Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 53


Bibiyata Akeyi 53
Viral

Page 53

*
Da gudu tashige gida,”
Girgiza kai MG kawai yayi yana mamakin yanda gudu bayi mata wahala, ”
Sanda yaga shigrwarta sannan yajuya suka wuce tana shiga tazube akan gado dan ba k’aramin gajiya tayiba ga takalmin kafanta asalin hill ne.”
Gabaki d’aya da takalminta ta zube, sanda hafsat tashigo kafin tacire mata. ”
Zqma tayi kusa da ita,”
Ita kuma *hanna* tayi lying a bed ta lumshe idanuwanta,”
Hafsat ce tata 6ata tace, sis, bata d’ago ba kuma bata bud’e idanuwanta ba tace uhumm, ” tak’ara ce kekam sis kinyi sa’a wallhy duk wani abunda ake buk’ata awajen namiji, mijinki nadashi,”
Umm kawai tace dan batasan amsar da zata bata ba. ”
Hafsat ce tak’ara cewa,”
Ni ma kitayani addu’a Allah yabani miji mai kyau Koda kuwa kwatan kwacin na yareema ne. ”
Sai alokacin *hanna* ta bud’e idanuwanta ta tashi ta zauna sannan ta kamo duka hannuwanta biyu tace”
Adda Hafsat ina labarinn mas’udd?” da kike neman wani kuma, ”
Hafsat ne tace hmmm kibar maganan mas’udd kedai kawai kitayani addu’a,”
Nisawa *hanna* tayi sannan tace tom amma d’azu aina ganki da captain bilal awajen kamu duk da cewa bansan mai kuke cewa ba amma abun yamin kaman akwai wani abuu. ”
Nisawa Hafsat tayi sannan tace eyyerr nima naso hakan amma bahakan bane.”
Wai yau bamu futo da wurii bane shine yak’ar6i phn numb d’ina akan Idan munshirya sai mu fad’a musu. ”
Umm *hanna* tace kawai dan bawai ta yadda dalilin hakanne yasa yak’ar6a ba,
Akwai wani dalilinsa daban,”
Jin ana kiran sallah yasa su tashi, toilet *hanna* taje ta d’auro alwala sannan tagabatar da sallan magrib sannan ta zauna akan sallayan sanda tajira akayi isha’ii sannan ta gabatar da isha’ii da shaf’ii da wutiirii, sannan tayi haramar kwanciya, phn d’inta ne tafara ringing dai-dai lokacin ” ko bata duba ba tasan waye zaikirata a dai-dai wannan lokacin,”
Nad’e pray mat d’in tayi sannan ta nufii wayan da niyyar d’auka, ”
Kafin ta isah ta katse,”
K’ara kira akayi tana isa tad’auki wayan amma ga mamakinta ba numb d’in MG bane kamar yanda tayi zato,”
sanda ta isa bed ta zauna sannan tayi picking, ”
Sallama tayi amma shiru tak’arayin sallama ba’a amsa ba, shiru akayi na tsowon 4 minute ita bata kashe ba kuma ba’ayi magana ba tun daga sallamarta kuma bata sake cewa komai ba sanda yacika 5 minute tayi niyyar ajiyewa tajii ance plz karki ajiye dannasan kina shirin yin hakan. ”
Runtse idanuwanta tayi jin yadda muryan ta daketa,”
Ko mafarki bazata manta wannan muryan ba. ”
Gabanta ne yahau fad’uwa da k’arfii kamar wanda k’irjinta zai fashe,”
Shiru tayi takasa, ”
Tacikin wayan aka k’ara cewa nasan kina jina k’inki amsani ne.”
Cikin rawar murya *hanna* tace mai yasa kakira? ”
Ta Cikin wayar akace sabilida in jaddad miki cewa haryanzu inasonki?”
Cikin murya mai kamada t kuka tace najeeb kasan kuwa mai kake fad’a? ”
Cikin wannan week d’inne fa aurena,”
Cikin rashin damuwa da abun da yake cewa da d’an tsawa-tsawa yace nasanii *hanna* nasanii basai kinfad’a mun zaki aurii d most richest hansome young man ba, ”
Wasu siraran hawayenen suka fara bin fuskarta tasan tabbas mutane dayawa zasuyii tunanin cewa dan kud’ii ko kyau ko kuma mulki ko sarauta na MG zata aure shi, ita a yanda takejii ko sonsa bbu azuciyarta har yanzu.”
Amma hakanma bata fita awajen al’umma ba, ”
Hmmm *hanna* har indai zaki ce sai kinyiwa mutane dai-dai to har abada bazaki fita ba.”
Kukane ya kufce mata tayi saurin rufe bakinta, ”
Cigaba yayi da cewa,”
Tabbas nasan yanzu *hanna* bakya sona kinsamu wanda yafini, ”
Nasan namiki laipy amma *hanna* nabaki hakurii a lokacin da nake neman afuwanki,”
Yakamata kiyafemin amma kika k’i har wata kaddarar tazo ta ratsa ta tsakaninu, ”
*Hanna* maiyasa? maiyasa kika ki yarda da tuba ta a lokacin daya kamata?”
Maiyasa zaki maida rayuwarmu hell? ”
Kinsan mai kike shirinyi kuwa Kinsan cewa daga yanzu Idan kikayi aure munrabu kenan har abada.”
Wai meyasa Kafin ki amince bakiyi tunanin yanda rayuwarmu zata kasance ba.” *Hanna* itadai kuka kawai takeyi dan batada bakin cewa komai, ”
Ko ayanzu tasan tanason najeeb amma kuma ba kaman sonda take masa da ba.”
Sannan kuma ita batason MG amma tana kallon girmansa da kuma kumarsa had’e da darajarsa, ”
Ko babu komai mutumin dayake sonka ba abun wulakantawa bane.”
Zamanda tayi ta MG duk da shi bamai fidda abun cikinsa bane amma ta tabbatar da irin sanda yake mata. ”
Wanda Idan za’a kasashi goma zaiyi wuya najeeb ya d’auki uku.”
Irin abubuwan da take masa Koda najeeb da bai kaishi komai ba tasan ba d’auka zaiyi ba. ”
Akullum yakan k’askantarda da kansa Idan yana tare da ita duk wani mulkii da sarauta yakan saukesu.”
Muryar najeeb ne takatse ta daga tunanin data lula. ”
Yace *hanna* nasan kinyii nisa,”
Allah yabada zaman lpy yana fad’in haka ya katse wayar, ”
Yana katsewa *hanna* tazauna tana kuka kamar ranta zaifita.”
Ahaka har k’arfe tara na dare yayi tana kuka fuskanta duk ya kumbura. ”
Sunyi lu6u-lu6u,”
Muryarta har ya dashe. ”
Har dushu dushu take ganii ga wani irin ciwon kai daya daya rufeta.”
Jitakeyi gaba ki d’aya ta tsani auran.”

Ana haka anty maman amal tashigo tazo kawo mata aika ta ganta cikin wannan halin.”
Zama tayi tana tambayanta maiyasameta?”
Shiru tayi batace komai ba, ”
Sanda ta rarrasheta tukunna cikin kuka tace,”
Anty wallhy nafasa auran ni bana sonsa. ”
Duk da ran anty ya6aci tace, mai kuma yayi zafii *hanna* saura kwana uku ne fa d’aurin aurenki.”
Eh anty dan girman Allah kitaimakamin wallhy nafasa auren,”
Cikin rarrashi anty tace, *hanna* kinason maida mahaifan mu k’ananun mutane kenan.”
Tayaya kike tunanin cewa zasu sami iyayensa suce anfasa aure? ”
Kinsan cewa mutumcinsu ne zai zube.”
Girgiza kai *hanna* tafarayi tace wallhy anty jinakeyi idannayi aurennan kamar wanda zan mutu.”
Anty dan Allah kitaimakeni wallhy zuciyana k’unci takemun.”
Duk wani rarrashin da anty tasan zata mata tayi amma *hanna* firr tak’ii.”
Har ranta yafara 6acii, ”
Cikin hasala anty tace tom Idan kikace bakya sonsa wakike tunanin zaki aura?”
Share hawayenta tayi tace,”
Anty najeeb, najeeb zan aura, ”
Wasu tagwayen marii Anty ta d’auketa dasu ta kowani bangare lokacii d’aya yatsunta yafuto atafin fuskanta.”
Kuka *hanna* tak’ara fashewa dashi Jin zafinn marin, ”
Cikin masifa Anty tace dan ubanki to najeeb d’in da kika nacewa an dad’e dayi masa mata.”
Tun kafin kisan zaki amince da auren MG iyayensa suka za6a masa mata. ”
Tun lokacin da kuka samu sa6ani basu bari kun dai-dai ta ba suka nema masa mata.”
Kuma yamusu biyayya ya amince amma ke dayake banza ce marar tarbiya kika nace masa. ”
Naki za6in iyayen kuma kika nuna ke basu isa dakeba.”
*Hanna* gaki ga duniya kije ki har indai maganar iyayenki ne bazaki bi ba, ”
To wallhy kin had’u da Ganin jarabawa a rayuwarki.”
Tana fad’in haka tatashi tafice daga d’akin ko aikan data kawo mata bata samu ta bata ba. ”
Tana fita ta wuce gida dama tana driven da kanta.”
Gida kawai tawuce. ”
Tana tafiya tana tunanin halii irinna *hanna* shegen taurin kai kamar y’ar mayu.”
Ita kuwa *hanna* kulle d’akin ta tayi tacii kukanta, ”
Wato najeeb yakirata ne dan ya ruguzamata d’an farin cikin data samu tashiga kwana 2, shiyanacan aure ake shirin yi masa amma tunani yakeyi ta yaudareshii.”
Kuka ta k’ara fashewa dashi ga wani irin rad’ad’ii da zogii da fuskanta yake mata tashi d’aya zazza6i ya rufeta. ”
Gashi ta kulle k’ofan da key tanajii su amira Suna ta bugawa amma jikinta yamata nauyi bazata iya tashi ba.”
MG yayita kiran wayar ta amma bata iya d’agawa ba.”
Sai yabar abun a gajiya kawai yace yanaga tayi bacci.”
Sai k’arfe shida *hanna* tatashi gabaki d’aya fuskanta ta kumbura dan kusan kwana tayi tana kuka sai a lokacin tayi sallah. ”
Bayan ta idar tatashi ta bud’e kofa.”
Bata dad’e da bud’ewa ba su amira suka Shigo ganinta Ahaka yasa sukayi saurin k’arasawa Suna tambayanta maiyafaru? ”
Kawai ce musu tayi ta kwana da zazza6i ne,”
Ahaka sukayi ta tausaya mata harsuna mata fad’an rashin kiransu da batayi ba kuma sunzo k’ofa a arufe. ”
Ahaka sukayi ta janta d tad’ii dan bbu yanda basuyi tasha magani ba tak’ii.” K’arfe had’u suka shirya zuwa family and friend MG bazai samu hallara ba dashi har ya wuce.”
Ahaka tayi kyau sosai amma kowa yaganta saiya fahimcii cewa tana tattare da damuwa.” shima a *zaranda hotel* akayi.”
Abu yayi kyau sosai bayan angama antafii,
Labba taturawa MG pics d’in yana kallo ya gano cewa Akwai abun da yake damunta ko shiyasa yayita kiran wayarta ba’a d’aukaba,”
Amma yayanke shawarar kiranta yajii komenen yake damunta. ”
Ba abunda yadamu *hanna* kamar rashin ganin Anty dabatayi ba awajen event d’in tabbas tasan ta 6ata mata rai.”
Hakanne yak’ara mata wata damuwar. ”
Bayan sun dawo gida ko hutawa batayi ba wayanta yafara ringing tana dubawq taga MG bata ja lokacii ba ta d’auka dan tasan tun jiya yake nemanta.”

 

To be countinued

 

Ur’s
*Z33yyb3rw3r*
[10/4, 7:23 PM] ‪+234 816 114 6563‬: *BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by

© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply