarden taganshi yana zaune kamar wanda yadad’e da zuwa, ”
Kallon ta yakeyi tun daga nesa, da badan zuciyoyinsu na manne da juna ba da yayi musu cewa ba ita bane.”
Har takaraso bai saniba kamshinta ne yasanar dashi isowarsa, ”
Sallama tayi ta gaidashi ya amsa, sannan yace sweety kinyi kyau sunkuyar da kai tayi tana wasa da yatsunta,” sanda sukafii mintii goma bbu wanda yasake cewa komai, kallonta kawai yake yi, ” sannan yatashi yace natafii fligt d’ina 7:30 zai tashi akano nakeso nayi sallar isha, bud’e baki tayi tace dama kawai kazo, murmushi yayi sannan yace ganinki aiba kawai bane,”
Ahaka taraashi har bakin gate dake bai Shigo da mota ba leqawa tayi taga gidan zagaye da sojoji, ”
Bud’e baki tayi tana kallonsu,”
Muryarsace ta dawo da ita kina mamaki ne? ”
Tun randa aka kawoki gidannan suke zagaye dake, yana fad’in haka yajuya,”
itama juyawa tayi da gudu ta shige gida, ”
Nan sojojin suka k’arkame kofa,”
Juyawa tayi tana mamaki wato shiyasa kai tsaye yasan yanda take. ”
Tana shiga bata samu kowaba tashige tayi sallah sannan akazo aka fara.”
Yau takasance gobe za’a fara event duk wani shirye shirye anankai har makeup artist anrigada an shirya su yanda komai zai tafii dai-dai washe gari ya tashi ranar laraba ranrda za’ayi kamu tun safe aka fara shirye shirye. ”

 

To be countinued

 

 

Ur’s
Z33yyb3rw3r

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by

© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

*_If a friendship last longer than 7 year’s, u are not just a frnd u r family, ” just like we are *MAIMUNAT* *_this whole Page is dedicated to u my frnd,”_*
*_Wsh u safe journey y’an kano zasuyi missing d’inki_*😉

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply