Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 56


Bibiyata Akeyi 56
Viral

Page 56

*
Abinda yatokarewa MG kirjii samada shekara goma, ”
Sai alokacin da yajii and’aura aurensa da *hanna* kafin yajii abin ya fad’a masa sai wani irin sanyii yaringa jii zuciyarsa namasa,”
Fara’a kawai yakeyi bakinsa kamar gonar auduga, ”
Sai gaisawa da y’an uwa da abokan arziki yakeyi tako ina,”
Yayinda ita kuwa *hanna* tun lokacin da taga 11:30 dai-dai yayi ga wani irin fad’uwar gaba dake damunta tasan cewa aikin gama yarigada yagama, ”
Kawai ta tsincii kanta da hawaye dan ko k’arfin kukan batadashi dake ta dad’e tanayi.”
Kuma tanajii ana tad’ii ta window cewa k’arfe d’aya bayan anyii reception zasu kama hanya.”
Cikin ranta tanajin wani zafii da rad’ad’ii sai kace wanda suka gajii da ita zasu bada ita k’arfe d’aya. ”
Ahaka ta zauna bbu yanda Ammah batayi da ita tayi wanka ba Amma firr tak’ii yii babu irin lallashin da batayi mata ba Amma tak’ii,”
Ganin lokacii yawuce yasa Amma taje tafad’awa mama, ”
Duk da mama itama najin zafinn rabuwar ta da d’iyarta tadaure ta shiga tafarayi mata fad’a.”
Sai alokacin *hanna* tasamu bakin yiin kuka tajuya takalli mama tace,”
Hava mama kumin dasauk’i mana tafad’a tana wani matsanancin kuka,”
Hava mama tafiya fa zanyi na barku Amma bazaku barnii naji da d’aya ba? ”
Mama yazanyi nashiga uku tafad’a tanamai fashewa da kuka.”
Nan da nan idanuwan mama itama yaciko sosai, tausayin y’ar tata yayi bala’iin kamata,” Tashi tayi da sauri tafice daga d’akin dan idan bahqka ba zuciyarta na iya tsinkewa tafashe da kuka.”
Mama bata wuce ko ina ba sai dak’in ta tana zuwa ta zube tana sauke ajiyar zuciya, ”
Ganin haka yasa umma matsowa kusa da ita tana tamvayar maiyafaru duk da tasan cewa yau Mama sai ahankali rabuwa da d’iya yanada matuk’ar ciwo.”
Matsowa tayi kusa da ita ta dafa ta. ”
Sannan tace hava aisha yanzu idan ke baki dauree ba tayaya kike tunanin yarinyar zata daure?”
Nasan da ciwo Amma hakuri zakiyi bayau fa kika fara aurar da d’iya ba dan haka kiyi hakuri ko itama yarinyar zata samu ta kwantar da hankalinta.”
Girgiza Kai Mama tayi Sannan tace kayyah yaya wallhy wannnan ba irin way’ancan bane kada ki manta, ”
Auren hajja nayi tunani Akwai wata agabana sannan auren hindu shima ta barmin *hanna* yaya kike tunani zanjii yanzu idan aka d’aukemin ita?.”
Banida wani mai taimakamin kinsan kulawar y’ay’a maza ba kamar na y’ay’a mata ba.”
Goge kwallar data zubo mata tayi Sannan tace yaya kije ki rarrasheta dan tak’iyin wanka,”
Jikin umma ne yayi sanyi liqis Sannan ta tashi ta nufii d’akin Ammah bata reda tak’ara maganaba, ”
Azaune tasamu *hanna* tana sheshekar kuka,”
K’arasawa kusada ita tayi ta dafa ta, cikin muryar lallashi tace, ”
Hava *hanna* mekikeyi hakan?”
*Hanna* kiyita kuka sai kace wanda aka miki auren dole? ”
Hava *hanna* kada ki kasance marowaciya mana kada ki kasance wanda bata sowa mahaifinta rahamar ubangiji.”
Ke kanki shaida ne wannnan ingan taccen hadisi ne cewa duk mahaifinda ya aurar da y’ay’ansa samada biyu zuwa gidan mazajensu lpy,
Suka kare mutumcinsu Allah namasa albishir da gidan aljanna. ”
Kukan *hanna* ne yatsagaita Sannan umma tacigaba da cewa,”
*Hanna* kisowa mahaifinku wannnan rahma, ”
Kiyiwa mahaifinku biyayya dan samun wannnan rahama.”
Ahaka umma tayi ta conviceing nata ta tashi tashiga wanka, ”
Tana fitowa tayi umma ta bata mayuka kala kala ta shafa,”
Sannan ta bata turaruka samada kala shabiyar ta shafa, ”
Kuma duka masu sanyiin kamshi.”
Sanda tagama shafawa Sannan umma tace tazauna ayi mata makeup Amma firr tak’ii, ”
Haka umma takyaleta bata matsa ba, dan tasan ko anyii zuwa jimawa idan taga anzo tafiya da ita zata 6ata da kuka.”
Haka tad’uko mata wata bak’ar exclusive mai ratsin farii dinkin riga da zani anyi plain na zanin. ”
Yazauna ajikinta d’an kwalin kuma tad’aurashi kawai batareda tayi wani style ba tazauna kawai tana tunani sai alokacin umma takawo mata tea da masa akan tacii,”
Dkayr tad’an tsakula dan d’acin abincin takeji, ”
Tea d’inma dakyar ta kurba d’an kadan Sannan tace ta koshi.”
Su kuwa can suna *faria suite limited* suna reception, ”
K’arfe 12:30 zasu gama,”
Dazaran sungama za’atafii da amarya, ”
K’arfe 12:40 suka gama reception alokacin motocii suka nufii gidansu dan d’aukan amare,”
Alokacin aka kira *hanna* zuwa d’akin baba anan tasamu duk y’an uwanta aciki Nasiha kowa yake mata sosai daga wannnan yagama wannnan yake kar6a, ”
Itakuwa Mama takasa cewa komai duk jkinta yayi sanyi sosai.”
Hawayene yake ambaliya afuskarta,”
Tanajin k’aran isowan motocii tayi saurin rarrrafawa gaban baba tana kuka tana cewa baba kamin rai natuba nabi Allah kayafemun baba karka bari su tafii danii. ”
Wallhy baba idan wani abuu namaka nadaina baba bazan sake ba.”
Baba bansan baka sona ba wallhy dakana sona bazaka bari su tafii danii ba,”
Ganin baba ya sunkuyar da kansa yasa ta rarrafa wajen abba tariqo kafarsa tana kuka abba kumin rai natuba nabii Allah nabiku abba kutaimakenii. ”
Wani irin tausayin ta cikin matan kuwa d’ai-d’ai wayanda basu fara hawaye ba.”
Ganin abba bai kulata ba yasa ta rarrafa gaban anty maamn amal, ”
Tana kuka tana anty dan Allah kiyafemun, kiyi wa su abba magana.”
Anty maman amal ce ta rungumota tana cewa baki min komaiba kanwata, ”
Wallhy ban kutace kiba,”
Ba kawai inaso ki fahimcii Abinda yakamata kiyi ne.”
Amma kiyi hakuri *hanna* gata ake maki ba wani abun ba. ”
Aure gatane agareki, aure shine martabarkii.”
Kiyi hakuri Ahaka matanda sukazo dauk’anta, sukayi sallama, ”
Tana jinsu k’arfin kukan ta ya k’aru,”
Ahaka suka shigo aka gama duk wani abuu daza’ayii, ”
Aka rufa mata abaya aka nufe waje da ita.”

To be countinued

Ur’s
*z33yyb3rw3r*

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by

© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply