Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 63


Bibiyata Akeyi 63
Viral

Page 63

*
Zagayo da ita yayi zuwa gabansa, sannan yazaunar da ita akan kujerar da yake zaune,”
Lallen hannunta yafara bii yana shafawa, bak’aramin kyau Lallen yamasa be. ”
Hannunta ya had’a duka biyun waje d’aya ya sumbata.”
Lumshe idanuwanta tayi ta bud’esu akan sa, ”
K’ura masa ido tayi dan wani irin kyau na musamman taga yamata,” kansa bbu hula gashinsa yasha gyara sosai. ” bak’ikirin Har sheki yakeyi,”
Batasan ta tsareshi da ido ba, kawai jitayi ya hure mata idanuwanta, ” kamshin vanilla flavour ne ke fita daga bakinsa,
Sunkuyarda kanta tayi tana murmushi,” gyara zamansa yayi zuwa kwanciya, d’aura kansa yayi, acinyanta ya Lumshe idanu Kamar maijin bacci.”
Ahankali yafara magana, sweety kitashi ga abincii adining, ” dannasan yanzu haka kinajin yunwa amma kike zaune.”
Kallon ikon Allah take masa Kamar bashine ya danneta yakuma hanata tashi ba, Kuma yake zancen abincii adining.”
Sweety ba magana nake miki bane? ” cikin tsiwa da rashin kunya tace, tsuntsu zanyi nqtashi idan baka d’agani ba?”
Tashi yayi kawai yatsaya yana kallonta,”
Ni kikeyiwa rashin kunya? ” ya tambaya, kawarda kanta gefe tayi, ciki- ciki yadda bazai jiba tace eh kaid’in,”
Ai kuwa karaf a kunnenta, ”
Fisgota yayi ta fad’o jikinsa,”
Bata ankaraba saiji tayi yafara kissing d’inta, da zafi-zafi Wanda kana kallo zakasan tsantsar mugunta yake Mata,”
Iya k’ok’arii tayi ta kwace amma takasa, ”
Kwalla ne tafara zuba afuskarta, dan ita kad’ai tasan tsanatsan azabar da takeji.”
Sanda yagaji dan kansa yasaketa, yakoma ya lafe akujera yana maida numfashi. ”
Itakuwa Kwalla ne kawai yake, kwarara, dan wani irin zogii da rad’ad’ii lips d’inta ke Mata,”.
Sanda yadawo normal yajuya ya kalleta yace tashi muje kici abinci,”
Babu musu tamiqe dan batasan mai zai sake aikatawaba, idan tasake masa musu.”
Zuwa tayi ta bud’e wermer’s d’in tafara saving d’inshi,” yana kallo yanda tacika plate da abincii kallonta kawai yakeyi baice mata komai ba, ”
Tea tahad’a masa sannan ta juya da niyyar zuba nata,” Kamo hannunta gamm yayi yace, ”
Wa kike tunanin zaicii wannan abincin?”
Kai tafad’a a dan tsorace, kallonta yakeyi Kamar mai nazarin wani Abu.”
Zaunarda ita yayi agefensa yace, zauna kici abincii danke aka kawo, ”
Kin ga ni ban iya cii ba.”
Kallon mamaki tamasa Wai bai iyacin abincii ba, ”
Dariya ne ta kufce mata aikuwa tashiga yinta bbu kakkautawa,”
Shikuma yatsaya kallonta, she’s unique yafad’a afili, ”
Murmushi yayi yace nabaki mamaki koh.” tace eh, ”
Amma bani kigani ko zancii,”
Ebowa tayi a spoon takai bakinsa, kawarda Kai yafayi Kamar Angela ta koshi da abincii, ”
Daidaitar bakinsa tayi ta tura masa.”
Sanda sukayi haka sau uku sannan ya cigaba da karban abincinsa yanacii, Sanda yajishi full, ya lakato kumatunta yace, lallai bakida wayo yanzu da ace nace kibani ne bazaki bani ta dad’in rai ba,”
Turo baki tayi tace wally nima tunda hakane saika ramamin, saika bani,”
Aikuwa yazauna yabata Sanda tak’oshi sosai tukunna, ”
Tashi duka sukayi da plate d’aya da cup d’aya da Kuma spoon d’aya ahannunta ta nufii kitchen,”
Binta da kallo yayi yanajin Sonta naratsa duk wani gabbai na jikin sa.”
Tana shiga tatsaya Kallon kitchen d’in, gabaki d’aya yatafii da ita, ”
Ganin ta dad’e ne yasa yabi bayanta,”
Ganinta yayi Sai bud’e ko”inq takeyi,”
Dariya qbun yqbashi yace Kamar ba itane ta cikaawa mutane kunne da kuka ba, amma yanzu tazaqe tana Kallon kayan.”
Batace komai ba, yak’ara cewa duk kinsa ancika mana gida da pink colour’s, Kamar yanda kasa aka cika mana da white ba, tabashi amsa,”
Fita yayi tabi bayansa, tana cewa Fita zakayi, eh yace atakaice, ”
Marairaice murya tayi tace dan Allah inbiyoka muje mu gaida su ummii,”
Wani irin dad’ii ne yaratsashi Ganin yanda tanuna muhimmancin iyayensa, ”
D’auko mayafii yace kawai,”
Up stairs tayi da gudu, ta bud’e wadrope ta D’auko katon hijab da tayi sallah dashi, ”
Har k’asa hijabin, tun tana saukowa yak’ura mata ido bak’amin kyau hijab d’in yamata ba,” gashi light blue kalan kayansa, ”
Sanda tazo kusa dashi kawai tadubi hijab d’inta tadubi kayansa, riqe baki tayi,” Dariya yayi ya girgiza Kai, ”
Juyawa tayi tace barina canja hijab,”
Riqota yayi yace muje, haka dole yajata, ”
Shashin mai martaba suka fara Zuwa, dan Zuwa 9:00.am zai Fita fadaa.”
Baijira iso ba taga Kai tsaya ya shige, dan dama shi ba’amasa iso baiso,”
Da sallama suka shiga mai martaba na zaune akujera, yaji dad’in ganinsu sosai addu’a yaringa musu da nasiha.”
Sai suka shiga Shashin kilishi daganan suka shiga na ummii, ”
Ummii Sai murnar ganinsu takeyi labba kuwa tana baccin gajiya.”
Tashi yayi zai Fita ummii tace a’a jira matarka, ”
Sosa Kai yayi yace ummii su Shahid ne zasu wuce inaso na rakasu.”
Murmushi ummii tayi tace ai itama yakamata taje rakasu, dan ta dalilinta sukazo,”
Kuma nasan yanzu haka basu gana da iyalansu ba, Kuma yakamata ta gansu,”
Ta6ata ummii tayi tace tashi kuje Allah yamuku albarka, da amin ta amsa sannan tafice, ”
Ganin yanda take tafiya yasashi rage saurii, ahankali yanda sojojin dake bayansu da Wanda ke gabansu bazasu jiba tace waikai ko acikin gidanma da sojoji kake yawo?”
Shima tambayanta yayi Wai bakisan Sunana bane?”
Daureta yayi bata k’ara cewa komai ba, ”
Wani dan k’aramin flate suka Isa,”
Da sallma yashiga yasamu sun Gama Shiri suna jiransa ne,”
Gaidasu *hanna* tayi suka amsa duka suna tsokanarta, wajen matan ta nufa taje suka gaisa, ”
Matan duk da yaransu kabilarsu da Kuma k’asarsu baizo d’qya ba Amma ta fahimcii sunada Sabo, dan d’an zamnsu Har suna ta hira sosai.”
Kar6ar yarinyar matar Shahid tayi, batafii 7month ba wasa takeyiwa yarinyar, matar Shahid tace na fahimcii kinason Yara Allah ybaki masu albarka, akunyace ta amsa ta amin. ”
Tamakar kanwarsu suka d’auketa suka runga bata shawarwarii,”
Fita rakasu sukayi saida jirginsu yatshi sannan, suka d’auko hanyar dawowa,”
Ganin *hanna* tayi shiru yasa yacewa driver yasanar da sauran idan sun samii wajan da ake siyarda chocolate su tsaya, ”
*Hanna* tajishi Amma taba kulaba, Hakan dazaiyi bashi zaisa ta manta alkawarin da jiya yamata na kaitq taga umma ba.”
Sanda akazo daidai wajen suka tsaya,”
Bud’ewa tayi zata Fita, yace Ina zakije?”
Ai basusan irin chocolate d’in da nakesoba, ”
Sai aka fad’a miki make zansayawa?”
Idan ba niba waye?” tafad’a had’eda Bud’ewa tafice,”
Shiga tayi ta za6o chocolate kala-kala wani soja yabiya kud’in suka nufo hanyar Fita, jitayi tabigi mutun gamm,”
Ledan hanjuntane tafad’ii, cewa yarinyar tayi Wanda zata d’an girmii *hanna* kamarda shekara biyu tace kiyi hakiri dan Allah dake *hanna* ne da laipy, ”
Kasa amsawa tayi tatsaya tana kallon *hanna* dan tabatrwa, tana tunano sunanda mahaifinta yagaya mata, *hanna* Kuma ta tsuguna dan d’aukan ledanta, Sanda tajira tad’ago tace mata,”
Dan Allah sunanki *hanna*? eh *hanna* ta amsa da rashin yarda afuskarta,”
Sannan tace wacece ke? ”
Zancenda akeyi a TV dake manne awajanne yasawa karima fashewa da matsanancin kuka,”
Alokacin *hanna* takai idonta wajan subhanallhi ta furta lokacin aka nuno gawar ministers of health, alullu6e data matarsa, ”
Gidansa yayi gobara, sannan Ana sanarda cikiyar iyalansa ba’asamu gawarsu ba, Kuma ba’agansu ba.”
Juyawa *hanna* tayi idanuwanta taff da Kwalla da niyyar ficewa, karimane ta cafko hannunta Wanda Hakan yasa d’aya daga cikin sojojin da sukazo da *hanna* ya nufota da niyyar dukanta, ”
Hanashi *hanna* tayi tace baiwar Allah sake mun hannu zantafii, muryarta Har na shid’ewa tace, kiyiwa girman Allah kitafii damu, inahh?”😳
*Hanna* tazaro ido,” gidanki dan Allah, dai-dai ta nutsuwarta *hanna* tayi tace intafii daku ku suwa? ”
Nuna mata TV karima tayi tace,”
Mune iyalansa da ake nema, wallahy ba gobara bane kashesu akayi, idan kika barii suka tafii damu muma zasu kashemu, jikin *hanna* ne yad’auki b’ari dasauri taja hannunta ta nufii Mota da ita, jaa tayi ta turje tace akwai kannena a can na b’oyesu, shiga *hanna* tace tayi itakuma ta tura wani soldier yaje ya ebosu,”
Suka shige motocin, duk abunda akeyi MG baya ganii hankalinsa nakan wayarda akamasa ake sanar dashi mutuwar minister,”
Yana ajiye wayar *hanna* ta bud’e tashiga, shigewa jikinsa tayi ta k’ankameshi tsamm,”
Jin yanda zuciyarta ke bugawa dasauri yanuna masa alamun ta tsorata. ”
Abinda yakawo ransa kawai shine taga gawarsu minister ne a TV,”
Lallashinta yakeyi yana buga bayanta ahaka suka d’auki hanyar komawa gida. ”

To be continued

Ur’s
*Z33iiyyb3rw3r*

*BIBIYATA AKEYI*

_Bismillahirrahmanirrahim_

Writing by
© _Zaynab Bawa_
( _z33iiyyb3rw3r_ )

*Allah subhanahu wata Ala yace,” duk mutumin dakafii k’auna dashi za’a tasheka ranar tashin k’iyama, * Ya rabb ka k’ara mana k’aunar manzonka acikin zuqatan mu, Ameen.”*

*Ka/ki kasance mai yawan tuna mutuwa, domin hakan zaisa ka/ki kasance cikin tsoron Allah.”*

*Kada ki/ka kasance mai k’askantarda mutane,” domin bakisan wataran waye mai taimakon kaba.”*

*Nasiha ce*

================

_Wannan shafii sadaukarwane ga duk wani masoyin *BIBIYATA AKEYI* inasonku ina alfaharii daku, dabazarku nake taka rawa_💃

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply