Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 7


Bibiyata Akeyi 7
Viral

Page 7

*_

Saurin karban wayan yayi tareda karawa a kunnensa, yafara, magana duk da bawae jin maiyake cewa nayiba amma nafahinci yanayin sa yasauya dan damuwar da take fustarsa ta sassauta, duk da dama bawae yakasance mutum mai fara’a bane amma akan iya gane lokacin dayake cikin bacin rai,

Sauke wayan yayi daga kunnensa tare da sauke wata nauyayyar ajiyan *zuciya*
Bawae dan yagama yadda da abinda Captain bala yace bane, amma hankalinsa yadan kwanta, domin yasamu sassauci daga yanda zuciyar sa ke bugawa,

Mikewa yayi akujerar dayake Zaune, ya lumshe idanuwansa, abubuwa kala kala yake sakawa acikin *zuciyarsa*

================
Bata isah gida ba sai karfe biyar na yamma, tura dan karamin kofar dake jikin gate din gidansu tayi tashiga da sallama duk da tasan bakowane awajan dazai amsaba amma yanada kyau shiga gida da sallama,

Cikin gidan tawuce kaitsaye, tasamu ammah zaune tana yanke, farcen kafanta, sannu da gida ammah tafada koda batasa ran amsawaba, amma dabi’ar tane koh bazata amsaba saita gaishe ta,

Idontane yakai kan kayan dake jikinta, ke zonan tayi saurin kwala mata kira, yitayi kamar batajiba dan idan zaka shekara kana ce mata ke bazata amsaba,

Sanin halinta ne yasa tayi saurin cewa *hanna* badake nakeyiba juyowa tayi au banji lokacin bane, Wani kululun bakin ciki ne yatokareta, aranta tanacewa yarinya batasan komai ba sai rashin kunya, afili kuma tace A’inah kikasamu wannan kayan jikinki ?????

Kallon gefe da gefenta tayi sannan tadago tace wanne???

ungo naki wannan najikinki mana to aini banga wani kaya ajikina ba nawane, oh namanta ashe ance idan mutum yafara tsufa yanada saurin mantuwa,

Tana fadin haka tayi saurin juyawa, dantasan abinda ta aikata don kokadan ammah batasan tsufa, Saurin shigewa sashin mama tayi tabar Ammah nata surfa ashar,

Shigewa tayi tana dariya afalo tatararda mama Zaune tana kollon wisal hausa, kewani irin shashancine haka zaki shigowa mutane daki babu sallama kamar wata tababbiya, turo vakinta tayi mana nayi sallama fa bakiji bane, kyaji dashi dai tafada tareda juyawa taci gaba da kallonta,

Wucewa tajeyi mama tayi saurin tareda keh A’inah kikasamu wannan kayan kuma, mama gidan anty na’ilah fah naje, shine kika samata kaya kaimama me shiga tsakanin yaya da kanwa fa zaiji kunya.

Uhm kawae tace tacigaba da kallanta, Bayan mangaruba kamar yadda suka saba kowa nacikin gida yana Zaune, antadi saikuma yan habaice habaicen daba’a rasasu acikin gidan, itade hankalinta gabaki daya baya wajensu yanakan phone dinta,

Jira takeyi kawae kiran najeeb yashigo, amma shiru saida
Har tayi shirin kwanciya tagama cire rai da kiransa, dan harta kwanta bacci, taji wayanta yafara ringing, koda taga number ne tarigada tasan waye yasa batayi Gigin daukaba sanda ta katse,

Tajira koda’a sake kira amma shiru harataji haushin kanta naja masa aji datatsaya yi gashi yanxu yakikira, Wani irin haushin kanta takeji nakin daukan wayan

Kusan 30 minute yakara kafin yasake kiranta, mai halidai bayafasa halinsa dan sai wayanna dab da tsinkewa kafin tadaga, shiru tayi takiyin magana, sallama yamata daga nasa wajan, amsawa tayi adakile,

Kingane waye A’a tabashi amsa shiru yayi danransa yadan sosu datace masa A’a kuma yasan bawai bata gane waye bane saitsan tsan rainin wayo,

Shitunda yakema bai taba kiran mace taki dauka ba saiyau, najeeb neh, oh yakake, lafiya ya mama da baba, kowa kalau, yayikyau amma meyasa kikace baki ganeba, hmm tace kawai tana masa magana cikeda rashin sabo,

Haka yayita jan ta dahira mai dadi hartadan sake dashi sai wajen 11:00 sukayi sallama dan bacci ne tab a idonta,

Sanda ya tabbatar da, yadasa mata wata irin soyayyarsa a zuciyarta kafin yabarta, bacci ne mai dadi yadauketa, cike da farin ciki da annashuwa,

Zaune take abakin wani ruwa awani hadadden beach gawasu tsuntsaye masu kyan gaske sunata zagaya wajan najeeb ne Zaune agefenta, inibi yadauka dake cikin wani faranti agaban Su cike yakeh kayan marmari,

Kana kallonsu kasan suna cikin wani irin yanayi na nishadi, Da farin ciki domin yadda fuskokinsu ke dauke da murmushi mai tsadan gaske,

Dauko inibin yayi yakaimata bakinta, lumshe idoh tayi hadeda bude bakinta, shirun dataji ne yasata bude idoh,

Sojojine zagaye da wajan da suke Zaune ga najeeb ahannun wani mutum wanda kana kallonsa daka tabbatar da balarabe ne sak

Yasawa najeeb bindiga akansa, magana yajuyo yanayi yana kallanta,
*Hanna* meyasa bayajin magana nahanaki meyasa kikeson sa rayuwar Su cikin halaka,meyasa kikeson saka zuciya na cikin kunci zankasheshi kuma zankashe duk wanda ya kusanceki da sunan so,

Ke tawace nikadai dan nafi kowa sanki, yana gama fadin haka ya sa kan bindigan akahon zuciyar najeeb sannan yadana kunamar bindigan wani irin raza nannan ihu tasake,,,,,,,,,,,,,

To be continue

Ur’s
Z33iiyyb3rw3r

BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writing by
Zaynab Bawa (z33iiyyb3rw3r)

_This page is dedicated to _you_ *_hajja_* *_ceh_*

Plx kuyi hakuri wannan page din bayawa

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply