Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 65


Bibiyata Akeyi 65
Viral

Page 65

*
Saida taga hankalinsu ya d’an kwanta sannan ta nufii nata shashin, sai 5 hameeda tazota sunyi hira sosai, hameeda sai tsokanar *hanna* takeyi, ganin *hanna* tak’i kulata yasata tunanin MG ya kashe bakinne, Itakuwa *hanna* tausayin ay’annan bayin Allah ne yacika ta,”
Dariya hameeda ta kyalkyale tace Wai, su *hanna* anjii maza baki yayi shiru, aini band’auka akwai abunda zai kashe bakinnan ba,”
Tsaki *hanna* taja tace da’allah malama ni kindameni, idan bazakiyi shiruba Allah saina bar miki falon,” Dariya hameeda ta gimtse tace,” yi hakurii bani nakar Zoman ba rataya akabanii.”
Tsaki *hanna* tak’araja sannan ta juya mata baya. ”
Duk wata zolayqrta da hameeda takeyi bata kulata ba, dan tasan ba Hakan bane.”
Kiran sqllar magrib ne yasa hameeda tashi da niyyar tafiya, ruk’ota *hanna* tayi tace hava Sis, gaskiya bazakitafii yanzuba, kibari yadawo sai mutafii tare,”
Bud’e baki hameeda tayi tace, kina amaryar zaki fitafita?.”
Murgud’a baki *hanna* tayi tace to sai me? ”
D’azuma munfita, Allah yashiryeki hameeda tace sannan tace nifa tafiya zanyii,”
Sama *hanna* tahaura t ebo mata turaruka kayan kwalliya, da abubuwa kala-kala.”
Har bakin k’ofa tarakota, tana shirin fita hameeda tace kinga ki koma baki tambayi mijinki ba.”
Hararanta *hanna* tayi kawai, tad’an rakata tace beb samun abun hawafa zaimiki wuya a, Allah kinga dare yayi.”
Suna tsaye saiga captain Ahmad yazo dasauri zaije masallaci,”
Ganin *hanna* atsaye yasashi nufan wajan, tmbyanta yayi mai sukeyi, nan tashaida masa cewa hameeda ce zata tafii, ”
Kollon hameeda yayi yad’an basar, yana gyara hannun rigarsa yace,” tajira nayi sallah nakaita. ”
Yana fad’in haka ya juya yqtafii.” . Gidan suka koma Ana idarda sallah, yazo yayiwa *hanna* Magana tarakatq Har gaban mootar, sannan suka tafii tanajin kewar y’ar uwartata,”
Bata dad’e da tafiya ba labba tashigo,, da harara *hanna* tabita tace, ” wato akawoni gidanku a ajiyenii, Amma ko leqe, dama bukatarku tabiya nashigo ko?”
Kama kinnuwanta tayi tace afuwan, wallhy tun 12 nakeso nashigo ummii tahanani Wai ba’a Zuwa gidan amare,”
Wallhy bbu yanda banyiba tahanani yanzu ma sulalewa nayi bata sanii ba.”
Dariya *hanna* tayi tace dan Allah kaji ummii menene agidanmun da ba za’a zoba? ”
Uhmmm kawai labba tace dan batasaon taja maganar.”
Hira sukayi sosai *hanna* tajii dad’iin zuwanta sosai, ”
MG nafita daga masallaci shashin ummii yawuce, zaunawa yayi akusa da ita bayan ya gaisheta ta amsa.”
Cikin sakin fuska tana tambayarsa ya *hanna* sosa kayi yayi sannan yace ummii tun kafin la’asar nafita sai yanzu zan koma, fad’a ummii tabishi dashi sosai tana cewa yad’auko yar mutane zai tafii yabarta ita kad’ai,”
Hak’uri yabata sannan yasanar da ita rasuwar minister dakuma tafiyar data taso jibi,”
Addu’a tamasa Amma Har cikin ranta bataso tafiyar ba.”
Amma dai zaka tafii da ita ko?”
D’ago kansa yayi dakekan cinyarta, yace ummii zantafii da ita bansan lokacin da tafiyar zata d’auka ba.”
Addu’a ummii tamusu sannan tarinqa masa nasiha akan yarigeta da amana. ”
D’aurawa tayi da cewa nasan kana sonta so mai tsanani Amma hakan bashi zaisa nadaina maka nasihar riqeta da amana ba.”
Nasan cewa zuciya batada k’ashi, Kuma dole wataran duk dad’ii akan samuu sa6ani, k’arqmar yarinya ce, dole saikayi hakurii harda irin furucinta, sannan abuu na biyu, kaji tsoron Allah kasan yana ganinka, kada ka zalumcii yarinyar mutane.”
Nasiha sosai ummii tamasa mai ratsa jiki, ” Sannan tace yatashi yatafii yabarta ita kadai.”
Tashi yayi yafita,”
Baiwuce gidaba sannin cewa tana tare dasu karima, yasa yawuce shaidawa mai martaba.”
Tashi labba tayi tace kada ummii tanemeta tamata sallama tafita,”
Tashi tayi ta nufii shashin su karima, sanda ta tabbatar ta basu komai dazasu buk’ata sannan tajuya zata tafii, muryar karima ne takatseta, mungode Allah yasaka muku da mafificin alkhairinsa, murmushi kawai hanna tayi afili acikin ranta Kuma tace ameen, Juyawa tayi ta futa.”
Nasu shahsin tashiga, kawai ganin mutum tayi harta tsorata, sai zuciyarta ta hasko mata taga fuskan awajen diner d’insu, da fara’a tqk’arasa tana mata sannu da zuwa, daqyar ta amsa, gaisheta *hanna* tayi nan ma intisar kamar mai ciwon baki tace lpy.”
Ganin haka dake *hanna* ita kanta miskilar kantane, yasa ta ebeta ta watsar.”
Sunfii 10 minute bbu Wanda yacewa wani k’ala *hanna* na danne-danne awayrta, Itakuwa tad’aura d’aya kan d’aya taunar chwengum kawai takeyi.”
K’as K’as ne ya ishi *hanna* yasa tad’anja tsaki, d’agowa intisar tayi tace, owh srry baki sanni bako, ni cousine d’in sace, owh namanta Kuma budurwarsa, gaban *hanna* ne yayi masifar fad’uwa, lokacii d’ aya qirjinta yafara bugun taratara, har wani dushi-dushi take kallo,”
Srry baikamata kisani yanzu ba, Amma gani nayi bbu yanda na iya yakamta ace kinsan wata na shigowa kada ki bararraje,”
Kinsan fa duk nisan jifa k’asa zai dawo,”
Sannan kada kiyi tunani ko wasa nake miki, ki rubuta ki ajiye Har indai inadarai, ya yareema kamar na aureshi angama.”
Ta bud’e baki zata k’arayin magana, sqiga sallamar MG, kawarda kai *hanna* tayi azuciyar tana cewa munafuki azzalumii kawai, saurin tuba tayi tana agtasfirulla tunowa da tayi cewa, ma mijinta take fad’awa way’annan kalamai koda azuciyarsane.”
Kallon *hanna* yayi yaga yanda ta kawarda kai kamar batajii shigowarsa b, Kuma yanada tabbacin tasan shigowarsa, aransane yace kowa yata6omin yar fitinar tawa, ko rshin dawowata da wurii ne yasa,”
Zuwa dabb da ita yayi sannan yace, sweety wayo ta6ominke?”
Yitayi kamar batajishi ba danko Juyawa batayiba.” Muryar intisar ce takatseshi, na cewa sannu da Zuwa ya yareema,
Juyawa yayi ya kalleta, wata irin kunyace takamashi matarsa takasa yi masa sannu Amma wata tamasa, murmushi yayi yace yawwa habeebty yaushe kika shigo?”
Gaban *hanna* ne yayi masifar fad’uwa jinda sunan daya karata wato ya tabbata cewa, ita budurwarshi ce.”
Wani irin zafii zuciyarta tafarayi mata,”
Kwallah yacika idanuwanta taff,”
Wannan wani irin ciin fuska ne agabanta yana kiran wata habeebty, lallai dama abunda take gudu kenan tasan cewa MG ba tsaran ta bane, dole zai nemi kyakkyawa da ajee kamarsa, ”
Shikuwa MG anasa wajen habeebty daya ambata al’adansu ne tun suna yara aka taso dasu da fad’in wannan kalmar ma y’an uwansu,”
Dan kowa yatashi dason kowa acikin zuciyarsa.”
Kok’ad’an dayasan wannan kalma zata k’ona rana *hanna* dabai fad’a ba.”
Cikin kissaa da kisisina intisar tace habeeby dear inkawo maka ruwane? ”
Kallon *hanna* yayi Wanda kanta ke gefe ganin ba tasan da halittarsa awajan ba sai jikinsa yayi sanyii sosai.”
K’ara cewa tayi nagaa amaryar tamu najiin kunya ne.”
Shiru yayi sannan yace ok tom, Danshi MG arayiwarsa bai iya baonsa mutumba, ”
Tashi tayi tafii hanyar falon data hango frigde aciki tanayi tana karairaya.”
Shikuwa Wanda takeyi dominsa baima saniva dan hankalinsa nakan sweetynsa, tashi yayi yazo wajanta, yana tambayarta maiyafaru Amma firr tak’ii magana, bayanda beyiba hankalinsa ne yatashi, baisandai menene ba Amma ya lura kamar Zaman intisar ne ya6ata mata rai, idankuwa hakanne mai take nufii kenan?” batason yan uwansa kome? ”
Dawowa tayi da robar fayrouz ahannun ta dakuma na swan, tana Zuwa ta ajiye.”
Kallonsu ahaka ya sosa mata rai amma tadake tace ya habeeby dear gashi nakawo maka, tashi yayi da toh, ya isa wajan, intisar hadda kissaa ma Amma asali tafii ki ransa da yaa yareema,ganin yanzu tanayi baya gwaleta ne yasata zak’ewa.”
Fayrouz ta Zuba masa acup yak’arba yana Sha, nanne Kuma hakurin *hanna* yak’are ganin cewa dazasucii abinciin rana tad’auko masa fayrouz yace ta canja Amma yanzu ya k’arba, lallai yanzu tayarda namiji dakalin majina ne ka haushi ka sule,”
Shikuwa MG ganin ita matarshine yanadakyau tasan abunda yakeso da Wanda bayaso yasa yace ta canja Itakuwa intisar da saninta da rashin sa bbu amfanii.”
Tashii tayi da gudu tayi sama tana Zuwa ta kwanta akan gado tacii gaba da kuka.”
Shikuwa MG yayi niyyar binta amma intisar ta tsareshi da sururtu ba ita tasakeshiba sai 10, a lokacin *hanna* tayi kuka Har k’arfinta yak’are tayi samada 2hour’s tana kuka.”
Banda nishi da ajiyar zuciya bbu abunda take iyawa.”
Bayan ya kulle k’ofa d’akinta yfara nufa, ayanayin daya ganta yai, bala’in birkitashi.”
Dasauri yak’arsa yad’agota yasata ajikinsa hannu biyu tasa tana dukansa tana tureshi, ”
Amma bai kyaleta ba, sanda ya manna ta dajikinsa yacii gaba da lallashi.”
Sai kusan 10 tukun tabar dukansa tafara ajiyan zuciya, ganin yak’ii saketa yasata dallara masa cizo ak’irjii, runtse ido yayi yajii zafiin Amma zafin kukanda takeyi yafii k’onashi. ”
Ahaka Har bacci yqd’uketa, Jin saukar numfashinta ya tabatrs masa sannu hakan.”
Tunanii kala-kala yarunga yi arnsa, sannan shima ahaka bacci yad’aukeshi. ”

To be continued

Ur’s
*Z33iiyyb3rw3r*

*BIBIYATA AKEYI*

_Bismillahirrahmanirrahim_

Writing by
© _Zaynab Bawa_
( _z33iiyyb3rw3r_ )

_Like my page on Facebook :::Zaynab BAWA novels_

Followed me on instagram ::::mhiz_z33iiyyb3rw3r

Ka/ki zamo mai yawan karanta, “`Allahumma ajirni fi musibati, wa’aklifli khairan minha“` aduk lokacin ka/ki ke cikin wata musiba.”

Ka/ki kasance mai karanta “`Allahumma la sahla illa ma ja’altahu sahla, wa’anta taji’alul amra iza shi’itah sahla“` aduk lokacinda wani abuu yashige maki/ka duhu, kukoma kanajin wuyar aikata abun.”

*Ka/ki kasance mai karanta,* *“`Allahumma antassalamuwaminkal salam tabarak ta ya zul jalalu wal’ikram“` *aduk sallah bayan ka/kin idar.”*

*Shawara ce*

================

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply