Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 57


Bibiyata Akeyi 57
Viral

Page 57

* A dai-dai wannan lokacii *hanna* kuka takeyi kamar ranta zai fita, ”
Kuka takeyi kamar wanda akace har abada bazata zo gidanba.”
Kuka takeyi tamkar wanda akace mata mahaifiyarta ta rasu. ”
Fulani ce riqe da ita d’ayan gefen kuma umma,”
Sai baki umma ke bata, ”
Alokacin aka shigar da ita wata mota k’irar *marcedeze benz* E350,
Yayinda duk sauran motocin corolla s ne wanda *hanna* kad’ai zata shigane ya banbanta,”
Haka *hanna* tanajii tana ganii aka turata cikin mota aikuwa saleem na gefen ta shima idanuwansa taff hawaye caff ta cafke hannunsa bbu yadda ba’ayi tasakeshiba amma fir tak’i duk da mabiyi da mabiyi bbu shiri amma akwai soyayya a cikin zuciyya ganin Haka yasa amma tace yashiga gaba,”
Yana shiga sannan umma ta shiga d’ayan gefen fulanii ta shiga d’aya, sukasa *hanna* atsakiya suka d’auki hanya.”
Amota Sai lallashin ta umma keyi, Fulani tace rabu da ita tayi abunta ai girman kenan, ”
Yanzu idan batayiba Sai ace tayi rashin kunya,”
Tafiyar mintii 25minute ce tasadasu da airport.”
Dan acikinsu akwai wanda zasu tafii Amota amma Sai sun raka amarya airport.”
Sabilida anason isan amrya ta isa da wuri akwai abubuwan da za’afara shiryawa kafin diner kuma anaso tahuta, ”
Ga kuma Fulani tsufa yafara kamata bazata iya tafiya mota da nisa ba.”
Ahaka suka futa *hanna* da k’awayrta da kuma sauran y’an uwa najiki suka nufii jurgin, ”
Sukuma sauran suka nufii hanya,”
Suna sauka motocii aka shurya na zuwa tar6ansu da iyalan gidan mai martaba Suna juransu, ”
Sosai aka musu tar6an karramawa gashi duk airport d’in da algaita kawai yacika ko ina,”
Harda kilishi wajan taryan amarya, ”
Sai murna takeyi tana rungumeta kamar da gaske da kuma y’an uwan ummii, suma sunyi murnar ganinta,”
Kowa Sai hugging d’inta sukeyi. ”
Alokacin *hanna* harta bar kuka ajiyan zuciya kawai take sakewa.”
Ahaka aka d’ugunzuma zuwa fada, umma ce ta rad’a mata akan tasauka da k’afar dama hakan kuwa akayi.”
Sanda aka kaita duk wani shashi na gidan ta gaida Kowa sannan aka nufii shashin da MG ke ciki Yanzu tazauna na d’ayan gefen upstair ashi zasu zasu zauna.”
Sun mace wajan kallon shashin wasu kanma sunyi zaton nanne wajan zqmanta. ”
Duk wanda yashiga wajan saiya yabawa wanda ke zaune awajan gurin tsafta Dan komai farine har kyalli sukeyi.”
Labba ne tabud’e d’akin da MG ke kwana tace *hanna* tashiga d’akin shiga tayi itada hafsat hameeda da amira, ”
Sauran kuma sauran d’akunan aka bud’e musu.”
Wani irin kamshi shashi yakeyi, ”
Barin d’akinda su *hanna*
Kam ba’a magana,” kamshin har wani fusgarsu yakeyi. ”
*Hanna* ta shiga tayi wanka tasa doguwar riga kawai ta kwanta akan gado tana tunanin gida.”
Kamshin pillow d’inne yasata lumshe ido daganan bacci yad’auketa.”
Sai kusan k’arfe hud’u wanda suke mota suka isoh.”
Shashin da *hanna* zata zauna sukaje suka ganii sunhanallah iyayen *hanna* sunyi k’o’ari wajan tsara mata d’aki. ”
Ahaka suka futa Kowa Sai san barka yakeyi,”
Gidan abba suka wuce daganan zasu wuce diner. ”
Hanna bata farka ba Sai k’arfe biyar,”
Tatashi ta watsa ruwa taqara komawa ta kwanta itaba bacci takeyi tunanin abubuwa kawai takeyi. ”
Misalin 6:00.pm aka fara shirin zuwa diner Dan 8:00.pm za’afara,”
Kafin saven mai makeup sunzo, ”
Sa hanna sukayi tashiga tayi wanka sannan tayi drying jikinta,” LBV makeover suka fara tsantsarata.”
Zuwa 7:45 angana makeup, ”
Alokacin idan kaga *hanna* yadda kasan yar tsana tsabar kyau,”
Wata farin wedding gown *hanna* tasa k’asanta tun daga nesa yakejan k’asa. ”
V head aka d’aura mata sannan aka yafa mata farin stone net.” da farin hill asalin mai tsinin jikinsa stones ne yadda kasan diamond. ”
Sunhanallah kaso kaga *hanna* awannan shigar. ”
Yadda kasan princess piona.” Su hameeda kuwa da sauran frnd natta, ”
Wani pink d’in material mai tsadan gaske sukasa da farin head sannan kuma da farin takalmi hill.”
Kowacce ta riqe yanonon farin gyale ahanunnunta, ”
Gabaki d’aya k’awayenta Su 6 ne Sai abin yabada kala.”
8 dai-dai akace Su fito ana k’ofar shashin basu d’auki lokacii wajan fitowa ba dan sungama shiri.”
Hanna sukasa atsakiya zuwa waje Suna fita hasken solar ya dallare Su,”
Alokacin suka k’ara bada kala,”
Motocii suka ganii guda talatinn da d’aya cuss, ”
15 agaba 15 abaya Sai kuma 1 atsakiya fara soll ferarri mai bak’in tinted, Su kuma sauran duka bak’ake ne wulik hadda tinted gabaki d’ayansu iri d’aya ne rang rover,”
Direct farin ferarri d’in suka nufa, dan sunsan cewa ita ce ta amarya ko ba’a fad’a ba.”
Dai-dai motan sukaje sukaja suka tsaya, ”
Bud’e driver seat akayi captain ahmed ne yasha milk d’in shadda ne ajikinsa yayi kyau sosai,”
Yana zuwa yabud’e mata motar yayi alamu da hannunsa alamun ta shiga motar ya sunkaya kai alamu girmama wa. ”
Cikin takun isa wanda takalmin k’ofar tane yadameta yasata tafiyar wanda hakan yazama kamarna k’asaita.”
Shiga motar tayi yayinda MG ya lumshe idanuwa sakamakon Wani daddad’an kamshi daya ziyarceshi, ”
Itama hakanne awajanta kamshi ne mai sanyi ya ziyarceta irin kamshin datajii a wannan d’akin amma na Yanzu dabanne.”
Tana shiga c. Ahmad yarufe kofa koda tad’an juya gefe kawai ta tsincii MG na kallonta ko kiftawa bayayi. ”
Saurin d’auke kanta tayi dan ita idan aka barta Sai tace da aljani tayi gamo.”
Tarasa Wani irin kyau yakeda shi. ”
Kyawunshi har Wani fusgarta yakeyi Cikin ladabi da jin kunyarsa ta gaidashi bai amsaba saima kafeta da ido dayayi.”
Jin shiru yasata d’agowa ta kalleshi nanma caraff idanuwansu ya had’e, ”
Wasu irin abubuwa taganii Cikin kwayar idanuwansa.”
Yanzu ma farar shadda ce kall ajikinsa har tafii ta d’azu d’aukan ido, ”
Farin talami da hula Sai farin diamond links,”
Gaskiya MG maikyqune. ”
Sunkuayarda kanta tayi tana wasa da yatsunta aranta tana tunanin maiyasa MG yake sonta,”
Nafarko itaba kyawun Azo agani ba. ”
Ahaka tayi ta tunani har suka shirya aka tashi motar da sauran motocin.”
Ahaka suka isa bbu wanda yacewa d’an uwansa Wani abuu.”
Hafsat kuwa motar captain bilal tashiga Suna tafiya Suna soyewa dan yanzu abukam yayi nisa.”
Soyayyarsu sukeyi. ”
Amira kuma yaya jalal najiranta dan tun d’azu yake kiranta,”
Duk da cewa bai fad’a mata komai ba amma tafahimcii cewa Yana sonta kuma Itama tasan tana sonsa kawai jiransa take ya furta bazata 6ata lokacii ba zata amincee. ”
Tsayuwar motar da sukajii ya tabbatar musu da an iso wajan.”

To be continued

Ur’s
*z33yyb3rw3r*

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by

© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

Wannan shafii sadaukarwane ga masoyana *Asma’u A muhammad*
Inasonki sosai kamar yanda kike sona,”
Ina jin dad’in yanda kike bibiyar labarina,”

*Khadeeja* hak’ika ke masoyiyar kwarai ce inasonki ina alfaharii dake, ”
Kisani ko acikin masoyana ke ta daban ce.”
Asma’u n Khadeeja gaskiya ina sonku irin sosai d’innan.”
Karku damu ana mugun tare.”
*I heart ❤ u girls.”*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply